← Book details Hamdah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 56 OF 62

Sashe 56

Hamdah Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Yace "Menene na kukan daga anyi miki nasiha sai ki kama kuka ke baƙya gajiya da kuka ne?".
kai na haÉ—a da guiwa naci gaba kuka na wan da nake jin sa har cikin raina. tada motar yayi kana yajuyo ya dube ni tare da faÉ—in
"Ya isa". da sauri na ɗago kamar an zabure ni na kalleshi hawaye tap idanuna sai na juya da sauri na ɓalle marfin motar nafi ina faɗin "Ina zuwa dan Allah Ya SALEEM".
nafaÉ—a ina fita a motar da sauri nanufi cikin asibitin ina ji yana kira na ban ko juyo ba...
ina isa bakin kofar room É—in da Inna take ciki na tura kofar da sauri nashiga,juyowa su Abbu sukayi da su Ummi da suma suka shigo yimata sallama zasu tafi, Inna ta É—ago idanunta tare da yafato ni da hannu da sauri na zo in da take sai ta riko hannuna tace
"Baku tafi ba kai mai sunan malam me kuke jira dare fa nayi".
juyawa nayi jin tana maganar tana kallon kofa, lokacin yake mai da kofar yarufe yakara so ciki,maganar tace tasani juyowa gare ta
"Wannan haske da kema kika kara bayamma ce kawai ai gashi ya bayyano kansa gasu a hannun ki sun fito raÉ—a-raÉ—a,bari cikin yayi wata 6 zan zo na É—auke ki mutafi kisha magani har sai kin haihu,yoo ai ba'a wasa da wannan cutar faraÉ— É—aya yake kashe jariri dole kisha ganyayya ki".
tafaÉ—a tana jujjuya hannuna,
baki Ya SALEEM ya taɓe tare da faɗin
"Ku wai har yanzu bazaku dai na wannan al'adar takuba garin jinya a kwaso wata cutar".
sai kuma yayi kasa da murya
"Babu inda zata bare aje garin yin wani jinya akashe min É—aya da wasu gangayya ki".
yayi maganar ne a iya laɓɓansa bai san yafito ba.
murmushi Ummi tayi dan tasan yayi maganar ne batare da sanin yafito ba,
Abbu kuwa dakuwa yayi masa yace
"Kaci gidan ku shine mu bamu mutu ba".
"Shi kanshi ma dai da bai mutun ba".
cewar Mamie,
Inna tace
"Rabu dashi yoo kai É—in badun taima kon Allah da ganyen ba da kakai nan,kai akwai wan da yakai ka laulayi ma haka a ka haifo ka fari soll da kai jiki duk bayamma kayi ta wahalar da mutane, ai idan É—an naka yayi gadon ka kam wannan Æ´ar tashiga uku,bari ma kaga a sallame ni in zan koma tare zamu koma da ita,a tare cutar da wuri tun kafin É—an naka yazo duniya ya wahalar da mutane".
Mamie tace
"Ai kam dan ita tasha wuyar ka tun ranar da kazo duniya har kayi arba'in".
murmushi nayi dan natuna wani rana Inna tataɓa yimin hirrar har take faɗa min ma ita ta yayeshi.
shiko fuska ya gimtse ganin su Aunty Rafee'at suna dariya,
Inna ta dube ni da murmushi tana faÉ—in
"To kuje sai da safe,kai kuma mai sunan malam gobe kazo min da farin goro".
sai kuma ta kuma mai da duban ta kai na taci gaba da faÉ—in
"Idan rayuwa ya juyawa mutum baya kada ya mance da Allah shike yaye da muwa da kunci,duk abun da yasa mi bawa da sanin uban giji,ina daɗa faɗa miki kada juyawar rayuwa tasaki mance wa da Allah kiyi amfani da hakan ki saɓa masa, ki gode masa sai ya yaye miki, ki yawaita ambaton sunan Allah da yawan addu'o'i a duk halin da kike ciki".
yanzu ba ni kaÉ—ai maganar Inna yajefa cikin wani yana yi ba gaba É—aya mutanen cikin É—akin sai da jikin su yayi sanyi Ya SALEEM ne yayi karfin halin cewa
"Wai wa'azi kika koma ne a buÉ—e miki gurin da zaki rika faÉ—akar da jama'a".
murmushi kawai tayi kana ta kuma duba na tace
"To kuje sai da safe mai sunan malam kar ka man ce gobe kazo min da farin goro".
to ya amsa da shi kana ya nuna min hanya da hannu a hankali nafara É—aga kafata sai kuma nakuma juyowa na kalle ta kai ta gyaÉ—a min haÉ—e da murmushi.
"Inna ina dai zaki kuma zuwa min muzauna?".
nafaÉ—a ina duban ta yayin da wasu zafafan hawaye naji suna zubo min wan da ban san dalilin zuwansu ba.
kai ta gyaÉ—a min tace
"Zan kuma zuwa mu zauna takwara ta Aysha, idan aka sallame ni".
kai na gyaɗa yayin da hawayen suka zubo nayi saurin tare su da bakin gyalena,karo na farko da na taɓa ji Inna ta kirani da asalin sunana kuma sunan ta da nace.
murmushi Aunty Rafee'at tayi cikin yanayin mutuwar jiki tace
"To in ma kina so kiji abun da zamu ce ne,to mu munci girman mun yafe wannan karon ma kisake zuwa ki zauna mata".
da sauri na juya nafita jin wani kukan na zuwar min
Ina jiyo muryar ta tana amsa wa Aunty Rafee'at maganar,
tun kafin na isa gun mota kukan ya kwace min nashiga motar na zauna ina ci gaba da kukan.
sai lokacin shima yashigo ya zauna jiki a sanyaye duk yan da yayi dani akan nayi shiru na dai na kukan na kasa da kukan muka isa gida.
yana dai-dai ta parking ya janyoni jikin sa nan yashiga kokarin sai da kukan ta hanyar ai kamin da zafafan sakon ninsa masu nutsar da kwantar da hankali,kana ya ruko hannuna muka fito har bedroom É—ina ya kaini kana yace na zauna zai je masallaci ya dawo,
yana fita na kulle kofar naje nayi al'wala nagabatar da sallar magriba ina zaune kan sallayar har aka kira sallar isha kana na mike na gabatar tare da shafa'i da wutiri. bayan nagama duk kanin addu'o'i na na mike na koma kan gado,babu jimawa ya dawo daga masallacin na buÉ—e masa kofa yashigo..
ranar a makale a jikin sa na kwana...
Washegari bayan ya dawo daga masallaci ganin inata hamma alamun baccin bai ishe ni ba sai ya janyo ni jikin sa muka kuma kwanciya...�

★★★★
After 5hr
★★★★
Chapter 56 · 0% Book details