← Book details Hamdah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 62

Sashe 40

Hamdah Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Mikewa nayi nashiga bayi nayi wan ka tare da auro al'wala zanin kayan da na tuɓe na ɗaura, nafito gabatar ba tar da sallar magriba na ɗaura da sallar Isha da yanzu a kashiga.
koda na idar gyale na nasaka a kaina na rufe jikina sabo da kaya na nabarshi cikin motar kuma nasan ko naje gun motar ma a kulle take.
parlour muka dawo muka yada zangon mu,
in da Fatu tashigo da kulolin abinci da ta girka,nan ta zauna muka cigaba da hira.
Sai wajen karfe 8:30 Ya SALEEM yashigo,
bayan sun gaisa da Inna yamike,
Inna tadube shi ganin na shirin barin parlour'n tace
"Kai mai sunan malam zauna kaci abin ci mana".
kofa yanufa tare da faÉ—in
"Nakoshi".
da sauri na mike nace
"Ya SALEEM kayana a mota zan É—auka".
waje yayi batare da yace komai ba ganin haka yasani bin bayan sa da sauri,ina fita na hango sa jikin kofar side É—in sa na cikin gidan ya zura key yabuÉ—e yashige ciki, da sauri na nufi gun
koda nashiga cikin parlour'n baya ciki dan haka nanufi kofar bedroom na tura na shi,
nan ma baya nan É—an tsayuwa nayi zuwa can naji motsin ruwa a bayi.
numfashi na sauke nabi É—akin da kallo a gyari tsaf kamar a kwai wan da ke rayuwa a cikin sa, wannan ai kin Inna kenan dan ko da da nake gidan duk sati sai tasa an buÉ—e side É—in mun share, haka zanyi ta mita nace ba mai kwana ciki tasa mutane suta wahala shida yakan fi watanni nawa ma bai zoba.
Ina nan tsaye yafito ɗaure da towel a kugun, sa kai na langwaɓar gefe
"Ya SALEEM kayana a mota nayi wanka ban sa kaya bafa kabani key na É—au ko jakar".
ido yaÉ—an tsuramin sai ya zauna bakin gado ya janyo É—an ma dai-dai cin jaka dake kan gadon yabuÉ—e,ido na waro ganin yazaro doguwar rigar bacci na da jallabiya da boxes É—in sa,
mamaki ne ya kamani taya akayi kayana yazo cikin jakarsa ban idda tunani na ba yakuma ciro Wani riga da siket É—ina na les haÉ—e da gyale da bra da pant,ya ajiyesu gefe
kana yaÉ—au rigar baccin ya mika min yana faÉ—in
"Karɓi kisa, wannan shi zakisa gobe".
yafaÉ—a yana nuna kayan da ya ajesu gefe,
tsayuwa na yi ina kallon sa da mamaki batare da na amshi rigar ba,
hannuna yariko yazau nar dani gefen sa,yagyara zaman sa yazamo muna fuskantar juna,ya janye gyalen kai na ya ajeshi gefe,kana ya kunce zanin da ke É—aure a kirjina yayi kasa dashi,
Ido ya tsurawa ababen kirjina a sannu ya kai hannunsa kan su yashafasu, kana yaÉ—a go rigar a hankali yasoma samin koda yasaka min, sai ya
mike ya É—au boxes É—in shi ya saka kana ya haye gadon tare da janyoni na kwanta gefen sa.
ya zura hannunsa cikin bra'n rigar yaciro ababen kirjina, yana É—an shafasu,ganin salon nasa yafara sauya wa sai nayi saurin kai hannuna kan cikina na shafa tare da faÉ—in
"Wash yunwa nake ji".
É—an sakai ta abun da yake yayi yaÉ—an É—ago yana kallon fuskata kana a sannu ya mosa lips É—in sa
"Bakici abinci ba?".
yafaÉ—a yana shafa cikina,
kai na gyaÉ—a da sauri
"Ok zo kici".
yafaÉ—a yana mikewa tare da É—agoni ya sauko a gadon,wata laida mai É—an girma dake kan bedside ya É—auka kana ya zauna kasa kan carpet yabuÉ—e laidar yashiga fiddo da kayan ciki,
gasheshshiyar kazace wacce taji gashi na musamman tasha kayan É—anÉ—ano da na kamshi,sai drinks har kala biyar.
ya dubeni kana yace
"Zo kice".
fuska na ɗan kwaɓe dan banso ace akwai wani abun ci a ɗakin ba dan tanan ne zan sami hanyar guduwa,
A hankali nazamo bakin gadon nasauko nazauna gaban sa tare da tanƙwashe kafafuna kamar yadda naga yayi,yagar naman yayi yakai bakin sa tare da yi min a lama da ido,a sannu nakai hannu nasoma ciki,ban wani ci mai yawaba nazare hannu na dan akoshe nake,
ido yaÉ—an zubamin kana yace
"Ci mana".
da sauri nace
"La na mance É—azu Ummi ta kirani ina sallah nakuma mance da na idar ban bi kiran ba, bari naje na É—auko wayar".
nan ma idon yatsura min kana ya gyaÉ—a kansa a hankali, da sauri na mike naÉ—au gyalena na rufa kaina nafita nanufi sashin Inna da sauri.
Direct É—akin Inna na shige a kwance na tadda ta tuni har tayi bacci numfashi nasauke a hankali nahaye gadon na É—au wayata nakashe ta gaba É—aya na kwanta...

washegari da asuba ana sallah a masallaci nafito na nufi É—akin sa dan nasan yanzu yana masallaci, kayan da yacire min jiya yace shi zan sa yau naÉ—au ka nafito da sauri nakoma sashin Inna...
da misalin karfe 11 tuni nayi wanka nashirya cikin kayan muna zaune a parlour yashigo,
sanye yake da kananun kaya
wandon jeans da t-shirt yellow,
yana shiga parlour'n ya baibaye da kamshin sa,
shaƙar kamshin nayi tare da lumshe idanuna nakuma buɗe su kamshin Ya SALEEM a kwai daɗi.
É—agowa nayi bayan sun gama gaisawa da Inna,ina É—agowa na sinci idanunsa a kaina,
"Ina kwana Ya SALEEM".
nafa ina janye idanunna a kanshi dan bana iya jurar kallon nan nasa mai sani narika jin wasu abubuwa suna tsargamin a cikin jiki sai naji duk kasala ta rufeni.
ya amsa gaisuwar
yana mike wa tsaye,bayan ya fita da É—an jimawa kaÉ—an muka fito da Inna dan dama ita nake jira tun É—azu tace na jira ta mutafi gidan su Rabi tare da natafi tun É—azu,ko da muka fito banga motarsa ba
"Ko ina yaje?".
nayi tan bayar a raina.
Muna tafe muna hira da Inna duk wan da muka haÉ—u da shi in har yasan ni ko Inna sai ya tsaya yayaba girma da kyan da na kara, har muka iso gidan wan da yacika da Æ´an biki tam,
Maman Rabi na ganin mu tataso daga cikin mutanen da suke zaune tatare mu tana faÉ—in
"A'a wanake gani haka an ya HAMDAH ce ko kama ce".
murmushi nayi tare da faÉ—in
"Ina yini Mama".
da gudu Rabi dake cikin É—aki da kawayen ta tafito tana faÉ—in
"Mama HAMDAH naji kamar kikace".
da sauri na juyo jin muryar ta ai ko da gudu tataho in da muke muka rungume juna cike da kewar juna muna dariya.
gaba É—aya idon jama'a yadawo kanmu wan da suka sanni kowa sai yabawa da san barka suke,
Rabi tajanyo hannuna muka shige É—aki in da kawayen ta suke, mutane biyu na sani acikin su suma dan Æ´an unguwar mu ne dan ni tun tasowa ta kawata É—aya ce itace Rabi'n,
Nan muka shiga hirar yaushe gamo acikin hirar nake tanbayan ta yaya lambun Baba na lambu,
dariya duk musa saka na tuno da baya, tace "Yana nan ko jiya ma a lambun sa muka tsiyo kayan miya, nace
"Allah sarki in sha Allah kafin na koma zanje na gaida shi"...�
Chapter 40 · 0% Book details