Sashe 73
Farhatul Qalbi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
wasu abubuwan." "Ah Zahara'u.. Yanzu kika shigo?" "Eh na zo ni Deluwa... Tafiya ma zan. Zan dora sanwa." "Allah sarki " Zahara'u ta fi ce. Ya yinda Deluwa ta tsugunna gaban wuta tana gyaggyara ledojin da zasu kama mata gaushin. Ba jimawa malam na lado ya shiga gidan . Bayan sa kuma Malam Ubaliyo ne malamin masallacin arewa. Gaishe da Marka malam Ubaliyo yayi ya tsugunna yana bin ta da kallon tausayi. Wai Marka ce a kwance bata iya daga yatsanta ma. Ciwon ya faru ne baki daya cikin kwanaki uku. Dan ko a satin da cutar zata same ta ma. Taje bakin kasuwa ta surfawa wanzam damuna ashariya ratsa ratsa da aibace aibace. Malam na lado ya kalli malam Ubaliyo. Malam Ubaliyo ya sauke zuciya kafin yace, "Ubangiji Allah ya yaye miki Marka. Ya sa zakkar jiki ce. Allah yasa wannan cuta ta ki.. Kankarar zunubai ce. Amin. Yauwa kafin ki kwanta ciwo ki gafarce ni. Du bada ba zaki iya magana ba ko ambatar wani abun. Malam na lado ya sanar mun damuwar sa ta, "Kan lalle kin tsaya kan bakan ki na cewar ya aiwatar da shika uku ga Deluwa matar sa. Dan Allah Marka kiyi hakuri ki janye zancen ki. Wannan tsauraran hukunci duk basu kamata ba. Yarinyar nan Hadiza itama ashe auren tuntuni babu kin saka ya shikata Marka. Aka dawo kan Sa'adatu itama ga abunda ya dawo akan diyar ta da ita kan ta . Na lado yace kince kar su soma dawowa gidan nan. Bayan har yanzu da aure a tsakanin saadatun da na lado. Marka kiyi hakuri da abunda labbana zasu furta. Amman bakya ganin wadannan hukunce hukuncen da kike yankewa suna tsauri da kaucewa aqidar islama Marka? Astagfirullah ki dubi zancen da zan fada da idanun Basira... Marka" Duk kuwa da a kwancen da ta ke. Hakan bai hana Marka dankara masa harara ba. Ji take tamkar inama zata iya mikewa. Ta yi kutufo da shi. "Marka... Dan Allah ki dubi komai yadda yake ki mayar da shi muhallin sa. Kiyi Imani da Allah da haqiqar sa Marka..Imani na gaskiya shi ne rayuwa da farin ciki. Ba a samun kwanciyar hankali sai dai imani da Allah mai girma da buwaya. Duk zuciyar da ba ta da imani za ta zauna cikin tsoro da rudani da rauni da rashin kwanciyar hankali. Imanin da ake samun tsira da shi shi ne imani da Allah, wanda ma anarsa shi ne gaskatawa da yankewa cewa Allah shi ne Ubangijin komai, mamallakinsa, mahaliccinsa, kuma shi kadai ya cancanta a kadaita shi da ibada, ta sallah da azumi da addu a da fata da tsoro da qasqantar da kai, kuma shi ne ya siffatu da siffofin kamala gaba daya, ya tsarkaku daga dukkan wani aibi da tawaya, mai girma da buwaya.Imani da Allah haske ne mai kaiwa zuwa ga adalci, haske ne zuwa ga yanci, haske ne zuwa ga ilimi da sani, haske ne zuwa ga shiriya, haske ne zuwa ga nutsuwa da kwanciyar hankali Marka... "Imani da Allah ya qunshi imani da Mala ikunsa, da littattafansa, da ranar lahira, da imani da qaddara, alkhari ko sharri. Irin wannan imanin shi ne samun arzikin mutum, kai shi ne ma Aljannar duniya ga mumini, wanda qarshensa Aljannar lahira ce Insha Allahu. Ashar ance: Shi ne qudurcewa da zuciya, da furtawa da harshe, da aiki da gabbai, yana qaruwa da da a ga Allah, yana kuma raguwa da sabon Allah. Idan an gane wannan to a sani tushen karbar ayyuka a wurin Allah shi ne Imani, saboda fadin Allah mai girma da buwaya : Duk wanda ya yi ayyukan qwarai yana mai imani . (Al-anbiya a : 94) Mahimmancin Imani "Haqiqa mafi falalar ayyuka da tsarkinsu a wajen Allah shi ne Imani, saboda hadisin da Abu Zarrin Allah ya yarda da shi ya tambayi Manzon Allah (S.A.W) ya ce, Ya Manzon Allah, wadanna ayyuka ne suka fi falala? Sai ya ce, Imani da Allah da jihadi a kan tafarkinsa (Muslim ne ya rawaito shi)Shi ne sababin shiriya da samun arzikin duniya da na lahira, saboda fadin Allah mai girma da buwaya : Duk wanda Allah ya yi nufin ya shirye shi sai ya yalwata zuciyarsa ga musulunci (Al-an am : 125).Kuma imani yana kawar da mumini daga sabon Allah, saboda fadin Allah Ta ala, Wadanda suka yi taqawa idan wani mai kewaye daga shaidan ya shafe su sai su tuna Allah, sai ga su suna gani (Al-aaraf : 201) Imani sharadin ne na karbar aiki, Allah yana cewa : Haqiqa an maka wahayi da wadanda suke gabaninka cewa lallai idan ka yi shirka, to tabbas ayyukanka za su rushe, kuma wallahi za ka zama daga cikin masu hasara (Azzumar : 65). "Tsarkaken Imani, Allah yana sa albarka a cikin aikin da aka yi a cikinsa, yana karbar addu i da shi, Haqiqa an maka wahayi da wadanda suke gabaninka cewa lallai idan ka yi shirka, tabbas ayyukanka za su rushe, kuma wallahi za ka zama daga cikin masu hasara (Azzumar : 65). Tsarkaken Imani, Allah yana sa albarka a cikin aikin da aka yi a cikinsa, yana karvar addu i da shi. Kiyi imani da Allah Marka. Ki mayarda dukkanin damuwar ki ga Allah. Domin shi din majibancin lamura ne. Ki roke shi domin shi din buwayi ne gagara misali. Ki tsame hannun ki ga dukkanin abubuwan da ba hurumin ki bane. Ki kyale malam na lado da harkar iyalan sa dan girman Allah Marka ..Ko kema Allah zai dube ki da idanun rahama ya yaye maki dukkanin abubuwan da ke damun ki..." Mugun kallon da ta watsa musu duka su biyun ne yasa Malam ubaliyo hanzarin mikewa tsaye ya kade jikin sa "To Allah ya kara lapia Marka. Biyu kyautar Allah, Kuna wasa? To Allah ya muku albarka duka. " Cewar malam Ubaliyo daya kallo yan biyun Deluwa da ke kan yar katifar su. Sallama ya sake musu kafin ya fi ce daga gidan. Malam na lado na biye da shi. Hakika malam Ubaliyo ya kambama taurin rai da kafiya irin Marka. Rai a hannun Allah amman taki saduda? Yayi Allah ya kyauta. Kafin suyi musabaha da malam na lado ya yanki layin gidan sa ya tafi . **THE ADAMS FAMILY** karfe tara saura kwata ya shiga gidan. Har karfe shadaya saura bai fita ba. Yana zaune a parlor. Kwanaki 4 kenan a jere yana yiwa sashen Haj Hameedah zaman dole. Maa na hankalce da shi. Amman tayi biris da shi. Har aka ja tsawon kwanaki 4. Haka zai karaci zaman sa yana soshe soshen keya. Waheedah kuwa da wuri take shigewa daki ta murza mukulli. Da ke an musu hutun second semester break. Tana gidah babu inda take zuwa. Zayn dinma bata bari su kebance su kadai. Gashi ya tsiri wani feleke agaban kowa ya rika nan nan da ita . Don haka take kauracewa ganin sa. Don tsaf zai iya aikata wani abun kunyan agaban Maa. Domin yayi na farko wancen satin bata kaunar amaimaita na biyu. Haj Hameedah na zaune a parlorn tana danna system din gabanta. Gefenta kuma tarin littattafai ne da suka danganci fannin tiyata. Ta daga idanu ta dube shi. Yana zaune ya tsurawa kafar bene idanu. Tamkar waheedan ce a wajen. Yadda ya mayar da hankalin sa kacokam wajen. "Nadra..." "Naam Maa." "Je ki kirawo Waheedah. " "Bari na kirata Maa." Cewar Zayn. Kallon da Haj Hameedah ta bishi da shi ne yasa shi komawa ya zauna yana mai sosa keyar sa. "Okay Maa." Mikewa Nadra tayi. Zayn ya gyara zaman sa yana hasaso ta inda zata sakko. Can Haj Hameedah ta mike itama tayi saman. Sun dan jima tukun kafin ita ta sakko ta koma parlor ta cigaba da aikin da take a kwamfuta. Can kuma Nadran ta sakko da wani akwati a hannun ta. Daga karshe kuma Waheedah ta sakko. Sanye cikin laffaya baka data sha aiki pink. Ta bala'in kata'in yin kyau. Da har Zayn ya kasa dauke idanun sa daga kanta. Ga wani kamshi da ke tashi daga kayan nata. Na turaren turara kaya na kamfamin yerwa incense and more. "Ta shi ku tafi .." Haj Hameedah ta fada tana kallon Zayn. Bakin sa ya wangale FARIN CIKI marar misaltuwa ya wanzu a ZUCIYAr sa. Ya kasa boye wa . Ya zube gwiwoyin sa yana mai yi wa Haj Hameedah godia. Kai kace wata babbar kyautar aka masa. Zayn ya mato akan kaunar Waheedah. Ta masa muguwar shigar zurfin da baya iya boye kaunar da yake mata a ko'ina. Waheedah dai tana tsugunne. Yatsunta ta hade su tana matsawa. Kunya duk ta ishe ta. "Allah ya saka da alkhairi Maa. Allah yaja kwanan ki. Ya biya miki dukkani n bukatin ki Maa. Allah ya shi albarka.* Zayn ya shiga yi wa Maa sumbatun godiya. Nadra nata dariya. Lalle Yayan na su ya zauce akan soyayyah. "Amin... Allah ya muku albarka duka. Ka riketa amana Zayn. Na baka amanar Waheedah kai ne mahaifin ta kai ne mahaifiyar ta a yanzu. Ka sani ranka zai yi mummunan baci idan har kayi mata wani abun. Waheedah kibi Zayn. Ya zama miji agareki. Duk abunda yace kiyi. Idan har bai sabawa addinin musulunci ba. Yi nayi bari na bari. Aljannar ki na ga karkashin kafar sa. Allah ya kauda fitinah a tsakani ya baku zuriya ta gari. Ku tashi ku tafi dare yana ja " Waheedah ta shiga tsiyayar da hawayen data rasa na menene ma. Amman dai yanada nasaba da nasihar Maa. Ta goge hawayen na ta. Haj Hameedah ta rungumeta jikin ta tana mai cigaba da saka musu albarka. Nadra ta rakasu har wajen motar. Zayn ya karbi akwatin ya saka a booth. Sannan ya bude gidan tuki ya shiga. Sai bin Waheedah yake da kallo. Ta sunkuyar da kanta ta cikin laffayar. Ya tashi motar suka bar gidan . A rahama suya ya tsaya. Ya siyo kaji da tsire. Ya sake tsayawa a wani shopping mart ya saya su fruits da yoghurt. Alokacin har an fara yayyafi na ruwa. Ya bude motar ya shiga yana murmushi. Ya rankwafa saitin ta. Da har tana jiyo numfashin sa. "My love..... Kinga an fara yayyafi na masoya.. Allah ya bamu albarkar wannan dare da zamu raya... Ki ce Amin " Bata