← Book details Hamdah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 62

Sashe 45

Hamdah Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Koda suka fita motar Raliya suka shiga suka É—au hanyar gidan bokan su,
tafiya mai nisa sukayi sosai har suka fita daga cikin gari kana suka shiga wata daji,nan ma sai da sukayi tafiya mai tsawo kafin suka shiga ai nahin dajin malam na kan tudu,
suna isa a gindin wata bishiya suka faka motar suka fito,a nan suka tuttuɓe takalmar su kana suka nufi wata bukka da ke gaban su..
Suna zaune sun naÉ—e kafa gaban bokan sun zubawa kasan da yake ta zanawa da bugawa ido,
zuwa can bokan ya É—ago tare da É—aukar gashin dabba dake gefen sa ya karkaÉ—a shi kan wata kwarya da ke gaban sa,sai ga kwaryar ta kama hayaki,
wani irin kazam tacciyar dariya yayi kana ya É—ago yana duban su yace
"Me kuke so a mata?".
gyara zama Na'ima tayi cike da murnar jin yau boka bai ce takoma ai ki yagamu a jira lokaci ba tace
"Malam Ni kawai ta fita tabar min gida da mijina shine kawai".
bokan ya girgiza kai kana ya mai da idanunsa kan kasan da ke gaban sa yayi wasu zane kana yakuma karkaɗa gashin dabbar dake hannunsa kan ƙwaryar nan sai kuma yaɗa go yadube ta yace
"FaÉ—i wata bukatar wannan babu haske a kanta duhu kaÉ—ai nake gani".
kallon juna sukayi ita da Raliya kana tace
"To Malama yanzu babu yanda za'ayi wlh bana kaunar ganin ta a gidan bana kaunar narika ganin yana shiga É—akin ta duk yan da naso nahana faruwan hakan abun ya gagara".
wannan dariyar nasa yakuma yi sannan ya É—aura yatsarsa kan zanen da yayi sai kuma yaÉ—a go yace
"Akwai in da za'ayi,
basai tana da sarki zai rika shiga É—akin ta har ya kusan ceta ba".
da sauri suka gyaÉ—a kai bokan yaci gaba
"Zamu sake mata jini ko da yaje É—akin nata ma haka zai fito daga karshe kuma ya hakura da zuwan".
Murmushi Raliya tayi cike da jin daÉ—in abun da bokan yafaÉ—a tace
"Shikenan hakan ma yayi in yagaji da kullum jini ya kaÉ—ata gida daga nan kuma kin huta da rakai".
nan bokan yacigaba da surkullen sa daga bisani yamika hannun sa tabaya yasaka cikin wata kwaryar dake bayan sa yaciro kwai guda daya,ya saka shi cikin kwaryar da ke gaban sa zuwa can kuma yaciro kwan, da ta sauya kala daga fari zuwa red da ɗan ratsin baki-baki yamika wa Na'ima da sauri ta sa hannu ta karɓa,
yace
"Kije ki nimi wani abu mai murfi kisaka shi ciki kirufe, duk ranar da kika ji karar fashe warsa to daga ranar ai ki ya gamu".
godiya suka shiga yiwa bokan tare da ajiye masa kuÉ—i masu yawan gaske kana suka mike suka nufi gun motar su suka saka takallamar su suka shige mota suka É—au hanyar gida.
koda suka isa Raliya ta sauke Na'ima ita kuma ta wuce hotel in da dama zataje in da wani ke jiran ta a can.
Na'ima tana shiga side É—in ta tanimi wani kwano mai murfi tasaka kwan ciki takai shi cikin bedroom É—in ta tayi masa kyakkyawan ajjiya,yayin da take jin zuciyar ta ke mata wasai bataki a yanzu kwan nan ya fashe ba a wuce gurin....

★★★★★★

Bayan wasu Æ´an kwanaki
tsaye nake a cikin É—aki rike da waya a kunnena muna magana da Ya Masa'ud dariya nayi da faÉ—in
"Kai dai Ya Masa'ud tun da kullum haka kake faÉ—a kakusa dawowa har yanzu kuma baka dawo ba".
A ɓangaren Ya Masa'ud shima dariyar yayi yace
"Yanzu kam in Sha Allah nakusa dawowa, na san kannan kin haifo mana Baby kinga zan shigo Nigeria da girma na
ko Jaleela daga lokacin bazata kara rainani ba dan tasan nakara girma na zamo Daddy".
dariya na saka jin abun da yafaÉ—a wai na haifo Baby,
"Kai Ya Masa'ud nice zan haifo Baby'n?".
shima dariyar yayi yana faÉ—in
"Eh mana".
A hankali yaturo kofar nayi saurin É—agowa nazuba masa ido,a sannu yatako inda nake,
lokacin Ya Masa'ud yake faÉ—in
"To Æ´ar gidan Inna Bari nashiga school sai nafito zamuyi waya".
nace "Toh Ya Masa'ud in ka fito kakira ni fa zan faÉ—a maka kayan tsarabar da yanzu nake so ka taho min da su".
zare wayar yayi tare da katse kiran yana rike da wayar ya'isa kan doguwar kujerar da ke cikin É—akin, ido na bishi da shi har ya zauna,
"Zo nan".
yafaÉ—a yana dubana a hankali natako nazo in da yake,laidar da yashigo rike dashi a hannunsa ya buÉ—e yaciro magunguna a ciki ya dubeni yana faÉ—in
"Zo kisha magani".
ido na waro da sauri nace
"Magani? me kuma zaisa nasha magani bayan lafiya ta kalau".
ido ya tsura min kana yace
"Zauna a nan maza yanzu kishan yesu duka".
fuska na kwaɓe nayi rau-rau da ido nashiga bubbuga kafafuna a kasa
"Allah Ya SALEEM ni lafiya ta kalau ni dai Allah lafiya ta kalau".
narika faÉ—a ina yarfe hannu da bubbuga kafa a kasa.
zaman sa ya gyara yace
"Ya isa to shikenan zo kisha wannan a madadin maganin".
yafaÉ—a yana nuna lips É—in sa
yaci gaba
"In dai ba magani kika shaba baƙya taɓa yi musu irin wancan tsotsar kizo kisha maganin ma kawai".
"Allah ni dai a'a".
"Ok to kizaɓi ɗaya ko shan magani ko shan wannan".
yakuma nuna lips É—in sa, kafaÉ—a na make nace
"Nidai a'a".
maganin ya ɗago yana kokarin ɓaresu da sauri na zube a jikin sa na rike hannunsa ina faɗin
"Ya SALEEM kada ka buÉ—e Allah zanyi a mai".
"Zakiyi abun da nace ne kokuma na buÉ—e yanzu kishanye su duka".
baki na turo nace
"Zanyi".
"Oya fara yanzu".
yafaÉ—a yana mai da kansa jikin kujera da É—an turo lips É—in sa,hakan da yayin sai ya bani dariya naÉ—an dara
idonsa É—aya yaÉ—an kanne
"Ok baza kiyi ba ko".
"Zan yi to ka rufe idon ka".
a sannu ya mai da idanunsa ya lumshe,
A hankali na maso da fuskata daf da nashi natsurawa kyakkyawar fuskarsa ido yayin da na shagartu da kallon fuskar nashi har nashiga yin maganar zuci,
"Ya SALEEM kyakkyawa ne".
nafaÉ—a tare da lumshi idanuna nakuma buÉ—e su, inayiwa Ubangijin da ya hacicci wannan kyakkyawan halittar tasbihi.
A sannu naji ya sakalo hannunsa ta bayana yazagaye ni batare da ya buÉ—e idanunsa ba yasoma magana

"Anya kuwa na kaiki ƙyau sai dai nasan nafiki hanci, masu ce miki hancin mu iri ɗaya da ke, faɗa miki kawai suke amma ba gaskiya bane dan nawa yafi naki".
Ido na waro cike da mamaki dan banyi zaton maganar tafito ba,kokarin mikewa nake a jikin sa ya daÉ—a rungume ne yana faÉ—in
"Ina kuma zakije bayan bakiyi abun da zakiyin ba,sai zuba min idon da kikayi kamar zaki cinye Ni".
cike da jin kunya na cusa fuskata cikin kirjin sa, murmushi yayi mai sauti kana ya ɗago kaina ya haɗe bakin mu....�

★★

A ɓangaren Na'ima
wani irin zabura tayi taduro daga kan gado tayi gun da ta aje kwanon da tasa kwan da bokan ta yaba ta sauri, zaman dirshem tayi a gaban kwanon takai hannu cikin hanzari ta buɗe murfin wani irin waro ido tayi a cikin kwanon............�

Mommyn Twins ce

*🌺HAMDAH🌺*

*NA*

*RASHEEDA S DIRECTOR*

_(Book one)_

*_________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍�*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*_________________________________*

MARUBUCIYAR👇🏻
*BA ABIN DA BAN GANI BA*
*INA SANE DA HAKA*
*ALFARMA*
*BAZAWARA CE ITA*
AND NOW👇🏻
*HAMDAH*

*Free page*

My no 08034690723

🅿�26

Waro ido tayi cikin kwanon ganin kwan yafashe ruwan kwan tamkar jini,
mikewa tayi ta tuma wani irin tsalle cike da farin ciki,tarika tika rawa tana juyi, da sauri ta je ta É—au wayar ta ta kira Number'n Raliya ta shai da mata abun da ke faruwa,ihun murnar Raliya tasaka a cikin wayar tana faÉ—in
"Shigiya damu take zancen".
Na'ima tace
"Ai kuwa haka zatayi ta yawo da kunshi a É—uwawu kamar mai yoyon fisari".
dariya suka saka
nan sukayi ta murnar su...
Chapter 45 · 0% Book details