Sashe 36
Farhatul Qalbi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
tukun sannan dakyar Umma Hadizan ta sanar mata komai. Ta kuma kira Waheedah itama ta dora da wasu abubuwan Ciki harda batun yadda suka wanye da Marka da safiyar yau. Haj Hameedah har hawaye ta zubar na tausayi. Anan ne ta kawo kokon barar samun Waheedah . Kan Umman ta bata Waheedah ta karasa makaranta awajen ta. Har ya zuwa auren ta. Saboda tsananin kaunar da Moha ke yi Mata. "Kinyi shiru Hadiza ..." "Ba shiru nayi ha Haj ... Ai da na kowa ne. Kuma da kyakkyawar mu'amala da zuciya kikeson kasancewar Waheedah a tare da ke. Idan ni na amince akwai kakarta da mahaifin ta. Sai hukuncin da suka zartar..." "Tohm shikenan ni de ina kan bakana. Ina kuma fatan hakan ya zamo mana alkhairi agare mu baki daya .." "Allahumma Aamin..." "Kije ki sanar da Najan Isubu kan yadda za'ayi da kayan dakin. Tunda Markan ta kafe..." "Tohm Umma... Maa na tafi " "Tohm Waheedah... " Moha harda kukan sa. Dakyar dai aka yageshi daga jikin waheedan. Ya tafi shi kuma ya koma dayan parlorn da suke ce da shi study anan ya zauna ya nata kuka . Umma Hadiza kuwa tacika da madaukakin mamakin Haj Hameedah da irin kaunar da take musu ko kadan ba kyama ko ganin kaskanci. Kasancewar su din ba wasu bane. Fyace talakawa da ke neman cin yau dana gobe .. _INA MASOYA KUMA MA'ABOTA KAMSHI MA SU KAUNAR KAMSASAWA A KODA YAUSHE? DOMIN KAMSHI RAHAMA NE.._ _TO KU MATSO, DOMIN WANNAN KARON MA ZAFAFA BIYAR SUN ZO MU KU DA TALLAN MASARAUTAR KAMSHI NA KAMFANIN TURAREN *YERWA INCENSE AND MORE*_ _A *YERWA INCENSE AND MORE* ZA KU SAMU TURARUKAN WUTA NA *GIDAH, NA KAYA, NA TSUGUNNO* BA A NAN KADAI SUKA TSAYA BA. AKWAI *KHUMRAHS* MASU KAMSHIN LARABAWA DANA FRUITS KAI DAMA KAMSHIN TURAWA. AKWAI KHUMRAHS TA MATAN AURE DA TA YAMMATA_ _SANNAN SU NA DA *TURAREN WANKA DANA SHAFAWA BAYAN AN KAMMALA WANKA.* BA ANAN TURARUKAN NA SU SUKA TSAYA BA. AKWAI *KULACCAM* MAI MATUKAR KAMSHI DA SANYAYA ZUCIYA, SANNAN SU NA DA *MADARORIN TURARUKA NA JIKI DA NA KAYA*_ _AKWAI TURAREN *AL'AJABU NA TSUGUNNO DA KHUMRAH* DIN SA_ _SANNAN SU NA DA *TURAREN GASHI NA CREAM DA KUMA SPRAY DIN SA NA FESAWA*_ _BA ANAN SUKA TSAYA BA. SU NA DA *TURAREN MOPPING, DA NA BANDAKI AKWAI NA RUWAN WANKI DA NA FESAWA A DRAWER KO AKWATI*_ _AKWAI KAYAN GYARARRAKI NA FATA. KUJERAR TSUGUNNO, KASAKE NA WUTA, COAL IGNITER TA KUNNA GARWASHI, ELECTRIC BURNERS DA ENGLISH COAL_ _AKWAI LAFFAYAS DA SAURAN TURARUKA NA KAMSHI KALA KALA_ _SU NA BADA KAYAYYAKIN SU AKAN FARASHIN SARI KO SAYA AKAN DAYA DAYA. SANNAN SUNA TURA KAYAYYAKIN SU KO'INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE. KAYAN SU YAN CHADI NE DA SUDAN DA KUMA YERWA WATO MAIDUGURI._ _KYAU, INGANCI DA RAHUSA SAI KAYAYYAKIN KAMFAMIN YERWA INCENSE AND MORE. SAI KUN GWADA ZAKU BAMU LABARI_ _NAMBAR TARHON SU DA ZAA KIRA KO MUSU MAGANA TA WHATSAPP ITACE: 08095215215_ _INSTAGRAM HANDLE DIN SU: @yerwaincense_and_more_ _YERWA INCENSE AND MORE: A NUMBER ONE STOP SHOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS AND MORE_ *_ZAFAFA BIYAR din samari ne a rayuwar INAYAH,kowanne a cikinsu akwai wani murdadden Al'amari da ya shata layi tsakaninsa da ita,wawakeken sirri wanda a koda yaushe take kiransa da SANADIN LABARINA_* *_Amma babban abun mamakin a koda yaushe shine,ita dai tasan cewa BABU SO tsakaninsu MEYA KAWO SHI?_* *_Duk da haka tana tunanin yun qundun bala ta fitar da FARHATUL K'ALB a cikin ZAFAFA BIYAR din samarinta,duk da batas on su zame mata GURBIN IDO wanda har kullum ba ido bane_* *YA KUKAJI SALON MASU KARATU?* *YADDA SALON YA BAMBANTA DAKO YAUSHE HAKA LABARAN SUKA BAMBANTA DA DUKKA LABARANMU NA BAYA* INAYA(riba biyu)___mamughee SANADIN LABARINA___Rano BABU SO___Billynabdul FARHATUL K'ALB___Miss xoxo GURBIN IDO____Huguma *ZAKI YARDA AYI TAFIYAR NAN BABU KE MADAM?* *_GARZAYA KI BIYA NAKI KUDIN KAN FARASHI KAMAR HAKA_* Biyar:::1k Hudu:::700 Uku::::500 Biyu::::400 Daya:::300 *_zaki saka kudin ta wannan account number din_* HAFSAT UMAR KABIR 2270637070 Zenith bank *Saiku tura shaidar biya zuwa ga* 07040727902 *IDAN KUMA KATIN WAYA NE ZAKU TURA TA NAN TARE DA SHAIDAR BIYAR* 09134848107 *_THANKS FOR THE CONTINUED PATRONAGE_* [11/23, 9:01 PM] Mummyn Yara: _*FARHATAL-QALB*_ _(FARIN CIKIN ZUCIYAH)_ _NA_ _NANA HAFSATU_ _(MX)_ _AREWABOOKS:MISSXOXO_ _WATTPAD: MISSXOXO00_ _ZAFAFA BIYAR PAID NOVELS_ _PG:41_ _WANNAN LITTAFI DA MA SAURAN NA *ZAFAFA* NA *KUDI* NE. DAN ALLAH KI/KA BIYA KUDI KI/KA MALLAKI NA KI. DON GUDUN SHIGA HAKKOKIN MASU RUBUTAWAR DA MA WADANDA SUKA CIRE KUDI SUKA SAYA..._ *Waheedah* na tafe akan hanya tana mamakin maganganun Haj Hameedah. Su kuma haka Allah ya yi su da kaunar mutane? Kyautatawa da sanin ya kamata? Ta sauke zuciya tana mai kambama dattako irin na Hajia Hameedah. A haka har ta karasa unguwar su Kai tsaye ta wuce gidan Najan Isubu. Bakinta dauke da sallama ta shiga. Najan na share tsakar gidan. Da sauri Waheedah ta karbi tsintsiyar bayan tayi sallama. "Da kin basshi Waheedah.." "A'a aunty zan karasa." "Toh sannu da kokari. Allah ya saka da alkhairi..." "Aamin Amin" Waheedah ta tattare tsakar gidan tas ta zuba dattin a shara. Sannan ta isa ga wata jarka ta tsiyayi ruwa ta wanke hannuwan ta da wani guntun sabulu data gani a gefen buta. "Zo ga abinci Waheedah.." "Wallahi a koshe nake aunty..." "Abar marmari ce... Shinkafa da wake. To bari dai na zuba miki ki kai wa Yayan ku da Najib... Ya ya jikin na su kuwa? Ina tason shiga idan na kintsa komai .." "Tom aunty... Angode. Allah ya saka da alkhairi. Da sauki. Na baro su a gidah " "Amin Aamin..To Alhamdulillah" "Aunty daman Umman mu ce ta aikoni wajen ki..." "Tohn Allah sa muji alkhairi Waheedah." "Aamin ... Dama dazu ne da safe Marka ta zo da wasu samari su biyu. Na san su ma ..." "Kwarai na ji zancen dazu a shagon Na'Ateeku. Fandau na fada. Kinsan uwar guntsi fetsi ce " "Eh... Tohm shine wai Markan zata bada hayar dakin. Tace na tattare kayana." "SubhanAllah.... Wallahi da naji suna zancen a shagon. Bata fadi wani daki bane. Da girman Allah na dauka dakin dake waje ne... Kai Marka batada kirki wallahi. Yanzu ya ake ciki...?" Waheedan ta sheda mata komai ba abunda ta bari. Ta karkare da, " Shine bayan na sanarwa Umman tace na gaya miki . Ko da akwai abubuwan da zaa tsitstsinta a sayar.. Tace dai na gaya miki. Dik abunda kika yanke yayi." Najan Isubu ta sauke zuciya tana matsa hannuwa. Cikin zuciyar ta kuwa tattare yake da tunanin yadda zata bullowa lamarin. Saboda gudun sharrin Marka .. "Shikenan Waheedah... Allah ya dafa mana, Aamin." "Amin aunty " "Dauki abincin kije... Zan biyo sahun ki insha Allah ... Allah ya dafa mana ya kawo mana mafita. Kije gani nan. Insha Allah." "Tohm Aunty..." Waheedah ta dauki kwanon abincin dake kamshin man kulli da albasa. Gefe daya kuma kamshin yajin tafarnuwa ne yake tashi. Ta fice daga gidan bayan tawa Najan Isubun sallama. Gidah ta nufa. Ta shiga bakin ta dauke da sallama. Yaya Kamal na daga gefen dakin su a zaune ya tsakure. Yayinda Marka ke ta kai da kawowa a cikin dakin Umman tasu. Wanda ya zamana na waheedah a yanzu. Ta gama fito da kwanuka da wani kwali babba da kayan su ke a ciki. Da sauri waheedan ta ajiye kwanon abincin agaban Kamal. "Gashi nan ku ci Yaya .. Kai da Najib. " Marka ta watsa mata wani banzan kallo tana mai nuna dakin da yatsanta daya. "Shiga ki kwaso sauran tarikicen kayayyakin ku. Kin zo kin tsaya qerere a kai na saboda rashin girmamawa ga nagaba da ke. " "Kiyi hakuri..." Ta fada a raunace. Kafin ta ajiye yar jakar ta a gaban Kamal ta shiga dakin da sauri. Dan wulaakancin Marka baki daya ta hautsina dakin. Wasu ababen fashewar baki daya sun fashe a tsakiyar dakin. Sauran tsakin dafawar su da wani ragowar manja baki daya Marka ta antayar da su a dakin.. Waheedah ta karasa fitar da komai ahankali. Wata drawer dinsu ce da kayan su ke ciki ta kasa janyota. Gashi hatasan kiran Yayan su. Ganin ba lapia ce dashi ba. Tanata kiciniya sai ga Najan Isubu ta shiga tanata rangajin rangada sallama . "Ko bakwa ji ne inata salamu alaikum.?" "Yo sallamar ce kikayi ta iya cikin ki... Kina rowar buda baki. " Marka ta fada tana yamutsa fuska "Tuba nake uwar kowa. Marka tsohuwa mai ran karfe .. kowa ya ja da ke juji ne...." "Najan Isubu manyan kasa. " "Wane ni ga ku? Tuba nake . Fatan na same ki lapia?" Marka ta shiga busa hanci da daga kai. Jin yadda Najan Isubun ke fadada mata kai da washin da take mata. Ta dan yi yatsina. Kafin ta gaftari ragowar goron hannun ta tace, "Lapia Lau... Ya Isubu kalau yake idan kun waya ko?" "Alhamdulillah Marka .. Yama gaysar da ku." Naja ta karasa fada hadi da yaye yamfadin kofar dakin da Waheedah ke ciki. Ta zura kanta tana duba komai. Shigewa ciki tayi. Ta tsaya tana bin dakin lungu da sako. Gabas da yamma. "Dawo ta nan ki dauke wadannan. Bar daukar kaya masu nauyi kina budurwa kinji ko?" "Tohn aunty ..." Ta karasa fada hade da sunkuyawa ta debi kayan da ke bayan kofa. Najan Isubu taja mayafi tayi madaurin kugu da shi. Ta shiga jan drawer a hankali har ta futar da ita daga dakin Sannan Waheedah ta tayata suka karasa fito da sauran kayayyakin. Shigar Najib kenan gidan. Najan Isubun ta sanya shi ya curo yamfadin kofar dakin da aseberin da ke jikin window din dakin. "Kayan sawar ku ne anan din ko...?" "Eh ..." "To kwashe su ki zuba acikin wadancan Ghana must go din." "Toh.." "Yauwa bara na leka na kira dan gwangwan din... " "Tom aunty..." "Marka zan wa dan gwangwan iso..." Bata tanka ta ba. Tayi kwafa dai kawai. Ganin hakan ya sanya Najan Isubu fita ta yiwa dan gwangwan da zai sayi kayan iso. Ya shigo da sallama. Ya gayshe dasu. Kana ya shiga kallon kayan yana taba wasu daga ciki don jin ingancin su. Bayan ya gama gani duka. Najan tace su fita. A wajen sukayi maganar kudin kayan. Baki daya ya saye su dubu biyar da dari hudu da hamsin.