← Book details Hamdah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 62

Sashe 2

Hamdah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Hamdah Hamdah Hamdah" can cikin bacci nakejin kiranda Inna taketa faman laftamin juyi yanaji cike da Jin da d'in baccin da nake nadad'a gyara Kwan ciyata.
Inna taturo kafa tana fad'in
"Kai Allah wadaren naka yalalace Wai ace yarinya bata da aikin yi sai bacci
dubi uniform in ma ko cireshi batayiba sabo da tsabar lalaci"
Dai-dai Nan Inna ta'iso bakin gadon tad'aka Mata duka
abaya.
Firgigit nafarka namike zaune da sauri Ina mussuke idanu,
Inna tace
"Mike da Allah bakida aikin yi sai bacci taya jiki zaiyi kwari kullum kina tafiya lagwai-lagwai kamar lagwani".
Turo Baki gaba nayi "to mezan Miki idan natashin?"
Tace "ko shara kije kiyi ai dai yafi kwanciyar Nan Kuma gashi almuru ta gabato inba so kk ki kwashi bakaken aljanu ba"
"Kai Inna Dan Allah ni kibarni nayi bacci na baga Fatu ba ai ai kintane basai tayiba ke bakya kaunar kiga mutum nahutawa saikin kwakulo Masa wani aikin."
Inna ta ce "kinci gidan ku yo dan da maiyi saike kizauna bazaki tab'uka komai ba sabo da son jiki irin naku na 'ya'yan yau"
Baki nakuma turowa gaba namike tsaye,
Sam matarna Bata kaunar taga mutum nahutawa kullum tafison tarika ganin mutum tsaye saikace wani soja.
nashige bayi nagara murfin kofar bayin da karfi, Inna tafice ad'akin tana cigaba dafad'in "iya shegen banza dan da maiyi saike kizauna bazakiyi ba"
Tub'e uniform nayi nayi wanka had'eda alawala sannan nad'auro towel nafito, Ina idar da salla namike nasaka Kaya yafito
sakar gida.

Nan na'iske Inna zaune kan tab'arma tana Jan jarbi wuceta nayi naje kicking nazubo a binci nadawo nazauna gefen ta nafara cin a bincin.
Sallama akayi dukan mu muka d'ago Rabi ce takaraso inda muke ta gaida Inna can kasan makoshi Inna ta'amsa gyara zamata nayi na ce
"Rabi zauna muci"
Ta ce "a'a nakoshi dama nazone kirakani kasan layi Mama ce ta'ai keni"
Nace "to Bari nakarisa cin a bincin saimuje"
"Kije gidan uban wa? Ke Rabi tashi kib'ace min da gani
yo nizaki kawo wa iyashege kizo kirika
kwasar yarinya kina kaita layi-layi salon
kiyab'amin kashin kaza a gari a ce ban'iya tarbiyya ba haryakai kunnen ubanta to bb inda zataje tashi maza kitafi"
Inna tafad'a tana nunawa Rabi hanya,
Rabi tamike tafita
Nace "haba Inna meyasa kk yin hakane Dan Allah kawai rakiyar dazan Mata shine yawon?"
"Au nazuba Miki Ido kirika yawo a wannan duniyar da mutanen cikinta suka gurb'ace Ina a nan ubanki yasani gaba yana yimin bita a kan ki kamar shi yahai feni,nifa wannan Rabin datake wurga kafa kamar shamuwar Nan Bata kwan tamin a rai ba, yaran yanzu kasaka musu ido ma ya'aka kare bare kakawar da Kai".

Ture plt in a bincin nayi namike nashige ciki,
Cikin d'aga muyar Inna take fad'in "shashancin banza"

Washegari Monday nagama shirina saf nazuwa makaran ta nad'au jakar makaran tana tafito
A kafa nahaura makaran tar namu saboda bb nisa saka ninmu,
A kofar shiga makaran tar muka had'u da Rabi Dan makaran tar bokon muma d'ayane da ita tare muka shiga,
a natashi muka fito
Har nad'au hanyar gida Rabi tabiyoni da sauri tana Kiran sunana
natsaya takaraso inda nake ta ce "Hamdah Dan Allah kirakani gidan Adda Samira dama can jiya Mama ta'aikeni"
Nace "to muyi sauri muje kinsan Inna tasan lokacin tashin mu yanzu idan taga ban koma gi da a lokacin ba zata biyoni"
Ta ce "tom"
Muka juya dasauri muka d'au hanyar gidan yayarta a kafa mukarika tafiya ga gidan da uban nisa Sai da muka gaji tilis kafin muka Isa gi dan aikuwa mukayi rashin sa'a Bata Nan haushi kamar nayi ya wahalarmu ta banza ko zama ban Bari munyiba nace mukoma Dan gabad'aya hankalina yakoma gida,haka muka Kuma dakawa da kafarmu bakaramar gajiya nayiba saijan kafa nake sabo da tsamin dakafar yy ga cinyoyina dasuke gogar juna sai zugi sukeyimin dakyar muka karasa gida.

Atsakar gida na tadda Inna da mayafi akanta
Baki tabud'e tana Bina da kallo nikuwa nawuceta nashige cikin parlour da sauri tabiyo bayana tana fad'in
"Mezan gani haka ke Hamdah wace irin tafiya naga kkyi" salati tashiga yi tana tafa hannu tare da fad'in "nashiga uku ni A'i wani al gungumin kk had'u dashi yy miki wanna irin zaluncin
Yau yankaki zanyi kafin ubanki yazo yakarasa ki
Ni tunda naga lokacin tashi yy Baki dawoba hankalina yakasa kwanciya ashedai darabon ganin bakin ciki shikenan kinjamana abun fad'a a gari".

Ido naware Ina kallon Inna cikeda mmk
Saikuma nabi jikina da kallo nakuma mai da dubana kan Inna da taketa buga kirji da sharb'e hanci,tana fad'in yankani zanyi,sorone ya lullub'ene lokacin da nagane abin da Inna take nufi,
Inna kuwa kwad'awa Fatu Kira tashiga yi tana fad'in tazo Mata da wuka,
Kara nakwalla tareda tuma tsalle narika zaga cikin parlour Ina fani "Fatu karki kawo wlh Inna banyi iskan ciba karki yankani"

Inna tarikoni tace "fad'amin d'an gidan uwan wayene shi?"
Na ce "wlh Inna babu kowa naraka Rabi ne gidan addan ta akafa shine kafata yakemin zafi"
Numfashi Mai karfi Inna tasauke saita sakeni ai da gudu nashiga d'aki Ina waigen kofa ko Fatu nazuwa da wukar.

Inashiga d'aki nahaye kan gado
shigata baifi da minti 10 ba Inna tashigo d'aukeda plt, nasan za'ayi
haka Inna wata irin mutum ce tanada fad'a yanzu zatayimin fad'an idan taga nab'ata
Rai zata biyoni ta
lallab'ani Amma fa bashi zai Hana anjima
takuma balbalamin masifa ba Kuma Bata son wani yayi min,kullum maganar Inna d'aya ce a duk san da
tatashi yimin fad'a
sai tace narufa Mata asiri ta dankani hannu iyayena ko gidan
mijina lfy,abun da kesa Inna fad'ar haka tun akan wata 'yar makotan mu
da tayi ciki a waje shikenan Inna tasinke kullum a cikin tsaro da
barazanar ta nake.

Plt maid'aukeda a binci ta'aje tazauna gefena tace "tashi kici takwara ta kinsan zama da yunwa bb kyau.........

Mommyn Twins ce
[6/1, 3:39 PM] Rasheeda S Director: *🌺HAMDAH🌺*

*NA*

*RASHEEDA S DIRECTOR*

_(Book one)_

*_________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍�*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*_________________________________*

*Free page*

*Labari mai tsada farashi mai sauki É—arin ki-ka 200 yabiya miki-ka bukata turo 200 ta wannan asusun bankin 3170524141*
*Rashida Salihu First bank*
*Ko katin waya na MTN 200 ta wannan Number 08034690723*
*tsiyan nagari mai da kuɗi HAMDAH labarine mai tsa da na baku shi a farashi mai rahusa*👌🏻

~wannan page ɗin na sadaukar dashi wa tsohuwa kakata Innar mu tsohuwa mai ran karfe madubin Director family~🥰🤗

🅿�2

Huf namike Dan dama yunwace sur cikina Sai da nafara cin a bincin kafin Inna tafita, Ina gamawa naje nawanko hannuna nadawo nakuma Kwan ciya.
Muryar Inna naji tana rafka
Salati sai kuma
Magana narikaji kasa-kasa da sauri namike zaune Jin muryar goggo Hauwa da a lamun fitar sautin kuka,
Cikin hanzari nadiro a gadon nafito,
Ido naware ganin goggo Hauwa shin fid'e atsakiyar parlour'n sai numfashi take fiddawa d'aya nabin d'aya nakuma Kai dubana takasa inda take kwancen dafe kirji nayi ganin jini nafita tacikin zanin ta, Inna tace
"Subhanallahi mezan gani ni A'i shekenan tayi b'ari"
A binda Inna naji take fad'ane yasani mai da duba na gareta dakyau, "B'ari" nanatata kallamar a raina,
Inna ta dubi Fatu da yanzu shigowar ta ta ce "yimaza kije ki taro Mana Mai a bin hawa mutafi asibiti"
Da sauri Fatu tafita Inna tashiga d'aki tafito da zani a hannu tazo kanta tana kokarin canza mata zanin,
Kara nakwalla lokacinda Inna tamirgina goggo Hauwa ganin yadda jini yakwanta a'inda ta kwanta nayi kan gaggo Hauwa ina fad'in "wayyo Allah goggo Hauwa karki mutu"
Fatu tashigo dasauri tace "Inna nataro Mai abin hawan"
Inna da Fatu su suka d'aga goggo Hauwa suka fita da ita nabi bayansu dasauri Inna ta ce nakoma gida suka haye a bin hawa suka tafi asibiti ina shiga gi da d'aki nawuce Dan gabad'aya ganin jinin Nan yatsora tani.

Sai yamma Inna ta dawo inajin da wowarta nafito Dan tun tafiyar su dana shige d'aki bankuma fitowa ba,
Na ce "Inna inasu goggo Hauwa'n?"
Ta ce "tana gidan ta nabarsu da Fatu zata zauna tayi Mata bakwai kafin tadawo"
Na ce "Inna harciwon b'arin tan yawarke?" Kai kawai tagyd'a min,harna juya zan fita sai nadawo dasauri na ce "Inna kikace Fatu saita kwana bakwai kafin tadawo?to waye zai rikayin wanke-wanke da shara da girkin?"
"Ke Mana bagakiba ke aikin me kk ke Zakiyi tayi kafin tadawo".
Jinayi kamar Inna tasa komin dutsai a ka, shara da wanke-wanken Nan basonsu nakeba garama girkin inason yi kodun nayita motsawa
Nace "Inna duk nikad'ai cap yaushe zan iya". Nafad'a Ina tura Baki,
Ta ce "ai dama ba Wanda a ka haifeshi da iyawa kowa Sai da yazo kafin ya'iya haka Zakiyi har ki iya uwar 'yan sonjiki"
"Ni dai wlh Inna bazan iyaba kice Fatu tadawo kawai tunda kince ciwon b'arin goggo Hauwa'n yawarke"
Dasauri najuya nashige d'aki, "yarinya sai shegen son jiki kullum kina gado kamar Mai kar yaiyen baya". Cewar Inna inajin ta nidai nayi shigewa ta d'aki.

Washegari da safe Inna tashigo d'aki inajin shigowar ta nayi saurin rufe idanuna tazo tashiga bubbugani tana fad'in "ke Hamdah Kin mance kinada makaran tane Baki tashi kinje kin d'aura a bin Kariba gashara da wanke-wanke ma kinsan dai Fatu batanan dai ko"
Da sauri namike zaune "Inna nayi latti fa" tace "yo shine kk kwance dan siya" Huf namike nasauko a gadon nashige bayi Dan gudun kada takuma kawo zancen wanke-wanke da shararnan.
Ina gama shiri nafito a kicking nasami Inna harta had'a a bin karyawa tazubo ta mikamin Ina kammala ci tami komin naira 50 nakarb'a inata murna nayi waje.
Chapter 2 · 0% Book details