Sashe 33
Farhatul Qalbi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
na" zahara'u ta kurma ihu tana jan kanta tamkar zata yage gashin kan ta. Haka dai ranar baki daya gidan tamkar zaman makoki haka yayi. Tsit ba surutun kowa . Sai kukan jaririn . Ga makota da Marka ta shelantawa zahrau ta haihu sunata zuwa . Sam marka ta kasa sanar da su ai aure ya kare Bakinta ya mutu murus. Ba maganar nan tata ta tsiya . Tayi tagumi taja kwafa. Haka tayita yi tana canza wajen zama. Yadda taga rana haka taga dare. Batayi bacci ba. Tanata tunanin mafita. Zuciyar ta kuma na kitsa mata wasu abubuwan da dama. Gidah ya shiga ya sauya kaya zuwa wasu na yadi . Riga da wando. Bai saka hula ba, Sai gashin kansa daya taje kawai. Ya feshe dukkanin jikin sa baki daya da turaruka. Kafin ya wuce sashen mahaifiyar su. Haj Hameedah. Bakinsa dauke da sallama ya shiga cikin sashen . Haj Hameedahn na zaune a parlorn farko hannunta rike da waya. Fuskar ta sanye cikin gilashin ta na kara gani Ya durkusa har kasa ya gayshe ta cikin girmamawa ta amsa da fara'a. Tana yi masa kallon karin bayani. Ganin ai ance an kai angwaye gidan su tuni Tuni ya gano kallon da take masa na menene. Ya sosa kasan keyar sa yana murmushi. "Zan tafi..... " "Toh. Allah yayi muku albarka. Ya kara muku zaman lapia da kaunar juna ..." "Amin Aamin...." Bata sake ce masa komai ba. Ta cigaba da danna wayarta. Amman cikin zuciyar ta addoin fatan alkhairi take musu da dacewar rahamar ubangiji.... Ya sake durkusawa ya mata sallama. Sannan ya fice. Kai tsaye ya shiga motar sa. Ya jima a zaune kansa akan sitiyari kafin ya tada motar da addua ya fuce daga cikin gidan. Kai tsaye ya wuce gidan sa. Wanda ke agaban na su Haj Hameedah a dayan layin mai titi wato new gra shurah phase 2.!! *_RANO SCRUMPTIOUS MEAL_* _(Where every flavour tells a story .....)_ *_By HAFSAT RANO_* _(Mother/wife/writer)_ _08030811300_ _IG:Rano_scrumptious_meal_ _INA MA'ABOTA ABINCI? WATO *TRADITIONAL FOOD IN KANO*? GANGARIYAR ABINCI NA AL'ADUN HAUSA DA NAHIYAR KETARE? BA ANAN KADAI MUKA TSAYA BA. MUNA DA LEMUKA WATO *LOCAL DRINKS*. ZAKU IYA KAWO NA HIDIMOMIN LIYAAFA MUYI MUKU_ _MU NA YIN:_ *_FUNKASO_* *_ALKUBUS_* *_SINASIR_* *_WAINA_* *_ASSORTED MEAT (KAYAN CIKI)_* *_COW TAIL/COW LEG (DAB'URI)_* *_CHICKEN AND FISH PEPPER SOUP_* *_LOCAL DRINKS:_* _HIBISCUS (ZOBO)_ _GINGER_ _AMAANI FRUITY SHAKE_ _MUN TANADAR MUKU MOUTHWATERING ABINCI KALA KALA WADANDA KE GINA JIKI DA KARA LAPIA. ABINCIN MU A TSAFTACE YAKE. KUMA MUNA YIN SU NE AKAN YADDA KOWANNE MUTUM ZAI IYA CI . AKWAI SPECIAL SOUPS NA MASU ULCER WADANDA BABU YAJI. AKWAI KUMA NA PEPPER DEM GANG GA MASU SON HOT AND SPICY...._ _KADA KU MANTA MUNA YIN NA TAKEAWAY/ORDER . MUNA KUMA YIN NA BIKI (WE CARTER TO SMALL/LARGE EVENT...._ _FUNKASO TO PAIR WITH COW TAIL:2K_ _WITHOUT COW TAIL:1K_ _ALKUBUS TO PAIR WITH ASSORTED MEAT (KAYAN CIKI) 2K. WITHOUT ASSORTED MEAT :1K_ _PLS NB: PAYMENT VALIDATES INTEREST..... DELIVERY WITHIN KANO:500 NAIRA_[11/23, 9:01 PM] Mummyn Yara: _ASSALAMU ALAIKUM..._ _YAU MUN KAWO KOKEN KU KARSHE . MUN NEMO MUKU INDA ZAKU SAMU LUSH AND COMFY BUBUS CIKIN FARASHI MAI RAHUSA DA INGANCI_ _LUSH/COMFY BUBUS BY: MRS. ZP_ _08147243787_ _WHATSAPP:+234 9332_ _WADANNAN BUBUS SUNA DA MATUKAR LAUSHI KUMA A SAKE SUKE BABU MATSI_ _KALA KALA NE DA SIZES DABAN DABAN...KUMA KOWANNE IRIN LIYAFA ZAKU SAKA KUJE. IRIN RICHLY LOOKS DINNAN DA SAI AN KALLE KU AN SAKE KALLA SABODA KYAWU DA INGANCIN SU. BUBUS DIN A HADE SUKE DA MAYAFAN SU.. ZAKU KUMA IYA PAIRING DA WASU MAYAFAN DABAN_ _WADANNAN BUBUS ANA BADA SU NE AKAN FARASHIN SAYA DAYA DAYA KO SARI..... 12K AKAN GUDA DAYA. IDAN SARI NE KUMA 11K. WADANNAN FARASHIN KASUWA NE. DUK INDA ZAKU ZAGA KUDIN SU YAFU HAKA.. MUNA ARHA NE DON KOWACCE MACE TA IYA MALLAKAR SU._ _MUNA TURA KAYAYYAKIN MU A KOINA A FADIN NAJERIYA DA KETARE .._ _ADIRESHIN SU: NA'IBAWA ZARIA ROAD, KANO.._ _IDAN ANJE SIYA ACE DAGA ZAFAFA NE. DOMIN MUN YABA DA KAYAYYAKIN SU. KUNSAN DAI BAMA TALLATA MUKU ABUBUWAN DA BASUDA KARKO_ _KYAU, INGANCI, RAHUSA SAI COMFY BUBUS DIN MRS. Z.P_ -------- _FARHATAL QALB_ _(FARIN CIKIN ZUCIYA)_ _NA_ _NANA HAFSATU_ _PG:38_ *Tafiya* yake a hankali cikin motar sa. Yayin da rediyon cikin motar ke tashi da sautin karatun alqur'ani mai girma. Na sheikh sudeis. Labban sa na motsawa ahankali saboda yanayin yadda yake bin karatun a hankali bil tartil da tajweed. Ya karasa kofar gate din gidan. Mai gadi ya taso da sauri ya tsaya dede kofar windown drivers seat. Zayn ya zuge glass din ahankali "Ranka ya dade ina wuni....?" "Lapia kalau Baba. Ya gidah?" "Alhamdulillah... Bari na bude gate din." "Sannu da kokari Baba..." Baba maigadin ya tafi da sauri ya bude wa Zayn gate din. Zayn ya shiga da hancin motar. Bakin sa dauke da addua. Inji yana ta yi. Mikano ne dake bawa gidan wuta baki daya.. Ya kai motar bakin parking lodge ya kashe. Ya fito daga ciki. Booth din motar ya bude ya dakko dan karamun trolley. Da hand luggage dinsa. Ya rufe ta da key ya shiga cikin gidan bakin sa dauke da sallama . Tana zaune ita kadai a parlor ta saka nighties riga da wando 3 quarter. Kwantaccen gashin kanta ya sha gyara. Ta daure kan da ribbon. Kafa daya na kan daya tana kallon movie din legally blonde. Ya shiga bakin sa dauke da sallama. Sai da yayi sau uku bata amsa ba. Sakamakon kure karar tv da tayi... Ganin tamkar hankalin ta baki daya ya koma kan kallon da take yi har bata jin sallamar da yayi. Hakan yasa Zayn ya karasa wajen kayan kallon. Yaja extension wire din ya ballota daga jikin socket baki daya komai ya mutu. Da sauri ta juya . Idanunta suka sauka akan nasa. Ta miqe ta nufe shi tana murmushi "Hubby ..." "Haba.. Kika bar karar tv tanayi ga dare? Sallama ta uku bakya amsawa. Baki dayan nutsuwar ki da hankalin ki ya koma kallon gaba daya .. Kalli kan ki Ahlaam.ko dankwali babu." Lafewa tayi a jikin sa. Yayin da ta dora kanta akan kirjin sa. Ta sa hannu ta na dan dukan kirjin sa ahankali cikin turo baki gaba tace, "Tsoro nake ji ni daya .... Ka ki dawowa." "Tohm kiyi hakuri ... Gidah na koma na sake yin wanka. Akwai kayana dana keson dakkowa shine na koma na dakko su .... Daga gidah nan na nayo kawai " Ya ja hannunta suka koma kan kujera suka zauna. Zaman kurame ba wanda yake magana. Can ya dubeta. Ta kwantar da kanta akan kafadar sa. Ko yar kunyar nan ta amare sam babu "Kinci abinci. ?" "A"ah...." "Meyasa?" "Na koshi...." "Saboda me? " "Salad ne dama kawai sai 3 cups of water. Haka dietary routine din ya ke.." Bai sake cewa komai ba. Ya girgiza kai kawai. "Ina dankwalin ki..?" "Yana daki." "Wanne dakin.?" cen na dakin sama." Ta karasa fada tana mai masa nuni da dakin da ke kallon kafar bene da ka hau sama a parlor na farko "Okay..." Ya miqe ya tashi ya haye saman. Yana ta dube dube . Can ya hango hular cikin wasu tarin undies da sleeping wears da ke kan gadon . Wasu a hanger wasu kuma acikin leda . Hular ya dakko. Ya shiga ninke kowanne yana mayarwa kan bedside drawer. Dayazo daukar brazier sai da ya kulle idanun sa sannan ya ajiye kan bedsite din Can sai ga shigar Ahlam dakin tana waka. Ya juya ya kalleta da hular a hannun sa. Ya miqa mata da hannun sa na dama. Ta kalli gadon tatas ya kwashe komai. Ya tattara ya ajiye su akan bedside drawer. Murmushin ta ne ya fadada ta rungume shi. Ta hanyar zura hannuwan ta ta riqo bayan sa. Yayin da fuskokin su ke kallon na juna . "Kinyi sallah ne....?" "No.." "Meyasa?" "Zanyi ai..." "Muje bandaki kiyi alwala ki zo kiyi sallah..." "Tohm.....". Ta fada da sauri ta juya ta shiga cikin bandakin. Shi kuma ya fita ya shiga wani daki da dama ya zaba tuni a matsayin na sa. Duake dakin yake da kayan furnitures fari da ruwan bula. Alwala ya dauro. Ya sauka kasa ya debo kayan sa ya kai cikin dakin ya jera acikin drawers kowanne a hanger. Zama yayi akan gadon hannun sa dafe da kuncin sa. Can ya shiga bandaki ya yo wanka ya sake dauro alwala. Dama already yayi sallah tun a gidah. Don haka babu bata lokaci ya sauya kaya zuwa na bacci. Riga da wando masu kauri. Dakin Ahlam ya nufa yana tafe yana duba wayar sa har ya karasa dakin. Ya shiga cikin bakin sa dauke da sallama "Kinyi sallar?" "Eh....." "Kinason ci ko sha na wani abun?" Ta girgiza masa kai kawai alamun a'ah... Ya sauke zuciya yana auna yadda zai fara komi. Abunka da ba sabun ba. Ga madaukakiyar kunya da ta lullube shi. Shi wallahi Ahlam kallon kanwa yake mata ta jini. Tamkar Nadra. Wadda suke uwa daya uba daya. Hayewa saman gado tayi bayan ta ja hannun Zayn. Ya bita tamkar raqumi da akala. Remote ta dauka ta canza channel zuwa Telemundo . Favorite drama dinta akeyi. Nan da nan kuwa ta kara volume ta mayar da hankalin ta kacokam kan kallon. Yayin da kanta ke kan cinyar Zayn . "Bakya jin bacci?" "Uhm ... An kusa gamawa ai..." "Okay...." Ya amsata yana rufe bakin sa. Sakamakon hammar data taho masa. Bacci yake ji baki daya . Saboda gajiyar da ke dawainiya da shi. Duk shagalin bukukuwan nan sam baya bacci dogo. Sai dai barawon bacci na yan wucewar wasu dakikai.. Wasa wasa har baccin ya sake jansa. Kansa har sarawa ya fara yi. Bacci ya dauke shi. Sai farkawa yayi ya sake ganin ta gyara kwanciya. Ta sauya channel kuma tana kallon The originals. "Bakyaji din still?" "Uhm..." "To ai shikenan .." Yana gama magana ya gyara kwanciyar sa. Hade da jan bargo ya lullube yayi kwanciyar sa. Nan da nan kuwa bacci barawo ya sace shi. Ya sha mamaki daya farka zai yi sallar dare. Dakyar ma ya tashi saboda alarm dake ta kada kararrawa. Ganinta yayi da robar ruwa agabanta . Ta bada lokacin ta baki daya akan tv