← Book details Hamdah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 61 OF 62

Sashe 61

Hamdah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A ɓangaren Na'ima
zaune take a cikin parlour'n ta yayin da Rufa'ila ke gefe tana ta mata hidima. nan wayar ta dake gefen ta ya kama ringing koda ta É—ago wayar taga aminiyar ta Raliya ce ke kiran nata da sauri ta É—aga kiran ta kara wayar a kunnen ta tare da faÉ—in
"Hello".
Daga cikin wayar Raliya tace
"Aminiya akai kyakkyawar albishir yanzu muka gama waya da malam na kan tudu yake cemin yadawo daga gurin ai kin da suka tafi".
da sauri Na'ima ta mike tana faÉ—in
"Ai kuwa wannan babban albishir ne kinci tukuicin yanzu kuwa zan je gurin sa wlh kar jiki yan da naji dama hakuri yana daf da karewa".
Raliya tace
"To muhaÉ—u a gurin sa dama nima akwai wani Alhaji'n da nake so yayi min ai ki a kansa yashigo hannu".
Na'ima tace
"Ai kuwa yanzu ma kuwa".
tafaÉ—a tare da kashe wayar tashige É—aki da sauri tazari makullin mota da mayafin ta tafita,tashiga motar ta ta É—au hanyar gidan bokan ta...

A kusan tare suka iso da aminiyar nata dan suna ta waya da junan su tun a hanya hakan yasa suka iso tare.
kamar koda yaushe suna fita acikin motocin su suka tuttuɓe takalmar su kana suka nufi bukkan malam na kan tudu.
suna zaune a gaban sa sun naÉ—e kafafun su kamar masu neman gafara shiko sai surkullen sa yake kana daga bisani ya É—ago ya dubesu yace
"Meke tafe daku yau nasan dai ai kin ku na wancan karo yaci".
Na'ima da tun É—azu taketa alla-alla bakon yaÉ—a go ya saurari bukatar su, ta gyara zama tace
"Boka akwai babbar matsala ai ki yaciwu da farko sai kuma gata da ciki daga baya narasa ta yan da akayi hakan ya faru, ta daɗa kanainaye shi bakaga yanda yake rawar kafa a kantaba,daga shi har iyayen sa kamar basu taɓa ganin ciki ba sai a kan ta,
boka nikam na kaÉ—e ka tai make ni kamar yadda kasaba tai mako na".
Wani irin dariya ya kece dashi kana yace
"Ai dama nasan za ayi haka dan nagani tun ranar".
da mamaki suke kallon sa dajin abun da yafaÉ—a gusar musu da mamakin su yayi da cigaba da faÉ—in
"Ai tun ranar da nayi bincike nagano tana da ciki to abun da yasa ban sanar muku ba naga hankalin ki a tashe ne kinaso ayi-ayi miki ai kin shiyasa,
tun wancan lokacin tana da shigan ciki sai dai karami ne sosai lokacin satin sa biyu ne kacal,
Sai nayi amfani da hikimar mu nayi miki ai kin,
muka É—aure cikin har sai ranar da kwai É—in da na baki yafashe kafin muka sake shi,in da koda asibitin duk duniyar nan za'aje lissafin daga kan wannan ranar da kwan yafashi zai nuna musu wa'adin shigar cikin acikin ta".
wani dariyar yakuma kecewa kana
yasoma zane-zanen kan kasa da bubbuga shi sannan yace
"Sai ku lissafa kwanakin da kwan yafashe shine watannin cikin sai dai akwai ɗaurin saki biyu in da babu wan da yasan dashi sai mu, mun so mu ɗaure cikin ne ƙwata-ƙwata in da bazai tashiba sai dai hakan bai samu ba dan aljani durkus ya kauce a lokacin".
shiru sukayi kowa da kalar tunanin ta can Raliya ta nisa tace
"Tabbas kuwa lokacin da Sakeenat ta faÉ—a min tana da cikin cikin wata É—aya ta cemin".
Na'ima kuwa wani numfashin ta sauke kana tace
"To yanzu malam wani tai mako za'ayi min?".
yace
"FaÉ—i me kike so ayi miki yanzu a aiwatar".
zaman ta ta gyara sosai kana tace
"A kasheta kawai dan nasan koda an zubar da cikin ma zata kuma yin wani tun da kullum yana like da ita, shine kawai samin kwanciyar hankali na".
tana faÉ—an haka wani irin bakin hayaki yafito fuuu daga cikin wani tukunyar kasa da ke gefe da bokon wani irin zabura sukayi dukan su sukayi baya.
da sauri bokan yace
"Maza janye wannan kudirin bama kisa yanzu munyi alkawari wa shugaba, sai dai duk abun da kike so a duniyar nan zaki samu ban da kisa".
yafaÉ—a da karfi yana zazzaro ido.
yana gama faÉ—an haka kuwa hayakin nan ya koma cikin tukunyar.
É—an matsoww sukayi jiki na rawa
suka haÉ—a baki wajen cewa
"A gafarce mu". cikin É—ar-É—ar Na'ima tace
"To Malama ni dai ayi min duk abu da ya dace".
hannunsa ya mika baya yaÉ—au wani kullin magani kana ya jefa shi cikin wannan tukunyar da ta fidda hayaki yanzu nan tukunyar ta fara fidda wani sauti kamar ruwa akan wuta yana tafasa,zuwa can yasa hannu yaciro kullin maganin ya mika wa Na'ima yace
"Mun girke shi mun kuma yi masa mugun kulle babu mai iya karya wannan sihirin in duniya ce kinsa mu, Je ki saka masa a abinci ko sha da zaran yaci shike nan duk abun da kike so kin samu".
da sauri ta mika hannu takarɓa tana zuba masa godiya kamar zata sa goshin ta a kasa,
sai dunkule maganin take a hannunta sai kuma tasaki wani shu'umin murmushi mai kunshe da ma'anoni iri-iri.
bayan Raliya ta gabatar da bukatar ta itama nan ya haÉ—a mata kalar nata lakanin kana suka cikeshi da kuÉ—i suka haye motocin su suka fice a cikin dajin in da kowa ta kama gaban ta Na'ima tayi gida Raliya ma tayi gidan su....
Tun da Na'ima ta dawo gida take tunanin ta in da zayi tazubawa SALEEM maganin nan acikin abin ci harya ci,dan yanzu rabon da yaci abincin ta harta mance,ko da É—in ma basosai yake ciba dan shi ba ma'abocin cin abinci da yawa bane yafi bukatar tea a koda yaushe kamar wan da yahaÉ—a jinsi da larabawa.
sai dai ta kudura wa ranta ko tawani irin hanya sai tabi wajen ganin ta zuba masa maganin yaci....

Tsaye nake gaban wardrobe fitowa ta daga wanka kenan ina kokarin ciro kayan da zan saka najiyo wayata dake kan mirror tana ringing,
a sannu na isa in da wayar yake na É—au wayar ganin kiran na kokarin yan kewa da sauri na É—aga na kai wayar kunnena tare da yin sallama.
daga cikin wayar ya amsa sallamar kana ya É—aura da faÉ—in
"A kawo min tea yau fa ba'a bani ba tun da safe".
To nace ina sau ke wayar.
Na'ima da yanzu shigo warta side ɗin shi tazo zata shiga cikin bedroom ɗin sa taji wayar da yake da sauri ta juya ta koma side ɗin ta,cikin hanzari ta haɗa tea taje ta ɗau ko kullen maganin da bokanta ya bata har jikinta na ɓari ta kunce kullin hannunta na rawa taɗebo garin maganin tazuba cikin tea ɗin ta garwaya da sauri tafito rike da cup ɗin tea ɗin ta nufi ɗakinsa...
sai da nasaka kaya kafin na wuce kitchen naje na haÉ—o masa tea É—in nanufi side É—in shi.
sallama nayi a bakin kofar bedroom É—in shi kana na tura kofar,
tsaye na ganta gaban shi tana mika masa cup,yayin da shiko system ne a gaban sa gaba É—aya ya mai da hankalin sa kan sa.
narke murya tayi
cike da kirsa take faÉ—in
"Barka da hutawa my SALEEM Bismillah".
tafaÉ—a tana daÉ—a mika masa cup É—in.
ganin haka sai naja na tsaya nan bakin kofa.
A hankali yaÉ—a go yaÉ—an kalleni sai ya mai da idanunsa kan abun da yake kana yace
"Cigaba da tsayuwar zakiyi har sai yayi sanyi?".
a hankali nasoma takowa na iso in da yake na mika masa cup ɗin, hannu ya miko zai karɓa ganin hannunsa bai iso ni ba kasan cewar Na'ima tana daf da shi sosai ne, sai na ɗago kafata zan kuma yin gaba sai naji nayi tuntuɓe da kafar mukum sai cup ɗin ya suɓuce a hannuna bai kai ga isa kasa ba nayi saurin taro shi akayi rashin sa'a ruwan tea ɗin yazube kasa har sai da ya fantsalu masa a jiki zuwa kan kafarsa.
ido na waro cike da fargaba,
dogon tsaki Na'ima taja tare da faÉ—in
"Ke makau niya ce jibi yadda kika ɓata min jiki".
tayi maganar tana yaguna fuska tare da zame jiki tayi gefe.
niko kasa nayi da kai na dan son ganin kafar da nayi tuntuɓen dashi.
É—agowa yayi tare da bin ta da wani irin kallo kana ya jinjina kai
baki na buɗe da zummar bashi hakuri ganin shima tea ɗin ya taɓa shi sai ya katse min nawa maganar da faɗin
"Je ki kawo min wani".
wani dogon tsakin takuma ja kana tayi waje a hankali nima nafita na nufi part É—ina da sauri dan guri yayi duhu duk da kuwa hasken wuta daya zagaye ko ina na gidan.
da sauri na haÉ—o wani tea É—in na kai masa koda na shigo bedroom É—in sa baya ciki sai motsin ruwa danaji cikin bathroom da ya shaidar min da yana ciki,aje masa nayi kan bedside najuya nafita da sauri dan so nake naje na kira Aunty Halima yau mukayi da ita zata dawo gashi har dare ban ganta ba gashi ina jin tsoro...

Tun fitar HAMDAH har dawowar ta akan idon Na'ima ne tana ganin fitar ta ta saki wani murmushi kana ta bayyano cikin parlour'n a file ta furta
"Wan da yariga ka bacci dole ya rigaka tashi".
takuma sakin wani murmushin jin daÉ—i da gaskata kanta da shirin da tsara yanzu kuma take ganin yiwuwar sa.
cikin sanɗa ta tura kofar har lokacin yana cikin bayin a hankali tarika ɗaga kafar ta har ta isa in da cup ɗin yake kana da sauri ta kunce kullin maganin ta ɓarbaɗa shi cikin tea ɗin ta ɗan garwaya da karamin cokalin da ke ciki kana ta juya cikin sanɗa tafita ta ja kofar a hankali ta rufe da sauri takoma side ɗin ta tana shiga cikin bedroom ɗin ta ta tuma tsalle tafaɗa kan bed cikin sannin murna da farin cikin yau burin ta zai cika na daɗa mallakar SALEEM har abada...
Chapter 61 · 0% Book details