← Book details Farhatul Qalbi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 78 OF 82

Sashe 78

Farhatul Qalbi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ki fuskanci gaskiyar zance. Dan Allah maganar nan ya kamata ki mata duba na tsakani. Ya kamata ace wadannan abubuwan duk an wuce su. Mu rungumi kaddara." "Amma Zayn k..." Bata karasa ba ya janye ta daga jikin sa zai tashi. Tayi saurin riko shi tana langabar da kai. Domin ita kanta tasan tsawon lokuta data diba bata tare da shi har jinya tayi awajen Ummimi . Tana matukar kaunar Zayn. "Shikenan nayi shiru..." Ta fada kanta a k sa. Dan murmushi yayi. Ya koma ya kwanta. "Abunda ya faru haka Allah ya kadarta. Sai fatan Allah ya kara mana zaman lapia da kaunar juna. Hadi da yalwar arziki da wadatar zuci . Ko?" "Eh...." Ta amsa shi . Tana kallon fuskar sa. Hannu ya saka ya kashe bedside lamp ya gyara kwanciyar su. Ahlam ta kankame shi sosai tamkar za'a kwace mata shi .. Daga nan kida ya soma canza salo. Suka shiga bude wasu shafukan na soyayyar su. Zayn yayi mamakin yadda Ahlam ta ke bashi hadin kai ba tare da kosawa ba kamar a baya. Nan da nan kuwa suka shiga faranta wa junan su. Zafafan kisses Zayn ya shiga showering jikin Ahlam da su. Ya kuma ji ta yadda yake muradi. Domin tasha gyara awajen Ummimi. Ta kanas aka dakko mata me gyaran jiki ta gyareta ciki da waje. Ranar dai saboda tsabar rashin juna da sukayi. Na ramakon kaunar da suka nunawa juna adaren jiya har makarar sallar asubahi suka yi. Waheedah dakyar ta iya tashi alarm nata dokawa. Taci mamaki da Zayn bai tashe ta ba yau . Allah ya temaka ta seta alarm. Domin shi ke tashin ta sai kuma ya wuce zuwa masallaci. Amman hakan ya mata dadi gudun tasowar fitna. Kafin Ahlam din taji haushi. Tanata sauri ta dauro alwala tayi sallah. Ta kwanta akan sallaya bacci ya dan dauketa na yan wasu mintina kafin ta mike ta shige bandaki. Tayo wanka saboda lectures din safen da zatayi. Ta zura kayanta bayan ta shafa mai. Ta goga hoda sama sama da man lebe bayan ta zizara kwalli Kitchen ta bude ta shiga. Cikin sauri ta tafasa shayi ta zuba a flask. Ta kai kayan tea din kan dinning area da bread ta ajiye da Nutella/spread. Tana cikin gyara zaman mayafin ta. Sai ga sakkowar Ahlam din da Zayn a tare. Idanun sa fes akan Waheedah . Sai sako yake aika mata ta kallon da yake bin ta da shi. Tayi azamar kauda kanta gefe . "Ina kwanan ku?" Ta gayshe su a tare cikin ladabi Zayn ya nufeta da sauri yana murmushi. Zai rungume ta ta ja baya da sauri. Ahlam na hankalce da su ta kauda kai gefe "Zan tafi lectures ne. Ban dade da shiryawa ba. Na kusa makara ne. Ban samu na hada breakfast ba. Sai tea kawai da bread." "Sannu da kokari, My Baby." Ita dai ta kakaro murmushi kawai. Tayi hanyar fita, "Na tafi school." "Ki jira ni...." Ya juya wajen Ahlam da ke zaune akan kujera. "Zan kai ta school ..." "Alright." "Daga can zan wuce aiki...." "Ba zaka dawo ka ci abincin ba?" Ya dan ja kasan leben sa. Kafin ya daga kai . "Zan dawo tohm. Bari na kai ta." Da sauri ya fice har yana tuntube. Waheedah tayi gaba ta fice daga gate din. Bai tsaya jiran baba mai gadi ya tura gate din da kansa ya futar da motar. Ya sake rufe gate din bayan ya fitar da motar daga cikin gidan. Tana tafiya ahankali tamkar wadda kwai ya fashewa a ciki. Ya tashi motar ya tuka har inda take tafiya. Ya zuge glass din. "Shigo na kai ki ..." Dan kallon sa tayi ta cigaba da tafiyar ta. Zayn abun ya so bashi dariya. Tun baa je ko'ina ba sun fara garashi kamar taya? Ya daure ya sake bin ta da motar. Ya faka ya fito daga ciki. Yayi taku uku ya riko damtsen hannun ta. "Nace ki zo na kai ki.... Meya faru ne?" "A'ina ? Na kawo maka korafi ne?" Ya girgiza kai alamar a'ah. Kafin ya riko hannunta ya jata har wajen motar ya bude ya sakata ya rufe. Ya koma wajen mazaunin driver ya zauna ya tashi motar. Yana tuki yana bin ta da kallo. "Nasan nayi lefi... Koma menene ni dai kiyi hakuri banason kina fushi da ni." "Fushi? Meyasa zanyi fushi da kai?" "Eh to ai ba haka kike mun ba. Baby." Ta kauda kai kawai tana turo baki gaba. Ya faka motar a gefen titi yana binta da kallo. "Zan makara fa..." Ta fada cikin muryar shagwaba. "Mu tafi kenan?" "Uhm." Ya danyi murmushi tukun sannan ya tashi motar. Suka dauki hanyar makarantar su.. Hannu ya saka ya kunna speaker din motar. Wakar indila ta love story ce keyi ahankali... "Wifey...I may not be able to say how much I love you or just how special you are to me, but I can say that my world is full of smiles and happiness whenever you are around. I love you with all my heart... Budemin na shigo kofar ZUCIYAr ki , Da sannu zan zamo dauwamammen FARIN CIKIN da zai bunkasa dukkan wani farin cikin rayuwar ki da mu baki daya.... Ki budemun..." Dan dariya ce ta kufce mata. Ta yi tana kallon sa. "Me zan bude?" "Zuciyar ki.... Zan zamo miki *FARHATAL QALB* da zaki gasgata abun da nake fada.." Hannun ta ta saka ta kare fuskar ta. Har ga Allah kalaman sa na dulmiyata cikin kunya. Har ta rasa ina yake nemo wadannan manya manyan kalaman na hausa.. "Wai meyasa kike jin kunya ta ne..?? Mijin ki ne fa ni... Ba yayan ki ba " "Kai Yaya na ne?" "A'ina na zama Yayan ki?" "Ya Zayn..." "Na raba ki da wani Ya Zayn. Ina mjin ki mu gama sharholiyar mu a gidah daya. Daki daya. Gado daya... Ki ce mun Ya Zayn? Noo! Ban karba baa wallahi." Dariya ta kyalkyale da ita. Daman kuma dariyar yake son sakata. Don haka shi ma ya murmusa kafin ya sake cewa, "Allah bana so. Ki sama mun pet name haka. Cuz I won't accept Zayn or ya Zayn ever again .. " "Toh.." Lakuce mata gefen fuska ya yi. A haka suka karasa cikin makarantar yana ta tsokanar ta. Ya curo kudin abinci dana handout ya zura mata acikin jaka. Bayan ya bata zazzafar sumba guda daya Tayi masa godiya. Kafin ta sauka ta shige cikin aji Bayason rigimar Ahlam. Da wajen aiki zai saboda lokaci ya ja Ya koma gidah. Yaci abincin a tsaitsaye . "Me zaa dafa maka da rana?" Sai da ya kware don mamaki. Tayi murmushi tana kada kai. "Kome kika dafa... Less spicy." "Alright..." Tashi yayi ya sumbace ta a gefen fuska . Ya mata sallama ya tafi aiki. Yanata mamakin wai Ahlam ce me tambayar abincin da za'a dafa? . Cike da farin ciki ya nufi mota ya wuce wajen aiki...Yana jin wata nutsuwa na zagaye shi da annushuwa. Hankalin sa a kwance. Yanata adduar Allah ya tabbatar da wannan zama nasu cikin zaman lumana da kaunar juna da kuma yalwar arzuka... Rayuwa na ta gudu, Haka zaman nasu ya kasance cikin Alhamdulillah,. Dan kowane rayuwar aure yana da ups and downs dinsa. Waheedah na kokarin bawa Ahlam girma. Ta na kuma bin ta da yadda ta so. Hakan ya sa Zayn ganin tamkar ana kwarar Waheedah. Duba da sai yadda Ahlam ta so take bin ta... Ga tunkaho da nuna mata gadara da karfin iko akan gidan. Tamkar na ta ne ita daya.. Don haka Zayn ya tunkari mahaifan sa da maganar canzawa Waheedah gidah. Ko zaman lapia zai kara wanzuwa dik kuwa da ahakan ma Alhamdulillahi.. Sun amince da maganar sa. Don raba gidan ma wani kwanciyar hankalin ne. Da dai-daita tsakanin su. Domin wata kazantar da ba ka gani ba tsafta ce. Nan da nan kuwa farfesa Adams ya ba wa Zayn wani gidah bungalow (flat/marar bene.) Kyauta. Mai kyau da shi a layin su Haj Hameedah din amman daga karshe yake shi ta baya. Zayn ya saka aka fente masa shi. Aka sake gyara shi sosai. Ya zuba masa kaya masu matukar kyau da tsada. Ya kuma samu Ahlam da zancen tayi murna kwarai da gaske. Domin tafu kaunar ita kadai anata gidan ta bararraje yadda take so.. Zayn bai gayawa Waheedah ba. Sai ana'i satin da zata koma. Suna zaune a parlour su ukun . Suna kallon film din titanic. Yana shan fruits din dake gaban sa. Suna hira jefi jefi. Ya ce, "Kun kasance duk abin da na taba so a soyayya. Kun sanya ni jin ana kaunata ta hanyoyin da ba zan iya tsammani ba. Ba zan taba neman karin ba. Ina son ku da ni tare har abada. Daga yanzu har zuwa numfashi na na karshe, zan ci gaba da kaunarku..Ina son ku sosai ..Na rasa yadda zan yi da son ku har ban san kalmomin da suka dace ba don bayyana abin da nake ji game da ku. Babu wata kalma da zata iya misalta kaunata a gare ku! Na kuma ji dadin yadda kuke mu'amala a yanzu sosai... Har cikin rai na nake jin dadin hakan. Allah kuma ya kara mana zaman lapiya Amin ya rabbi..." "Amin...." Suka amsa baki daya. "Ke Waheedah baki sani ba. Amman Ahlam ta sani . Na sanar da ita .." Waheedah ta daga kai ta kalle shi ya jinjina mata kai alamar tabbatarwa. "Nan gidan kamar yadda yake da sunan Ahlam .. Kema Allah yayi na sama maki wani matsugunin wanda yake da sunan ki kema... Amma fa wani hanzari ba gudu ba... Ba bene ba ne flat ne.. Sannan kuma ba anan unguwar ba ne... A tasu Maa ne." Ya fada yana tsokanar Waheedah daga karshe. Wani FARIN CIKI ne ya mamaye ZUCIYAr Waheedah da gauraye . Murmushin fuskarta yaa fadada. Kai kana kallon ta kasan taji dadin zancen sa. Ba dan Ahlam na wajen ba. Har tukwicin sumba ta so ba shi. Sai ta danne dai . Ta shiga godiya agare shi. Zayn yaji dadin hakan kwarai matuka. Ahlam ma ta tayata farin ciki. Ana'i washegari zata koma Zayn ya kai su gidan su wajen Haj Hameedah da Haj Aisha.
Chapter 78 · 0% Book details