← Book details Hamdah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 62

Sashe 10

Hamdah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gyara tsayuwar sa yy da kyau ya Kara wayar a kunne tare da yin sallama ya ce "barka da warhaka
Abbu".
A b'angaren Abbu ya amsa Masa da "yauwa".
Sannan Abbu yad'aura da fad'in "yagidan da iyalin?".
Ya ce "alhmdllh".
"Masha Allah, idan kafita yau kaje kanimawa HAMDAH makaranta tacigaba, Bai kamata ace an dakatar Mata da karatunta ba, kayi Mata duk wani abinda yadace inyaso ko zuwa satin samane saita fara zuwa".
Shuru yy batareda yace komai ba, Abbu ya ce "hello SALEEM kanatare da ni?". Tafiya yasoma sannan ya ce "Eh". Atakai ce,
Abbu yaci gaba da fad'in "Sannan kazuba Mata duk wani abun bukata kamadaga kayan abinci da na Sha da sauran su, duk da nasa an Kai wasu jiya Amma yanada kyau ka Kara mata, kadaiji abinda nafad'a ko?".
"Eh". Yakuma fad'a tare da sauke wayar a kunnen sa Jin Abbu yakatse Kiran.
Dai-dai lokacin ya Isa jikin mota yashige ciki Yana am sa gaisuwar da Malam Sule Mai wankin mota keyimasa,
Salele yakaro jikin motar da sauri yarusuna yashiga gaida shi, Rai b'ace yadubi Salele batare da ya am sa gaisuwar da yake masaba ya ce
"Zaka iya tattarawa kakara gaba tunda ai kin ya isheka!". Kuma durkusawa yy kamar zai zuba goigowonsa kasa ya ce "wlh Oga nace tabari ita taki a gafar ceni".
tsaki yaja yafigi motarsa yy gaba.

Ina shiga d'aki bayi nashige dagudu narufe kofar, Jin karar tashin mota yasani d'ale saman toilet naleka ta window, ganin shine yafita sai naduro daga saman toilet É—in, kayan jikina dasuka gama jikewa yatub'e nawurgasu cikin washing machine,
Najanyo towel dake sakale jikin karfe na silver dake gefen bayin Wanda yake mazaunin igiyar shanya,
Nad'aura,nafito nanufi jikin wardrobe Ina tura Baki had'eda kunkuni
"Shi wanna yafiye takuri baya tab'a barin mutun yasake, Kuma an jima komawa zanyi naje nacigaba".
gajeren tsaki naja naji haushin yadda yakatsemin wasana da yanzu inacan Ina kan zuba ruwa Mai dad'i a jikina.
Kaya nasaka nafito parlour.
Kitchen nanufa, Ina shiga nafara bud'e-bud'e ko zan Sami ragowar breakfast in da Aunty Rafee'at tagirka d'azu, Dan zuwa yanzu nafara Jin yunwa, bb ko alamar abinci agun Dan haka nashiga tunanin mezan girka Dan nasawa cikina.

Jinayi kamar ana buga kofa ido nawaro tareda kasa kunne da kyau,
Tabbas kuwa knocking ake, da karfi kirjina yabuga gaba ki d'aya nagama sinkewa dan nasan Ya SALEEM ne ko wancan mahau kaciyar matar tasa,
Jin an cigaba da knocking in, ahan Kali nafara taku na Isa jikin kofar kitchen, ahan Kali nabud'e kofar Saida naleko na tabbatar da babu kowa cikin parlour'n sannan nafito, Jin an daina buga kofar sai naja natsaya cikin parlour'n,
Nakai minti 5 a tsaye, sai Kuma aka cigaba da knocking in.
Zurunayi Ina kallon kofar a yanzu Kam nasan cewa ba Aunty Na'ima bace Dan ko d'azu da tashigo ai Bata tsaya bugun kofa ba Kai tsaye tashigo,
Saidai banada tabbacin cewa ba Ya SALEEM bane,
Wani numfashi nasauke.

Tabbas inko shine bashakka yau saiya b'allani cikin gidan Nan, Yakuma Hana a d'aurani haka zan cigaba da rayuwa a gurgunce.
Hawayene yasoma gangaromin batare da nasan da zuwan suba,

Ahan Kali nasoma tafiya na Isa jikin kofar, hannuna na rawa nad'aura saman handlle É—in rumtse idanuna nayi naja numfashi da karfi sanda na murd'a handle in, nad'an Masa da baya naja kofar batareda nabud'e idanuna ba,
Baya nakuma yi lokacin Dana gama bud'e kofar nabud'e idanuna dasauri Jin yace b.........

Mommyn Twins ce

*🌺HAMDAH🌺*

*NA*

*RASHEEDA S DIRECTOR*

_(Book one)_

*_________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍�*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*_________________________________*

MARUBUCIYAR👇🏻
*BA ABIN DA BAN GANI BA*
*INA SANE DA HAKA*
*ALFARMA*
*BAZAWARA CE ITA*
AND NOW👇🏻
*HAMDAH*

*Free page*

My no 08034690723

🅿�7

"Barka da warhaka Hajiya".
Nannauyan ajiyan zuciya nasauke a fili,ganin ba Ya SALEEM d'in da nake zato bane, Kai kawai na iya gyad'a Masa Dan har lokacin jikina Bai daina cirawaba,
Mutumin ya ce "Oga SALEEM ne ya yace nakawo wad'annan".
Yafad'a Yana nuna kayakin abinci daki jibge a gifen sa,bin kayan nayi da Ido, katon-katon in taliya da macaroni Indomie Couscous mangyad'a yello da manja shinkafar dafawa da farar shin kafa da semo buhu d'ai-d'ai, Arish Naman saniya Dana kaza wacce aka gyarata aka yayyanka kwai kiret-kiret sai busashen kifi da d'anye Maggi curry time dadai sauransu, kayan d'and'ano kala-kala.
Sai kayan tea suma komai akwai.

Muryarsa na sinkayo Yana fad'in "Hajiya Bari nashiga dasu ciki".
Kai nakuma gyad'a Masa namasa gefe nabashi hanya, buhun shinkafa yad'auka ya ce "Ina kitchen in yake".
Da hannu nanuna Masa kofar kitchen, asannu nakoma cikin parlour nazauna kan 1str,
Jidan kayakin yasoma Yana shiga dasu ciki tas yakwashe yashiga dasu sannan yakimsa komai in da yakamata kana yafito yymin sallama yafita.

Mikewa nayi nashiga Bedroom Jin sautin Kiran sallah dake tashi cikin masallacin kofar gidan,
Direct bathroom nashige nayi alawala nafito nagabatar da Sallah, Ina idarwa namike nanufi kitchen,
Tsayuwa nayi Ina karewa cikin kitchen É—in kallo yakimsa komai yadda yakamata, a sannu na Isa jikin kofar store da ke Nan cikin kitchen É—in.
Natura nashiga Shima yashirya komai yadda yakamata,

katon É—in macaroni nabud'e naciro laida d'aya, nad'ibi albasa 'yan madai-daita guda uku nakomo kitchen,nad'au 'yar madai-dai ciyar roba namaso jikin Fridge Wanda suke jere subiyu babba da karami,
Nabud'e karamin, Jan namace da kayan ciki sai d'anyen kifi aciki, nad'ibi zallar hanta d'an dai-dai sannan narufe Nazo na aje, nad'au wuka na yayyankashi d'an madai-dai ta nawanke nazuba cikin tukunya, sannan nakunna Gas nad'aura tukunyar,
Nayanka albasa guda biyu cikin ukun dana d'ibo nazuba,na b'are Maggi da curry nad'ibi garin citta da kanumfari sai d'an gishiri d'an kad'an,
duk nahad'a nazuba sannan narufe tukunyar.

Babban Fridge É—in nakuma bud'ewa gefe d'aya kayan ganyene irinsu karas kabeji green beans latas da dai sauransu su,
D'aya gefen Kuma drinks ne kala-kala nad'ibi karas da green beans, na yanka karas sirara sannan nawan kesu natsane guri guda,
Tattasai da taruhu na nikeshi d'an dadai, sannan
Nabud'e tukun Yar hantar tanuna, nasauke,
wata tukunyar nad'aura kan Gas nazuba ruwa cikin sa narufe, batareda b'ata lokaciba ruwan yatafasa kasan cewar ruwan bashida yawa,

Rabin laidar Macaroni nazuba cikin ruwan dake tafasan,
Dan nasan ko wuni zanyi bazan iya cinye laida guda ba,
Bayan 7min nasauke najuye cikin 'yar karamar kwando,nawanke tukunyar Dana tafasa macaroni'n nakuma maidashi kan Gas
nasulala mangyad'a d'an dai-dai yadda nake bukata na yanka albasa cikin sa yana soyuwa najuye kayan miyar Dana rigada na jajjaga minti 4 yy nazuba Masa ruwa d'an kad'an nazuba kayan d'and'ano sannan narufe,Saida yatafa sosai na tabbatar da maggi'n Dake ciki sun narke sannan nazuba tafashashiyar hantan namota nakuma maida marfin narufe,
Zuwa can nabud'e nazuba Macaroni nayuya sosai yadda zasu garwaya da juna,sanin Macaroni da hantan sun d'an nuna tun agun tafashe sai na zuba yankakken karas da girinbins iÉ—in narufe sanna narage wutan namasa gefe Ina sauke numfashi.

Lumshe idanuna nayi Jin daddad'an kamshin Dake fita daga cikin girkin,
Banyi mamakin yadda na'iya had'a girkin batare da yabani wuya wajan iya sarrafa shiba,sanin cewa hakan koyar wace ga Aunty Rafee'at Dan duk Randa taje Dass ita takemana girki harta koma, duk sanda take kitchen Ina tare da ita, hakan ne yasa nau ikan girki iri da kala suke zaune cikin kwakwalwata, duk kiwuyata banayiwa girki Dan Yana burgeni sosai akasin wanke-wanke da shara dasuke cimin tuwo a kwarya.

Numfashi nakuma sauke sanda nakalli inda nab'ata,Baki naturo gaba,tuno maganar da Aunty Rafee'at tayimin d'azu dazasu tafi har narakasu bakin get Bata fasa fad'amin ba,

ta ce
"Duk sanda kikayi ai ki kitabbata kin tsaftace inda Kika b'atan kada kibar jikin ki da datti kada kibar muhallin ki da datti kidage sosai wajen saftar jikin ki da muhallin ki,nasanki da kiwuya HAMDAH Dan Allah kirage".

Asannu namaso nafara
Tarkasa kwanunkan danayi amfani dasu nawanke namaida komai mazau ninsa,
Nashare cikin kitchen in har inda ban b'atan bama nakuma gogeshi tsaf,ni kaina gurin yabani sha'awa tabbas tsafta wata abace Mai girman gaske.

Tuni ruwan cikin macaroni'n yatsane nakashe gas in nasauke tukunyar,
Kula Mai d'an girma nad'auka nakwashe girkin a ciki sannan nazuba Wanda zanci a plate,
Parlour nadawo nazauna nasoma cin abin cin.

Ina gamaci namaida plate in kitchen, Nazo nakulle kofar dazai sadaka da babban parlour'n gidan, wan da tanan ne Aunty Na'ima tabi tashigo,kasan cewar akwai hanya nakowani part dake cikin gidan tacikin babban parlour'n,
Nakuma je namurza key na asalin kofar parlour'n,
Sannan nazo nakunnan TV nakwanta saman doguwar kujera, ba jimawa bacci yad'aukeni.

Ban farkaba sai wajen karfe 6, asannu natashi nashiga Bedroom naje nayi alawala Koda na idar da sallar, ina kan sallayar aka Kira Sallahr magriba namike nagabatar da shi.

Bayan na idar shiru nazauna Kan sallayar, ahan Kali naketa jin tsoron danaketa danneshi natasomin ganin guri yafara duhu,
Ban tashiba Saida nagabatar da Sallah'r Isha,
Tuni guri yagama duhu duk da kuwa hasken wutan lantarkin daya haska ko Ina nacikin gidan,Amma duk da hakan acikin d'ar-d'ar nake, gagurin yatsaya cak bakajin motsin kowa.

asannu namike na ninke sallayar na aje nazauna bakin gado gaba d'aya kewar Inna yacikani,
"Ko yatake?".
Nayi maganar afili, sai Kuma nakwab'e fuska "namasan ita batunani takeba tunda da gangan tasa aka kawoni gidan Nan, ai dafarko da Ya Masa'ud tace za'amana aure shine zatasa a canza da Ya SALEEM,
Kuma sati d'ayan zanyi bazan Kara ko kwana d'ayaba".
Nakareshe maganar tareda yin rau-rau da ido.

Najima sosai zaune agun daga bisani namike naje kitchen nazubo a binci, bedroom in nadawo Ina gama ci naje nawanko bakina, Nazo nahaye gado,
Ganin baccin bazuwa zaiyiba kasancewar ban Jima datashi daga baccin ba, sai nafito parlour nakunnan TV don yad'ebemin kewar Inna, sai wajen karfe 11 nakashe TV'n nashige bedroom lokacin Kam bacci ne Tam idona.

Washegari
Bayan nayi Sallah kwanciya nakumayi bani nafarkaba sai karfe 9,
Nasauko a gadon duk jikina a mace Dan baccin Bai isheniba, nadai tashine kawai saboda hud'ubar da Aunty Rafee'at tayimin na baccin safe,
Har nakai bakin kofar bathroom saikuma najuya na wuce cikin window nazuge labule,
"La harya fara". Nafad'a tareda sakin labulen najuya da sauri nanufi waje.
Chapter 10 · 0% Book details