Sashe 60
Hamdah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yau gidan cike yake tam da jama'a kamar ranar da akayi rasuwar, yau kwanan Inna uku kenan da rasuwa.
Muna zaune da su Ummi jama'a sai shigowa suke dan dole Ummi tasa nafito parlour dan wasu da dama idan suka shigo sai sun tambaya ina nake.
jin ta aziyyar da mutane ke yimin nason fama min mikin dake cikin zuciya ta sai na mike na koma É—aki ina share wasu zafafan hawaye da suka zubo min, Aunty Jaleela ce tashigo da sauri rike da wayata da tun ranar rasuwar ban ma san in da yake ba ta mika min tana faÉ—in
"Karɓi a na kiran ki Ya SALEEM ne naɗa ga yi magana".
tafaÉ—a tana samin wayar a kunne.
hawayen na share kana nayi sallama,
batare da ya amsa sallamar ba yace
"Kuka kike ko?".
kai na girgiza kamar yana gabana sai kuma nace
"A'a".
numfashi ya fesar kana yace
"To zo gani a waje".
a hankali na zare wayar na mike nashiga bayi na wanko fuskata nafito,Aunty Jaleela na tsaye ganin na nufi kofa sai ta bi bayana tana tan bayana ina zani nace mata Ya SALEEM ke kirana,jin haka yasata tsayuwa a parlour nikuma na wuce ina É—an rike zundireriyar hijab É—in da ke jikina.
a daf kofar shiga side É—in na ganshi tsaye,ido ya zuba min har nakaraso in da yake,
ganin kallon da yake bina da shi yasani yin kasa da kaina a hankali ya furta
"Kinyi kuka mana".
É—agowa nayi na É—an kalle shi sai nakuma yin kasa da kai na,hannuna na ya ruko yana faÉ—in
"Fuskar ki ta nuna ai, baza ki sawa zuciyar ki hakuri bako?".
"Bana sanin san da hawayen yake sauka ne amma na dai na kukan".
janyo hannuna yayi yasoma tafiya kana yace
"To ki dage ki iya mai da hawayen idan zasu zubo,gobe zamuje asibiti a dubaki".
na buÉ—e baki zan yi magana sai nayi shiru lokacin muka karaso farfajiyar gidan ina É—agowa mukayi ido huÉ—u da Na'ima tafito daga side É—in Inna taÉ—au hanyar part É—in Mamie,
kawar da kaina nayi ganin irin kallon da take binmu da shi har ta wuce sashin Mamie.
maganar sa najiyo a hankali
"Ta a ziyya za su miki".
É—ago kai na nayi jin abun da yafaÉ—a nan idanuna ya sauka kan wasu mutane guda biyu da ka gansu kaga manyan mutane,muka karaso in da suke,
gaishesu nayi suka amsa kana suka É—aura da yi min ta'aziyya.
rau-rau nayi da ido sai ga hawaye ya cika ido na,Ya SALEEM yace
"Kukan zaki fara kenan".
kai na girgiza da sauri ina mai da hawayen.
muna tsaye muna gaisawa da mutanen Na'ima ta fito daga side É—in Mamie ta nufi na Ummi.
É—aya daga cikin mutanen yace
"Sai a hankali zata dai na rashi a kwai zafi sai hakuri".
Nan suka É—an yi min nasihohi kana suka yi wa Ya SALEEM sallama suka shiga motar su suka tafi.
yace na koma ciki bari ya fita a kwai masu jiransa a waje,nace masa to.
na juya na nufi ciki shikuma yayi waje,
kafin na karaso kofar side ɗin Na'ima ke fitowa daga cikin sa ko minti 4 batayi da shiga ba tafito wai har tayi ta'aziyyar kenan,wani irin kallon sama da kasa tabini da shi kana ta taune laɓɓanta na kasa tare da girgiza kai
sannan tace
"Ya hakuri".
"Muna koyi".
nima na faÉ—a a takaice,
kai ta guma girgizawa tawuce ni.
ban ma san tanayi ba nawuce ciki abina....�
Ranar da Inna ta cika kwanan bakwai Æ´an uwa na nesa da na kusa suka fara komawa ciki kuwa har da su Aunty Rafee'at da tun ranar rasuwar suna gida muna tare da su.
da daddare Ya SALEEM yazo yace mutafi, kuka nasaka mishi nace nidai bazan koma ba sai da su Abba suka yi da gaske wajen lallashi suka ce ga Aunty Halima Æ´ar baffan su Abbu'n mutafi tare zata É—an rika É—ebe min kewa tun da bata da aure kuma ba yanzu zata koma ba ita ma mijin ta ya rasu watan sa huÉ—u da rasuwa kenan.
kafin na yar da na bishi muka koma har da Aunty Halima.
ranar da muka koma nayi kuka sosai dan ina shiga gidan Inna ta faÉ—o min arai ga kuma tsoron nan dake nan cikin raina,ranar sabon lallashi Ya SALEEM da Aunty Halima sukayi...
tun da muka dawo gidan kullum muna tare da shi in yafita kuwa zan koma gun Aunty da ta sauka cikin ɗakin da Inna take sauka idan tazo gidan...�
Haka rayuwa yacigaba da tafiya kamar sannin ku yanzu kwanaki basa da wuyan juyawa.
kwanta tashi asarar mai rai rayuwa sirri inji masu iya magana.
Yau kimanin kwanakin Inna arba'in da rasuwa hakan kuwa yayi dai-dai da lokacin fara tafiya ai kin hanjji ma niyyata sunata shiri domin tafiya ai kin hajji in da wasu garuruwan ma da dama jirginsu yafara tashi ciki kuwa har da garin Bauchi'n Yakubu.
Mamie da Abbu suna daga cikin maniyyatan wannan shekarar,kamar yadda suka tsara wa kansu duk bayan shekaru uku Abba da Ummi zasu tafi bayan wani shekaru uku kuma Abbu da Mamie.
a na saran gobe da karfe 8 na safe jirginsu zai É—aga insha Allah.
yau tun da sassafe nayita masawa Ya SALEEM nace sai dai ya kai ni gida naje nayiwa su Mamie Sallama,yace na bari sai da daddare ko kuma da safe muhaÉ—u a airport.
nace nidai a'a.
yace to nahakura duka na kirata a waya nayi mata sallamar,kuka na saka mishi nace ni dai na yar da ya kai Ni da daddaren.
murmushi yayi kana yace
"Kin sau ko layi kenan"...
kamar yadda yafaÉ—a kuwa bayan sallar isha ya kwashe mu har da Aunty Halima ya kai mu gidan...
A farfajiyar gida muka dadda Abba da Abbu da alama dai tattaunawa suke irin na Æ´an'uwan taka muka gaidasu kana muka wuce, Ya SALEEM kuma ya tsaya a gun.
koda muka shiga side É—in Mamie nan muka taddasu gaba É—ayan su dasu Aunty Rafee'at suma É—in sallamar suka yi musu har da Ummi duk suna cikin parlour,da goggo Hauwa da itama tazo É—azu dan yi musu sallamar.
hira sosai ake cike da É—ebewa juna kewa kowa yana faÉ—in kalar tsarabar da za a kawo miki, Mamie ta dubeni kana tanisa tace
"Ni banji kince ga abun da kike so a kawo miki ba,ko wannan karo kin yafe ne akawo miki É—ankwale kawai".
tafaÉ—a tana dariya.
dariya duka a saka Aunty Jaleela har da buga cinya tace
"Allah Mamie kikawo mata É—ankwali mu kikara mana tsarabar tun da bata so".
baki na murguÉ—a mata tare da faÉ—in
"Ni nace miki bana so ai na barine kugama faÉ—an naku sai na faÉ—a mata nawa dan kar kusa ta mance da nawa".
a can kasan raina kuwa ba haka abin yake ba Inna ce kawai ta faÉ—o min shi yasa nayi shiru in da tana nan da har da ita acikin tafiyar bayan rasuwar tane Abbu yaje ya amso kuÉ—in kujerar ta,da kyar na dage na iya mai da hawayen da suka ciko idona.
maganar Mamie ne yasani dawo a hankali na kalle su
"To me kike so a kawo miki HAMDAH?".
murmushi nayi da faÉ—in
"Mamie dogayen riguna da gyale da warwaro da zobe".
tace
"To ba damuwa naki zan fara siya kafin nasu".
dariya Aunty Rafee'at tayi tace
"Mamie abun ma wariya ne to me za a siyo wa baby'n ciki".
É—an kallon cikin nayi da yafara tasowa amma sai ka lura zaka gane sai dai inajin nauyin sa.
Mamie tace
"Ai kuwa dele na amma fa idan miji ne to akwatin sa ma daban ne, idan kuma kishiya ce ko ruwan zam-zam bazata gani ba, sai ta jira idan Ummi'n Fauzan taje tazo mata da shi dan nabar mata ita".
dariya aka saka gaba É—aya cikin muryar dariya Ummi tace
"A'a dai Mamie'n Nusaiba in dai kishiya ce kikawo mata tsaraba in kuma miji ne to ki bari idan naje ni zan kawo masa".
dariya Abbu yayi da yanzu shigowar su shida Ya SALEEM da alama sunji muhawarar da ake, Ya SALEEM kuwa murmushi ne É—auke a fuskarsa, na lura in dai ana magana kan cikin nan sai yayi ta murmushi.
Abbu yace
"To dayake magana ne kan kishiya kowa yanata kakkaɓewa a jikinsa to ni ina so in matace kuwa duk tsaraɓar da zanyi natane".
Aunty Rafee'at tace
"Yauwa Abbu ka siya mata irin kayan da Mamie da Ummi basu taɓa sa irin saba".
goggo Hauwa tace
"Ai kam a siya wa kawata tun da duk kishi ya ishe su"..
haka a kayi ta hira cikin raha da jin daÉ—i da É—ebewa juna kewa,
duk hirar da ake kuwa baka taɓa jin maganar Ya SALEEM sai dai wani sa'in yayi murmushi.
har wajen karfe 10 muna zaune anata hira sai a lokacin Ya SALEEM ya mike yace mutafi.
kafaÉ—a na make nace nidai kwana zanyi,zai kuma magana Abbu yace ya barni nakwanan haka yatafi badun yaso ba.
Washegari gaba É—ayan mu mun hallara a parking space har da su Aunty Rafee'at dan suma anan É—in suka kwana.
motar Abba Ummi Aunty Rafee'at da Aunty Jaleela Fauzan suka shiga, inda mukuma muka shige motar Abbu Iro direba shi zaija motar Abbu na gefen sa Ni da Mamie da goggo Hauwa da Nusaiba muna baya,
Aunty Halima Kuma barta ita ta zauna a gida.
a haka muka jera muka nufi airport
muna isha motar Ya SALEEM yana isowa
dai-dai kuma lokacin kuma ake ki ran sunan mahajjata dan haka batare da ɓata lokaci ba muka fito su Abbu suka nufi ciki muna ɗaga wa juna hannu.
Naso bin su Ummi mu koma gida Ya SALEEM ya hana haka ya É—auke Ni a motar sa muka koma gida.
muna isa na kira Aunty Halima nace tahau napep ta dawo dan Allah tace min zata dawo amma sai jibi....