← Book details Hamdah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 62

Sashe 14

Hamdah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Lamo nayi a cikin ruwan inajin daÉ—in yan da ruwan yake ratsa ko ina na jikina wutsilwutsil haka narika yi kamar mai yin iyo cikin kogi, nakai minti 30 a cikin ruwan kana namike na É—au soso da sabulu wanke jikina koda nagama wanke lungu da sako najikina ruwa na sakarwa kai na daga tsayen da nake ya wanke kunfar sabulun, kana nafito daga cikin ruwan bawai dan nagaji da ruwan ba sai dun ganin lokacin salla natafiya,
nazaro towel naÉ—aura a kirjina al'wala nayi kana nafita a cikin bayin.

Gaban wardrobe na isa na buÉ—e naciro zani na kunce towel É—in naÉ—aura zanin sannan na mai da towel É—in bayi nashanya na dawo É—akin nazura hijabi na shin fiÉ—a sallaya na tada sallah.

Koda na idar nacire hijabin tare da naÉ—e sallayar na ajesu ma ajin su,
gaban mirror na isa nazauna,
mai na shafa naÉ—an murza pauda a fuskata tare da É—an goga man baki kan lip ina kana namike naje naciro wata doguwar riga robal material mara nauyi nazura bayan nasaka pan da bra,
gaban mirror'n na dawo na feshe jikina da turare kana naÉ—au wayata wan da duk abin da nake ida nuna na kansa naje bakin gado nazauna naja pillow nakwan ta,
nan nafara latsa wayar.

Number'n Ya Masa'ud na laluɓo nakai wayar kunne na gyara ƙwanciya ta lokacin da naji layin tashiga,
har kiran ta katse ba'a É—aga ba, kuma mai da kiran nayi harna cire rai da É—aukar wayar nasa jin wannan kiran ma na kokarin katsewa.

Acan kasar India
Masa'ud ne zaune cikin É—an ma dai-dai ciyar parlour'n wan da yake masau kinsa,
littattafai ne a gaban sa ya mai da hankalin sa kansu sai dubasu yake,daga can cikin bedroom yarika jiyo sautin ringing É—in wayar sa,
ture littafan yy gefe yamike tsaye yanufi bedroom
yatako gaban bedside drowar in da wayoyin sa ke É—aure a kai,
É—au kar wayar yy tare da zama saman bedside É—in yy saurin É—aga kiran yaka wayar a kunne.
fuska É—auke da murmushi yace
"Kaji manya Æ´ar gidan Inna".
Baki nawashe jin abin da yafaÉ—a cike da mamakin yan da akayi yagane nice na kirasa tun banyi magana ba.
nace
"La Ya Masa'ud kai ma kasan nice?".
ya ce "Eh ai Abbu faÉ—amin wannan layin nakine".

Baki nakuma washewa kana nace
"To ykk ya India da mutanen garin".
Dariya yaÉ—anyi mai sauti kana yace
"Suna lfy zance kina gai dasu".
YafaÉ—a da yanayin zulaya
"To". nace cike da jin daÉ—i tare da cewa
"Ya Masa'ud har yanzu baka kusa da wowa ba?".
Yace
"Nakusa in Allah ya yarda".
Nace to kakawo min tsaraba".
"Bakida matsala jaka guda zan ciko miki na tsaraba amarya to ya Yayan namu yake?".
Baki natura nace
"Nidai kabar cemin a marya ba kai ne kaki da wowa ba ai da ma Inna tace da kai za'a mana aure gashi kaki zuwa ammana da Ya SALEEM".

Dariya yy kana yace
"to ai dani da Ya SALEEM É—in duk É—aya ne"

Da sauri nace
"A'a kam ai kai kana dariya shikuma bayayi kullum yayita É—aure fuska kamar dodo nidai idan ka dawo zancewa Inna amana auren da kai kawai".

Kai ya jinjina tare da mikewa yazo bakin gado yazauna
yana mai cigaba da dariya haÉ—e da zallar shauki da jin-jina shiririta irin na HAMDAH kodaga maganar ta zaka gane É—in bin yarin ta tattare da ita,
yace
"To ai mace bata auren maza biyu a lokaci guda kuma nan gaba zakiga yana miki dariyar, ina dai baya dukan ki?".

Kai na gyaÉ—a kamar ina gaban shi kana nace
"Eh ai Inna tace duk ran da yabigeni sai tasa Abbu yabigeshi shima".

Yace "to kin ga bazai ma faraba tun da yasan idan yabigeki shima dukan shi za'ayi".

Dariya nayi har da buga cinya sai kuma na rike haɓa naɗan waro ido ina ɗan girgiza kai nace
"Cab Kato dashi ai sai dai Abbu yaÉ—au katon bulala in ba haka ba bazai ji zafi ba ko Ya Masa'ud?".

Yace "ai dama babban bulala zai É—auka yan da zaiji zafi sosai".

Kai na jinjina alamar gamsuwa
Hira sosai mukayi da Ya Masa'ud sai dariya muke dan shi Ya Masa'ud bashida É—aurewa.
Nan yace min yana karatu ne idan yagama zai kirana mukayi sallama na sauke wayar.

Yau kowa sai da yasan an siyamin waya dan ina katse kiran Ya Masa'ud Ummi na kira muka gaisa har da Fauzan.
Sannan na kira Mamei ita ma muka gaisa nasa tabawa Nusaiba.
Abba ne kiran karshe daganan na aje wayar gefe na gyara ƙwanciya ba jimawa bacci ya ɗaukeni.

Ban far kaba sai wajen karfe 5 alawala nayi nazo nayi sallar la'asar koda na idar nafito parlour na nufi kitchen, abinci mai saukin dahuwa na girka taliya ce miyar jajjage
ina gamawa nazuba wan da zan iya ci cikin plt sannan nafito parlour, TV na kunna kana nazauna nan tsakiyar parlour'n Ina cikin cin a bincin a ka kira sallar magriba, bayan na gama naÉ—au plt É—in na kai kitchen nawan keshi kana na Mai dashi mazau ninsa sannan nafita na koma É—aki.
Wanka nashiga ban wani jima cikin bayin ba nafito dan ban tsaya wasan ruwa ba yanzu, wata riga da wandon bacci na ciro nasaka rigar takai min har guiwa wandon kuwa dogone har kasa, sai hula mai raga dana murza a kaina.

Kasan cewar nayi alawala sai na shinfiÉ—a sallaya nazura hijabi nagabatar da sallar magriba ban tashi kan sallayar ba har sai da nagabatar da sallar Isha.

A ɓangaren Ya SALEEM karfe 6 yadawo daga offece koda yashiga bedroom in sa rage kayan jikin sa yy yafaɗa bathroom wan ka saosai yy da ɗan ruwa mai zafi dan son cire gajiyar daya ƙwaso.
Na'ima ta turo kofar tashigo jin motsintsa a bayi sai tafi takoma É—akin ta dan dama waya take da wata a miniyarta jin da wowarsa ne yasa akatse wayar nan suka ci gaba da wayar su.

Shiko SALEEM ko da yafito wata farar tattausar jallabi yazura yanufi masallaci da sauri jin an tada salla,
da misalin karfe 8 yashigo gidan ta kofar side in sa ta baya yashiga batare da yabi ta babban parlour ba, yana shiga É—aki ida nunsa suka sauka kan laidar da Abbu yabasa É—azu zuwan sa yace yabawa HAMDAH,
É—an guntun tsaki yaje har ya juya zai haye gado sai kuma yakuma juyowa ya isa in da ya aje laidar yaÉ—auka tare da kuma jan wani tsakin yanufi kofa,
takofar da yashigo tanan yafita yanufi kofar side É—in ta dake tanan parfajiyar gidan.

Yatura kofar yashiga asannu yatako cikin parlour'n babu kowa sai tv dake tafaman ai ki shi kaÉ—ai,
É—an tsurawa tv'n ido yayi ganin wani Amirican Film in da a ke haskowa.

Mikewa nayi zaune jin karar buÉ—e kofar da akayi a sannu nazuro kafafuna kasa namike tsaye natako bakin kofa buÉ—e kofar nayi a hankali naÉ—an leko kaina ganin shine a tsaye saina karasa buÉ—e kofar nafito na tsaya nan bakin kofar.
É—an juyowa yy yakalleni sai kuma ya mai da idanunsa kan tv'n,
a hankali na juya zan koma ciki na najiyo muryarsa cikin faÉ—a
"Ok komawa zaki kibarni rike dashi sabo da ni É—an ai kenki niko".
cak natsaya tare da juyowa na kalle shi sai kuma na kalli hannunsa jin ya ambaci rikewa
"To in banda abin shi taya zanyi nasan wani abune tafe dashi tun da ba faÉ—a yayiba ko Allan musuru gareni da zan sani".
Baki na turo "shidai kullum a masifa zai kare".
Nafaɗa can kasan makoshi ina takowa in da yake,hannu na mika na rike lai dar da nagani rike a hannunsa, wan da nafi tunani shi yake nufi nabarshi da shi rike, ina rike lai dar yasake da sauri na daɗa rikewa dan tun kan na ida rikewa yasake kaɗan yarage yasuɓuce kasa,najuya nanufi ɗaki.

Shiko gyara tsayuwar sa yy yayin da ida nunsa ke kan tv,sai kuma yaÉ—anyi baya kaÉ—an yazauna saman kujerar dake bayan sa sosai ya mai da hankalin sa kan suburbuÉ—ar da a ke da bindiga a cikin TV'n.

Ina shiga na isa bakin gado nazauna nafara buɗe laidar wani ɗan ma dai-dai cin ƙyaƙƙyawar kwano ce mai murfin glass a ciki,
naciro shi daga jikin murfin ina iya hango abin da ke cikin ƙwanon,
da É—an saurina nabuÉ—e marfin wani kamshine yabigi hancina na haÉ—iye miyau daya taru cikin bakina,
Lafiyayyiyar dambun namace wan da yaji kayan kamshi da É—an-É—ano sai fidda wani kamshi na musamman yake,
É—ebuwa nayi nakai baki dan na gama zakuwa najishi cikin bakina a sannu nashiga tauna shi yayin da da É—in ha É—eÉ—É—iyar danbun naman ya gauraye cikin bakina,
Ko ba'a faÉ—a min ba nasan wannan haÉ—in na Mamei ce.
Aje ƙwanon nayi gefe na mike da sauri nafita dan naje kitchen na ɗauko plt.

Ina fita naɗanyi turus a bakin kofa hangoshi zaune kan kujera yaɗan ƙwanto da bayansa ya jingina da jikin kujerar hannayen sa kuma suna sakale a bayan keyarsa yayi pillow da su.
Mayar da dubana nayi kan TV'n daya kafe da ido sai ai kin harbe-harbe da naushe-naushe suke.
Asannu nanufi kitchen har na É—au plt É—in zan juya sai kuma na tsaya tare da É—aura yatsata kan kumatu alaman nazari
"Yauwa tun da gashi yazo bari na girka masa shayin da Aunty Rafee'at tace".
gaɗa kai nayi alamar gamsuwa da zancen zucin da bake Nan take na ɗaura tukunya nazuba ruwa kofi ɗaya da ɗan kaɗan naɗibi ganyen na'ana'a nazuba sai ƙwayan citta guda biyu da ɗan kanumfari shima baisfi silli huɗu ba nawa ciki na kunna wuta.
Ina nan tsaye ruwan ya tafasa kasan cewar ruwan bashida wani yawa É—an barinsa nayi yakara tafasa saboda kayakin da ke cikin sa suÉ—an nuna,
Zuwa can na kashe wutar nasauke na tacesa cikin cup ƙwalbar zuma na ɗauko na siyaya cikin cup ɗin kana nasa spoon na mosa, naɗau ƴar karamar tray na ɗaura cup haɗe da spoon akai kana naɗauka nanufi parlour'n.
Chapter 14 · 0% Book details