← Book details Hamdah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 62

Sashe 11

Hamdah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da dariya d'auke a bakina nakaraso in'da Salele yake,
Yana ganina yy saurin gyara rikon tiyon hannusa,
Na ce "Salele barka da safiya". Namiko hannu Ina fad'in
"Kawo tiyon natayaka".
Cikin sauri ya ce "a'a 'yargidan Inna kirufamin asiri karkisa narasa ai kina, jiyan nanma bansaniba ko Oga yahakura ko Bai hakura ba, idan yanzu Yakuma fitowa yasameki shikenan nakad'e".

Baki natab'e najuya inafad'in "ohon ku Allah yasa akwai ruwa a bayi".

Ya ce "yauwa yimaza kije na bayin kiyi wasanki hankali kwance".

Nidai ban Kuma kulashiba nawuce a bina,
Ina shiga ciki direct bathroom nashige natub'e kayana nasun kuya zuba ruwa a jikina Saida nagaji Dan kaina kafin nayi wankan soso da sabulu nad'auro towel nafito.

Gaban dressing mirror nazauna,
Mai nashafa sannan nayi simple makeup, namike na isa gaban wardrobe naciro wata doguwar Riga robal material nasaka, sannan nasaka d'an kwalin a kaina batare da na d'aura ba nafito.

Kitchen nashiga na kunna gas nad'aura ruwan zafi, bud'e karamin Fridge nayi nad'au kifi guda d'aya wanda dakyar na'iya ciroshi saboda kankarar da yy duk sun manne da junan su, acikin roba nasaka nabud'e tukunyar Dana d'aura Kan Gas nasaka Kofi nad'ibi ruwan zafi nazuba Kan kifin,
Bayan 10 second duk kankarar jikin sa yazamo ruwa nasiyaye ruwan, sannan nayayyan Kashi gunduwa-gunduwa nakuma wankeshi tsaf nad'au wata tukunyar najuye ciki, d'aya gefen Gas in nakunnan nad'aura tukunyar kifin nazuba Masa ruwa d'an dai-dai.

Nazuba citta na yanka albasa nazuba kana nazuba kayan d'and'ano sannan narufe,
Ganin alamar ruwan zafinnan yafara tafasa ne,nad'auko flakes nazuba ruwan ciki tareda jefamasa Lipton Mai citta narufe flakes É—in na'aje gefe.

Nad'ibi taruhu kwalli uku da albasa 'yar madai-dai ciya na jajjagesu,
Sannan nad'ibi kwai guda hud'u nakad'a na juye jajjagen taruhu da al'basan Nan cikin sa,kayan d'an-d'ano nazuba d'an dai-dai saboda kada yayi yawa, saboda idan yy Masa yawa nasan bazai yi dad'iba.

Bud'e tukunyar kifin nayi, saurin rage gas in nayi ganin yy yadda nakeso yanuna luguf ruwan ciki yakafe, juye kifin nayi cikin wani roba Mai d'an fad'i,
Saida nabarshi yad'an wuce yanda zan iya sa hannuna ciki,kasussuwan kifin nacire gabad'aya sannan najuye kifin cikin kwan Dana kad'a namosa,
Tukunyar tuya nad'aura nasulala Mai Saida yy zafi sannan had'in kwai da kifin Nan nazuba ciki,
Haka narika soyawa kamar waina.

Ina gamawa nakimsa gurin, sannan nakwashi breakfast Ina nakaisu parlour,
Ina Zama cikin parlourn naji ana buga kofar shiga Side in Dake ta babban parlour, Ido nawaro sai Kuma nasauke numfashi tuno cewa kofar a kulle take tun jiya,
Lomar a bincin nakai Baki tare da fad'in "ai kigama yi Allah bazan bud'eba sai kin Sami sauki.

Tun daga wanna ranar kullum side Ina akulle take,
Wasu lokutan zanyi tajin ana bugun kofa ta cikin babban parlour sai dai bantab'a yunkurin bud'ewa ba sanin cewa Aunty Na'ima ce.

Yau kwanana shida a gidan hakan kuwa yy dai-dai da sauran kwana d'aya na koma ayadda nasanyawa kaina iya kwanakin da zanyi a gidan.

Acan cikin garin Dass kuwa,
Zaune Inna take a sakargida bisa Kan tabarba, kwad'awa Fatu Kira tayi, cikin hanzari Fatu tafito daga cikin kitchen, tazo in da take tadurkusa taredafad'in
"Gani Inna". Waya Inna Tamika Mata ta ce
"Ungo maza kiramin Mai sunan Malam yau ace kwana biyu banji halin da 'yarnan ke cikiba, Kullum su Idris surika cemin wai lfyrta Lau,
tana tareda wanna Mai zuciya kamar fad'a wutar, wayasan kalar muguntar dayake shuka Mata".

Murmushi Fatu tayi tareda karb'ar wayar, tun ranar da a kakai HAMDAH Inna ke maganar ko wace hali take ciki, acikin kwana biyun sau uku tana baiwa Fatu waya ta ce takira Mata Abbu da Abba ta tanbayesu wai ya lfyr HAMDA'n, duk San da ta tan bayesu sai suce Mata tana Nan lfy.

Number'n Ya SALEEM ta danwa Kira.

Zaune yake bisa kujerar dining table rike da cup in tea a hannusa yanad'an kurb'a, akai-akai yake kallon gogon Dake d'aure a hannun sa,
Na'ima ko na hakimce a gifen sa yayin da itama breakfast in take, aje cup in yy tareda mikewa tsaye, dai-dai Nan wayarsa tafara tsuwa, Mika hannu yy yad'au wayar dake bisa kan dining in,kamar bazai d'aukaba ganin Mai Kiran nasa, haryau a cike da Inna yake Dan gani yake kamar itace tashirya komai gameda auren, har Kiran takusa katsewa sai Kuma yad'aga.

Jin an d'aga kiranne Fatu tayi saurin mikawa Inna wayar tanafad'i
"Gashi ya d'aga Inna".
Tamiko hannu cikin hanza ta karb'i wayar takaishi kunne.

Ta ce "Assalamu'alaikum Kai Mai Sunan Malam haka ake a gidan ku abaka mata kamar an baka mutuwa, ai dai ni Dana raineta ai kakira kayimin godiya, to baiwa HAMDAH'n waya naji lfyrta".

D'an guntun tsaki yaja a dakile ya ce
"Akan wanna ne zakiwani kirani da sassafen Nan to kikirata Mana kiji lfyrtan saini Zaki Kira".

Ta ce "Dan gidan ku in da tanada wayar da zan tan bayeka lfyrtane, kasiya Mata wayar Mana kaga ko zan Rika kiran naka, iye shegen banza Mai bakar zuciya, kada kakawomin shed'ananci yanzu nahayo mota Nazo Bauchi'n".

Tab'e Baki yy tare da fad'in
"Inko ni zan siya Mata waya to lallai bazata rike wayar ba, yaran yanzu ba'a barsu sun rike wayar bama yasuka kare bare an barsu".

Salati Inna tayi ta ce "yo Mata agidan auren ta harwani dokar rike waya za'ayi Mata? Ai dai duk wani tarbiyyar daya kamata ayimata a gida duk ammata, yanzukam tarbiyyar shizata bazashi wajen yin biyayyar aure,maza Bata wayar ko Kuma in d'ago ubanka Dana Isa da shi yakawo Mata".

Kashe wayar yy yajefata cikin aljuhu yajuya yafara sauka daga step in dining in,
Na'ima da tun farin wayar tabaza kunne tana Jin dagar dasuke, wani murmushi najin dad'i tasake ko ba komai hakan ma yy Mata, takuma gas kata cewa SALEEM natane ita d'aya Dan tanada kyakkyawar tabbaci akan hakan, Dan saboda sanin ko waye SALEEM in da Kuma yanda akayi harta sameshi.
Mikewa tayi cikin kirsa da nufin yimasa rakiya kafin ta an Kara sai ganin fitarsa tayi.

Yana fita motarsa yashiga Yana dai-daita zamansa Kiran Abbu yashigo wayarsa, yad'auka tare da yin sallama,
Abbu ya amsa tare da fad'in
"Akan me Inna zatace kabaiwa HAMDAH waya kk to maza ka kirata ka had'asu".

Numfashi yaja kana ya ce
"Abbu bana gidane idan nadawo zan had'asu".
Ya ce "kana dawowa ka tabbata ka had'asu".
"To".harzai sauke wayar yaji Abbu nafad'in
"Kadai gama shirya Mata komai ko Monday Mai zuwannan yakamata tafara zuwa makaranta".
Dafe kansa yy shi gaba d'ayama yagama mancewa da wanna zance, "Eh". yace sanna yakatse Kiran yaja motarsa yabar gidan, tsaki yarika saukewa akai-akai yajuya akalar tafiyar tasa izuwa wata makaranta dake Nan cikin unguwar tasu, sai dai da d'an rata sakanin su,
Yab'ata lokaci sosai acikin makaran tar Dan Saida yagama Mata komai kafin yafita ransa a b'ace Dan yy lettin zuwa Office.

A hanya yakira Jamilu wani tela ne Wanda yake Bababa plaza Dake cikin kasuwar winti, bayan sun gaisa ya ce
"D'inki nakeso daga Nan zuwa yamma".
Jamilu ya ce "an gama kakawosu yanzu za a fara".
Ya ce "Uniform ne Kai zakaje kasiyo". Yafad'a Masa Sunan makaran tar yace yagane kalar uniform É—in su,sannan yace
"To ai ma bawani d'inki Mai wahala bane awa 3 yy yawa, to Amma bansan girman jikin wacce za'ayiwa d'inkin ba".
Ya ce "bawata babba bace 'yar kimanin shekaru Sha hud'u zuwa Sha biyar ce,batada kiba sosai Kuma ba arame takeba, tanada d'an tsawo dai ba can sosai ba".
Tuni Jamilu yad'auki komai da yafad'a Masa na yanayin girman jikin ta a kwakwalwar sa, kasan cewar kwararran telane, suna gama wayar yatura Masa kud'i wanda zasu ishesa harda saura Mai yawa.

Da misalin karfe 6 yataso daga Office Saida yabiya shagon Jamilu ya amshi d'inkin kafin yanufo gida, Yana shiga gida part in ta yanufa, saboda Kiran da Abbu yy tamasa bayan wayan dasukayi da safe, Kuma yasan fitinar Inna ce kesa Abbu Kiran nashi.

Tura kofar yy yajishi gam, akufule yashiga bubbuga kofar Rai b'ace yakwaso gajiya kamata yy ace Side É—in sa yanufa yawatsa ruwa yahuta, Amma fitinar 'yar tsohuwar nan yasashi dolenshi sai yazo Nan gashi Dan sabar rainin wayo takulle kofar ko mayune cikin gidan ba mutaneba.

Ina tsaye gaban mirror bayan fitowata daga wanka,Jin kakar bugun kofar da ake yasani saurin karasa saka doguwar rigar baccin nada soma sata a jikina,
Nayi saurin bud'e wardrobe na d'au wata Yar karamar gyale nasaka a kaina, duk abin da nake cikin rawan jiki nake,
Gaba d'aya na firgita da kalar bugun kofar da ake,
Sorona d'aya kada ace Aunty Na'ima ce ke kokarin b'alla kofarnan tashigo ta kasheni, sabar firgici ban San San da nafito cikin parlourn ba,
Shiru nayi Jin bata kofar babban parlour ake bugawa ba, ta asalin takofar Side in ce, ahan Kali nasoma taku duk da kuwa kwab'e ni da zuciyata take Kan cewa Na'ima'n ce tazo ta wanna kofar Dan nabud'e tasamu tashigo, tsayuwa nayi daf da jikin kofar Jin shiru an daina bugawa,
D'an d'aga muryata nayi na ce

"wanene?".

Cikin tsawa ya ce "Zaki bud'e kofarne ko ya!".

Wani irin kad'awa anjin cikina yy da sauri na murza key in tareda murd'a handle, turo kofar yy da karfi kasan cewar Ina daf da kofar Kuma nad'an sun kuyo da kaina yasa kofar yabigi goshina, baya nayi luuu tareda saka Kara nadafe goshina,
Natafi da baya luuu nagaru da gijin garu still kaina yakuma garuwa da jikin garun, wani Karan nakuma sakewa tare da rike kaina da hannuna biyu Ina jujjuya Kan Jin wani irin azabar zafi da sarawar da Kan keyi, shigowa cikin parlour'n yy cikin d'aga murya ya ce "I...........

Mommyn Twins ce

*🌺HAMDAH🌺*

*NA*

*RASHEEDA S DIRECTOR*

_(Book one)_

*_________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍�*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*_________________________________*

MARUBUCIYAR👇🏻
*BA ABIN DA BAN GANI BA*
*INA SANE DA HAKA*
*ALFARMA*
*BAZAWARA CE ITA*
AND NOW👇🏻
*HAMDAH*

*Fee page*

My no 08034690723

🅿�8

"Idan Baki rufamin bakiba saina Kuma had'a Kan naki da garu yarab'e gida biyu!".
Cikin hanzari nakai hannu Kan Baki na hawaye yasoma zarya Kan fuskata.
Chapter 11 · 0% Book details