← Book details Hamdah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 62

Sashe 47

Hamdah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ina nan kwan ce a in da ya barni yanayin fitar sa yada É—a sani jin tsoro,nayi ta zuba ido ko zai dawo amma shiru haka bacci ya É—auke Ni cikin zullumi,
washegari kasan cewar ina fashin sallah har a ka fita a masallaci ina kwance.
da misalin karfe 8 inanan kwance yashigo da sallama, ido na zuba masa yayi kyau cikin shiga na alfarma sai baza kamshi yake har yakaraso bakin gadon.
A hankali najanye blanket É—in da na rufe jikina na mike zaune
"Ina kwana Ya SALEEM".
bafaÉ—a ina duban sa, ida nunsa ya lumshe yakuma buÉ—e su kana ya miko min hannu yayi min alama da in zo.
a sannu nazamo daga kan gadon na mike tsaye,har lokacin bai sauke hannunsa ba bai kuma cire idanunsa daga kaina ba, ganin hakan sai
a hankali na miko hannuna zuwa kan nashi,sai ya rike hannuna tare da dun kule shi cikin nashi ya janyoni jikin sa ya rungume ni.
nan wayar ta fara kara a lamar shigowar kira,a sannu yaÉ—ago hannunsa da ke rike da wayar yayi picking na call É—in ya kai wayar kunnen sa,
É—an shiru yayi yana sauraron maganar da ake tacikin wayar,
zuwa can ya zare wayar batare da yace komai ba ya katse kiran,
a hankali ya É—an rankwafo da kansa tare da É—ago kai na dake cikin kirjin sa a sannu yakai bakin sa kan goshi na ya manna min lafiyayyen kiss kana ya É—aura idanunsa a kaina, a sannu yashiga motsa lips É—in sa
"Zanyi tafi yanzun nan jiya da daddare nasamu kira daga abuja".
sai yariko kafaÉ—u na yana cigaba da faÉ—in
"NaÉ—an makara tun É—azu ya kamata na tashi".
yafaÉ—a yana sakin kafaÉ—u na, a hankali na furta
"Allah ya tsare ya kiyaye hanya".
kai ya jinjina kana yace
"Babu rakiya?".
yafaÉ—a idanunsa a kaina,a sannu na isa in da hijabin sallah na yake na É—auka na zura kan rigar baccin da ke jikina,nazo in da yake sai yaruko hannuna muka nufi kofa,har muka isa parking space yana rike da hannuna,yabuÉ—e motar yashiga gidan baya batare da yasake hannuna ba,yana dai-dai ta zaman sa sai yaÉ—an janyoni na rankwafo da kaina cikin motar,
da hannu yayi min nuni da lips É—in sa tare da tsare ni da ido,
sarai na fahimci me yake nufi sai na juya ƙwayar idona nayi kamar ban fahimci abun da yake nufi ba,
hannuna da ke rike a hannunsa yaÉ—an matse kana ya É—an suke fuska,
a sannu na matso da kaina nacuno lips É—ina naÉ—an É—aurashi kan nashi,da sauri ya kai hannunsa ta bayan kai na yin hakan yasa bakin na ya daÉ—a mannuwa da nashi sosai, ida nuna na lumshi kana a hankali na kamo lips É—in sa naÉ—an tsotsa sai na sake,da sauri na janye kaina jin yana kokarin zuro harshen sa cikin bakina, ina É—ago kai na na hango Aunty Na'ima tana tahowa in da muke,
shiko kokarin daÉ—a janyo ni yake sai kuma yasaki hannuna ganin direba ya karaso in da muke.
tsayuwa ta na gyara tare da É—an matsawa gefe,cikin karairaya da cika da basewa ta karaso tawani shige gabana ta tsare bakin kofar motar,tasun kuyo jikin motar cikin kwarkwasa tasuke murya tare da faÉ—in
"My SALEEM ina fata dai ba daÉ—ewa zakayi ba kasan zanyi missing É—in ka sosai".
bayan ta nabi da Ido ganin yan da take wani yauki kamar zata zube jikin sa.

lekoni yayi yana faÉ—in
"Shiga ciki ki aje wayar ki kusa".
kai na gyaÉ—a tare da yin murmushi najuya a sannu na nufi kofar side É—ina na haura saman step É—in karshe sai natsaya tare da juyowa.
lokacin taÉ—an matsa baya tare da rufa masa kofar, a sannu direba yaja motar suka fito daga cikin parking space ya juya kan motar zuwa hanyar fita,a hankali yazuge glass É—in gefen sa,yakura min ido nima shi nake kallo, a hankali motar ke tafiya har suka fice daga gidan har sai da mai gadi ya maida get yarufe kafin na janye idanuna tare da sauke numfashi,
sai naji duk babu daÉ—i,a Æ´an kwanakin nan babu shakka abu mai kama da sabo yashiga sakani na da Ya SALEEM.
A sannu na juya zan shige ciki ina ɗagowa sai ganin Aunty Na'ima nayi ta...........�

Mommyn Twins ce

🌺 *HAMDAH*🌺

*NA*

*RASHEEDA S DIRECTOR*

_( Book one)_

_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍�*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*

_imayiwa ɗauka cin al'ummar musaimai barka da sallah Allah ya mai-maita mana_🥰

🅿�27

Tana watsamin wani mugun kallo,baki na taɓe dan ni har yau kallon mara kai nake mata najuya nashige ciki na mai da kofa narufe tare da murza key,
da sauri na nufi bedroom jin wayata na ringing,Ina shiga kiran na yankewa,zama nayi bakin gado tare da É—aukar wayar, kokarin mai da kiran nake
sai ga wani kiran ya kuma shigo wa,zama na nagyara tare da picking call ɗin na kara wayar a kunne da sallama, shiru yayi nima daga ɓangaren na hakan take jin yayi shiru sai na ja pillow na Kwanta jikin sa,a hankali najiyo muryar sa
"Ba nace ki aje wayar kusa da ke ba?".
ido na lumshe tare da kuma buÉ—e su
"Ai shi gowata kenan naji wayar na ringing".
shiru yakuma yi zuwa can yace
"Me kike yi a wajen tuntuni?".
kwan ciyata na gyara batare da nace komai ba, kuma jefo min tanbayar yayi
"Me kike a wajen tun É—azu?".
"Babu komai". nafaÉ—a a takaice dan nidai a sanina yanzu ya fita a gidan kuma nima yanzu nashigo na iske kiran sa,amma yake faÉ—in tun É—azu.
numfashi ya É—an furzar wan da sai da naji sautin sa a hankali ya furta
"Ki kula sosai". a hankali na zato wayar jin ya katse kiran, bin wayar nayi da kallo,tare da nanata kalmar ki kula sosai da ya faÉ—a nayi "to me zan kula da shi sosai É—in?".
nafaÉ—a a fili, wayar na aje gefe namike nashiga bathroom nayi wanka nafito na,ina gama kimsawa na nufi kitchen nahaÉ—a breakfast mafi sauki nadawo parlour ina zama najiyo wayata na ringing mikewa nayi na koma É—akin, da É—an mamaki na É—aga kiran ganin shine yakuma kiran....
tun da ga kan wannan lokacin duk bayan minti 30 bayan kira wani kiran zai kuma shigowa wani bin ma 20 minutes sakani har yashiga cikin garin Abuja, lokacin da yashiga cikin Abuja yakirani yake faɗa min yanzu suka shiga nayi masa sannu da hanya dakuma fatan alkhairi,tun daga lokacin bai kuma kira na ba sai da daddare lokacin ma har na kwanta.....�

Yau kimanin sati biyu kenan da tafiyar Ya SALEEM kullum muna waya da shi kamar ko da yaushe duk bayan mintuna ko a wanni,sai dai a cikin kwanakin satin karshen kiran wayar da yakeyi yaÉ—an rago akasin na sauran kwanakin satin farko,yau kwana biyar kenan rabon da muyi waya da shi tun ranar da ya kira ni yace min ai ki ya masa yawa kuma zasu shiga meeting.bai kuma kira naba har yau,
na É—an damu sosai da rashin kiran nasa duk da ko da munyi wayan ma bawata magana ce ko hira muke ba maganar sa baya wuce É—aya zuwa biyu,sai dai ya sabar min da kiran nasa har nakeji na É—an fara damu da rashin kiran nasa.
yau tun tashina nake niman layin sa amma baya shiga....
a hankali na mike daga kwance da nake na É—au wayata da ke ringing É—an kurawa lambar da ke yawo kan screen É—in wayar ido nayi ganin lambar ba na Nigeria bane,da sauri nayi picking na call É—in ganin yana daf da yankewa nakara wayar a kunnena tare da yin sallama,
daga cikin wayar na sinkayo muryar sa yana amsa sallamar.
É—an numfashi na sauke wan da hakan yayi dai-dai da saukar numfashin sa wan da sai da najiyo sautin sa,
"Ya SALEEM". nakira sunan sa,
"Na'am". ya amsa cikin wani irin voice da yasa ni lumshe idanuna,zamata na gyara tare da faÉ—in
"Inakwana Ya SALEEM".
a hankali cikin yanayin sa yafurta "Wuni dai". ido naÉ—an waro nace "Yanzu fa gari ya waye".
muryar sa na kuma sinkayo wa
"Oh sorry hakane Amma a Nigeria".
langwaɓar da kaina gefe nayi tare da marairaice murya
"Nigeria kuma?". nafaÉ—a tare da curo wayar a kunnena nakuma kallon lambar da yakirani da shi É—in,
mai da wayar nayi jin yana faÉ—in
"Eh amma a nan in da nake basafiya bace yanzu".
"Ya SALEEM yaushe zaka dawo?".
É—an shiru yayi kana a hankali ya furta
"Bana kasar kinaso na dawo ne?".
shiru nayi,kuma jefo min tanbayar yayi
"Kinaso na dawo?".
nan ma shirun na kuma ina wasa da Æ´an yatsuna,
" *HAMDAHHH*"
yakira sunana cikin wani irin sauti mai rasa ƙwaƙwalwa da shiga jiki,wannan shine karo na farko da nataɓa ji Ya SALEEM yakira sunana haka kawai,
rausayar da kai nayi tare da kaɗa ƙwayar idona nace
"Na'am". numfashi ya furzar,a hankali na ciro wayar jin alamar ya katse kiran,bin wayar nayi da kallo tare da sauke numfashi....

na mike a hankali nashiga bayi,
da damuwa nashiga tuɓe kayan jikina dan son kimsa jikina karo na biyu a safiyar nan,ba shakka zuwa yanzu nafara tsorata da lamarin jinin nan,iya adadin kwanakin al'ada ta kwana huɗu ne a na biyar kuma zanyi sarki ban taɓa kai wa ko da kwana shida ba sai gashi wannan karo har kimanin sati biyu,
nafara damuwa ganin kwanaki suna ta ja jinin kuma bai tsaya ba.
wanka nakuma nafito na kimsa cikin riga da zani na atamfa,
ina gama shirin na mike dan yau ina son zuwa gida, na yafa gyale naÉ—au Æ´ar karamar side bag da waya ta nanufi waje na kulle kofar side É—ina gaba É—aya kana nafita a gidan,na tare mai a dai-dai zuwa gidan mu...
Chapter 47 · 0% Book details