Sashe 46
Farhatul Qalbi Part 1 Complete Hausa Novel · about 2 min read
Ya Ibrahim... Allah ya kara budi." "Aamin Aamin..." Ya fada yana doka murmushi. Tamkar fatar bakin sa zata yage. Har mai adaidaitan ya ja suka tafi. Ibrahim bai dena daga hannu yana musu bye-bye ba. Mai adaidaitan ya duba mudubin yana murmushi . Can ya karya wuya ya juya. Yana cewa da su, "Amma fa gayen can yana kaunar ki kanwata . Allah sa dai ba wanke gara kuke masa ba. Dari biyar zuwet a marrar nan a biya maka kudi ai sai mai kaunar ka..." Waheedah dai murmushi kawai tayi. Batace komai ba. Fanna uwar magana ta shiga labarta masa komai. Basira na tayata. A haka suka karasa makarantar. Har kofar gate ya kai su. Suka sauka suka shiga ciki. Bin kowane lungu da sako suka shiga yi da kallo. Sabbin dalibai irin su gasu nan birjik. Kowa cikin uniform dinsa fari. Sai daukar idanu suke yi. Lamarin sai wanda ya gani kawai. School bulletin suka je. Suka kwafi time table. Karfe takwas da rabi suka shiga class bayan sun tambaya an nuna mu su. Babu bata lokaci kuwa. Bayan sun kammalu a lecture hall. Malamin da zai koyar da su ya shiga. Ya gabatar da kan sa. Ya kuma raba attendance sheet kowane row. Sannan ya shiga yi musu introduction na course din da zai dauke su. Ya basu course outline. Nan ta ke ya fara lecturing din su. Cike da kwarewa da sanin kan aikin. Turyan turyan yake yi. Daki daki da kuma tsayawa yayi bayanin inda yaga kamar ba zasu gane ba. Yanayin yadda yake koyar da su baki dayan su suna ganewa. Yanayi ana wasa da dariya. Babu bata rai na wasu malaman. Ya kammala musu darasin ya fita. Nan take kuma wata lecturer din ta shiga. Bayan ta gaya musu sunan ta. Sai kuma ta juya allon ta rubuta sunan course din da zata musu na: Legal and ethical aspects of professional development in nursing..... Lamarin sai sam barka kawai. Domin itama suna game koyarwar ta. Ciki harda su Waheedah da ke jotting key points da take fada acikin littattafan su... Sannu ahankali haka suka karasa duk wasu lakcoci na ranar. Sun kuma gane kowanne. Bayan an tashi suka hau dan sahu suka koma unguwar su. Kowannen su cikin zukatan su chunkushe da farin cikin kasancewara rana irin ta yau. Mai dimbin tarihin da ba zasu taba mantawa ba.