Sashe 69
Farhatul Qalbi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ma menene auren? Don naga tamkar baki sani ba. Aure shine hada wata irin alaka tsakanin mace da namiji , wannan yana nufin hade rayuwarsu su zama daya, haka nan kuma makomarsu ta zama daya. Kowace irn al umma akwai irin matsayin da ta bawa aure a musulunci wani dauri ne da yake halattawa ma aurata {mata Da miji) jin dadi a junansu ta hanyar saduwa da kuma sauran muamaloli, ALLAH (SWT) ya halicci mace daga hakarkarin namiji ya kuma sanya soyayya da tausayi a tsakaninsu (kamar yadda ya gayamana a alkur ani mai tsarki ). Wannan yana nun mana cewa alaka tsakanin mace da namiji ALLAH ne ya kulla tun fil azal. Abin da ALLAH kuwa ya hada babu mai rabawa . wannan shine yasa a dabi ance kowa ne namiji yana bukatar mace, haka kuma kowace mace tana bukatar namiji. Wato ko wane daya bazai iya wadatuwa dakansa ba, ya rayu shi kasai dole ne sai da wanin sa. "ALLAH (SWT) da ya sanya wannan danga ta tsakanin mace da namiji bai barsu haka nan kara zubeba , suyi ta saduwa barkatai ba tare da wani tsari ba.saboda idan abin ya zama haka tsarin rayuwar yan adam zai wargaje. Domin kuwa za ai ta samun yaya barkatai batare da masu daukar nauyinsu ba. Don kuwa basu da wani uba guda daya tsayayye wanda zai dauki dawainiyarsu. Wannan zai sa rasa tausayi tsakanin alumma, domin kuwa babu wani wanda zai nuna cewa akwai wata alaka ta jinnu tsakaninsa da wani wanda har zaisa ya rinka jin tausayinsa yana raga masa. Saboda haka ALLLAH ya hallata aure tsakanin mace da namiji, ya zama kuma cewa aure sunnace guda ta annabi ce da take wajibi a wajen duk mai iko yayi shi. Kuma yazama dole kafin ayishi sai anyi sadaki da waliyai da kuma shaidu. Sadaki yana nufin ladan da zaa baiwa mace saboda halarta farjinta, kasancewar kuma mace bata aurar da kanta , ya zama dole asamu waliyi (mahaifinta ko danginta maza ko alkali ko sarki) da zai aurar da ita. Wannan zai iya zama garkuwa gareta daga wulakanici da zai iya yiwuwa mijinta yayi mata. Shaidu kuwa, domin su shaida kulla dangantaka aure tsakanin maauratan domin kiyaye da yin shaida kan dukan wani hakkoki da suka rataya da aure, zuriya da sauransu.Musulunci addini ne da ya kunshi komai da komai don inganta rayuwar dan Adam a duniya da Lahira. "Bai bar dan Adam ya yi amfani da hankali da tunaninsa kawai don tsara wa kansa makoma ba, saboda shi dan Adam mai rauni ne, mai son zuciya ne, mai hadama ne, mai rowa ne, kai karewa ma mai butulci ne ga wanda Ya halicce shi... Astagfirullah, To in har zai yi butulci ga Mahaliccinsa, ta yaya zai tsara rayuwar da sauran abokan zamansa za su ji dadi? "Aure daya ne daga cikin ginshikan rayuwar al umma, wannan ya sa Musulunci bai bar shi sasakai ba ka idoji da dokoki ba. Kuma baya ga ka idojin zamantakewa a tsakanin ma auratan, duk da ba a fata, amma ya tsara yadda za a rabu idan aka kasa samun jituwa ko maslaha a tsakanin miji da matar. A cikin Alkur ani Mai girma a Suratul Bakara Aya ta 221. Allah Madaukaki Yana cewa: Kuma kada ku auri mushrikai mata (arna), har sai sun ba da gaskiya. Hakika baiwa mumina ta fi mushrika koda ta kayatar da ku. Kuma kada ku aurar wa mushrikai maza wadanda kuke yi wa walicci, har sai sun ba da gaskiya. 'Hakika bawa mumini ya fi kafiri, koda (kafirin) ya kayatar da ku. "Wadancan suna kira ne zuwa ga wuta, Allah kuma Yana kira ne zuwa ga Aljanna da gafara da izininSa. ' tsarki, amma duk sauran abubuwa sun halatta su yi da su. 223. Matanku gonakinku ne, sai ku zo wa gona kinku ta inda kuka so, kuma ku gabatar da (basmala da hamdala da addu i na alheri) don kanku, ku ji tsoron Allah, ku sani hakika ku masu gamuwa da Shi ne. "Kuma ka yi wa muminai albishir dakyakkyawan sakamako). Hadisin Annabi (SAW) da Buhari ya ruwaito ya ce, Dukkan abin haihuwa an haife shi ne a kan tafarkin Musulunci, sai dai iyayensa su mayar da shi Bayahude ko Banasare ko Bamaguje. ki sani, allah Mai ji ne, Masanin abin da kuka fada ko kuka aikata... Kina saurara na?" Ahlam ta dan juyar da kan ta. Ummimi ta zura hannu ta kwace wayar da Ahlam din ke kokarin boyewa bayan ta gama chatting. Ta cigaba da cewa, "Bana jin kinsan hakkokin miji akan matar sa, An karbo daga Abu Hurairah (RTA) yace: Manzon ALLAH (SAW) Yace: dan mutum ya kira matarsa zuwa ga shimfidarsa amma bata je masa ba, sai ya kwana (a wannan daren) yana fushi da ita, Mala'iku za suyi ta la'antarta har (zuwa) wayewar gari . Bukhariy da Muslimne suka rawaito shi. "A wata ruwayar ta su kuma:; Idan mace ta kwana tana mai kauracewa shimfid'ar mijinta, Mala'iku za suyi ta la'antarta har (zuwa) wayewar gari A cikin wata ruwayar kuma: Manzon ALLAH (SAW) Yace: Na rantse da wanda rai Na yake hannunsa, babu wani mutum da zai kira matarsa zuwa ga shimfidarsa kuma sai taki zuwa gareshi, face wanda Ke cikin sama Ya yi fushi da ita har sai (mijinta) ya yarda da ita A cikin wannan Hadisi: "akwai dalili mai karfi akan haramcin bijirewar mace dan mijinta ya bukace ta zuwa ga mu'amalar aure, domin cewa lallai fushin ALLAH zai tabbata a gareta, a tare da haka kuma akwai la'antar Mala'iku".Wajibi ne mace ta zamo mai kokari wajen sauke hakkokin mijin ta akanta daidai gwargwado ba tare da jinkirtawa ba, ko a sanya sharuda ko sharadin sai ya mata wani abu ko ya bata wani abu wannan haramun ne, matukar dai tana halin lafiya, wajibi ne akanta ta sauke hakkin mijin ta musamman hakkin mu'amalar aure duba da in taki amincewa hakan zai cutar da shi ya iya jefa shi cikin hali na damuwa ko sabon ALLAH.Manzon ALLAH (S.A.W) Yace; Idan namiji ya kira matar shi ga bukatar sa to taje masa ko da tana kan tanda ne [Tirmidhi] Wannan hadisin; Dalili ne akan wajibcin da'a ga miji musamman da'a mu'amalar aure, kuma yana nuni mace ta gabatar da da'an akan shagalgalun ta. Shima kuma miji wajibi ne gare shi, matukar yana ha'lin lafiya ya amsa kiran ta in ta bukace sa, domin dukkan su masu hakki ne akan junan su, rashin bata hakkin ta itama zai cutar da ita ya iya Kaita ga sabon ALLAH, ALLAH ya tsare... "Haka zalika ki sani aljannar ki tana karkashin kafar mijin ki. Duk kaurace masa da kike a shimfida da kuma kin ladabci agare shi da kula da shi. Lalle kina tattare da fushin mahaliccin ki. Tunda baliga ce ke. Kinsan gaskia kinsan akasin ta Ahlam . Ki sani shirka babbar abace . Domin kuwa hada Allah da wanin sa ne. Bayan Allah buwayi ne gagara misali. Bai haifa ba. Kuma baa haife shi ba. Ba shida kishiya ba kuma ya son a m sa kishiya. Kin dau sirrikan ki komai da komai kina gayawa kawar ki saboda ke din bakida hankali Shashasha ce kuma sakarai lamba daya. To ki sani daga yau wallahi babu hannuna a auren ki da Zayn. ..." Da sauri Ahlam ta kalli Ummimi. "Saboda me Ummimi?" "Saboda bakida hankali. Auren ku ya zo karshe ni dai awaje na. Don ba zaki cutar da su ba. Wallahi kinji na gaya miki. Dan uban ki baa kara auren aka auro mahaifiyar ki? Ko ita kadai kika tashi kika gani agidan ku. ? Wacce bakar mummuna kuma muguwar rayuwa kika daukawa kan ki? Duk akan ya karo aure? Ke dai bakida mutunci." Kawai Ahlam ta fashe da kuka. "Ummimi amana ta yaci fa. Ya rasa wadda zai auro sai Waheeda h dana rika a matsayin yar uwarta kanwa ta ta jini Ummimi? Taya zanyi zaman kishi da Waheedah Ummimi? Taya? Meyasa Zayn zai munafurce ni ya auro Waheedah Ummimi? " Ummimi taja tsaki. Kafin tayi kwafa tana kada kai. Cikin hasala tace, "Halayen ki .. Su suka fara nesanta ki daga zuciyar Zayn. Bakida kirki Ahlam . Summimi kasau ce ke. Mai bin Shawarar kaawaye . Gashi kawar ta kai ki ta baro ki. Kafata kafarki kinji na gaya miki. Dukkanin hirararakin naku da kawar taki duk mun saurara. Zakuje wajen boka ko da zai lalata rayuwar Waheedah. Ta fita daga gidan Zayn. Ku kuma raba Zayn din da mahaifiyar sa data kawo shi duniya. Sannan ku mayar shi saniyar tatse da rakumi da akala sai yadda kikayi da shi ko? Yar banzar yarinya yaushe har kikasan wadannan mugayen alkaba'en.? Ki auri mutum da hakoran sa 32. Da mahaifiyar sa da ta dauke shi wata 9 ta haife ta shayar da shi har girman sa ki ce zaki raba su? Haka zalika Allah ya hada auren sa da Waheedah. Yarinyar da biyayya tayi ba zabin ranta ba aka aura masa ita kice ta ci amanar ki zaki salwanta rayuwar ta? Karya kike wallahi. Ba boka da ke aiki kamar yankan wuka ba. Kinsan Allah kinga wayar nan daga yau tabar hannun ki. Ke da ki sake saka yarinyar nan kawar ki a idonki ko kuyi magana a waya sai ranar da Allah yayi da rabo. Amintar ku ta kare wallahi. Ba bu ke babu ita. Auren ku kuma bazai bata zumunci ba wallahi. Dole a hakura da shi. Idan kinyi hankali inda rabo kya dawo. Amman dai yanzu ya kare. Tunda ba kaunar sa kike ba..." "Wallahi Ina kaunar sa." "Kina kaunar tasa kike Shan magungunan hana daukar ciki? Matar da bata son karuwa da mijinta ai ba mata bace. Ko kuwa?" Ta juya tana kallon yan parlorn. Suka amsa baki daya. Dukkanin su ransu ba dadi. Mahaifin Ahlam ya tashi a zuciye. Gamin yadda take bin Ummimi da wani kallo. Ya wanke kuncinanta da mari har hudu. Tamkar ruwan taurari me hatsihatsi haka Ahlam ta shiga gani tsabar gigicewa da zafin marukan. "Marar mutunci. Shashasha. Sokuwa kuma sakarai marar kwakwalwa. Ki sunkuya ki bawa Ummimi hakuri kuma ki bawa Haj Hameedah hakuri dan uban ki.... Wannan da haihuwar ki gwara a ..." "Dan Allah kar ka karasa. Ka dubi