← Book details Hamdah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 59 OF 62

Sashe 59

Hamdah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sama-sama nake jiyo maganar tasu sai kuma na mike da sauri ina kokarin durowa a godon,
Mamie tace
"Tsaya HAMDAH ki nutsu kinji".
tafaÉ—a tana mai dani zaune ido naÉ—an tsura mata,sai ta gyaÉ—a min kai tace
"Zauna ki huta,zakici abin ci?".
kai na girgiza mata,tace
"To in haÉ—a miki tea kisha ko kaÉ—an ne ko HAMDAH kisha kaÉ—an kawai".
shiru nayi,sai ta sake ni ta juya kan bedside É—in da kayan tea suke jere agun tashiga haÉ—a wa kana ta miko min cup É—in tana faÉ—in
"Karɓi kisha kinji?".
tayi maganar cikin muryar lallami.
A hankali na miko hannu na karɓi cup ɗin nakai bakina wani irin bugawa naji zuciya ta tayi da sauri na ciro cup ɗin batare da na kurɓi tea ɗin ba,na aje cup ɗin kan bedside na mike da sauri yayin da nake jin kaina
yana wani irin juya min da mugun sara min.
muryar Mamie naji tana faÉ—in
"HAMDAH hakuri zakiyi zamukuma yi baki É—aya Inna kwana ya kare yanzu addu'ar mu shine kaÉ—ai tafi bukata a yanzu".
da sauri na kalli ta cikin fizgar numfashi nace
"Mamie da gaske wai Inna rasuwa tayi bazan sake ganin taba daga yau kuma bazata tafi da niba zata bar ni a nan".
Wasu zafafan hawaye ne suka shiga zubowa Mamie tace
"HAMDAH duk wani wan da kika gansa a duniyar nan tofa karshen sa kenan yanda mukazo da É—ai-É—ai haka zamu koma lokacin Inna ne yayi mutuwa akwai zafi amma hakuri shine maganin".

Zuwa yanzu bana gane mema take faÉ—a da sauri na nufi kofa ina ji tana kira na tuni nayi waje da gudu na nufi side É—in Inna,
a guge nafaÉ—o cikin parlour'n har lokacin mutane na nan dam dan sai karuwa mutane suke daÉ—a yi,
É—akin Inna nashige da gudu nafaÉ—a saman gadon ta sai a lokacin naji wani irin kuka sai kawai na fashe da wani irin kuka mai karfi cikin sananin tashin hankali.

Hankali tashe su Ummi da wasu daga cikin mutanen da suke zaune cikin parlour'n suka rufamin baya Ummi na kokarin hanani kukan,
wata Æ´ar baffan su Abba Aunty Halima tace
"A'a kada ki hanata kuka kibar ta tayi shine samin sassaucin zuciyar ta, É—azu ai kasa yin kukan tayi barta tayi kukan zuciyar ta zai É—an sami sassauci"...
kukan nake babu kakkau tawa har numfashi na nawani irin tafiya yana dawowa kamar zan shiÉ—e...
nakai tsawon awa guda ina kukan zuwa lokacin har muryata ta toshe bata fita da karfi. sai a lokacin suka shiga rarrashi na amma ina bana ko jin abun da suke fa....

A ɓangaren Ya SALEEM kuwa yanzu da muwar sa ta kasu kashi biyu,har suka isa makabarta yana tunanin yanzu wani hali take,ɗaya ɓarin zuciyar tasa kuwa ɗin bin damuwar rashin Inna ne aciki,
Kakar su abin alfaharin su yau sun rabu da ita rabuwa na har abada.
har aka kamla bisu suka juyo yana alla-alla ya'iso gida yaga awani hali take yanzu.
koda suka iso gida kan cewar har lokacin da mutane a kofar gidan ga waÉ—an da suka dawo daga makabarta sai ya faka motar a in da yafaka É—azu yafito yashiga cikin gidan da sauri,
direct part É—in Mamie yawuce ganin basa nan sai ya fito ya nufi part É—in Inna,
haka yakusa cikin jama'ar yashige É—akin inda yake jiyo sautin kukan ta,
nan ya iske su Ummi suna ta faman lallashin ta a sannu ya raɓa gefen su suka bashi hanya yakarasa bakin gadon,
" *HAMDAHHH*".
yakira sunana a hankali,ban amsa ba sai dai sautin kukan da naÉ—an rage dan zuwa lokacin wani irin masifaffen ciwon kai nake ji,
a sannu ya mika hannu yakamo nawa yaÉ—a go ni zaune, idanuna sunyi wani irin kunburi sabo da sabar kuka har bana iya buÉ—e su duka.
hannun nawa yarike da kyau yaÉ—an jawo ni na sauko a gadon, kana yanufi kofa yana rike da hannuna har lokacin kukan nake muka fice daga cikin side É—in gaba É—aya.
haka mukayi ta gilmawa cikin jama'a duk wan da ya kallene sai ya kuma kallona da fuskar tausaya wa,waÉ—an da suka sanni kuwa faÉ—i suke
"Dole kiyi kuka".
É—akin shi nada dake ta nan farfajiyar gidan yanufa da ni a cikin makullan dake haÉ—e dana motar sa yazura É—aya daga cikin su yabuÉ—e kofar,
muka shiga, É—akin tsaftsaf kamar da mai kwana cikin sa sai tashi da daddaÉ—an kamshi yake.
a bakin gado ya zauna tare da zaunar dani a jikinsa ya..........!�

*Free page saura kaÉ—an yakare waÉ—an da basu biya ba su hanzar ta*

Mommyn twins ce

🌺 *HAMDAH*🌺

*Na*

*RASHEEDA S DIRECTOR*

*_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍�*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*

_BOOK_ _ONE_

Last Free page🙌🏻

My no 08034690723

_Wannan page ɗin ɗungurugum ɗin sa sadau karwa ne ga ƴan group ɗin HAMDAH Shalele Fans_🥰🤗 _walla bani da bakin yi muku godiya_
*_jinjina gare ki ta hannun daman Rabin jiki Khadijah🥰 Fans suna ta miki godiya fa dayi miki addu'a Allah yabiya miki bukatan ki da biya musu kuɗin karatu da kikayi_*😍

🅿�32

Ya gyara min zama sosai a jikin sa kana a hankali yasaka hannu ya rungumo ni yana É—an jijjiga ni kamar wata jaririya,
kana a sannu ya tallafo fuskata ya sanya kwayar idanunsa cikin nawa da suke tsiyayar da kwalla,
kana a hankali ya furzar da iska mai zafi cikin bakin sa
a hankali ya furta
"Kiyi hakuri ki dai na kukan nan haka yau kwana na wa kullum acikin kukan nan kike kinsan fa ba ke É—aya bace hakan zai iya janyo dake da abun cikin ki matsa kinaso asa mi matsalar ne?".
komai ban ceba bankuma fasa kukan ba,
"To kinaso nima nafita nayita kukan irin naki ne iye *HAMDAHHH*? Inna ta tafi addu'ar mu kaɗai yanzu take bukata haka zamu zauna madadin mubita da addu'a sai mu bita da kuka anya kuwa Inna zataso hakan,yakike gani zataji idan muka bita da addu'a madadin kukan namu? idan akayi kaɗan sai a kara da hakuri dole zamuji zafin rabuwa da mutum irin Inna, sai dai bamuda yan da zamuyi wan da yafimu sonta ne ya ɗauke ta acikin mu, kodun ya jarraba imanin mu, kinaso muzama daga cikin marasa imani da tawakkali da karɓar kaddara kowace iri ce?".
ido kawai na zuba masa jin yau karo na farko yayi doguwar magana irin haka.
yayin da nashi ga sauke ajiyar zuciya da son dai na kukan sai dai nasan ko da na iya daina kuka mai sauti abune mai wuya na iya dai na zubda kwalla,Inna uwace agare ni ba kaka ba.
Ya SALEEM yana da taurin zuciya a duk family'n mu babu wan da baiyi kuka ba hatta Abba da Abbu sai da suka zubda kwalla amma shi ko É—igon hawaye ban gani a idanunsa ba sai dai yan da idanunsa suka sauya daga farare tass zuwa ja...

Tafin hannunsa ya sanya kan fuskata yashiga share min hawaye kana a hankali yafurta
"Ki dai na kukan haka ki huta tukun".
yafaÉ—a cikin muryar lallashi kana ya haÉ—e bakin mu sai da ya tabbatar da ya sai da kukan kafin ya zare bakin sa,
kana yashiga tuɓe min kayan jikina koda yazare min doguwar rigar jikina yarage daga ni sai pant dan ko bra babu ajikina, kasan cewar shi ɗazu yasaka min kayan.
mikar dani yayi kana shima yamike yaruko hannuna muka nufi bathroom dake nan cikin É—akin,
ya tai maka min nayi wanka muka fito na mai da kayan da na tuɓe,kana ya zauna kan gado ya ɗan kishin gida yayin da ya kwantar dani a gefen jikin sa,
naji É—an daÉ—in jikina kuwa danayi wankan.
dubana yayi da kyau ganin inata mammatsa idanuna yace
"Kukan zaki fara?".
kai na girgiza cikin disashshiyar muryar ta da ta dishe dan kuka nace
"Kai na ne ke min ciwo".
nafaÉ—a ina matse idon,
a hankali yashiga shafa kaina kana yace
"Zakisha magani?".
kai na girgiza da sauri, tare da faÉ—in
"Zai bari da kanshi".
numfashi ya sauke kana yace
"Idan baki kuma yin wani kukan ba shine zai dai na".
shiru nayi ina daÉ—a manna kaina da kirjin sa...

Har lokacin sallar la'asar tayi muna tare da shi acikin É—akin a kuma cikin ki jikin sa, sai da a ka kira sallar kafin ya ciro ni a jikin sa kana yaruko hannuna muka fito a É—akin.
side É—in Ummi yanufa da ni,
a parlour muka taddata da wasu Æ´an uwan mu, da alama sallah suka dawo yi,
akusa da Ummi na zauna
sai da yaga na zauna kafin yafita yanufi masallaci.
Mikewa tsaye nayi Ummi ta dube ni da sauri tana faÉ—in
"Ina zakije?".
nace
"Sallah zanje nayi".
tace "Ai ho" sai ta mike ta kamo hannuna muka shige cikin bedroom É—in ta..
tana tsaye a kofar bathroom har na idar da al'wala nafito kana ta shin fiÉ—a min sallaya na haye kai na tada salla,ita kuma ta zauna gefe na a bakin gado.
ina tada sallar naji wani irin kuka yazo min,haka nayi sallar hawaye na wanke fuskata, na daÉ—e inayiwa Inna addu'a a cikin sallar ko da na idar ma naÉ—au lokaci ina yi mata addu'a kana daga bisani nashafa sai na jingina kaina jikin kafar Ummi.
kai na ta shafa alamun lallashi sai ta miko min wani littafin addu'oi tace
"Karɓi zai sama miki salama da yardar Allah".
na miko hannu na karɓa kana na buɗe nasoma karan ta addu'o'in sai naji hawayen yana raguwa...�

Da daddare Ya SALEEM yakawo min kaya na acikin É—an ma dai-dai cin a kwati.
Ni dai tun da nashiga bedroom ɗin Ummi ban kuma leka ko da parlour ba,Ina zaune a cikin ɗakin,in Ummi ta fita to Aunty Jaleela zata shigo ko Aunty Rafee'at ko kuma wasu daga cikin dangin mu ba a taɓa barina na zauna Ni kaɗai,
ko bayi zan shiga to sai na sami mai rakiya ya tsaya a bakin kofar har sai na fito.
kullum Ya SALEEM zai shigo sau biyu da sassafe kafin mutane sufara zuwa sai kuma dare bayan sallar isha...
Chapter 59 · 0% Book details