← Book details Hamdah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 62

Sashe 48

Hamdah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Koda muka isa na sauka nabiya mai adaidai kuÉ—in sa na shiga cikin gidan direct part É—in Ummi na nawuce,da sallama nashiga parlour'n cike da É—okin ganin ta.
Aunty Jaleela Fauzan Nusaiba Fadil babban yaron Aunty Jaleela Ummi duk suna zaune cikin parlour'n kasan cewar yau Saturday.
da gudu Fauzan Nusaiba Fadil suka taso suka rungume ni suna ihun murna,
Nima rungume su nayi cike da son yaran kana na janyosu muka karasa cikin parlour'n,
Muka zube saman kujera kusa da Ummi,masawa gefe Ummi tayi tana faÉ—in
"Jimin sha-shan ci zasu karya min kafa". fuska É—auke da dariya nadube ta ina faÉ—in
"Kai Ummi karya kafa kuma".
Aunty Jaleela dake baiwa Feedrah nono ta harareni tare da faÉ—in
"Ai HAMDAH hankalin ta É—aya dasu babu girma sai na jiki".
baki na murguÉ—a mata naruko hannun Ummi nace
"To ina Ummi na ne".
tace "To sai ki karya ta ki huta".
ido na waro nace
"Cap bakin ki ya tsari kuntun a yaba".
Ummi kam ido taÉ—an tsuramin kamar mai son gano wani abu,
sake hannunta nayi na mike ina faÉ—in "Fauzan Nusaiba Fadil kuzo muje sashin Mamie".
naɗau Feedrah data saki nono tana ta juyo kai kamar mai jin abun da ake faɗa na saɓe ta a kafaɗa muka nufi kofa.
Aunty Jaleela tace
"Ai gara kuyi tacan daga zuwan ki kincike mana guri da surutu".
gyara rukon Feedrah nayi ina faÉ—in
"Ai zan dawo ma"....

A parlour muka iske Mamie zaune,ta É—ago da murmushi tana amsa sallamar mu,hannu ta miko tana faÉ—in
"Kawo min kishiyar nan nan na rankwashi kanta É—azu sun shigo da ma ashe baccin gangan take".
dariya nayi ina zama gefen ta tare da gaishe ta,ta amsa fuska ɗauke da murmushi ta karɓi Feedrah tana faɗin
"Zo nan mai gajeren hanci".
"Kai Mamie mai dogon hanci dai, tazo nunawa Abbu kwalliyar tane".
Mamie tayi dariya tana faÉ—in
"To ai sai ta koma babu abun da zaiyi da kwalliyar tata".
Da gudu Nusaiba ta mike tanufi É—akin ta tana faÉ—in
"Bari naje na É—auko pawda a kara shafa mata".
nace
"Yauwa yi sauri".
har ta isa kofar É—akin ta sai ta juya tanufi kofar bedroom É—in Mamie tana faÉ—in
"Bari na É—auko na Mamie a shafa mata".
dariya mukayi dukan mu ta shige ɗakin tafito ɗauke da pawda, karɓe pawdar Mamie tayi tana faɗin
"Ai ba kalar ta bane wannan"....
Mamie tarika zolayar Feedrah tana cilla ta sai dariya take ganin ana ta yi mata abun da take so wato rawa da cilla ta sama.
Muna zaune har aka kira sallar azahar,
Mamie tace Fauzan ya kama Fadil sutafi masallaci dake nan kofar gida,
ta mikawa Nusaiba Feedrah tace
"Rike ta ke HAMDAH kije kiyi sallah sai ki dawo ki riketa sai taje tayi itama".
tafaÉ—a tana mikewa,
mika hannu nayi na amshi yarinyar nace
"Je kiyi sallar".
nafaÉ—a ina duban Nusaiba,
dubana Mamie tayi tare da faÉ—in
"A'a je kifara yi ke sai kizo kici abin ci".
kasa nayi da kaina tare da É—an murza yatsuna nace
"Ni nayi". ido Mamie ta É—an tsuramin na lura tun shigo wata irin wannan kallon take ta bina da shi irin dai kallon da Ummi tayi min É—azu, kai ta jinjina kana tace
"Ai ho to shikenan".
tafaÉ—a
É—an jim tayi idanunta a kaina kana tace
"Amma dai baki da lafiya ko? naga kin É—an zuba kaÉ—an".
Kai na girgiza alamar a'a
juyawa tayi bata kuma cewa komai ba tashige É—aki tana faÉ—in
"Je ki zubo abinci a kitchen".
"To. nace,
A file na furta
"Ba dole na rame ba jinin jikina na ta kan tsiyaye wa, dan dai wannan jini bana al'ada bane".
numfashi na sauke ba shakka ni kaina inajin ƴar ramar da nayi har da haske ma kuwa sai dai nasan ba komai bane yasani yin rama da hasken face wannan jinin dake zuba babu ko kakkautawar,a ƴan kwanakin kuma zazzaɓin dare na yawan damuna sai dai duk na alakanta hakan da wannan zuban jininne.
yau ma nayi niyyar yin wanka naci gaba da ibada na dan dai nasan wannan jinin shine jinin ciwon da ake faÉ—an nan kuma nasan shi baya hana yin ibadar Allah...
Bayan naci abincin sashin Ummi muka koma muka yada zangon mu a can sai yamma barista Aliyu mijin Aunty Jaleela yaza ya É—auke su.
tun a lokacin Ummi tace nima na shirya natafi nace mata ni kwana zanyi, faÉ—a takama yimin wai dan Ya SALEEM baya gari shiya nace zan kwana wata mace ne naga take yin haka kowa ma in mijinsa yayi tafiya zama yake a É—akinsa batare da yaje ko ina ba.
ni dai É—aki na shige naje na sarkake jikina nagabatar da sallar magriba da yanzu a ka kira......

Ina kwance a kan gadon Ummi kiran Ya SALEEM yashigo wayata,a hankali naÉ—aga kiran tare da yin sallama,shiru yayi bai amsa sallamar ba bai kuma yi magana ba har na fara tunanin ko kiran ya yanke ne, ina kokarin ciro wayar najiyo muryarsa
"Wa kika tanbaya kika fito *HAMDAHHH*".
shiru nayi ina daÉ—a gyara rukon wayar a kunnena,
a hankali yakuma furta
"Dare yayi yanzu kikwana amma gobe kikoma gida kada ki kuma fita sai da sanina in ba School zaki ba".
da sauri nace "To".
jin yace nakwana koma ya akayi yasan nazo oho....

Washegari da yamma yakirani yace nakoma gida sabo da gobe Monday a kwai School.
ganin bana da niyyar tafiya yasa Ummi korani dan a gaban ta mukayi wayan tasa direba ya mai doni gida....

★★★★
*After 2 week*
★★★★

Hakan yayi dai-dai da watan Ya SALEEM 1 kenan da tafiya,har kuma yau wannan jinin nanan nazuba min sai dai bakamar na sauran kwanakin da suka wuce ba, yanzu nakan wuni jinin bai zuba ba sai idan dare yayi sai ya dawo wani sa'in ma har na kwanta bacci bazan ganshi ba sai da asuba idan natashi yin Sallah sai naga É—igonsa a pant É—ina,
zazzaɓin daren kuwa sai ma karuwan da yake daɗayi,yanzu ba dare kaɗai ba har da rana yana yimin,
Yau tun a makaranta nake jin wani mugun sanyi har jikina na rawa haka na dawo gida da zazzaɓi mai zafi a jikina,
da kyar na iya cire uniform nasa wani doguwar riga mara nauyi na haye gado,duk yanayin juyawar zafi irin na Bauchi da aka fara amma Ni ji nake kafar acikin fridge nake tsabar sanyi.

Wani irin sanyi nake jinsa har cikin soka da kashin jikina, har dare ina rufe ruf,
ina jin wayata nata ringing tun É—azu amma bana jin zan iya tashi bare har na iya É—au kar kiran,
dakyar na iya miko hannuna in da nafi tunanin wayar tana gun na laluɓo ta na ɗauka.
koda na É—aga kiran ban iya kai wayar kunnena ba sai aje shi nayi daf da fuskata, can najiyo muryar sa yana faÉ—in
"Hello *HAMDAHHH*".
sai da ya nanata kalmar har sau uku.
idanuna na rumtse sai ga hawaye sharr cikin tsananin jin azabar ciwon da nake ciki murya na rawa nace
"Na..na.na'am".
sai kuma na fashe da kuka
da sauri yace
"Ke menene me ya faru??!".
kukan na cigaba da yi kuka irin na wan da yake cikin jin azabar ciwo,
cikin muryar damuwa sosai yaci gaba da faÉ—in
"Meyasa me ki menene??!".
yafaÉ—a cikin É—an É—aga sauti,
ida nuna na rumtse da karfi jin jiri na fizga ta
a wahalce nace
"Sanyi sanyi sanyi nakeji Ya SALEEM wayyo Allah na".
"Ya salam!".
yafurta cikin É—aga sauti.
kife fuskata jikin pillow nayi na daÉ—a dukunkune jikina cikin blanket ina fidda numfashi'n wahala,ina jiyo muryarsa yana ta magana sai dai bana fahimtar me yake faÉ—a yanzu...
ranar haka nakwana cikin matsanancin zazzaɓi kamar zai buɗa min ƙwaƙwalwa,
washegari da misalin karfe 9 inanan kwance kamar jiya dan ko sallar asuba ban iya tashi nayi ba..
da karfe a ka turo kofar cikin zafin nama nake jin taku cikin É—akin sai kuma wani sassanyan kamshin dake daÉ—a matsoni,
idanuna na rumtse a wahalce,cike da tsoron jin takun mutum cikin É—akin kukan azaba haÉ—e da tsoro na sake, a bakin gadon a ka zauna sai naji ana Jan blanket É—in da na tukuikuye ciki,
kuka nakuma sakewa duk da sautin muryata baya fita sosai nakuma kankame idanuna sosai.
da sauri a ka janye blanket É—in sai saukar hannun mutum naji a kan kirjina zuwa gefen wuyana,
cikin sananin tashin hankali nashiga yunkurin mikewa duk da nasan abune mai wuya na iya mikewan.
"Subhanallah ya akayi haka zafin jikin yayi yawa!".
muryar sa ce ta doki kunnena da mamaki tsoro da wahalar da nake ciki nashiga buÉ—e idanuna na sauke idanuna akansa,
Kyakkyafta idon nayi dan son tan-tan ce shi É—in ne koko gizo ne.

Shi ko cikin hanzari yashiga ɓalle boturan rigar sa yazame rigar a jikin sa tare da cire singlet ɗin ciki, da sauri yakai hannu yaɗa go ni gaba ɗaya daga kasa yariko doguwar rigar dake jikina yazare shi ta sama rigar ce kaɗai a jikina babu ko bra sai pant kawai, cikin hanzari ya haɗani da jikinsa ya rungume ni sosai ya cusani cikin jikinsa,
wani irin numfashi na sauke jin É—umin jikin sa,sai na daÉ—a lafewa sosai cikin jikin nasa ina sauke numfashin wahala,
shi ko shafa kaina zuwa baya na yarika yi,
mun jima sosai a haka kana a hankali yaciro ni cikin jikin sa yakwantar da ni tare da jan blanket yarufe ni, da É—an sauri yamike yashiga bayi zuwa can yafito ya É—aukeni yanufi bathroom É—in dani yadire Ni cikin bathtub da ya cika ruwa cikin sa a hankali na lumshe idanuna ina mai jin daÉ—in ruwan É—umin da ya saka ni ciki,a hankali narika sauke numfashi akai-akai,zuwa can yaÉ—au sabulu yashiga wanke min jikina ko ta ina ya wankeni tsaf kana yanaÉ—oni cikin towel yafito dani,har lokacin idanuna a lumshe suke dan nagaza buÉ—e su jin wani irin jirin dake fizga ta.
Chapter 48 · 0% Book details