Sashe 24
Hamdah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
murmushi mai sauti nayi jin Aunty Hafsat tana cewa "Kaga Æ´argidan Inna girma yazo babu tsalle-tsalle".
dariya Umma Habiba da Mamie sukayi kana Umma Habiba tace
"Ai kam É—iyata an girma yau she zaki zo mana Maiduguri".
nace
"Sai Alhj Dikko yamutu zanzo". dundu Umma Habiba tasake min a baya tana faÉ—in "Baza muga mutuwar shi yanzu ba dan wata naki".
mikewa nayi da gudu nayi cikin bedroom É—in Aunty Jaleela ina dariya da faÉ—in "Akan wannan tsohon Umma zaki karya min baya dan muzama iri É—aya da shi".
Acikin bedroom ɗin Aunty Rafee'at ce da Aunty Jaleela da kawayen su tam ciki, ina karaso wa ciki na saɓi jariri yar da ke kan kafar wata kawar Aunty Jaleela, hotuna nashiga yi mata nakuma ba da wayan a ka ɗaɗɗauke mu tare.
Bikin suna yayi kyau sosai an ci an sha,sai wajen magriba a ka fara watsewa,
tunkafin magriba Dr Faruq mijin Aunty Rafee'at yazo yaÉ—au keta sukayi gaba,
Iro drever shi yazo É—au karsu Mamie dan haka nabi motar su muka wuce state locos tare.
Muna isa direct part É—in Ummi muka wuce ni da su Umma Habiba,
A bedroom muka tadda ta,nan kowa yafara shirin sallah,
nidai zama nayi bakin gado dan ina fashin sallah,
Hotunan da nayiwa jaririyar Aunty Jaleela nashiga laluɓowa cikin wayata ina faɗin
"Ummi kinga yarin yarnan kuwa kyakkyawa fara soll Allah naji haushin da a ka aske mata gashi, gashin ta mai yawa suka kama sukayi mata aski".
Ummi tace
"To in ban da haukarki sai a bar mata gashin ai dole sai an aske in ma suka bari dan gaye ai sunyi wa kansu dan nan gaba kaɓewa zaiyi a bunshi".
Wayar na mika mata nace "Kalleta fa kigani Ummi
Allah naga alama yarinyar nan idan tagirma kama dani zatayi, in lokacin gashin ta yayi yawa kamar nawa".
murmushi Ummi tayi tana duban hotunan,
Umma Habiba da ke zaune kan sallaya bayan ta'idar da sallah tace
"Uhum kinbi kin damemu da maganar wannan mummunar yarinyar".
Aunty Hafsat da fitowar ta daga bayi kenan ta amshi zancen da faÉ—in
"Ai kam mummuna kam ina wani ƙyan a nan har Asmah tafita kyau".
Baki na buɗe najuyo ina kallon Asmah ƴar Aunty Hafsat ɗin dake ƙwance tana bacci a gefe na,
kumatun ta naja tare da dungurin goshin ta nace
"Haba Aunty Hafsat kirasa wacce zaki haÉ—a ta dashi sai wannan mummunar yarinyar mai katon kumatun Allah yasa wake mata".
Da sauri Aunty Hafsat ta karaso bakin gadon tasoma jijjiga Asmah da ta fara motsi,tace
"Hannunki sai ya makale kika kara dungurin ta ai ko ke bazaki haifo kyakkyawar yarin ya kamar ta ba".
Fuska na yamusa nace
"Allah in dai kamarta zan haifa gara ban haihun ba".
nafaÉ—a ina mikewa,
ido Ummi tabi bini da shi tana faÉ—in "Allah yashirya".
Ni dai jakata na É—auka nashige bayi dan na kimsa jikina,
Koda nayi wanka kayan jikina na mayar nafi babu kowa cikin ɗakin duk sun koma parlour,sai na haye gado nayi ƙwanciya ta,
ƙwanciya ta baifi da minti 10 ba Ummi tashigo haɓa tarike tana faɗin
"Au ƙwanciya kikayi?to tashi maza gacan Iro na zaman jiran ki nayi masa magana zai mai daki gida".
nace "Ummi a daren nan kawai sai gobe zan tafi".
"Ai to shikenan cigaba da ƙwanciyar har Abba'n ku yazo yasa meki yarage naki".
Mikewa nayi naja jakata da mayafina nabi bayan ta ina bubbuga kafafuna a kasa.
Ko da muka fito parlour Sallama mukayi dasu Umma Habiba sukace idan Allah yakaimu gobe zasuzo min, sa sabo da jibi suke so sukoma Maiduguri.
Har gun mota Ummi ta rakani har sai da taga fitar mu kafin takoma,
Muna isa nafito daga cikin matar Iro yajuya nikuma na nufi ciki,na É—ago kafata zan É—aura saman step É—in da zai sadani da cikin part É—in, nayi saurin mai da kafata kasa cikin hanzari najuyo jin muryar sa a baya na yana faÉ—in.
"Ina kiƙa fito?".
tsayuwa ta nadaɗa gyara wa dan ba shakka na razana daganin sa a nan ƙwata-ƙwata ni ban ma lura da yana gunba,
"Ina kika fito".
Yakuma jefomin tambayar.
"Gida". nafaÉ—a a takaice,
fuska ya suke kana yace
"Wakika tambaya da zaki fitan".
shiru nayi a kan raina nace
"To in zan fitan wa zan tanbayan in kuma shi yake nufi to a ina zan ganshi har na tanbayan".
Ƙwafa yayi tare da juyawa yasoma tafi batare da yace komai ba. da sauri na haura nashige ciki.
Washegari bayan naga ma gyaran ko ina nacikin side É—in nashiga kitchen domin kirkawa su Aunty Hafsat abinci kafin su iso.
Gas na kunna na É—aura tukunya tare da zuba masa ruwa É—an dai-dai, sannan na É—auki É—an ma dai-dai ciyar rubo na je in da fridge yake nabuÉ—e na É—ibi koda, na a je gefe kana naÉ—au wata robar albasa da tumatir da attaruhu na É—iba cikin ta,na aje kusa sannan na É—auko garin tafarnuwa maggi kori garin citta man gyada koren tattasai,duk na aje su kusa.
Nazuba ruwa cikin robar kodan na wanketa tafita fes. Sannan na yayyanka ta kanana sai na zuba a cikin tukunya tare da É—an kara zuba mata ruwa kadan saboda ganin nacikin tukunyar yaÉ—an kone, na rufe.
sai da ya fara nuna har ruwan cikin yakafe sai na wanke kayan miyar na yayyanka albasa da taruhu da tumatir É—in nazuba a ciki, na sa maggi da garin tafarnuwa da garin citta kadan, Sannan na rage wuta sai na shiga gaurayawa inayi ina zuba man gyada wan da nariga da na soyashi É—an dai-dai na zuba iya yadda nake bukata kana naci gaba da juyawa har sai da albasa da tumatir da attarugu nan suka nuna,sannan na sauke. tuni kitchen É—in yagar waye da kamshi.
Wata tukunyar na É—aura nazuba ruwa ciki na É—auko couscous na a je kusa.
numfashi na sau ke tare da rike kugu ina bin in da na ɓata da kallo, a sannu na sunkuya nashiga tattara gurin,na junkura zan mike saiji nayi a bu yafaɗo a baya tim,
Wani irin kara nasake cikin tsananin tsoro da firgici da kaÉ—uwa nakuma zandara wani ihun jin yadda naji faratun a bun ya karceni a baya,sai narika jin yana tafiya cikin rigana yanayin kasa,
Wani uban tsalle natuma nayi gefe, sai ga kadangare yafaÉ—i kasa tim, nan take naji numfashi na nakokarin barin jikina, da mugun gudu nafice cikin kitchen É—in nayi waje a guje bana ko ganin gabana,mafaka kawai nake nima dan jinake kamar kadangaren na jikina,kofa nagani kawai a buÉ—e wan da a cikin yanayin da nake ciki bazan iya tan-tan ce wacce kofa bace nakusa kaina ciki,
Yasa kai zai fito dai-dai lokacin nasako nawa kan sai ji nayi na garu da jikin sa,kara na sake nayi baya cikin kiɗi ma yayi hanzarin riko hannuna,kokarin fizge hannun nake ina jujjuya kaina cikin kiɗima da tashin hankali,yakuma rike hannuna da ƙyau yana faɗin
"Ke meye haka?".
jin muryar sa yasani buÉ—e idanunna sai kawai nafaÉ—a jikin sa na kankame shi tare da sakin kuka mai sauti.
baya yarikayi a hankali har yakoma ciki yamai da kofar yarufe kana ya zaroni cikin jikin sa yana cewa
"Ke wai menene hakan?dubi yan da kika fito".
yafaÉ—a yana zama kan kujera, bai kaiga rufe baki ba na faÉ—o kansa na kankame shi da karfi na cusa fuskata cikin kirjinsa cikin muryar kuka nace
"Ya SALEEM kacire min kacire min dan Allah wayyo Allah na kacire min Ya SALLEM yana cikin rigana yana bayana wayyo Allah naaa!!!".
Nakuma kankame shi da iya karfina nake cusa jikina cikin jikin shi.
Cikin rashin fahim ta yaÉ—ogo hannun sa yasau keshi kan bayana
"Meye a cikin rigan naki?".
yafaÉ—a murya can kasa, cikin jan shashsheka nace
"Kadangare kadangare ne yana cikin rigata".
A hankali yarika yin kasa da hannunsa yasau keshi kan zip É—in rigata, yasoma yin kasa da shi har yakai karshe sai ya É—an É—ago yakuma sa hannayen sa biyu yaware rigar.
Ido yatsurawa bayana sai kuma yasaka yatsar sa yana bin in da shatin faratun kadangaren ya karceni,gantsare wa nayi tare da kuma kankame shi nace
"Shine kacire min kacire min dan Allah".
nafaÉ—a cike da muryar tsoro nakuma cusa fuskata sosai cikin kirjinsa.
Numfashi ya fesar tare da faÉ—in
"Ke ni banga komai ba, da kadangare sai ya zauna a jikin ki kiyita wannan tsalle-tsallen da shi".
nace
"Ya SALEEM kataɓa shi fa shine".
"Ni ban taɓa shiba shatin faratun sa na taɓa".
YafaÉ—a yana cigaba da tafiya da yatsarsa kan zanen ciwukan da faratun kadangaren yayi min.
Numfashi nasauke da jin hakan na ɗan sami nutsuwa, sai na mike a jikin sa,na zauna gefe da shi na rakuɓe guri guda ina wiki-wiki da ido, gaba ki ɗaya jikina wani irin yam-yam yake min musamman raɗaɗin da nake ji a bayana, sai ji nake kamar kadangaren ne ke tafiya cikin bayana.
Mikewa yayi yashige bedroom ɗin sa niko sai daɗo rakuɓe wa naji jikin pillow'n kujera.
ya É—an jima sosai cikin bedroom É—in sai gashi yakuma fitowa da wasu kayan da ban a jikin sa bana É—azu da suke jikin saba.
Bin in da nake rakuɓe yayi da ido yayi mamakin ganina har lokacin zaune a gon.
"Zaman me kike baki tafiba".
yayi maganar ida nunsa kan agogon da yake É—aura wa a hannunsa,
rau-rau nayi da ido cikin rawar murya nace
"A kwai kadangare ne".
É—agowa yayi ya kalleni sai kuma yacire idanunsa a kai na yajuya yayi waje.
Yana fita direct parlour'n ta yanufa can bakin kofar kicin yahangi ɗanƙwalin ta yashe a gun,a sannu yatako ya'iso gurin daga in da yake tsaye yana hango cikin kitchen ɗin, in da ya hargitse gaba ɗaya kamar an yi dambe a gun, tsaki yaja yatako ciki yana cigaba da bin kitchen ɗin da kallo, can yahangi katuwar kadangare manne a jikin garu ganin window'n kitchen ɗin abuɗe ya tabbatar masa da tanan ne kadangaren yabi yashigo.