Sashe 81
Farhatul Qalbi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
na fifitata akan Waheedah. Nake ganin Waheedah itace me budadden idanu ta iskance akan karatun da take. Sai gashi ana zaton wuta a makera... Naga aya akan wadda na zaba... Ranar daurin auren an daura nan mijin ya zo ya saketa kan zubar da cikin ta uku bata gari bace... Sa'adatu ta yanke jiki ta fadi ana fadar hakan. An kaita asibiti zaa dawo da ita nan nace ban amince ba.. kaya zata zamar mana.. Sai gashi ita Allah ya warkar da ita. Ni ce na zama kayan. Sai dai a kwantar a tayar... Nayi kurakurai da manyan laifuka da baki ba zai iya fade su duka ba. Saboda girman haramcin su .. Ni dai ku yafemun... Dan Allah ku yafe mun.." Kuka ne yaci karfin kusan dukkanin su. Ciki harda malam me carbi da ke gefe... Daya bayan daya suka shiga cewar sun yafe Inna Sa'adatu ta tashi daga inda take. Duk ta yamutse. Ta motse ta lalace. Kamar ba wannan saadatun me tsiwa a baya ba.. Gaban Umma Hadiza ta tsugunna ta shiga rokan gafarar ta. Hawaye suka shiga reto a jemammiyar fuskar tah. Umma Hadiza tayi murmushin yake. Hannunta daya na kan na inna Sa'adatu. "Na yafe ma ki Sa'adatu . Allah ya yafe mana gaba daya.. Nima ina neman yafiyar dukkanin ku. Wadanda nayi wa lefi akan sani ko akasin sa. Ni da yarana baki daya mu na neman afuwar ku. Allah ya yafe mana baki daya Amin." Haka dai suka shiga neman afuwa da neman yafiyar junan su. Alhamdulillahi kowa ya yafewa kowa acikin su baki daya. Wannan yasa Malam me carbi sa ke jan kunne agare su .. Kafin yayi musu zai tafi Marka ta saka aka deba masa lemuka da ruwan da Waheedah ta kawo. Da rabin kwanon kayan masarufin. Yayita godiya ya yi musu sallama ya tafi. Najib ya rike masa kayan yayi masa rakiya.. Waheedah da zainab ne suka hada wuta suka dora taliya yar kakkaryawa da miya Ranar anci an gyatse... Anyi wasa da dariya... An saada zumunci sosai. Harda hotunan tarihi suka yiyyi... Da Waheedah ta tashi tafiya. Ta dakko yan kudaden ta na sadaki da taketa ajiyar su. Duk kuwa da tayi amfani da wani kaso daga ciki ..Ta dankawa mahaifin ta .. Don FARIN CIKI fashewa yayi da kuka. Ya rungume ta yana sanya mata albarka ,. Tace yaja jari da su. Yana kaunar iyalin sa. Da matar sa ta baya Hadiza. Dan dai auren ya rabu ne. Ya so tayi komai . Sai aka dakatar kan dukkanin su AS ne.. Don haka kar a mayarda auren tarihi ya maimaita kansa . Kar su sake samun wasu iyalin wadanda zasu zo dauke da cutar amosanin jinin suyi ta wahala har karshen rayuwar su .. Don haka ya hakura .. Har mota suka raka Waheedah wadda Nassem kanin Zayn ya zo daukar ta. Shima ya gayshe da su cikin girmamawa... Taro ya watse . Kowanne ya koma muhallin sa cikin FARIN CIKIN ZUCIYAH..... BAYAN SHUDEWAR WASU LOKUTA Anyi bikin Nadra an gwangwaje... Dangi zumunci ya kara bunkasa . Zuciyoyin su sun samu farin ciki da kara kusanta a tsakani.. Allah ya azurta Waheedah da karuwa. Ba karamin kyau baby bump din ya mata ba. Idan ta saka uniform din school of nursing sai kuga yayi das das ajikin ta. Gwanin ban sha'awa.. Soyayyar duniya Zayn ya dauka ya dorawa cikin Waheedah. Ta kara samun kulawa da tarairaya daga dangin ta da na sa. Ciki kuwa harda Ahlam . Domin yanzu tuni komai ya wuce sun dedeta kansu. Suna kuma ziyartar gidajen juna. Wani lokacin har tsokanar su Zayn yake .. Yana cewa suna hade masa kai bai yadda ba. Itama Ahlam ta koma makaranta karo karatu na digiri na biyu. Ya yinda Zayn arzikin sa ya yalwata. Ya hada da aikin office da kasuwanci. Ya mallakawa matan na sa biyu mota iri daya. Ta Ahlam fara ta Waheedah ja. Lamarin sai godiyar ubangiji. Fannah da Basira ma lokaci daya aka saka bikin su. Ibrahim ne ya auri fannah. Ya yin da Salman lecturer dinsu na school of nursing kuma ya auri Basira. Waheedah ita ta zama uwar biki. Babbar kawar amare. Gidan su wajen Marka ta koma ta tare har aka kammala shagalin bikin na tsawon kwanaki uku. Ya yinda gefe daya bangaren na ahalin malam na lado ma sai sam barka komai yana tafiya ahankali cikin nutsuwa da kwanciyar hankula... Da waraka ta fannoni da dama... Don Umma Hadiza ma wani mutumi mai rufin asiri a gidan da ke kallon na gwaggo haule. Matar sa ta rasu ta bar masa yara biyu. Shekara daya kenan da wata uku bayan rasuwar ta. Ya samu mijin gwaggo haule da zancen neman auren Umma Hadizan. Da fari Umma Hadizan ta ki. Kasancewar ga yara manya agabanta auren me zatayi? Da kyar da sudin goshi gwaggo haule ta shawo kanta. Aka daura auren ranar wata jumu'ah. Ta tare agidan. Mai gate da dakuna uku da parlor har biyu. Kuma Alhamdulillahi yaran mutumin na kaunarta. Ta rike su tamkar yaran data haifa daga cikin tah. Ta kance ai 'da na kowa ne.. Hakan yasa dangin sa dana marigayi ya matar sa suka sake kaunatar Umma Hadizan. Suna masu yabon ta a ko'ina... ZAYNUL_WAHEEDAH (DESTINED LOVE) Samun karuwar da tayi ... Yazo mata da lauyi kala kala. Ciki harda kasala da bacci uwa kasa. Da tayi ishai take zubewa tayi bacci.. Kusan ko yaushe sai ya dawo da daddare ya ke tashin ta ... Taci abinci sai ta sake komawa baccin. Yau ma hakan ta ke. Mai gadi na bude masa gate ya shiga da motar sa ya yayi parking awajen adana motoci. Ya bude kofar da zata saadaka da cikin gidan da spare key din da ke hannun sa. Bakinsa dauke da sallama ya shiga. Sai kamshin turaren wuta ne ke tashi . Ya sake bude kofofin hancin sa yana mai shakar niimataccen kamshin. Hannu ya saka ya bude dakin ta. Tana kwance akan gado tana bacci. Ya danyi murmushi hadi da ajiye yar jakar da ke hannun sa a gefe . Ya zare safar kafar sa ya isa ga gadon da take kwance. Ya yaye duvet din ahankali ya shiga ciki. Ya shiga unbutton din maballan jikin rigar sa. Ya cireta ya ajiye a gefe. Jikin Waheedah ya shige sosai tamkar za'a kwace masa ita... Ya saka hannuwan sa akan rassan jikin ta yana mai mata tafiyar tsutsa.. Cikin wani salo na tafiyar da soyayyah . Ya dan saka hakoran sa ahankali ya ciji kunnenta.. Ta shiga ture shi daga jikinta. Idanuwan ta a rufe. Baccin ya ki sakin ta.. "Kasa uwar bacci ....." Ya fada ahankali cikin kunnenta.... Yana mai yawo da harshen sa acikin kunnenta. Da sauri ta farka daga baccin. Ta shiga ture sa da iya karfin ta . Ya hanata, Ta hanya sake makaleta. Yana mai shafa gadon bayan ta, "FARHATAL QALBi nahhh, A yayin bayyana miki adadin yadda nake jin son ki a zuciyata, zan iya yin amfani da kalmomi irin su .hmm ko dan ina ganin cewa babu wata kalma da za ta iya wakiltar matsayinki a gare ni. Sai dai a yau a kuma yanzu ina mai kara sanar da ke cewa, ina kaunar ki .. Irin son da gangar jiki ke wa zuciya. Zuciya ta ke wa rai... Kin zamo mun FARIN CIKIN da ke cikin ZUCIYAH marar misaltuwa.." Yana magana yana zame rigar da ke jikinta a hankali. Dama ta bacci ce iya cinya. Ya sake jan bargo ya rufe su yana mai aikawa wasu rassa na jikinta sako da suke tafiyar da shi a koda yaushe. Ta shiga ture hannuwan sa. Tana mai turo baki gaba.. Cikin kwarewa ya burkito ta .. Ya kamo bakinta ahankali ya hade da nasa waje daya . Sumbatar ta yake cikin kwarewa da nuna tsantsar kaunar sa agare ta ... "Ka bari ....." "Sshhhh...... Please Waheedah.... Please" Ya shiga rokonta ta hanyar sanya idanun sa cikin nata.. Baki daya ya narke mata. Wasu zafafan sumba ya shiga aika mata tun daga tafukan kafafuntaa zuwa kirjin ta. Wanda suka haddasa mata tashin tsigar jiki. Kofofin jikin ta suka shiga budewa da son kasancewa da shi. Suna mai maraba da sakonnin da ya ke aika musu Hakan ya sa Zayn sa ke kai mi wajen. Zare rigar tata gaba daya ya jefar. Ya kashe fitlar bedside ya sake kankame ta ajikin sa. Duk kaucewar Waheedah sai da ta kasa hakuri. Ta bashi hadin kai. Suka shiga nunawa juna bajinta.. Bayan sun samu nutsuwa ne. Zayn ya dauki Waheedah suka shiga cikin bandaki. Ya sakar musu shower akan su. Suka tsaya ruwan shower din na zuba ajikin su. Ya shiga kwaranya akan sumar gashin Waheedah... Zayn ya saka hannu yana shafa gashin na ta. "Waheedah nah.. I never loved you any more than I do, right this second. And I ll never love you any less than I do, right this second..." Ta dago idanunta da suka jike da hawayen FARIN CIKIN kalaman sa da ke tsuma ZUCIYAr ta a koda yaushe... Ya gyarda mata kai, Ya sanya harshen sa yana mai goge mata hawayen da harshen sa, Hadi da cigaba da cewa, I love you and I don t want to lose you. Because my life has been better since the day I found out..... You are my sunshine, My moon and all my stars Da wannan kalaman ya hade bakunan su waje daya .. Daga wanka kuma suka shiga bude shafin wata kaunar. Dakyar Waheedah ta yageshi daga jikin ta ... Suka shiga mayar da numfashi. Daga karshe dai sukayi wankan me dalili dana tsarki. Kafin su sanya wasu kayan baccin su koma parlor .. Tv suka kunna suna kallon wani American film 'legally blonde..' Rayuwar su gwanin sha'awa... Tamkar irin masoya dinnan da suka shekara dari suna bawa soyayya hakkin tah. Zaman su suke lapia kalau ba wanda ke jin kansu . Ko sun haura da kansu suke shiryawa ba tare da kai wa wanin su kara ba...