← Book details Hamdah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 62

Sashe 25

Hamdah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ƙyallen da take sauke tukunya da shi yaɗau ka sai da yarufe glass ɗin window'n kafin ya isa in da kadangaren yake yakama shi da shi sannan yafito yaɗau ɗan ƙwalin ta dake kofar kitchen ɗin yayi waje,
A cikin a Flaw's ya wurga kadangaren yanufi side É—in shi a in da yabar ni anan ya taddani,
Ganin
ɗan ƙwalina rike a hannunsa sai naɗa go hannuna nashafi kaina sai yanzu nasan cewa babu ɗan ƙwali a kaina sai dai gashina a tupke yake da ribom,

Kujerar dake ɗan nesa da ni ya zauna tare da wurga min ɗan ƙwalin yamaso da table ɗin da system nashi ke ɗaure a kai gaban sa yasoma latsawa,
batare da ya kalleni ba yace
"Tashi kije na cire".
naÉ—au É—ankwalin na É—aura jiki a sanyaye namike a hankali nasoma tafiya,har nakai bakin kofa yace
"Zonan".
A hankali nadawo in da yake na tsaya gaban sa,hannuna yariko yajuyani ta baya yakai hannu bayana yaja zip É—in rigata yayi sama da shi. kasa nayi da kai na dan nagama mancewa da rigar a buÉ—e take.
"Jeki". yafaÉ—a yana sauke hannunsa, kai na a sunkuye nafita..................

Mommyn Twins ce

*🌺HAMDAH🌺*

*NA*

*RASHEEDA S DIRECTOR*

_(Book one)_

*_________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍�*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*_________________________________*

MARUBUCIYAR👇🏻
*BA ABIN DA BAN GANI BA*
*INA SANE DA HAKA*
*ALFARMA*
*BAZAWARA CE ITA*
AND NOW👇🏻
*HAMDAH*

*Free page*

My no 08034690723

🅿�14

A kofar parlour natsaya ina leka cikin parlour'n, najima sosai a tsaye a bakin kofar da ƙyar na iya tattaro jarumtata nashe ciki,
cikin sanɗa nake ɗaga kafata duk in da zan sauke kafar sai na kalli gurin da ƙyau, dan gani nake kamar zan sauke shi kan kadangaren.
cikin sanÉ—a nashige cikin bedroom, Ina shiga kira na shigowa wayata,nakarasa bakin gado in da wayar ke ajiye, sunan Ummi ce yabai yana kan screen É—in wayar, da sauri na hayo kan gadon na É—au wayar nayi picking call É—in na kara wayar a kunne tare da yin sallama.

Daga bangare Ummi ta amsa sallamar tare da amsa gaisuwar da nake mata,kana ta É—aura da tan bayata lafiya ta da nagi dan, nace duk muna Lafiya,
tace
"To madallah da ma su Umma'n ku Habiba ce suka ce na faÉ—a miki bazasu sami zuwa gidan kiba,dama Sadeeq ne ya kawo su shi yawuce Jos to sai gashi ya juyo É—azu yanzu yace sushirya suwuce gida yanzu."

Langwaɓar da kai nayi cikin marairaice murya nace
"Ayya shine zasu tafi bazasu zo bako kicewa Uncle Sadeeq É—in dan Allah yayi hakuri yabarsu suzo".
"Hm Sadeeq ai bazai ma yar da ba nima yanzu muka gama yi da shi sukara ƙwana dan yahuta gobe suyi sammako, daga nan zuwa Maiduguri ai ba karamar tafiya bace da ke shi tafiyar dare baya damin shi,sai dai kawai in sun Kuma zuwa wani lokaci".
Nace "To Allah ya kiyaye musu hanya".
tace
"Amin". Mukayi sallama na sauke wayar.

Yau wuni nayi a ɗaki ban ko leka parlour ba, har yamma zuwa lokacin nasoma jin cikina na murɗan yunwa, bana da wani zaɓin da yawuce nasamar wa cikin na a bin da zan saka masa, dan ko breakfast banyi ba,
A hankali namike na nufi parlour daga É—an nesa na tsaya ina kollon kofar kitchen,har yanzu gani nake kamar kadangaren yana ciki.
Numfashin tsoro naja tuno da yan da naji shi cikin rigata É—azu.
juyawa nayi naje na buÉ—e fridge É—in da ke nan cikin parlour naÉ—au drinks guda biyu nakoma É—aki, ranar shi nasha madadin abinci.

Washe gari
Ban fitoba sai wajen karfe 11 kasan cewar mun sami hutu a makaranta,
Yau kam yunwar da nake ji yagirmi nasha drinks kaÉ—ai dan bazai É—auke ni ba.
NaÉ—au gyale na na yafa shi a kaina, tare da É—aukar waya ta da kuÉ—i na nufi waje.

Can na hangeshi zaune cikin wasu Flaw's masu ɗauke da jerin kujeru na alfarma, sanye yake dawasu fararen kaya riga da wando wandon iya guiwar sa,daga kasan irin mai roba ɗinnan ce tasuke takasa sai igiyoyi a bakin,rigar kuma mai dogon hannun ce sai dai sakiyar rigar a buɗe take daga kirjin sa zuwa dai-dai mafarin cikin sa, ya sarkafe kakafun sa da suke mike kan wata kujerar dake gaban sa, yaƙwanto da bayan sa jikin kujerar da yake kai, a hankali yake ɗan karkaɗa kafafun sa yayin da idanun sa ke lumshe. fuskar sa na kallon tacan ya baiwa hanyar fita baya.

A hankali nake tafiyar harna É—an gotashi sai naji yace
"Ke zonan". cak naja natsaya,
in badun hankalina na kan shi sabo da alla-alla da nake nayi na fita a gidan kada yajuyo ya ganni ba, da bazan ji a bin da yafa É—a ba, sabo da muna da É—an rasa sakanin mu, kuma maganar a hankali ya furta, bugu da kari kuma fuskarsa bama ta hanyar take kallo ba, gakuma idanunsa da suke a lumshe.

A hankali najuyo natako nazo in da yake,natsaya batare da nace komai ba,
Shima kuma idanunsa suna nan a lumshen.
ƙwayar idanuna na juya nasau ke shi kan kirjin sa, da bakin gashi ke ƙwance lip-lip kan farar fatar sa.
saurin janye ida nuna nayi daga kallon sa,jin wani abu mai kama da tsoro ya gilmamin ganin wani sashi na kirjin sa a bayyane.
"jibi yadda yabuÉ—e jikin sa ko zafi yakeji da wannan sanyin da ake yi oho, amma ya iya cewa ana sanyi ina jika jina shikuma fa".
Nayi maganar a kasan raina.
laɓɓansa yashiga mosasu batare da yabuɗe idanun nasa ba, cikin wani irin murya da yafi kama da mai jin bacci yace
"Ina zakije?".
yayi tanbayar a gajarce, baki na turo gaba sai nashiga kame-kame ina faÉ—in
"Um..um.." sai kuma nace
"Gida zani yunwa nake ji".
É—an sakaita kaÉ—a kafar da yake yayi, sai yaÉ—ago hannun sa ya shafi sajen fuskarsa zuwa kan É—an gyemun sa,
cikin sautin muryar da yayi magana da shi dafari.

yace "Babu a binci a gidan nan ne?".
kai na girgiza sai kuma nayi rau-rau da ido na ce
"Ai a ƙwai kadangare ne a cikin kitchen nikuma yunwa nake ji".
Sai yanzu ya buÉ—e idanunsa ya É—an zubamin su,saurin yin kasa da kaina nayi nashiga wasa da bakin gyale na,
"Ban cire ba kenan, karya nake yi?".
YafaÉ—a ida nunsa a kaina,É—agowa nayi da sauri nashiga girgiza kaina.

Kuma mai da idanun sa yayi ya lumshe su kana yace
"Wuce ki koma ciki". yafaÉ—a kamar maiyin raÉ—a,
Ido nawaro jin a bin da ya faÉ—a, in koma yunwar takashe ni.
ji nayi kamar in rushe da kuka, a hankali na juya na ja kafafuna na koma ciki,
koda nakoma tsayuwa nayi a cikin parlour ina hangen kofar kitchen,
duk da cewa ina da tabbacin cewa tabbas da gaske yacire kadangaren,
amma hankali na yakasa ƙwanciya sai gani nake kamar in nashiga zan ganshi,
gyalen jikina nazare shi na a je saman kujera tare da wayata,
a hankali nataka zuwa kofar kitchen dan bana da zaɓin da yawuce wannan,
koda nazo bakin kofar leko da kaina nayi narika dud dubawa,
naÉ—au lokaci kafin nashige ciki, sosai
nabaza idanuna ina dubawa banga wani alama na abin da nake wa tsoron ba,
dan haka cikin dai ɗar-ɗar ɗin nashiga ƙwashe kayakin da nayi ɓarinsa cikin kitchen ɗin, har da
miyata da nayi jiya duk suka ɓare, nakimsa gurin tsaf,
duk a binda nake cikin dau riya nakeyi dan ko ni nataɓa a bu yayi motsi sai na
razana, haka nagama kimsa gurin cikin É—ar-É—ar,
Ina gamawa na
É—aura girki mafi sauki, koda na gama nazubo shi cikin plt nafito....

★★�
2 week later
★★�

Zaune nake a parlour najiyo knocking É—in kofa sai da a kayi har sau uku kafin na mike na isa jikin kofar na É—an buÉ—e shi kaÉ—an batare da na wangale kofar ba,
Salele nagani tsaye rike da jaka a hannun sa,
Bin jakar nayi da ido sai na mai da kallona kanshi ganin yan da yaketa washe baki nace
"Salele wannan jakar fa?".
nayi tan bayar ina nuna jakar da yatsa,
Kuma washe baki yayi tare da faÉ—in,
"Jakar Inna ce gasucen" yafaÉ—a yana nuna farfajiyar gidan.

Kofar na daÉ—a wangale shi gaba É—aya naleko kaina waje can nahangi Inna tafito daga mota kenan tana gyara É—aurin zanin ta, goggo Hauwa na tsaye Ya SALEEM na gefen su,
Wani irin ihun murna na sake nayi waje da gudu har sai da na ture Salele Allah yakare yarike jikin kofa,
In da suke nayi a guje ina faÉ—in
"Oyoyo Inna!".
rungume ta nayi cike da tsananin farin ciki ina ci gaba da faÉ—in Oyoyo Inna.
Dariya goggo Hauwa tabimu da shi ganin Inna'r ma ta rungume Ni tana washe baki tabbas tasan munyi kewar juna.
Nan muka É—un guma mukayi ciki,
Ni dai ina rike da hannun Inna har muka shiga cikin parlour.

Suna zama nawuce naje na É—ibo musu drinks, da ma na É—aura a binci ban ko sauke ba nashiga kitchen na tadda yanuna sai nazuzzu ba musu cikin plt nakawo musu,suna ci muna hirar yaushe gamo,
Nan Ya SALEEM yashi go ya zauna gefen goggo yana yi mata ya hanya.
tun kan yakai ga rufe baki Inna tace
"Mu da ba'a tan baye muba Allah bai kimu ba,yo ko dai baka tan baya ba ka dai ga kalau na iso a bina"
dariya goggo Hauwa tayi tace
"Kin dai tari numfashi'n sane Inna, ba gashi nan zaune ba ai zai gai da ki".
Chapter 25 · 0% Book details