Sashe 5
Farhatul Qalbi Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
"Kiyi hakuri. Insha Allah kwanannan samari zasu fara zuryaa a kofar gidan nan. Komai lokaci ne. Mijin ta na nan kusa da yardar Allah. Wanda zai share hawayen ahalin gidan nan kai dama na kusa da ku baki daya. Insha Allahu. Kice Aamin Marka.." Umma hadiza dake daki hawaye suka shigaa zirara a idanunta. Tabbas Najan Isubu aminiyar kwarai ce data san dattako take kuma yi musu madaukakiyar kauna marar misaltuwa. "Marka, Sa'adatu, Malam baku ce Amin ba." "Aamin Najaatu." Malam Nalado ya fada yana sosa keyar sa. "Uhum.... Inji me ciwon baki."Cewar Sa'adatu hadi da yin kwafa ta juyar da kanta gefe. "Aamin inda gaske ne hakan zai kasance ba karairaki bane da wucewar zance." "Insha Allah Marka... Na'Ateeku abunda yasa ki kaga na kauda zancen maganar sa akan irin lalurar su Najibu ce. Ta sikila da ake cewa amosanin jini." Marka taja dogon tsaki tana kauda kai gefe. "Ke wallahi Najaatu kin iya samun waje kiyi ta sakin ta." "Allah ba karya nake ba Marka." "Wohoho ni lauya zan ce ne banaso wallahi. Na'Ateeku ban taba gani ya kwanta ciwo ba. Zaki jajiba masa." "Marka abunda nake nufi shine. Shima ai yanada iyali dake dauke da irin ciwon su Kamal. Ba wai ina nufin shine mai ciwon ba. Amman yana dauke da wasu sinadarai na ciwon wanda idan ba'ai gwaji ba kafin aure shine zakiga anata hayayyafan yara masu dauke da ciwon. Yanzu kai ya waye Marka... Sai anyi gwaji kafin ayi aure saboda gudun 'barakar ciwuka. Hakan yasa na ce miki ki bar zancen Na'Ateeku da Waheedah. Domin kulla auren su kan iya haifar da illoli da yawa astagfirullah. Ba tsumi babu dabara. Maganin kar ayi kada a so ma " "Keda Naja kinada kale kalen balai wallahi. Allah shi kyauta " "Wannan shine tushen gaskia Marka. Ba Na'Ateeku ba. Ko wani ne daban yazo neman auren Waheedah ko zainab dole ne kafin ayi auren suje suyi gwaji. Wannan shine babbar shawara da ma'aikatan lapia suka kafa. Don gudun bacewar rana. Azo ana danasanin auren." Marka ta tabe baki hade da jan karamin tsaki. "Gidan aikin da zataje ina fatan nima inada nawa kason acikin albashin nata.?" "Duk ba zai gagara ba Marka. Kuma insha Allahu tare daku duk zamuje taron nan ayi mana gwajin." "Uhm.." cewar Marka. "Bari na tafi. Allah ya kiyaye gaba." "Toh Najaatu. Agyada gidah." "Gidah yaji." "Ke kuma tashi kafin na hamb'are ki. " Takarasa tana mai wurgawa Waheedah harara. Gaba daya maganganun Najaatu sai shawagi sike mata akai. Ta kaikaice kai ta hango ledar taliyar kakkaryawa da tumatirin gwangwani. Na'Ateeku ya sake fado mata arai. CikiN zafin nama ta mike ta shige kuryar daki . Waheedah ta mike jikinta a sanyaye ta shigaa dakin su Kamal. Umma hadiza kuma ta tafi ta yowa Najaatu rakiya. A soro Najaatu ta sake kwantar da hankalin umma hadiza. Da karfafa mata gwiwar ta zage damtse ta fara aikin nan da karfin ta. Ko zata kwatowa kanta da yaranta yanci a idanun su Marka ......... Tab!!! Lamarin ga ya ta azaara Jama a wannan karon zafafa da zafin su suka taso. Ga fa gidan Malam na lado nan mai dauke da iyali da kuma gyatumar sa Marka. Ya rayuwar waheedah Zata kasance acikin wannan littafi. Shin su wanene wai The Adams family?? Na tabo muku bangaren zayn Adams Nasser kuwa? Hmmm inji me ciwon baki Lalle labarin nan yana tafe da wani salo na daban mai taka rawar gani a wannan zamanin namu Gefe d aya dauke labarin yake tafiya da zazzafar kauna marar algus . FARHATAL QALB!!! Lalle FARIN CIKIN ZUCIYAH ..yanki ne dake take rawar gani a zukatan bil adam. Musanman zuciyoyi biyu da ke begen kaunar juna . A stunning love story t afford to miss this chance Ku shigo a dama da ku dan ganin yadda tafiyar Zata kasance . Zafafa biyar. Yan biyar masu baiwa. Hikima, Fasaha da tsarkakkun alqaluma Yadda zaku biya *_ZAFAFA BIYAR din samari ne a rayuwar INAYAH,kowanne a cikinsu akwai wani murdadden Al'amari da ya shata layi tsakaninsa da ita,wawakeken sirri wanda a koda yaushe take kiransa da SANADIN LABARINA_* *_Amma babban abun mamakin a koda yaushe shine,ita dai tasan cewa BABU SO tsakaninsu MEYA KAWO SHI?_* *_Duk da haka tana tunanin yun qundun bala ta fitar da FARHATUL K'ALB a cikin ZAFAFA BIYAR din samarinta,duk da batason su zame mata GURBIN IDO wanda har kullum ba ido bane_* *YA KUKAJI SALON MASU KARATU?* *YADDA SALON YA BAMBANTA DAKO YAUSHE HAKA LABARAN SUKA BAMBANTA DA DUKKA LABARANMU NA BAYA* INAYA(riba biyu)___mamughee SANADIN LABARINA___Rano BABU SO___Billynabdul FARHATUL K'ALB___Miss xoxo GURBIN IDO____Huguma *ZAKI YARDA AYI TAFIYAR NAN BABU KE MADAM?* *_GARZAYA KI BIYA NAKI KUDIN KAN FARASHI KAMAR HAKA_* Biyar:::1k Hudu:::700 Uku::::500 Biyu::::400 Daya:::300 *_zaki saka kudin ta wannan account number din_* HAFSAT UMAR KABIR 2270637070 Zenith bank *Saiku tura shaidar biya zuwa ga* 07040727902 *IDAN KUMA KATIN WAYA NE ZAKU TURA TA NAN TARE DA SHAIDAR BIYAR* 09134848107 *_THANKS FOR THE CONTINUED PATRONAGE_* [11/23, 9:00 PM] Mummyn Yara: _*FARHATAL-QALB*_ _(FARIN CIKIN ZUCIYAH)_ _NA_ _NANA HAFSATU_ _(MX)_ _AREWABOOKS:MISSXOXO_ _WATTPAD: MISSXOXO00_ _ZAFAFA BIYAR PAID NOVELS_ _PG: 6_