← Book details Hamdah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 62

Sashe 42

Hamdah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yana rike da hannuna muka shiga cikin asibitin muna shiga direct office É—in likitar yanufa yayi knocking É—in kofar,zuwa can wata nurse ta buÉ—o kofar dasauri taÉ—an rusuna tare da faÉ—in
"Good morning sir".
"Morning". yafaÉ—a a takai ce,da sauri tayi baya tare da buÉ—e kofar gaba É—aya,ya janyoni muka shiga,Dr Maryam babbar mata ce dan takusa kai Ummi na, da sauri taÉ—a go da murmushi É—auke a kan fuskar ta tana faÉ—in
"Barka oga SALEEM". kujerar da ke fuskantar ta tanuna tana faÉ—in
"Bismillah".
kafaÉ—una ya rike ya zaurar da ni kana shikuma yazauna kan wani kujerar da ke gefe,wani gaisuwar ta shiga yi masa kana ta É—aura da faÉ—in
"Itace mara lafiyar? Amma dai kanwar ka ce ga kamanni hancin ku iri É—aya".
Eh yace a takai ce. tamai da duban ta gare ni
"Ya da hawaye bakison zuwa asibitin ne?".
tayi maganar da murmushi komai ban ceba sai ci gaba da masar ƙwalla nake,
tace "To me ke damin ki?".
baki na turo nace
"Kai na ke ciwo".
"Bayan shifa?".
nace
"Babu".
Dubana takuma yi kana tace
"Akwai zazzaɓi a jikin ki ga idon ki ya nuna ya kikeji a cikin jikin na ki?".
"Ni bana jin komai".
Tanbayoyi tarika yimin amsar dai É—aya nake bata wani ma shiru nake daga bisani tadubi Ya SALEEM tace za'ayi min test za a kuma É—auramin drip ko a gida ne dan naji daÉ—in jikin sosai,
kuka na fashe dashi ina faÉ—in
"Allah ni baza a samin ba kuma gida zan tafi". na meke tsaye da sauri ya mike tare da yimin tsawa,
Dr Maryam tace
"A'a kyale ta bari kawai ayi mata allura na saukar da zazzaɓin sai kuma magani".
ta dubi nurse É—in da ke tsaye a gefen ta tace ta haÉ—a allura,kana ita kuma ta yawo takar da taÉ—anyi rubuce rubucen ta tamika masa, nan da nan nurse É—in ta haÉ—a allurar ta mika mata da kan ta tayi min,tace nazauna naÉ—an huta sabo da allurar,na zauna tare da lumshi idanuna,
murmushi Dr Maryam tayi tace
"Ya sunan ta zaka bawa Faisal É—ina ita dan halinsu É—aya shima da yake na miji baya son zuwa asibiti in bayajin daÉ—i sai nayi da gaske a gidan ma kafin na dubashi".
nan da nan annurin kan fuskar Ya SALEEM ya É—au ke ya tamke fuska tamau,
kuÉ—i ya zaro ya aje mata kan table É—in gaban ta tayi ta masa godiya,kana tace ya baiwa nurse É—in takardar ya mika mata tafita zuwa can tadawo rike da laidar magani tamika masa,
A hankali na buÉ—e idanuna jin bacci nason É—auka ta azaunen,
Dr tace
"Zaku iya tafiya Allah ya sauwaka".
Amin yace har lokacin fuskar sa babu annuri,namike a hankali yana biye da ni muka fito,koda muka fito hanyar fita daga asibitin na É—auka dan banaji zan iya komawa motar sa,
"Ke ina kuma zakije?".
ban kulashi ba nacigaba da tafiya ta, cak yaɗaga ni yayi cikin mota dani kunya kamar nanisa dan ga mutane da yawa a gon,yashiga motar shima yaja muka fita daga cikin asibitin,ganin ya ɗau hanyar gidan sa,da sauri na dubesa cikin zubda ƙwalla nace
"Nifa gida zan tafi ka sauke ni a nan na tari mai a dai-dai ta".
da sauri ya juyo ya kalleni sai kuma ya mai da idon sa kan titi, dai-dai lokacin da yake yanko kwanar da zata sadashi da gidan shi,batare da yace komai ba,muna isa bakin get yayi hon mai gadi ya wangale masa get a sannu ya isa cikin parking space ya paka motar kusan a tare muka fito yazago gefen da nake cikin suke fuska yadube ni da kyau yace
"Idan kika kuskura kika sake sa kafa da sunan fita a cikin gidan nan ranki sai ya ɓaci,oya wuce ki shiga ciki."

Da sauri na juya tare da fashewa da kuka na toshe bakina da tafin hannuna nanufi ciki da gudu.
Hannunsa ya cusa cikin sumar kansa tare da furzar da iska daga bakin sa a sannu yasoma tafiya hanyar side É—in sa.

Koda nashigo a kan gado na zube nayi kuka mai isata har bacci ya É—au keni.
sai bayan azahar na farka sosai naji zazzaɓin da ciwon kan yasauka, nayi sallah kana na naje kitchen nakirka abinci mai sauki,
Ina zaune a parlour ina cin abin cin yashigo da sallama,acan kasan wuya na amsa sallamar batare da na É—ago ba naci gaba da cin abinci na,a sannu yakara so cikin parlour'n yazauna gefe na tare da saka hannunsa a kirji na yatura cikin rigata ta sama yana kokarin cafko ababen kirjina, da sauri na yunkura zan mike yayi saurin riko ni ya mai dani kana ya daÉ—a cusa hannun nasa ya cafko ababen kirjina,
kiciniyar kwatan kai na nashiga yi amma na kasa,jin kuka na kokarin kwace min da sauri na danne kukan,wasa da breast É—ina yake yayin da ida nunsa ke kan suskata a hankali ya furta
"Ke ki nutsu magani zaki sha".

Kai na juya
sai kawai na fashe da kuka ina faÉ—in
"Ni bazan shaba karabu da ni".
nafaÉ—a cikin matsanancin kuka,
sai nafizge daga rukon da yayi min namike a guje nayi cikin bedroom narufo kofar da key.
Ko da dare yayi haka yazo yayi ta bubbuga kofar cikin muryar faÉ—a yake faÉ—in nabuÉ—e,ina jin sa nayi masa banza.
Tun daga ranar na dawo zaman ɗaki ko parlour bana fita, in kaga na fito naji fitar sane shima ɗin sai na tabbatar, dan da zarar naji karar mota zan zo jikin window na leka in na tabbatar da shi ɗin ne yafita to zan fito nagirka abin da zanci na koma....�

Yau kimanin biyar kenan kullum sai yazo haka zai gama tsayuwar sa yatafi bazan ko tanka shiba, tun idan yazo yana yimin magana cikin tsawa da faɗa har ya dawo yin muryar lallaɓi...

Yau yana tashi daga offece state locos yanufa part É—in Mamie yafara zuwa ya gai sheta kafin ya wuce part É—in Ummi,
kamar ko da yaushe bayan sun gaisa taje takawo masa abinci yana ci suna ɗan taɓa hira har ya kammala,cikin hirar tasu Ummi ke cea
"Ya zaman iyalen naka? ka daure ka kwatanta a dalci kada ka dubi dan gan takar da ke sakanin É—ayan su, kai dai ka kwatanta adalci saka nin su Allah ya taya ka ruko ya baku zaman lafiya."
"Amin."
yace tare da gyara zaman sa ya kalli agogon da ke É—aure a hannunsa, kana yaÉ—an muskuta tare da É—an sosa bayan keyar sa kansa a kasa yasoma magana
"Ummi bata da lafiya kuma takulle kanta taki shan magani".
Da mamaki Ummi ta zuba masa ido idan ta fahimci in da maganar nasa ta doso to HAMDAH yake nufi, cike da mamakin tace
"Wafa HAMDAH ce ta kulle kanta?".
Kai ya gyaÉ—a alamar Eh.
É—an shiru tayi tana nazarin maganar nasa da yabata shi a dunkule,abin ka da babba nan da nan tayi wa maganar nasa wasali,da sauri takuma cewa
"Sai ka zuba mata ido ta rufe maka kofa SALEEM?".
Ummi tayi maganar da mamaki,
Murmushi yayi kana ya mike yana faÉ—in
"Ummi kinsan bata son magani, ta buya wa magani ne".

Baki Ummi ta buÉ—e tana binsa da ido yayi mata sallama ya tafi. numfashi ta sauke tare da
jinjina kai,
taɗau wayar ta ta laluɓo Number'n HAMDAH...�

Ina tsaye jikin wardrobe ina ciro kayan da zan sa najiyo karar wayata da na kulle cikin wardrobe tun ranar da ya dawo dani dana jefa jakar da wayan ke ciki cikin wardrobe, kullum sai naji wayan na ringing sau ba adadi haka zai gama ringing É—in masu kiran su gaji su hakura kullum kuma haryau,
É—an kallon gefen da wayar ke ciki nayi sai kuma na kawar da kaina naciga da abin da nake,
kirar ta katse wani yakuma shigowa,
A hankali na matso ɗaya ɓarin wardrobe ɗin na buɗe naciro jakar da wayan take ciki,na buɗe na ciro wayar,ido na ɗan waro ganin tulin missed call ɗin koda na buɗe sai naga kusan duka kiran Ya SALEEM ne sai Inna da Aunty Rafee'at sai kuma na yanzu Ummi na,
kokarin bin kiran Ummi'n nake sai ga wani kiran yakuma shigowa, baya nayi na zauna bakin gado na É—aga kiran tare da sallama,
daga ɓangaren Ummi ta amsa sallamar, ina kokarin gaishe ta tada katar da ni da faɗin

"Ke HAMDAH wai nikam yaushe ne zakiyi hankali ne kam a rayuwar ki,
dan iya shege zaki kama kirufe masa kofa bakida hankali ne mijin naki zaki rufewa kofa".

jin yanda Ummi ta dage take ta faÉ—a da sauri nace
"Ummi kitsaya kiji ba.."
da sauri ta dakatar dani
"Bana son jin komai dan ban tanbaye kiba, ke kinsan girman laifin da kika ai kata kuwa? da mijin naki kike fushi dan baki da hankali,
to ina mai tabbatar miki yanzu-yanzu kitashi kije kini mi
yafiyan sa,kuma wlh na sake jin kwatankwacin irin haka yasa ke faruwa sai nayi
mugun saɓa miki,kuma sai na sanar wa Abba'n ku abun da ke faruwa
tun da ke har yanzu bakida hankali,
Har SALEEM ya buÉ—i baki yafaÉ—i abin da ke faruwa a gidan sa ai abun yakai ya kawo,waya
san kalar abun da kike ai katawa ma
wannan É—in ma Allah ne yaso na sani,ai da barin ki da ciwon ki yayi kije can kita fama har ana bin ki a kan inganta lafiyar ki kinai wa mutane
tsiya,Allah yasa ki kure shi ya tattakaki,
Kuma ina mai umurtar ki yanzu kitashi kije ki bashi hakuri, kina jina dai ko?".
Chapter 42 · 0% Book details