← Book details Hamdah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 62

Sashe 13

Hamdah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kallonsa ya maida kan Ya SALEEM da yayi kicin-kicin da fuska yana ai kamin harara kamar zai kai min bugu na tabbata in badun Abbu na gunba bb abin da zai sa bai kai min hannun ba.
"Meye ke in ba mayyar ba".
Yayi maganar a kasan zuciyarsa,tare da É—an jan guntun tsaki a file.
Niko baki naturo tare da É—an murguÉ—a shi ganin yan da yawani murtuke fuska.

Gyaran murya Abbu yy kana yazura hannunsa cikin aljuhun rigarsa yazaro waya yami kamin yana faɗin "Ungo karɓi nakine duk san da kkson jin muryar Inna sai ki kirata duk Number'n ƴan uwan ki yana ciki, wayar ita zata rika tayaki hira basai kin tafi ba kin jiko? Inna'r ma tana zuwa kuzauna a nan tare".
Da sauri na karɓi wayar cike da tsananin jin daɗi narika juya wayar a hannuna cikin muryar dariya nace
"Ngd Abbu".
Wata Æ´ar karamar laida yamikomin mai É—auke da kwalin wayar da i'giyar cj, na amsa.
Yace "to tashi ki É—au jakarnan kimai dashi ciki".
Tun kafin yakarasa namike da sauri yayin da ida nuna ke kan wayar ina ta lallatsa shi bakina kuwa yakasa rufuwa naja a kwatin nanufi bedroom cike da farin ciki.

Numfashi Abbu yasauke kana ya maida hankalinsa kan Ya SALEEM yace
"Shi yaro ɗan lallamine idan kace zaka tan ƙwasashi da karfi sai yakarye batare da yayi yan da kakeso ɗin ba, idan kabishi cikin dabara da lallami to fa bazaka taɓa shan wuya wajen sai tashi kan hanya ba".
Shidai Ya SALEEM kan sa yaÉ—an dukar kasa batare da yace komai ba.
Abbu yaci gaba da faÉ—in
"Gidan dai lfy babu komai ko ya ita É—ayan iyalin taka?".
"Lfy lau tana ciki batasan kashigo ba".
YafaÉ—a yana mikewa tsaye
Abbu yace "ƙyaleta in bacci take ka gai data in tatashi."
Kofar babban parlour da ke nan cikin parlour'n yanufa yana faÉ—in
"Ba bacci takeba".

Ina aje akwatin najuya nakoma parlour'n ina jin wani irin daÉ—i a raina bakaramin daÉ—i naji da Abbu yabani wayar nan ba har na mance da batun tafiya Dass can gefe nazauna saman 1str ina cigaba da latsa wayar,
Zamana baifi da 4min ba su Ya SALEEM suka shigo yana gaba Na'ima na biye da shi sai wani yamusa fuska take da kaga yanayin yan da take tafiyar da yamusa fuskar da take zaka san dole a kayi mata,a kasa gefen Abbu in da É—azu ya zauna nan yakuma zama,itama ta zauna gefen sa.

ÆŠan sun kuyar da kai tayi cikin yamusa fuskar da take tace
"Ina kwana". tafaÉ—a a gajarce.

Abbu da bai ma fahimci yanayin taba ya amsa cikin sakin fuska kana ya É—aura da faÉ—in
"Kuna lfy ya gidan da bakuwar taku?". "Lfy lau". tafaÉ—a can kasa.

gyara zama Abbu yy kana yace
"Masha Allah".
sai kuma ya É—an yi gyaran murya yaci gaba da faÉ—in
"To madalla acigaba da hakuri dai dan yanzu kece babba ga HAMDAH nan kanwar kuce sai kunyi hakuri da wasu lamuran ta,
mu samman ke da kullum kuna tare da ita a gida dole wasu
a bubuwan ke zaki rika É—aurata kan hanya,
ki ɗau keta tamkar kanwarki idan kinga tayi wani a bin da ba dai-dai ba ki nuna mata rashin dacewar shi, ita bakuwace a wannan ɓangare dole sai an nuna mata wasu abubuwan, sannan HAMDAH yarin yace sai kunyi hakuri da ita,
Allah yabaku zaman lafiya da hakuri da juna".

"Amin". Ya SALEEM yace.

Itako wani irin kallon shekeke tabi Abbu da shi sai kuma tayi wani irin shu'umin murmushi.

akasan ranta kuwa faÉ—i take
"Uhum dole kace yarin yace ita naga yarin yarce kaɗauko ta ka kawo ta gidan nan a matsayin mata, wai ni za'a kife bai-bai kuma ai kanwata bazata taɓa shigowa gidan nan a matsayin da nake ba, kishiya-kishiya ce Allah yasa wake tazamo kanwata".

Shiru tayi da zan cen zucin da take ganin Abbu ya mike yana faÉ—in

"To nabarku lfy a kula a daÉ—a yin hakuri da juna".

Murmushin yake tayi tace
"To Abbu mungode Allah yatsare a gai da gi da".
tafaÉ—a tare da mikewa tsaye tanufi kofa.

Ni duk a bin da suke ma sama-sama nake jinsu gaba É—aya hankalina nakan game in da nake bugawa a wayar, ganin Abbu yamike ne yasani mikewa da sauri na a je wayar nace
"Abbu tafiya zakayi?"
Nayi maganar a marairaice.

Murmushi yy kana yace
"Eh zan tafi daga nan office zan wuce".
Nace "to kagai da su Ummi dasu Fauzan".
Yace "zasuji, ranar juma'a su Fauzan in zasuzo suyi miki kwana biyu ranar Lahadi su koma sabo da makaranta".
To. nace cike da jin daÉ—i, yayimin sallama suka fita.

Suna fita na koma nazauna na ɗau wayar Game in da naketa bugawa tun ɗazu nakashe, nashiga contact numbers in ciki nafara bi ina dubawa duk lambobin mutanen gidan mu yana ciki Number'n Inna nashiga laluɓowa cike da zakuwar jin muryarta na dannawa Number'n nata kira.
Bugu É—aya a nabi taÉ—aga da tare da yin sallama
ko sallamar da take ban amsaba cikin zakuwa da É—onkin jin muryarta nace
"Inna nice Abbu ya siyamin waya".
NafaÉ—a cike da zallar jin daÉ—i.

Washe Baki Inna tayi tana dariya tace
"Kai to madalla gaskiya Abbu ya ƙyauta kuwa, yauwa kinga yanzu zan rika jin muryar ki batare da na kira wancan mai bakar zuciyar ba, dama nima nace yau zan zo to yanzu kam hankalina ya ƙwanta yanzu dai sai nakuma sa rana zan zo".

Da sauri nace
"Inna kizofa".tace
"Zan zo"
Hira muka buÉ—e sosai.

A can waje
har jikin mota Ya SALEEM yaraka Abbu,
Abbu ya buÉ—e marfin motar yashiga yana dai-dai ta zaman sa yakalli gefen sa, numfashi yasauke tare da mika hannu yaÉ—au wata laida dake kan sit É—in gefensa yamikowa SALEEM yace
"Ungo kaiwa HAMDAH Mamei'n kuce tabani na bata kaga na mance sai yanzu da nagani". To yace tare da
Karɓar laidar, Abbu yatada motar yy masa sallama mai gadi yabuɗe masa get yafita,har sai da motar Abbu yafice a gidan kafin yajuya
part in sa ya nufa rike da laidar yana shiga bedroom ya aje laidar saman bedside drowar yashiga bayi wan ka yayi a É—an gaggauce kana yafito ya shiriya cikin wani danda tsatstsiyar yadi kalar lemon grind wan da tasha ai ki da farin zare da É—an ratsin red a jiki kaÉ—an.

Yasaka hula kalar kayan yaÉ—aura wata tsadaddiyar a gogo a hannunsa, sai bakar takallimi feshe jikinsa yy da turaruka masu daÉ—in kamshi da kasha,
wayo yinsa yaÉ—iba dasuke kan mirror yazura É—aya cikin aljuhu É—aya kuma yarike a hannunsa,
Ya É—au jakar system É—in sa yarataye a kafaÉ—ar sa kana yaÉ—au makullin mota yafita,

Direct parking lot yanufa da É—an sauri kasan cewar yaÉ—an makara da zuwa offece É—in, yashige motar yafice a gidan.

Bayan mun gama waya da Inna
Number'n Aunty Jalela dake kusa da nata na dannawa kira sai da yakusa katsewa kafin ta É—aga.

Jin ta É—aga yasani faÉ—in
"Hello Aunty Jalela nice HAMDAH ce".
tace "nasani ai ya akayi ya rashin jin magana?".
Baki na turo gaba cikin murguÉ—a bakin nace
"Nidai inajin magana dan nakiraki na faÉ—a miki abbu yasiya min waya shine zakice min haka, ko Ummi na ban kira ba ina gama waya da Inna naga Number'n ki kusa da nata shinefa na kira".
Nakarasa cikin É—an É—aga murya da gatsali kamar dai yanda kullum idan muka haÉ—u sai munyi faÉ—a.

Tace "To an ji Æ´ar masu baki ko yaushe ne zaki nutsu? Allah yasa ma kina tare da wan da zai gyara miki maza Allah yasa kiyi masa halin ya nakaÉ—a miki duka".
Baki nakuma turowa nace
"Daga kiran ki sai ki kama yimin sururu toma bazan sake Kiran kiba".
nakatse kiran ina ci gaba da mitar.

Cikin tsananin zakuwa da begen Aunty Rafee'at na danna Number'n ta
bai daÉ—e yana ringing ba ta É—aga
sinkayo muryarta nayi daga cikin wayar tana faÉ—in
"Ah Æ´argidan Inna kice dai har wayar tashi hannunki".
Dariya nayi nace
"La Aunty Rafee'at dama kinsan nice?".
Aunty Rafee'at tayi murmushi mai sauti kana tace
"Nasani mana ai É—azu Abbu yakirani da layin yace min nakine".
dariya nakuma yi dafaÉ—in
"Ai É—an É—azu kaÉ—an Abbu yakawomin wayar".
tace "Kinji daÉ—i kenan?" nace "Naji daÉ—i sosai Aunty Rafee'at".
tace "Ah to madalla lallai yaukam kice waya zatasha danne-danne".
dariya mukayi gaba É—ayanmu.
Cikin dariyar nace
"Aunty Rafee'at kince zakizo kuma bakizoba".
"Zanzo a cikin satin nan, ina fata dai duk abin da nace kirika yin nan kinayi".
É—an shiru nayi tace
"Iye HAMDAH kinayi kuwa?".
nace "Eh". tace "An ya kuwa?". nace "Allah da gaske"
tace "To har da girkawa Ya SALEEM tea in da nace".
É—an shiru na kuma yi sai kuma nace
"To zan yi idan yazo zan girka masa".
"Yauwa ko kefa ko bai zobama ki girka ki kai masa É—akinsa kuma É—an abin makulashe idan kika girka shima kiÉ—an rika kai masa ko bai cibama watarana zai ci".

Nace
"Kai Aunty Rafee'at Aunty Na'ima cefa ke yimasa girki"
Tace "Ina ruwan ki da Na'ima ai bata isa ta hanaki girka masa ba kafin ya santa ai ke yafara sani kin fita kusan ci da shi ke dai kiyi abin da nace miki".
To nace.

nan muka ɗan taɓa hira daga bisani mukayi sallama jin an tada salla a masallaci yasani mikewa nanufi bedroom.

Ina shiga na a je wayar saman mirror sannan na nashige bayi ruwa na kunna yafara sauka cikin bath kana nasoma tuɓe kayan jikina ina gamawa nashige cikin bath ɗin da sauri dan na zaku najini cikin wuwan wan da yacika cikin bath ɗin tam.
zama nayi cikin ruwan naɗan ƙwantar da bayana na ɗago kaina nayi pillow da bakin bath ɗin ruwan yakawo min har haɓana.
Chapter 13 · 0% Book details