← Book details Hamdah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 62

Sashe 49

Hamdah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A kan gado ya ajeni ya isa gaban wardrobe yaciro doguwar riga mara nauyi da pant yazo ya saka min, kana ya ɗau rigarsa daya tuɓe yasa ka.
yafita zuwa can yadawo É—auke da cup É—in tea Mai kauri ya É—ago ni ya tallafo ni jikin sa yakai cup É—in bakina a hankali cikin muryar tausaya wa yace
"BuÉ—e baki kisha".
A hankali nabuɗe bakina yadaɗa manna min cup ɗin nakama shan tea ɗin a hankali kurɓa ɗaya zuwa huɗu nayi da sauri na kawar da kaina jin tea ɗin kamar baya wucewa a wuya yake tsayuwa yana shirin dawowa.
ganin yan da nake jujjuya kai yasashi a je cup É—in da sauri
ya mike tsaya yaje ya ciro hijabi cikin wardrobe yazo yazura min,
kana yanaÉ—e hannun rigarsa yasun kuce ni yanufi kofa da ni,
a hankali na buÉ—e idanuna kan fuskarsa sai kuma na mai da da sauri na rufe saboda jiri,cikin disashshiyar muryar wahala nace
"Ya SALEEM Ina zamuje?".
"Asibiti zamu".
yafaÉ—a yana daÉ—a gyara rukon da yayi min.

"A'a Ya SALEEM kar muje zasu bani magani"
"A wannan yanayin da kike ciki me yafi dacewa da ke in ba maganin ba".
kaina na daÉ—a mai dashi kan kirjinsa ban kuma cewa komai ba dan maganar da nayi yanzun ma cikin karfin hali na yishi amma ni kaÉ—ai nasan irin azabar ciwon da nakeji.
Yana isa gun mota yabuÉ—e gefen mai zaman banza yasakani ciki kana yagyara min zama yaÉ—an kwantar da sit É—in ta yadda zanyi daÉ—in zama na kwantar da kaina jikin sit É—in,ya mai da marfin yarufe kana da sauri yazaga gefen direver yashiga ya tada motar mai gadi yayi hanzarin buÉ—e get yasakai yafita.
yana tukin ne amma rabin hankalin sa nakai na dan duk bayan dakika sai yajuyo ya kalleni,
Hannunsa É—aya yaÉ—a go yayin da É—aya hannun sa ke kan sitiyarin motar,
a hankali yasauke hannun kan gefen fuskata yaÉ—an shafo shi,
cikin yanayin sa yamosa lips É—in sa
"Idon ma ciwon yake ne uhum *HAMDAHHH*"
kai na É—an girgiza a hankali nace
"Ina jin jiri ne in na buÉ—e sai na rika ganin guri yana juya min".
iska ya furzar daga cikin bakinsa tare da faÉ—in
"Kin bar ciwo yayi yawa a jikin ki meyasa baki faÉ—a min ba".
shiru nayi,kai na yaÉ—an janyo zuwa kafaÉ—ar shi sai nazamo jikin sa nakwanta gefen jikinsa a haka muka isa asibitin.
ya gyara fakin a cikin gunrin da aka tana da domin adana motoci yafita yazaga gefen da nake yabuÉ—e,
a hankali na É—an buÉ—e idanuna jin yana kokarin É—aukata,a hankali nace "Kabari zan tafi da kaina".
nafaÉ—i hakan ne saboda ganin mutanen da suke cike a harabar asibitin,hannuna yariko yana faÉ—in
"Ok to sauko".
yafaɗa tare da taimaka min nazuro kafafuna kasa namike tsaye, gefe na ya dawo ya tallafo ni gefen jikin sa a sannu nashiga ɗaga kafa ta,wani irin jiri ne ya fizgeni sai wani duhu ya gilma min natafi luuu zan faɗi sai yayi saurin rukoni ya mai dani jikinsa,tundaga lokacin ban kuma sanin abun da ke faruwaba.....�

*After 10hr*

Sai a lokacin na farka daga doguwar sumar danayi,sai dai idanuna suna lumshe,muryoyin mutane da dama narikaji sama-sama,can nasinkayo muryar Abbu cikin damuwa yake faÉ—in
"Faruq har yanzu fa bata farfaÉ—o ba gaskiya a sake duba ta sosai ace mutum tun safe har dare yana kwance babu motsi tun É—an motsin da tayi É—azu da ake ta jan jinin ta bata kuma motsawa ba har yanzu sai uban ruwa da allurai da ake ta narka mata, in ma yaya ne muyi mai yiwuwa kawai yau É—in nan mubar kasar nan da ita".
sautin murmushin Dr Faruq najiyo tare da faÉ—in
"Ai Abbu ta farfaɗo tun ɗazu abun da yasa bazaku gane farfaɗo war nataba a cikin bacci ne tafar kan, yanzu kam bacci take kuma wannan baccin da take shine nasarar da muke hangowa na samin lafiyar ta, in Sha Allah idan ta farka daga baccin da take zataji sauƙin jikin nata sosai".
Abbu yace
"To Allah yasa a dace". kaf gurin suka amsa da ameeeen.
hannuna da naji yayi min nauyi sosai nashiga kokarin É—agoshi a hankali nashiga buÉ—e idanuna har na ware shi tarrr saman pop'n room É—in,muryar Inna naji a kusa dani tana faÉ—in
"Idris Shu'aibu gashi tana motsi da hannunta sosai yanzu, la tama buÉ—e ido".
tafaɗa tana daɗa rike hannuna da nake ta kokarin ɗagashi, a hankali nashiga juya ƙwayar idanuna cikin ɗakin,inda tuni
Abbu Abba Ummi Mamie Aunty Rafee'at Aunty Jaleela Dr Faruq barista Aliyu suka nufo gadon da nake kwance kowa bakin sa É—auke da hamdala.
nan suka shiga jera min sannu ba adadi,Ni dai da ido nake bin su..

Baki Inna ta washe tana faÉ—in
"Ikon Allah sai kallo sannu kinji Æ´arnan".
Dr Faruq yaÉ—an matso yana duba ruwan da ke É—aure a hannuna hannun da Inna ke rike dashi ganin inata kokarin É—ago hannun,yace
"Inna saketa ruwan ma yakare bari nacire mata".
yana cirewa na É—ago hannun da kyar naÉ—an yarfe shi, dubana yayi yace
"Ya kike jin jikin dai Æ´argida Inna? akwai jiri ko ciwon kai??".
kai nagirgiza
a hankali nace
"Banajin jirin yanzu kaine kawai yake min ciwo".
murmushi yayi dafaÉ—in
"Zai bari shima".
nan suka fita shida barrister Aliyu,
Mamie da tun É—azu taketa sakin murmushi tace
"Kai ma dallah Alhamdulillah sannu kinji É—iya ta".
kai na gyaɗa mata sai sannan naga ashe ba ita kaɗai ba fuskokin kowa ɗauke yake da yelwa tacciyar murmushi Ummi na kam ido ta zubamin tanata sakin murmushi,Abbu da Mamie wani tsagwaran farin ciki ne a kan fuskar su,Mamie nata ya gaza ɓoyuwa har sai da ta matso kusa dani sosai tariko hannun da naketa ɗan tanƙwashe yatsun hannu tariko shi tana faɗin
"Yaya dai HAMDAH hannun nayi miki ciwo ne?".
tafaÉ—a cikin bayyana murmushin ta a fili da nuna tsantsar kulawa,
kai na gyaÉ—a mata alamar Eh,
hannun ta É—an rika matseshi a hankali tana yimin sannu.
Inna tace
"Yo ba dole hannu yayi tsami ba yasha ruwa da allurai".
kallo na na mai da kanta kana nace
"Yunwa nakeji". da sauri Aunty Rafee'at tajuya gefen ta inda basket ke ajiye cikin hanzari ta haɗo tea tazo in da nake,Mamie ta taimaka min namike zaune karɓar cup ɗin Mamie tayi tace Aunty Rafee'at ta taimaka min naje na wanko bakina tukun.
Aunty Rafee'at tariko hannuna nasauko a gadon a hankali muka nufi bayi,na wanko bakina muka fito,
a bakin gadon na zauna Mamie ta mika min tea É—in da tariga da tafifitashi yahuce haÉ—e da yankan bread,tea É—in kawai na amsa ban da bread Dan ni ban fiye shan tea da bread ba,nakuwa sha da É—an yawa kana na mika mata cup É—in,Inna ta samin pillow ta bayana najingi na dashi tace na huta da kwanciyar nan haka,
"Inna yaushe kika zo?".
nafaÉ—a ina duban ta ganin itama bakin ta yakasa rufuwa,
washe baki takuma tace
"Tun lokacin kina rai ahanu Allah yo ai ni tun da naji kina kwance a gadon asibiti a sume mayafi na kawai na É—auka nahayo mota nayiyo nan".
Aunty Jaleel tace
"To da rantan a hannun wa yake".
"Tafi can da alla yarinya karama da babban ciwo koke da girman ki ma irin wannan ciwo yaka maki sai kin wujujjuge bare ita kankanuwa da ita".

A hankali a ka turo kofa a sannu na É—ago kaina kasan cewar ina fuskantar kofar ce,
yana rike da laida a hannunsa
gaba ki É—aya jikin sa a sanyaye yake kallo É—aya zaka yi masa ka gane hakan,
karaf ida nunmu ya haÉ—u da na juna,waro ido yayi a kaina da alama mamakin ganina azaune yake,
wani irin murmushi yasake yayin da yake bina da wani irin kallo mai cike da É—inbin farin ciki,gaba É—aya mutanen cikin É—akin suka juyo jin an buÉ—e kofa ba a shigo ba,
ganin gaba É—aya hankalin sa yayi nisa yasa Abbu yin gyaran murya,a kunyace yamai da kofar yarufe ya tako cikin É—akin,a gefen gadon ya tsaya sai dai har lokacin fuskarsa da sihirtaccen murmushi,
Inna ta dubeshi tana faÉ—in
"Yauwa mai sunan Malam kasiyo maganin ko, ta ɗan taɓa shayi sai tasha yanzu maza bata yanzu tasha".
rau-rau nayi da ido jin abun da Inna ta faÉ—a na kalleshi idanuna taf da hawaye shima ni yake kallo,
murya na rawa nace
"Ya SALEEM zanyi amai".
É—an jim yayi dan yasan tabbas nasha zanyi aman gashi babu ta yan da zaiyi ya dakatar da aman a wannan lokaci,
Inna kuwa daÉ—a duban sa tayi tace
"Yo bin nata zakayi bazaka bata ba jinya za'ayi shi bashan magani ne".
tuni hawaye yafara sauka a idona
Inna kuwa taci gaba da faÉ—in
"Maza bata tasha".
a hankali ya buÉ—e laidar yaciro magungunar yabuÉ—e ya mika min,Mamie ta mikamin gorar ruwa ina rike da maganin a hannuna hawaye naciga ba da zuba a idanuna Inna tace
"Iya shegen banza baza kayi mata tsawa tasha ba ka zuba mata ido ne".
idanunsa ya lumshe tare dakuma buɗe su lokaci guda,miko hannunsa yayi ya karɓi maganin da gorar ruwan yawasa maganin cikin laidar.
salati Inna tashiga yi da tafa hannu tana faÉ—in
"Kai mai sunan malam bin nata zakayi ina É—azunnan take kwance kamar gawa shine yanzu taki shan magani kamara mata baya".
Abba yace
"SALEEM ya ka karɓi maganin kabata tasha mana".
bayan keyarsa yaÉ—an sosa kana yace
"Dr yace sai taci abinci kafin tasha kuma tea kawai akace tasha".
Ummi tace "To ai ga abinci nan sai a saka mata taci".
da sauri nace "Ni bazanci wannan ba".
Abbu yace "To shikenan Rafee'at da Jaleela kuje ku girko mata wani sai taci tasha maganin".
To suka amsa dashi.

Baki Inna tawashe kamar ba ita ke masifa yanzu ba ta dubeshi tare da faÉ—in
"Wai cikin wata nawane yace maka Mai sunan malam?".
kamar bazaiyi magana ba jin takuma maimaita tanbayar nata a hankali yamosa lips É—in sa
"Wata ɗaya". yafaɗa a dakile akuma takai ce".............!�

*FREE PAGE YAKUSA KARE WA*😉
*A MATSO A CIGA DA BIYA WAÆŠAN DA BASU BIYA BA SUZO SU BIYA*

Mommyn twins ce

🌺 *HAMDAH*🌺

*NA*

*RASHEEDA S DIRECTOR*

*_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍�*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*
Chapter 49 · 0% Book details