← Book details Farhatul Qalbi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 82

Sashe 24

Farhatul Qalbi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ne ya rasu. Jana'iza karfe 10. " "Allahu Akbar... Rai yayi halin sa. Allah ka jikan musulmai ka kyautata namu zuwan." "Amin Amin..." Haka dai sukaita yan addoin su. Kafin Kamal da Najib su tashi su fita don halartar jana'izar. Sai da Waheedah ta tabbatar ta kammala duk wasu aiyuka tukun sannan ta dauki kwandon kulolin abincin . "Umma zan tafi." "Tohm Waheedah Allah ya kai ki lapia ya dawo da ke lapia. Tsautsayi da asara Allah ya kiyaye. Sharrin mutum dana aljan baki daya Allah ya tsare. Ki kula dai sosai. Yi nayi bari na bari. Duk kuwa da ba halin ki bane. Amman dai ki tsaya amatsayin ki idan kinje. Ki kauda kai akan komai kina ji ko?" "Eh Umma..." "Yauwa, To Allah yayi albarka. Dan Allah ki sake yiwa Hajiar godia sosai. Ki kuma ce ina gaysheta. Dan Allah " "Tohm Insha Allah Umma." Waheedah ta fice daga gidan. A bakin zaure ta hango mahaifin su malam na lado. Yana jera rake akan wheelbarrow. "Baba ina kwana.....?" "Lapia kalau ... Ya jikin Hadizan?" Ya tambaye ta muryar rada rada yana magana yana kalle kallen kofar gidan da kwanar layin. Waheedah tayi murmushi kawai. Kasan zuciyar ta mamakin ashe Umman su zaman su take. Babu auren mahaifin su akanta. "Ina tambayar ki kinyi shiru " "Da sauki .. Da sauki jikin." "Toh Allah yakara lapia. Ki mata sannu idan kin koma." "Tohm.." kawai Waheedah ta amsa masa. Da ta dan tsaya ko zai ce wani abun dangane da Umman ta su Wani rake ya dakko ya miqa mata acikin leda fara. "Ungo kya sha..." Hannu biyu ta saka ta karbi raken. "Nagode ... Allah ya karo kasuwa mai albarka." "Amin...." Ya amsata , Ya cigaba da gugar bayan raken da wuka. Cigaba da tafiya tayi tana mai jujjuya ledar raken da ke hannun ta. A haka har ta karasa unguwar ta new gra shurah. Kanta tsaye ta shige gidan bayan ta gaysar da masu gadin dake bakin gate din a zazzaune. Ta murda kofar sashen na Haj Hameedah. Kofar gam take a rufe ba a bude ba kamar jia. Wani madanni mai zanen (bell) kararrawa ta gani a jikin kofar Nan da nan ta danna shi sau uku. Ba jimawa kuwa a ka bude mata kofar. Ta shiga ciki bakinta dauke da sallama. Nadra ce a zaune da Yayan su da suke kira da Zayn. Sai Ahlam daga gege tana danna waya, Tunda ta yi sallama ta shiga ya zuba mata idanu. Dakyar ya janye ya kauda kansa gefe bayan yaci magani. "Ina kwanan ku?" Ta durkusa har kasa ta gayshe su Suka amsa da fara'a lullube a fuskokin su. Banda Zayn daya sake tamke tasa fuskar . "Ina Maa?" Ta tambaya ahankali cikin zazzakar muryar ta. "Maa tana asibiti. Ba daddwa aka kirata surgery' na gaggawa ta tafi." Nadra ta fada tana murmushi. "Allah sarki.. Allah ya temaka, Amin." "Amin . Tace idan kinzo ga abincin ki nan kusa da wata food flask . Na food flask din tace na Umman ku ne " "Alah sarki. Mungode llah ya saka da alkhairi." "Aamin Amin Waheedah. Je kici abincin ko?" "Ai a koshe na ke....Sai dai ko na kai na Umman mu." "Hakan ma yayi .." Ahlam ta dan daga kai kafin tace, "Waheedah kin iya dama kunu please?" "Eh Yaya na iya." "Okay akwai wai garin a kitchen. Pls ki hadamun yanzu. " "Tohm Yaya...." Zayn ya bi Ahlam da kallo. A hankali yace, "Yanzu ke ba zaki dama kunun ba?" "Ban iya ba ne shysa..." Ta amsa shi kanta tsaye. Bai sake cewa komai ba. Ya maida kansa kan tv. Hade da kallon agogon da ke daure a wutsiyar hannun sa. Waheedah na shiga kitchen ta shiga dudduba inda garin yake. Cikin ikon Allah kuwa ta hango shi. Kasa kunna gas din tayi. Ta sake komawa parlorn. "Ya Ahlam... Ko zaa kunnamun." "Okay Gas cooker din?" "Eh..." "Nadra kunna mata please." "Tohm..." "Kinga uhmm Waheedah please ki soyamun hadda wainar flour pls " "Tohm...." Zayn dake jiyo komai ya tabe bakin sa kawai yana girgiza kai. "Ya akai babes???" "Bakomai, Ahlam.." "Ahlam gatsal? Oh please . " "Ai sunan ki ne.... Shine sunan ki" "Koma sunana ne ai be kamata kana fadansa zalla ba. Badan pet names.... Taya zamuyi marital life dinmu ba soyayya ne pls...." "Sanda ZUKATAN mu suka samu FARIN CIKIN kasancewar mu..." "Bangane ba... Kana nufin yanzu ba acikin farin ciki muke da junan mu ba?.... Zayn Adams.. Bangane ba... J-SKINCARE PRODUCTS.. 0813 801 1240 NATION WIDE DELIVERIES. Black soap Kiddies Black soap Sugar body scrub Body butter Kojic acid soap Turmeric soap Goat milk soap Honey soap Carrot soap Face and body cream Hair growth oil Muna yin contact na sabulun cold process ga masu yin biki ko suna Instgram page:J-skincare products Tiktok:jannatskincare Phone number 0813 801 1240 *_ZAFAFA BIYAR din samari ne a rayuwar INAYAH,kowanne a cikinsu akwai wani murdadden Al'amari da ya shata layi tsakaninsa da ita,wawakeken sirri wanda a koda yaushe take kiransa da SANADIN LABARINA_* *_Amma babban abun mamakin a koda yaushe shine,ita dai tasan cewa BABU SO tsakaninsu MEYA KAWO SHI?_* *_Duk da haka tana tunanin yun qundun bala ta fitar da FARHATUL K'ALB a cikin ZAFAFA BIYAR din samarinta,duk da batason su zame mata GURBIN IDO wanda har kullum ba ido bane_* *YA KUKAJI SALON MASU KARATU?* *YADDA SALON YA BAMBANTA DAKO YAUSHE HAKA LABARAN SUKA BAMBANTA DA DUKKA LABARANMU NA BAYA* INAYA(riba biyu)___mamughee SANADIN LABARINA___Rano BABU SO___Billynabdul FARHATUL K'ALB___Miss xoxo GURBIN IDO____Huguma *ZAKI YARDA AYI TAFIYAR NAN BABU KE MADAM?* *_GARZAYA KI BIYA NAKI KUDIN KAN FARASHI KAMAR HAKA_* Biyar:::1k Hudu:::700 Uku::::500 Biyu::::400 Daya:::300 *_zaki saka kudin ta wannan account number din_* HAFSAT UMAR KABIR 2270637070 Zenith bank *Saiku tura shaidar biya zuwa ga* 07040727902 *IDAN KUMA KATIN WAYA NE ZAKU TURA TA NAN TARE DA SHAIDAR BIYAR* 09134848107 *_THANKS FOR THE CONTINUED PATRONAGE_* _*FARHATAL-QALB*_ _(FARIN CIKIN ZUCIYAH)_ _NA_ _NANA HAFSATU_ _(MX)_ _AREWABOOKS:MISSXOXO_ _WATTPAD: MISSXOXO00_ _ZAFAFA BIYAR PAID NOVELS_ _PG:27_ ===== Tunda ya dawo daga office yake a gajiye. Kansa har wani sara sara masa yake yi. Abun ka da farar fata tuni har tayi ja. Jijiya katuwa ta futo radau ta wajen goshin sa. First aid box ya dakko dake kan beside drawer. Ya bude ya zaro panadol pain and fever . Ya ballo biyu ya kurba da ruwa ya sha. Ya dan jima a bakin gado yana jiran kan ya dan lafa masa. Dan so yake yaje ya dubo mahaifiyar su ganin motar ta a fake ta dawo. Kan ya na dan lafa masa ya miqe ya shige bandaki ya watso ruwa. Ya sauya kayan zuwa farar riga ta jallabiya. Da dogon wando aciki da singlet. Ya dakko turaruka ya feshe jikin sa da su. Ya kullo dakin sa bayan ya kammala ya tunkari sashen Haj Hameedah. Bakinsa nata motsawa sakamakon zikirin da yake yi Da sallama ya shige cikin gidan. Mahaifiyar tasu na zaune akan kujera hannunta da remote control tana kallon tashar labarai ta aljazeera. Juyawa tayi tana amsa sallamar sa. Yayinda kunnuwan sa suka dauki sautin karatun Waheedah daketa rerawa a daki. "Maaa!" "Na'am Zayn .." "Ashe kin dawo ...? Ya aiki?" "Alhamdulillah. Munyi mun kammala lapia sai fatan Allah ya bata lapia Amin " "Amin Yaa rabbi." "Tunda na dawo ai ko sama ban hau ba " "Labarai kike kalla... Amma ai ba murya." "Eh wallahi. Na rage ne. Saboda karatun Waheedah. Qira'ar dadin sauraro. Kai Alhamdulillahi ala ni'imatul Islam and all it entails." "Aamin Amin.... Karatun dadi kam." "Wallahi. Karka so kaji yadda nake ji a raina. Beauty with brains. Yarinyar nan tayi kokari wallahi " Shi dai bai sake cewa komai ba. Illa dai ya maida kansa ga tv da suke kallon kurame. "Baka da lapia ne." "Kai na ne yake ciwo." "Allah ya kara sauki. Ga abincin ka can akan dinning. Na dawo late so spaghetti ce kawai da soyayyen kifi." "Nagode sosai Maa. Allah ya saka miki da alkhairi." "Amin..." Tashi yayi ya tafi dinning din. Kamshin abincin nata dukan hancin sa. Ya ja kujera ya zauna yana mai matso da kayan abincin gaban sa. Can sai ga Waheedah ta sakko kasan. Caraf suka hada idanuwa da Maa . Ta zube a k sa fuskarta dauke da murmushi "Ashe kin dawo? Sannu da zuwa. Ina wuni. Ya aiki?" "Alhamdulillah Waheedah. Ai na dan jima da dawowa. Ina zaune anan ina sauraron karatun ki da kira'ar ki mai dadin sauraro." Waheedah tayi murmushi kawai . Kafin tace, "Umman mu na gayshe ki. Tace a miki godia, Allah ya saka miki da alkhairi Amin." "Allahumma Aamin....... Kinci abincin rana kuwa?" "Ai a koshe nake Maa." "Ah haba dai . Abincin safe ai baya rike ciki Waheedah. Kije kitchen naki yana nan dana Umman ta ku. Sai ki tafi dashi " "Mungode Allah ya biya ki da aljanna." "Amin Waheedah. Tare da ku baki daya.... Ina yayyunki maza.?" "Suna gidah na baro su. Amman daya ne ya girme ni. Muna kiran sa da Yaya Kamal. Dayan kuma kanina ne Najib." "Allah sarki.. ... Suma suna wani abunne na aiki haka?" "A'a saboda basuda lapia " "Toh pha. Wacce irin rashin lapia ce haka?" "Sickle cell. Amosanin jini." "Wayyo. SubhanAllah! Allah yabasu lapia mai dorewa Amin . Allah sarki hadiza. Waye me sickler agidan na ku." "Gaskia ba kowa. Dan de likitoci sunce da Umman mu da baban mu dik AS ne ko me ne shysa suka haifo sikila." "SubhanAllah. .. Allah yasa kaffarane Amin. Ke de me lapia ce amman ko?" "Eh ni AS ce .." "Yauwa gwara da kukayo gwaji. Saboda fadaawa halakar haifo yara marasa cikakkiyar lapiar da za'ayi ta magani har karshen rayuwa." "Wallahi..." Waheedah ta fada a sanyaye "Je ki ci abincin Waheedah. Allah ubangiji yana tare da ku. Ya kuma san komai. Da yardar Allah . Zai kawo muku saukin rayuwa kinji?" "Amin.. Insha Allah ." "Allah ya basu lapia Amin." "Amin" "Idanun ki short sitedness ne ko long?" "Short ....." "Allah yabaki lapia kema kinji ko?" "Amin Maa." "Yauwa yalla. Je kici abincin. Allahumma bareek." "Amin Maa." Mikewa tayi ta shige cikin kitchen din. Babban plate ne da yaji tuwo da miyar egusi da tasha nama. Basmala tayi. Ta zauna tana ci.
Chapter 24 · 0% Book details