Sashe 45
Farhatul Qalbi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
wata leda viva. Ta fice wajen tana, "Kuyi hakuri kawayen amana.... Bari na sauya kaya " Dakin su Zainab ta shiga ta sauya kayan. Ta shafe jikinta da mai. Ta goga ruwan alumun a hammatar ta. Sannan ta shafe jikinta da turaren ruwa. Duk sanda ta shafa ko ta dauki kwalbar sai ta tuno yayan su marigayi Kamal. Yanzun ma hakan ne ya kasance. Siraran hawaye suka zubo mata kan fuskar ta. Ahankali cikin rawar murya tace, "Allah ya jikan Yaya Kamal.. Rabbi ka gafarta masa. Ka shayar da shi ruwan alkausara. Rabbi kasa yana aljannatul firdwas madaukakiya da shi da sauran musulmai baki daya, Amin " Da sauri ta karasa adduoin ta sauya kayan nata zuwa wanda ta dakko. Bata wani tsaya kwalliya ba. Ta dai shafa farar hoda da man lebe. Ta yi daurin dankwalin channel o. Ta yafa wadataccen mayafin da Umman su ta bar mata. "Muje..." "Kawata kina lokaci. ." cewar Basira. "Kece me yin lokaci tawan..." Waheedah ta fada tana murmushi. "Gaskia Basira ta fada... Kina kamshi muna bin ki da humra. Kinga yadda kika tsatso kyau tawan? Sai ma a uniform. " Fannah ta fada tana dariya Ita dai Waheedah murmushi kawai take. Tayi wa Deluwa sallama suka fice bayan ta sake duba jikin Najib. "Ni fa gida zan wuce ...." Basira ta fada . "Kai kawata...." "Allah tafiya .kawata " "Eh kinsan ni kadai ce basu dawo ba ." "Eh kuwa." "Nima dai tafiyar zanyi. Zan tsaya shagon Na'Ateeku na sayo cefanen da Umma ta bani." "To shikenan... Idan na dawo zaku jini. Godia nake kawayen amana .. Allah ya albarkar ci zumuncin mu. Aamin" "Aamin Yaa rabbi ." "Aamin Aamin ." Mikewa tayi kanta tsaye zuwa hanyar new gra shurah inda gidan aikin Umman su yake. Ta dade bata je ba . Rabon ta da zuwa tun suna rubuta jarabawar kare sakandire. Bakinta dauke da adduoi ta karasa shiga layin. Manya manyan motoci suna fa ke a kofar gidajen unguwar. Kanta tsaye ta shiga cikin gidan na The Adams Family.... Taci saa kuwa kofar sashen baa kulle take ba. Wata mai aiki tafuto daga cikin gidan tana tattare kofar. "Sannu Ina wuni...?" "Lapia kalau.... " "Ya aiki?" "Alhamdulillah..... Ki shiga suna ciki." "Tohm..." Ta amsata cike da ladabi. Ta kutsa kai ciki bakinta dauke da sallama. "Wa'alaykm Salam.... Ahhh wata sabon ga ni..." Nadra tafada tana mikewa tsaye.. Bata da kyama ko ganin kaskancin na kasa da ita. "Ina wuni sis....?" "Alhamdulillah...dear sis." "Maa ga Waheedah... Umma ga Waheedah.." Daga kitchen suka fito a tare. Haj Hameedah da Umma Hadiza. Fuskokin su fadade da murmushi. Ta tsugunna har kasa ta gayshe da su. Suka amsa duka fuskokin su a sake. "Lapia lau...... Waheedah na." Maa ta fada tana murmushi. "Alhamdulillah....." Umma Hadiza ta amsa ta. "Je ga abinci can a dinning ki zuba kici." Haj Hameedah tace da ita. "A koshe naki Maa." "To kya tafi da shi... Kwana biyu kin manta da mu. Sai yau?" "Tuba na ke Maa..." Zama tayi tanata lankwasa hannayenta kafin ta sake cewa, "Na samu admission a school of nursing....... _INA MASOYA KUMA MA'ABOTA KAMSHI MA SU KAUNAR KAMSASAWA A KODA YAUSHE? DOMIN KAMSHI RAHAMA NE.._ _TO KU MATSO, DOMIN WANNAN KARON MA ZAFAFA BIYAR SUN ZO MU KU DA TALLAN MASARAUTAR KAMSHI NA KAMFANIN TURAREN *YERWA INCENSE AND MORE*_ _A *YERWA INCENSE AND MORE* ZA KU SAMU TURARUKAN WUTA NA *GIDAH, NA KAYA, NA TSUGUNNO* BA A NAN KADAI SUKA TSAYA BA. AKWAI *KHUMRAHS* MASU KAMSHIN LARABAWA DANA FRUITS KAI DAMA KAMSHIN TURAWA. AKWAI KHUMRAHS TA MATAN AURE DA TA YAMMATA_ _SANNAN SU NA DA *TURAREN WANKA DANA SHAFAWA BAYAN AN KAMMALA WANKA.* BA ANAN TURARUKAN NA SU SUKA TSAYA BA. AKWAI *KULACCAM* MAI MATUKAR KAMSHI DA SANYAYA ZUCIYA, SANNAN SU NA DA *MADARORIN TURARUKA NA JIKI DA NA KAYA*_ _AKWAI TURAREN *AL'AJABU NA TSUGUNNO DA KHUMRAH* DIN SA_ _SANNAN SU NA DA *TURAREN GASHI NA CREAM DA KUMA SPRAY DIN SA NA FESAWA*_ _BA ANAN SUKA TSAYA BA. SU NA DA *TURAREN MOPPING, DA NA BANDAKI AKWAI NA RUWAN WANKI DA NA FESAWA A DRAWER KO AKWATI*_ _AKWAI KAYAN GYARARRAKI NA FATA. KUJERAR TSUGUNNO, KASAKE NA WUTA, COAL IGNITER TA KUNNA GARWASHI, ELECTRIC BURNERS DA ENGLISH COAL_ _AKWAI LAFFAYAS DA SAURAN TURARUKA NA KAMSHI KALA KALA_ _SU NA BADA KAYAYYAKIN SU AKAN FARASHIN SARI KO SAYA AKAN DAYA DAYA. SANNAN SUNA TURA KAYAYYAKIN SU KO'INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE. KAYAN SU YAN CHADI NE DA SUDAN DA KUMA YERWA WATO MAIDUGURI._ _KYAU, INGANCI DA RAHUSA SAI KAYAYYAKIN KAMFAMIN YERWA INCENSE AND MORE. SAI KUN GWADA ZAKU BAMU LABARI_ _NAMBAR TARHON SU DA ZAA KIRA KO MUSU MAGANA TA WHATSAPP ITACE: 08095215215_ _INSTAGRAM HANDLE DIN SU: @yerwaincense_and_more_ _YERWA INCENSE AND MORE: A NUMBER ONE STOP SHOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS AND MORE_ *_ZAFAFA BIYAR din samari ne a rayuwar INAYAH,kowanne a cikinsu akwai wani murdadden Al'amari da ya shata layi tsakaninsa da ita,wawakeken sirri wanda a koda yaushe take kiransa da SANADIN LABARINA_* *_Amma babban abun mamakin a koda yaushe shine,ita dai tasan cewa BABU SO tsakaninsu MEYA KAWO SHI?_* *_Duk da haka tana tunanin yun qundun bala ta fitar da FARHATUL K'ALB a cikin ZAFAFA BIYAR din samarinta,duk da batason su zame mata GURBIN IDO wanda har kullum ba ido bane_* *YA KUKAJI SALON MASU KARATU?* *YADDA SALON YA BAMBANTA DAKO YAUSHE HAKA LABARAN SUKA BAMBANTA DA DUKKA LABARANMU NA BAYA* INAYA(riba biyu)___mamughee SANADIN LABARINA___Rano BABU SO___Billynabdul FARHATUL K'ALB___Miss xoxo GURBIN IDO____Huguma *ZAKI YARDA AYI TAFIYAR NAN BABU KE MADAM?* *_GARZAYA KI BIYA NAKI KUDIN KAN FARASHI KAMAR HAKA_* Biyar:::1k Hudu:::700 Uku::::500 Biyu::::400 Daya:::300 *_zaki saka kudin ta wannan account number din_* HAFSAT UMAR KABIR 2270637070 Zenith bank *Saiku tura shaidar biya zuwa ga* 07040727902 *IDAN KUMA KATIN WAYA NE ZAKU TURA TA NAN TARE DA SHAIDAR BIYAR* 09134848107 *_THANKS FOR THE CONTINUED PATRONAGE_* [11/23, 9:02 PM] Mummyn Yara: _*FARHATAL-QALB*_ _(FARIN CIKIN ZUCIYAH)_ _NA_ _NANA HAFSATU_ _(MX)_ _AREWABOOKS:MISSXOXO_ _WATTPAD: MISSXOXO00_ _ZAFAFA BIYAR PAID NOVELS_ _PG:50_ "Waheedateey......!!!" Ibrahim ya kira sunan Waheedah , Cikin karya harshe da jan sunan ya kara masa gard'i.. Juyawa tayi don gayshe shi. Saboda baki dayan unguwar su shi kadai ne ke kiranta da Waheedateey.. "Ina kwana Ya Ibrahim...?" Karasawa yayi ku sa da ita. Ta matsa gefe. Suna tafiya tare. Ahankali tamkar rad'a ya ce da ita, "Alhamdulillah.... Waheedateey.... Masha Allahu!! Naji a unguwa kun samu gurbin karatun nursing ko?" "Eh...." "Na tayaki murna sosai wallahi...Na kuma yi farin ciki. Allah ya cika miki sauran burukan ki Waheedateey. Ya bada sa'ar karatu. Aamin." "Aamin Ya Ibrahim...." Suka cigaba da tafiya cikin silar kurame da basa magana. Sanye cikin takalmi dan Madina. Ya zube hannuwan sa acikin aljihun wandon sa. A haka suka karasa gidan na su Fanna. Wanda sunci saa . Fitowar ta kenan itama cikin uniform. Ta yi kyau kwarai matuka itama . Suka dashare wa juna baki kafin su rungume junan su cikin tsantsar so da shakuwa. "Kawata.... Lamarin ba sauki...." Cewar fannah... Ta karasa fada tana tafawa da Waheedah... Waheedah tayi murmushin da hakoran ta suka bayyana... Ibrahim ya dashare nasa hakoran yana kallon Waheedah cikin tsantsar so da kulawa. "Kema tawaje na kin fito shar da ke na ke gaya miki...." Suka sake tafawa. Sai a sannan fannah ta dubi Ibrahim da ke gefen su ya zubawa Waheedah idanu ko kyaftawa ba ya yi.. "Ina kwana Ya Ibrahim...?" "Lapia Lau fannah .. Ina taya ku murna.. Allah yasa kun shiga a sa'a." "Amin Ya Ibrahim .." "Aamin Aamin.... Muje Allah ya sa dai Basira ta shirya " "Amin dai..." Mikewa suka sake yi ba ni sa da gidan su Fannah. Suka karasa gidan na su Basira. "Bari na kira ta.." cewar fannah.... Ta shige cikin gidan da sauri. Ibrahim ya sauke nannauyar ajiyar zuciya. Guguwar so na da 'da kada shi. Yau ga shi ga Waheedateey din sa a tsaye su kadai. Ya lankwasar da kai. Cikin salon soyayya yace da ita. "My life ....." Wayaga an tsikari kakkausa. Sam bata ma san wai da ita yake ba. Sai da ya sake cewa, "Waheedateey.... My life." "Ya Ibrahim .." "Ki tema ka ki agaza ki dena fakewa da Yayan nan.... Kinji?." "Uhum..." "Haba mana.... Wai Yaya .. ki dena kallo na a matsayin Yayan ki .. Kaunar ki na ke... Kauna ta gaba da yan uwantaka.. Kauna ta soyayyah .. Kaunar aure. Ta hanyar zama daya. Kinji?" Ta rasa abun da zata ce da shi. Tamkar ta kurma ihu haka take ji. Allah da ikon sa sai ga fitowar Fanna da Basira. Basira ma ta shirya tsaf. Uniform dinnan ya dau guga. Ko'ina tsaf tsaf. "Shegiyar gari... Kawalliya. Umma tace tana bin ki bashin wankan yau." Basira ta fada tana nuna Waheedah.. Hakan da Basira ta fada. Ba karamun mafaaka ya kawowa Waheedah ba. Tayi saurin shigewa cikin gidan na su Basira tana cewa, "Tuba nake .. Kai na bisa wuya. Dole na gayshe da ummah..." Ta karasa fada hade da shigewa dakin Umman Basira tana gayshe da ita. Sannan ta fito suka dauki hanyar makaranta. Ibrahim na biye da su yaki komawa gidah. Suka tsaya a bakin titi suna jiran dan adaidaita sahu. "Ya Ibrahim da ka koma...." "Haba Waheedateey... Ai ba zan iya tafiya ba na bar ki... Zuciyata ba zata samu sukuni ba." Fannah da Basira suka tsunkuli juna suna dariya. Waheedah kuwa ta kasa cewa komai ba. Saboda rashin abunda zata ce da shi Sun kai mintina ashirin kafin su samu adaidaita ya tsaya. "School of nursing....." Suka hada baki wajen gayawa mai adaidaita sahun. "Dari shida...." Ya basu amsa yana karo wakar Abba gidah gidah da ke tashi a gidan rediyon daya jogana. "Haba malam...." "Haba Yayanaa... 600 fa ka ce." "Kaga mai gida nawa zasu bayar?" Ibrahim da ke gefe ya tambaye shi. "Ah aboki na. Saboda kai su bada 500. Shine gaskiya." "To godia muke .. ku shiga Waheedateey .." ya karasa fada yana mai laluba aljihun wandon sa. Ya ciro nera dari biyar data hade jikin ta ya mikawa mai adaidaitan. "Sannu da kokari ... " Basira ta fada. Hade da shigewa ciki. Fanna tabi bayan ta. Ta zauna a tsakiya itama. Tana wa Ibrahim din godia Daga karshe kuma Waheedah ta shiga . "Mungode kwarai