← Book details Hamdah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 62

Sashe 22

Hamdah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kitchen É—in babban parlour nashiga na kunna Gas kana na cika ruwa cikin tukunya mai É—an girma na É—aura kan gas É—in,
naja kujera na zauna ina zaman jiran ruwan yayi zafi.

Ina nan zaune har ruwan yayi zafi naÉ—au boket da na ganshi a cikin kitchen É—in na juye ruwan a ciki naÉ—au ka nanufi side É—in shi,
Sallama nayi daga bakin kofar bedroom ko da a ka amsa ban shiga ba sai da naÉ—an tsaya kaÉ—an kafin daga bisani na tura kofar.

Wannan karon yana zaune a kan kujera, ita kuma tananan in da na barta É—azu tayi shame-shame,
Kokarin dire boket É—in nake nan tsakiyar É—akin tayi saurin cewa
"Shiga dashi cikin bayi mana".
A sannu nanufi kofar bayin ina shiga ciki bra da pant É—in ta nafara ka karo da su yashe a kasan bayin,kafa nasaka na turesu gefe na isa na a je boket É—in najuya nafita.

Koda na koma part ɗina a ƙawance na iske Aunty Rafee'at tana ganina tayi murmushi tare da faɗin
"Um mata masu miji daga tafi amsa kira sai a mance da ni har na fara tunanin ko in tafi ne".

Murmushi nayi na ce
"Ai girka ruwan da nayi ne yasa na daÉ—e ayya Aunty Rafee'at da tafiya zakiyi?".
Nayi maganar a marairaice,
tace
"Ruwa kuma?".na ce
"Eh ai Aunty Na'ima ce tace na girka musu ruwan wanka da ita da Ya SALEEM shi yasa ma na daÉ—e".

Da sauri tamike zaune tare da waro ido tace
"Mene girka musu ruwan wanka da ita da Ya SALEEM??!"..
kai na gyaÉ—a,
daɗa waro idonanun ta tayi da ƙyau da ƙyau tace
"Ke baki da hankali ne nikam ke HAMDAH wace iri ce ke, ke babu zu ciya ne a jikin ki, HAMDAH yaushe zakiyi hankali ne kam wai har yanzu bakisan ciwon kankiba baƙyajin wani a bu a cikin zuciyar ki ke,
Ke bakida kishine a rayuwar ki, girka musu ruwan wanka??!
sugama a bin da zasu yi kece Æ´ar girka ruwan wanka dan tsabar rashin mutun ci da rainin wayo babu ruwan zafi ne a bayi da har sai kinje kin girka musu a kitchen kin kawo musu,
dayake kema sha-sha-sha ce mara zuciya shine zaki biye musu.
to wlh bari na faɗa miki daga yau sai yau nakarajin makamancin irin haka sai ranki ya ɓaci. da ma a she har yanzu tana kan saki ai kin kina yima ta??"....

Kai na girgiza na ce
"Allah bana yi".
Ta ce
"Bagashi yanzu tasaki kinyi ba".
"Aunty Rafee'at yanzufa yana nan Allah in banyi ba duka na zai yi".
tace
"Ya kashe ki ya kashe kima, dan rainin wayo sai kace Æ´ar ai ki a ka kawo masa gida wlh Allah bazai barshi ba".

Haka tarika masifa Ni dai shiru nayi nazuba mata ido,
ta mike taja maya finta taɗau jakar ta, tace har idan ban gyara ba babu ruwan ta da Ni kuma bazata sake zuwa gida naba, haka tatafi da ɓacin rai.

Ko da tafita a farfajiyar gidan suka haÉ—u da Ya SALEEM ko kallon in da yake batayi ba tafice daga gidan,
koda cewa Ya SALEEM ɗin wanta ne wan da suka fita ciki ɗaya, amma sam bata jin daɗin rashin daraja wa da nuna rashin kulawar da yake yi kan HAMDAH.....�

★★�

Yau tun kafin a tashimu a makaranta hadari ya haÉ—u baki kirin,kan kace me ruwa yafara sauka, koda a ka tashe mu haka É—alibai suka zauna cikin aji wasu kuma motocin gidan su suka zo suka É—auke su.
Muna zaune da wasu Æ´an a jin mu hira a ke amma ni gaba É—aya hankali na da ido na nawaje kan ruwan da ake shekawa, a hankali namike nadubi
Bilkisu wacce sit É—inmu É—aya da ita nace
"Bilkisu Ni zan tafi ga jakata ki tafi min dashi gidan ku gobe sai kizo min dashi?".
Ido tawaro tace
"Acikin ruwan nan kidubafa ruwan karuwa yake daÉ—a yi ki bari mana a É—auke tukun".

Mika mata jakar nayi ina faÉ—in
"Gashi Ni dai natafi bana son ruwan yajikamin littattafai ne" .
tana amsa najuya da sauri nafita dan gaba É—aya na masu najini cikin ruwan.
Haka nafita a cikin makarantar naÉ—au hanyar gida a kafa,
ahankali nake tafiya ruwan na sauka a kai na,
har na iso kofar gida zuwa lokacin kam ruwan yafara sauki natura karamar kofar get nashi.

Ina isowa dai-dai parking space kamar an ce na waigo kuwa ina juyawa muka haÉ—a ido da shi, yana tsaye cikin parking space É—in da a lama dawowarsa kenan,
wiki-wiki nayi da ido sai kuma nashiga wasa da Æ´an yatsuna.

"Ke zonan!". yafaÉ—a cikin kakkausar murya,É—an zabura nayi a hankali na tako É—an nesa da shi na tsaya,
gefe da gefen sa ya waiga da alama a wani a bun yake nema,ido na waro ganin ya sunkuya yana kokari É—aukar wani bulala da ke gefen sa,
YaÉ—a go ya cafko hijabi na,
yaÉ—aga bulaliyar zai zabgamin, kai nashiga girgizawa cikin muryar tsoro da sanyin da naji yana shigana murya na rawa.

nace
"Dan Allah Ya SALEEM kayi hakuri".
NafaÉ—a ina ja da baya
gaba ki ɗaya jikina ya ɗauki ɓari,
Cikin muryar faÉ—a yashiga faÉ—in
"Me yadawo da ke a cikin ruwan nan, me yasa baki bari an É—auke ruwan kafin ki dawo ba, shine zaki biyo cikin ruwan nan ki da wo!".
yafaÉ—a cikin tsawa,
"Dan Allah Ya SALEEM kayihakuri wlh ruwan ne yaki É—auke wa".
Saukar bulalan naji a baya na, kara nasake tare da tuɓe hijabin naruga a guje nayi ciki na barsa nan rike da hijabin a hannu.

Direct bayi nashige nasoma tuɓe uniform ɗin jikina da sai ɗiga yake da ruwa zuwa lokacin sosai nakejin sanyin nan nashiga na a gaggauce nayi wanka nafito ina saka kaya nahaye gado dan masifar sanyin nakeji har ina karkarwa,
Blanket naja na dukunkune ciki ina cigaba da rawar sanyi.

Har yamma ina ƙwance zuwa lokacin jikina yahaɗa zafi rau, ga masifar ciwon kai, ga hancina da ya toshe da ƙyar nake iya jan numfashi,
da ƙyar na lallaɓa nata shi naje kitchen nahaɗa zallar tea nazo nasha, sai sannan nasamu nayi sallah.

Ranar haka na ƙwana da masifaffen ciwon kai da toshewar hanci,
Washe gari kam ban iya zuwa makaranta ba haka nayita ƙwanciya, a wunin ranar ma.

Haka nashare satin nan bana zuwa makaranta ko parlour bana iya zuwa, in kaga naje to kitchen nawuce shima É—in nakan wuni ban lekaba da zarar na zuba tea cikin flaks to sai washe gari nakuma shiga,
babu wani abincin kirki da nake ci zallar tea ne kawai nake iya sha...

Yau Monday ana tashin ɗalibai Bilkisu tanufo gidan su HAMDAH rike da jakanta ƙwanƙwasa kofar get tayi mai gadi yataso yabuɗe tare da liko kansa yana tanbayar wanene,
dai-dai lokacin motar Ya SALEEM ke danna hon É—in fita daga gidan,
mai gadin yayi saurin cewa tashigo tashigo tatsaya nan gefe da get É—in,
Shiko yayi saurin buÉ—e get É—in a sannu ya iso in da suke kamar zai wuce sai kuma yatsaya ganin tanayiwa mai gadin magana da a lama dai tambaya take.

Zuge glass É—in motar yayi kasa kana ya kalleta yace
"Gurin wa kika zo?".
Da sauri Bilkisu tace
"Ina yini".
Kai kawai yagyaÉ—a batare da ya amsa ba,
tace "Nazo gun HAMDAH ce nakawo mata jakarta ne, tun wancan satin tabani na aje mata kuma naga tun lokacin bata kara zuwa makaranta ba shine na kawo mata".

Mamaki mai haÉ—e da takaici ne yacika shi, wato makarantar ma bata zuwa tana nan jakar makarantar yana wani gun,sai yanzu yatuna ma ranar da ta dawo daga makaranta a cikin ruwa babu jakan a tare da ita.
tsaki yaja kana yaja motar sa yafice batare da yakuma bi ta kan Bilkisu'n ba.
Mai gadi ne yace tashiga ciki tananan yanuna mata hanyar part É—in.

Ina zaune bakin gado rike da cup ɗin tea na zuba masa ido shima yanzu sam bana iya shan sa dan ƙwata-ƙwata ma yunwar bana jin ta, sai na wuni banci komai ba dan banajin sha'awar komai.
najuyo sallama a parlour a je cup É—in nayi namike nanufi parlour'n.

Bilkisu nagani tsaye murmushi namata takaraso in da nake tana faÉ—in
"HAMDAH lafiya dai ƙwana biyu baƙya zuwa makaranta?".
Cikin murya ta da mura yagama toshesa nace
"Bana da lafiya ne".
tace
"Ayya sannu, dama jakar kine nakawo miki". Na am sa ina faÉ—in "Nagode dan Allah kisanar a makaranta bana da lafiya ne yasa bana zuwa".
Tace to tayimin sallama tatafi,nakoma ɗaki naƙwan ta.
Daren yau kasa bacci nayi dan ciwon yafina kullum haka kawai hawaye ke tsiyaya a idona, ga idon yayi ja sai nauyi da zugi yake min, ciwon kan ma haka sai nakeji kamar kan zai fashe numfashi kuwa sai da baki nake yinsa,ga masifaffen san yin da nake ji har cikin kashina.
Kuka na saka ina kiran Inna da Ummi na, haka nata kuka sai wajen asuba kafin nasamu bacci yaÉ—au keni,
Na É—an jima kuwa ina baccin sai wajen karfe 10 kafin na farka, sai dai har lokacin babu a bin da yaragu daga ciwon da nakeji.
na lallaɓa
Naje nayi wanka da ruwa mai zafi, nazura doguwar riga mara nauyi mai gajeren hannu na dawo kan gadon nakuma ƙwanciya na dukun kune cikin blanket, narufe ida nuna bawai kodun inajin bacci ba sai dun kai na da idona da nake ji kamar zasu cire.

"HAMDAH! HAMDAH!! HAMDAH!!!".
Muryar Ya SALEEM najiyo daga bakin kofa yana kiran sunana,rumtse idanunna nayi da karfi jin yan da yake ƙwaɗa min kiran cikin tsawa.
Yaturo kofar da karfi yashigo, kaina na da É—a dannashi sosai jikin pillow jin yana daÉ—a saramin da karfi-karfi,a fusace yanufo bakin gadon yana faÉ—in
"Zaman me kike yi a gidan da sati guda bakije makaranta ba".
Kankame ida nuna na daÉ—a yi da karfe,
yakai hannu yafizgo blanket É—in Dana dukun kune ciki, yafincuko ni na mike zaune yaÉ—aga hannu zai kai min bugu,na buÉ—e ida nuna a wahalce cikin disashshiyar muya ta da mura yagama toshewa,
Chapter 22 · 0% Book details