← Book details Hamdah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 58 OF 62

Sashe 58

Hamdah Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Wani irin tsayuwa nayi ganin su Abba da Abbu Goggo Hauwa durkushe a gaban mutum an rufe shi da zani tun daga kansa har zuwa kafafun sa yana kwance kan taburma.
Goggo Hauwa sai sharɓe hawaye take tana ta kokarin danne kukan da yake ta kokarin kwace mata, su Abbu kuwa ɗan gajerun hawaye ne a karkashin idanunsu sai kai yatsa suke suna ta ɗan goge shi,kamar an zabure ni nakuma faɗin
"Inna Inna Inna wai kina ina ne Inna ni dai kizo mutafi kawai".
nafaÉ—a ina ta waiga gefe da gefe na,kuka Aunty Rafee'at ta sake da karfe ta rungume ni Aunty Jaleela ma ta taho ta rungume ne. ido nake bin ko wannensu da shi sai kuma na fizge jiki na na juyo gun su Ummi na ce
"Ummi Mamie Inna fa ko tatafi ne Ni dai zan bita mukoma".
hawaye Ummi ta share tamiko hannu tana kokarin ruko Ni da faÉ—i
"Zo ki zauna tukun".
baya nayi tare da ɓoye hannuna ta baya na.
tuni kukan da Mamie da Goggo Hauwa suke ta ɓoyewa yafito cikin muryar kuka Mamie take faɗin
"Innalillahi wa'inna'ilaihirraji'un² kudubi halin da HAMDAH take ciki wlh bata cikin hankalin ta,kidawo cikin hayya cikin ki HAMDAH!".
tafaÉ—a tana girgiza ni.
Ido kawai nabita da shi, Abbu ya mike yaruko hannuna yadube ni da kyau yace
"Zo ga Inna nan kiyi mata addu'a Inna ta rasu tariga mu gidan gaskiya".
shima ido kawai na zuba masa har ya jawo hannuna yakawo ni in da suke durkushe yayi kasa da hannuna ya durkusar da ni kamar yadda sukayi, sai kawai na zame kasan nayi zaman dirshem,
cikin karfin hali Abbu yakai hannunsa yaja zanin da aka lulluɓe mutum da naga suna durkushe a gabansa nan farin kyalle ya bai yana,
a hankali yakuma kai hannunsa yakun ce igiyar da aka ɗaure saman farin kyallen da shi kana yaja ƙyallen.
Wani irin bugawa kirjina yayi da mugun karfi har sai da nakai hannuna dai-dai kan kahon zuciya ta na dafe da karfe.
ganin fuskar Inna ya bayyana idanunta a rufe kamar mai yin bacci yayin da fuskar ta ke É—auke da murmushi kamar a kirata ta amsa.
da sauri na kai hannu nashiga girgizata ina faÉ—in
"Inna Inna kitashi".
sai kuma na waiga gun su Abbu da tuni hawaye suka shiga zarya kan fuskokinsu nace
"Abbu Abba meyasa Inna ta kwanta a kasa kuce mata ta tashi ta hau godo, shine aka lulluɓe ta aka rufa mata kanta Inna bata son tarika rufe kanta fa in zatayi bacci kar kurufa mata kanta kubar ta a buɗe kuce ta tashi tahau gado".
mai da kallo na nayi kanta nacigaba da girgiza ta
"Inna ba kince zamu tafi Dass idan aka sallame kiba to kitashi mutafi yanzu Inna nidai kitafi da Ni tsoro nake ji,kitashi mutafi Inna Inna kitashi".
nafaÉ—a da karfi ina jijjigata.
tuni É—akin yakaure da koke-koke.
Wasu maza su biyu ne suka shigo rike da makara suka sauke kusa da ita suka dubi Abbu sukace
"Alhj mutane suna ta jira a waje an kimsa ku a ke jira".
yagirgiza kai kana ya mika hannu yamai da likafanin ya rufe mata fuska yaÉ—au reshi kamar na É—azu kana yaja zanin yakuma rufe ta da shi.
kankame ta nayi da karfi ina faÉ—in
"Abbu ka buÉ—e ta Inna bata rufe fuskar ta in zatayi bacci".
mikewa tsaye Abbu yayi kana ya dubi Abba da kansa ke durkushe yace
"Shu'aibu kama mu sata a kan makarar".
binsu da idanuna da babu ko É—igon kwalla acikin sa nayi sai kuma na
Kife fuskata a jikin ta da karfi nace
"Abbu kusata a kan gado kada kusa ta akan makarar".
Ya SALEEM da shigowar sakenan yadube su yace
"Wai meye hakan kenan kun sata gaba kuna ta wani koke-koke amfanin me kukan zai mata in baza ku iya mata addu'a ba kuje waje dan Allah".
yafaÉ—a yana nuna musu hanya,yakuma cewa
"Kuje waje".
dukan su suka fita har dasu Mamie karaso wa in da nake kwance jikin Inna yayi yaruko kaÉ—ata yaÉ—a go ni kana yaruko hannuna su Abba suka É—agata suka sakata cikin makarar,yajan yo ni muka fito yakusa cikin jama'ar yashige dani cikin wani É—aki dake kusa da na Inna shima mutane ne dayawa cikin sa harda su maman Rabi da wasu Æ´an Dass anan ya zaunar dani kana yafita,lokacin su Abbu suka fito da Inna daga É—akin ta suka nufi waje shima yarufa musu baya....

Idanuna narika ware wa ina bin É—akin da nake cike da kallo maganar maman Rabi naji tana faÉ—in
"Sai hakuri HAMDAH Inna tazo kan ka ida iya rayuwar kenan Allah ya jikan ta yamata rahama halayen ta nagani yabita".
A sama naji maganar ta sai kuma kamar an zabure ni na mike da sauri nafice cikin É—akin nanufi kofar bita daga parlour,
cikin hanzari Mamie ta mike tana faÉ—in
"Tsaya HAMDAH ina zakije".
tuni nayi waje dai-dai lokacin a ka sallamar da sallar da aka mata da gudu nayi gun lokacin ake kokarin É—ago makarar sai na faÉ—a kanta na rirrike ta da karfi ina faÉ—in
"Ina zaku kai ta kar ku tafi da ita Inna ki tashi kar su tafi da ke".
É—agoni yayi cak a kanta kana ya juyo ni muna fuskantar juna,sai Abbu da Abba da wasu Æ´an'uwan Inna su biyu suka É—ago makarar suka nufi in da motar kai gawa da aka shigo dashi cikin get,da sauri na waiga sai nashi kokarin janye hannuna ina faÉ—in
"Ya SALEEM ka sake ni zasu tafi da ita, kace kar sutafi da ita karku tafi da ita Inna wayyo Inna wayyo Inna karki tafi kibar niii......"
wani irin luuuu idanuna sukayi...�
da sauri yataro ta tafaÉ—o jikinsa dai-dai lokacin su Mamie suka karaso in da suke ihu Aunty Rafee'at take tana faÉ—in
"Wayyo HAMDAH ki tashi".
tafaÉ—a tana jijjigata ajikin Ya SALEEM,Mamie da Ummi kuwa salati suka shiga yi,
cikin azama ya cicciɓe ta yayi hanyar part ɗin Mamie wan da yafi kusa da inda suke, direct bedroom ɗin ta yashiga da ita yashin fiɗata saman bed,
Suma suka rufa masa baya ban da Ummi da ke tsaye tana ambaton sunan Allah.

A can cikin bedroom É—in Mamie kuwa da sauri Mamie Aunty Rafee'at Aunty Jaleela da su Nusaiba da suka shigo da gudu yanzu duk suka nufi bakin gado in da yakwantar da ita yana tsaye a kanta yana kallon ta gaba É—aya babu numfashi a jikin ta,
da sauri Mamie ta iso tashiga girgiza ta tana kiran sunan ta,sai kuma ta juya taÉ—au gorar ruwa dake É—aure kan bedside tabuÉ—e ta yayya fa mata, nan ma ko gizau tana nan kamar É—azu,
jin karar motoci alamun an fara tafiya makabar ta, kallon su Aunty Rafee'at da suke ta rusar kuka yayi kana yace su fita dukan su dan tanan ne kawai zai sa Mamie taji karfin guiwar kulawa da ita yadda yakamata in suna nan suna wannan kuka to fa bazata iya taɓuka mata komai ba.
a gaba yasasu suka fita yakuma ce musu kar su kuskura ya dawo yasa mesu agun,nan yanufi gun motar sa yashiga yabi bayan sauran ragowar motoci suka É—au hanyar makabarta...

A can cikin É—akin Mamie kuwa,duk wani ruwan da take ta yayya fawa HAMDAH a banza dan ko gizau batayi ba tana kwance kamar gawa,cikin sananin tashin hankali tafito waje ta nufi side É—in Inna dan É—azu in ba idanunta bane suka gane mata ba dai-dai ba to É—azu taga wata mako ciyar su wata ma ai kaciyar asibiti.
tana shiga parlour'n kuwa ta hango ta da sauri ta isa ta ruko hannunta tare da faÉ—in
"Dan Allah Hajiya zo muje ki duba HAMDAH tana kwance babu numfashi tare da ita".
tayi maganar hankali tashe, matar ta mike suka fita da sauri suna shiga É—akin tacewa Mamie tabata ruwa,
tamiko mata wanda ta yayyafa mata É—azu tace
"Mai sanyi zaki bani".
da sauri Mamie ta isa in da fridge yake taciro ruwa mai sanyi tazo ta mika mata,takarɓa ta buɗe marfin ta tsiyaye ruwan a hannunta ta yayyafa mata daga fuskar ta zuwa kirjin ta tayi hakan har sau uku kana nan ma bata mosa ba.
sai ta mikawa Mamie gorar ruwan kana ta shiga É—an danna kirjin ta a hankali a hankali.
cikin tashin hankali ganin har lau babu wani alamar motsi
Mamie tace
"Hajiya kodai asibiti za'a kai ta abun yayi mata yawa gashi tana É—auke da jaririn ciki".
numfashi Hajiyar ta sauke tace
"To gaskiya kam in dai haka ne gara a hanzarta kai ta asibitin
dan gudun faruwar wata matsalar, amma dai bani ruwan nagani".
takuma karɓar ruwan tazuba da yawa a hannunta tawasa mata a fuska,
wani irin dogon numfashi taja, takuma wasa mata, nan ma takuma jan numfashi.
hamdala Mamie tashiga yi da godiya wa Hajiyar tace
"Ba komai amma dai kada a barta a gida a kaita asibiti a dubata da kyau".
Nan tayiwa Mamie sallama ta fita ta koma side É—in Inna.
Chapter 58 · 0% Book details