← Book details Hamdah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 62

Sashe 17

Hamdah Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Washegari yakama ranar lahadi da safe muna zaune a parlour kiran Abbu yashigo wayata, Fauzan da ke rike da wayan yana buga game yamika min, na amsa tare da É—aga kiran nakara wayar a kunne da sallama.
"Ina ƙwana Abbu".
"Lfy lau HAMDAH ya ƙwanan gidan da kannen naki?".
"Duk muna Lfy".
yace "To madallah kishirya musu kayan su an jima da yamma zan sa a dawo da su gida".

Ido naɗan waro sai kuma na marairaice fuska tare da langwaɓar da kai gefe na ce
"Ayya dan Allah Abbu kabarsu su kara ƙwana".
"A'a HAMDAH su dawo kinga gobe Monday a ƙwai makaranta kema kuma kinga goben zaki fara zuwa makarantar, kibari idan suka sami hutu mai yawa sai suzo miki har sai sun kare hutun kafin su koma".
"Ayya Abbu to muzo tare?".
da sauri yace
"A'a baƙyaso sukuma zuwa miki hutun ne HAMDAH?".
"Ina so". Yace to kiyi hakuri suna samin hutu nayi miki alkawari zan kawo miki su kinjiko?".
Kai na gyaɗa kamar yana ganina jiki ba ƙwari nasauke wayar.

Tun da mukayi waya da Abbu walwala ta taragu,
hankalina bai kara tashi ba sai da yamma tayi ganin guri yafara duhu nasan komai a kayi zuwa yanzu Baba Iro direba yana hanyar zuwa É—aukar su Nusaiba.
Muna zaune a parlour suna cin abincin da na girka mana ni dai nakasa ci, natasasu gaba nayi jigum ina kallon su,
Da sauri na ɗago jin a na knocking jiki ba ƙwari namike na isa jikin kofar na buɗe,
rau-rau nayi da ido ganin baba Iro tsaye, ɗan guntun ƙwallar da tatsiraro daga idona ɗaya na share tare da amsa sallamar da yake.
Ya ce "Jeki kirasu suzo mutafi ga hadari ya taso kar ruwa ya iske mu a nan".
Baki na turo najuya a hankali ina tafiya a hankali wai ko dun ruwan zai sauko su fasa tafiyar.
Har gun mota na rakasu da ɗan guntun ƙwalla ta ina tsaye har motar tafita a gidan muna ɗagawa juna hannu.
A hankali kali najuya nakoma bakin kofar side É—in na haura saman step uku wan da dole sai ka haura kan waÉ—an nan matakalar kafin ka shiga cikin side É—in, natsaya kan step na karshe tun ban shiga cikin part É—in ba naji part É—in yamin girma.
zuru nayiwa bayan motar da nake hangowa daga in da nake tsaye wan da sai yanzu yasami damar haurawa titi sabo da a baben hawa da suke wucewa.
wani walkiya ne mai haɗe da tsawa ya welga dai-dai san da suka haura kan titin cikin tsananin tsoro da firgicin ganin hasken walkiyar ya hasko fuskata, bashiri na rufe ida nuna tare da calla kara na kame guri guda jikina na ƙyarma, numfashi na yayi wani irin fizga kamar zai bar jikina.
A hankali ruwa yafara sauka mai É—auke da wata sassanyar iska mai matukar daÉ—i, a hankali nashiga sauke numfashi yayin da sassanyar iskarnan mai matukar daÉ—i ke kaÉ—awa ina jinsa cikin ilahirin jikina, a sannu narikajin zuciyata na sanyi tsoran na tafiya,
A sannu nashiga buÉ—e ida nuna har na buÉ—e shi gaba É—aya.

wani murmushi ne ya suɓuce min ganin ruwa na sauka a gabana, tabbas nayi missing ɗin shi rabon da nashiga ruwa tun ƙwana uku da suka wuce, dan ƙwana biyun da mukayi da su Fauzan bana samin damar da zamu gana da ruwa da zaran Nusaiba taga na tuɓe kayana nashiga bayi tarika buga kofar bayin wai nayi na fito itama zata yi wankan.

zama nayi kan step É—in da nake tsaye a kai naja sket É—ina sama nasaukar da kafafuna kasa na mikar da su ruwan na sauka a kansu, hannuna biyu na mika ina tarar ruwan ina wasa shi a duskata yana gangara cikin kirjina na...

Fito warsa daga bedroom kenan da shirin sa na tafiya masallaci da É—an sauri yake tafiyar jin karar hadari sonsa ruwan ya'iskeshi cikin masallacin dan bayason rasa jam'i ko kaÉ—an.
ko sakiyar parlour bai isa ba ruwa ya kece dai-dai lokacin yaji sautin kararta tsaki yaja dan yasan itace mai wannan ihun,juyawa yy zai koma bedroom yagabatar da sallarsa a can, dan daga in da yake yana jiyo sautin tada ikama da ake a masallaci.
sai kuma yaja ya tsaya yana nazarin ta in da yajiyo sautin karar nata wan da yafi masa kama da tawaje ne ba taciki ba, kuma tun da tayi ihun sau É—aya bata kumaba, da É—an sauri yajuya yashige bedroom, in da laima ke aje ya isa ya É—auka yafita.
Yana fita da mamaki yaja yatsaya bakin kofa duk da guri yayi duhu gakuma ruwan saman da a ke, hakan bai hanashi hangota ba sabo da hasken wuta da ya haske ko ina nacikin gidan.
Yayi mugun mamakin ganin ta zaune cikin ruwan da magriban nan.
Cike da ɓacin rai yabuɗe laimar yanufi in da take.

Saukar ran ƙwashi naji a kaina ƙwarara guda uku ba zato ba sammani, wani irin firgitaccen kara na sake a matukar razane na mike tsaye naduro daga saman step ɗin na ɗaura hannaye na duka biyu a kaina nashiga yamutsa gashin kaina har sai da ɗanƙwali na yafaɗi kasa, na mugun fir gita dan ni a tunanina aljanine yaran ƙwasheni dan da ma Inna tasha faɗa min na daina zama a bakin kofa da rashin ɗaura ɗan ƙwali da almuru in ba haka ba watarana sai aljanu sun min ranƙwashi a ka.

A kiɗime nashiga ja da baya nakuma rufe idanuna gam naki buɗewa dan karma naga aljanin, cikin tsananin firgici da tsoro nakuma ƙwallal kara ina faɗin
"Wayyo Allah Inna kizo aljani ya ranƙwashe wayyo Allah na wayyo Ummi na".
Ban kaiga rufe baki ba naji an damko hannuna, kuma dibirbir cewa nayi nashiga kokarin janye hannuna jin rikon bana wasa bane sai kawai nasaki kuka, har lokacin ida nuna a rufe ban kuma fasa kokarin janye hannun nawa ba.
muryarsa ne ya doki kunnena cikin tsawa yace
"Ke rufemin baki Sha-sha-sha kawai".

Duk da sautin muryarsa dake yawo cikin kunnen na bai sa na yar da shi É—in bane kawai nafi yar da aljanine,
Sosai nake kukan kamar zan sheÉ—i sai fizge-,fizge nake,hannuna da yake rike da shi yamatse da karfi dare da kuma bugamin tsawan. "Kina hauka ne wai ke wate iri ce a daren nan kifito cikin ruwa kizauna dan sabo da tsabar sakarci cikin ruwa gurin zamane!!!". naÉ—iye kukan nayi ba shiri na buÉ—e idanuna jiki na rawa na zuba idanuna kan fuskar shi,kura masa ido nayi sosai ganin shiÉ—in ne dai, kai nashiga girgizawa,
Yace "Cire marasa kunyar ida nunanan naki a kai na wuce kibar nan sha-sha-shar banza kawai!.
Yafaɗa tare da sakarmin hannu wan da nake Jin sa kamar ya ɓalla min shi, da sauri mai haɗe da sassarfa najuya nanufi ciki,
yana tsaye har sai da yaga shige War ta yaja tsaki yanufi masallaci.

Ban tsaya ko ina ba sai bedroom nashige bathroom da sauri natuɓe kayan jikina na shan yasu naja towel na ɗaura nafita nafaɗa kan gado naja blanket na dukunkune ciki,
tsit nayi cikin blanket É—in a haka bacci ya É—auke ni".

Washegari bayan nayi sallah nakuma komawa bacci karfe 7 yunwa ta tadani dan rabona da abinci tun jiya da rana, bayi na shiga a gaggauce nayi wanka haÉ—e da brush na É—auro towel nafito.
Ina fita nanufi kitchen batare da nasaka kayaba da towel É—in É—aure a kirji na dan yunwan nakeji bilhakki,
Ina shiga kitchen nashiga kokarin haÉ—a breakfast mafi sauki.

Tsaye yake jikin mota cikin shigarsa ta alfarma sai baza kamshi yake, a hankali yabuÉ—e marfin mota yana kokarin shiga sai kuma yaja baya tare da dai-daita tsayuwar sa,yaÉ—anyi shiru alamun nazari,makullin motar dake rike a hannunsa yake É—an kaÉ—ashi,mai da marfin motar yayi yarufe kana yajuya a hankali yanufi side É—in ta.

Cikin kankanin lokaci na haɗa breakfast ɗina soyeyyen ƙwai da tea naɗau plt ɗin ƙwan da cup ɗin tea ɗin na nufi kofa,
Ina fita daga cikin kitchen É—in sai ganin Ya SALEEM nayi ya.............

Mommyn Twins ne

*🌺HAMDAH🌺*

*NA*

*RASHEEDA S DIRECTOR*

_(Book one)_

*_________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍�*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*_________________________________*

MARUBUCIYAR👇🏻
*BA ABIN DA BAN GANI BA*
*INA SANE DA HAKA*
*ALFARMA*
*BAZAWARA CE ITA*
AND NOW👇🏻
*HAMDAH*

*Free page*

My no 08034690723

🅿�10

Yana tsaye cikin parlour, burki naja a bakin kofar kitchen É—in sai kuma na turo baki tuno razanina da cin zalina da yayi jiya.
Shiko fuska ya suke ya É—ago hannun sa yakalli a gogon da ke É—aure a hannunsa kana ya mai da dubansa kai na.
yace
"Mekike yi har 7:30 a gida baki shirya kin tafi makaranta ba!?".
Chapter 17 · 0% Book details