Sashe 58
Farhatul Qalbi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ce akan zahara'u yar wajen ki " "To... Ina sauraron ka dai Na'Ateeku. " "Wato hakika banji dadin abunda Adamushe yayi mata ba. Ga yara ga wanda aka yaye ko?" "Kwarai... Ai bashi da mutunci. Kakan sa ma haka ya dinga shikan matan sa. Gado ne." "To Allah shi kyauta ..." "Aamin Na'Ateeku." Ya sake sauke zuciya ya cigaba da cewa, "Wato idan ba damuwa... Ni ina bidar auren ta. S" Bai karasa ba Marka ta dora hannu a hanci ta saki guda "Na'Ateeku dagaske kunnuwa na suke jiye mun?" "Kwarai Marka ... Ta kwanta mun, Ta yi mun. Don na kammala dakin da na ke ginawa acikin gidah na ma. Bani kuma da matsalar komai. Ita kawai zaa daura aure a kawo. Idan da son samu ne ma a hade da na zainabu. Ance farkon watan gobe ne ko?" "Kai naji dadin zancen nan. Na'Ateeku da ma da tsinanniyar yarinyar nan ta ki ka har ciwon kirji nayi saboda takaici. Kai din babu macen da zata ki ka. Kuma kanta tayi wa. Yanzu bagashi ba. Ta rasa mijin auren tana yawon rariya? An gama. Zahara'u ta zama ta ka Na'Ateeku. Ba ka da shauran damuwa. Ka samu mai sunan Malam ku tsara komai." "Godiya na ke Marka. Allah shi saka maki da alkhairi. Kifin gwangwani, Shayi da biredi mai yanka yanka, Ga tsiren kasuwar dare ba fashi zahara'u kullum idan aka yi auren nan sai taci. Ranar tuwon laraba kuwa indomi din haladu mai shayi da lafceciyar wainar kwai da lemon kwalba zata ci babu ita babu tuwo. Ga wannan kya ci goro ba yawa." Ya karasa fada hadi da ciro gudar dari biyar ya mika mata. Tamkar Marka ta zuba ruwa a k sa ta sha don farin ciki. Su kayi sallama da Na'Ateeku. Ta zura kudin ta a zani tanata murna. Da guda ta koma cikin gidah. Ta kamfaci ruwa a cikin jarka ta zuba a k sa. Tayi goho ta dukar da kan ta ta shiga shan ruwan kasan . Ta dago bayan ta sha. Ta sake dora hannu a hanci ta saki guda. "Menene Marka.?" "Shafa mana Marka." Duk matan suka shiga tambayar Marka . Fuskar ta kumshe da farin ciki marar misaltuwa ta ce, "Zahara'u ce akazo neman auren ta. Auren kuma tare akeso a daura da na zainab. " "Barka Marka... Barka." Suka shiga tayata murna. "Wanene manemin Marka?" "Hmm abu kamar almara. Na'Ateeku dai in karkare muku zan ce. Yace wanke zahara'u zaai kawai a mika ta. Shirgegen dakin daya gina acikin gidan sa na ta ne ya ce. Baya bukatar komai daga gare mu. Ya ce, Kifin gwangwani, Shayi da biredi mai yanka yanka, Ga tsiren kasuwar dare ba fashi zahara'u kullum idan aka yi auren nan sai taci. Ranar tuwon laraba kuwa indomi din haladu mai shayi da lafceciyar wainar kwai da lemon kwalba zata ci babu ita babu tuwo... Na san kuma taliya ma yar kakkaryawa zasu dinga ci." Baki daya sai gidah yahautsine da ife-ifen farin ciki. Zahara'u da ke daki sai murmushi ta ke. Idanuwan ta na hango mata kifin gwangwani da wainar kwai da tsiren da zata dinga ci. Duuu yan wajen tsakar gidah suka shige daki don taya zahara'u murna. Marka nata taka rawa da sakin guda . Hadi da tattaro tsinuwa da mugayen alkaba'i tana dorawa a sunan Adamushe mijin zahara'u na da . "Mummunan banza mummunan wofi. Da hanci bajajje a saman fata. Baki uwa bayan tukunya. Yana tafe yana hankada kirji sama. Dan iska matsiyaci. To ga naateeku nan zai share mana kukan mu. Ahh shokeeei." Ta kwarfata hannuwa kasa ta mayar sama wai ita nan rawar shoki ta ke kwasowa. Ba wata kwalliya tayi ba. Ta zura doguwar riga baka da dankwalin ta. Wadda Haj Hameedah ta bata. Ta shafa man lebe da farar hoda hade da dan zizara kwalli a idanun ta Ta dauki sabon medicated glasses din ta ta saka shi a fuska. Ta dauki yar karamar jakar data zura kayan ta ta fita daga cikin dakin da ya ke a matsayin na ta. Tana bude kofar parlor ta hangi Ahlam malale akan kujera hannunta rike da waya tana dannawa "Sis..." Sai da ta fada sau biyu sannan Ahlam ta farga. "Naam dearest one ... Sai ina?" Waheedah tayi murmushi kafin tace, "Kinsan dama na gaya miki zanje gidah, za'a kawo kayan auren yayata. Ranar Monday insha Allah zan dawo nan din daga school. " "Oh haka fa. Allah sarki, Ki gayshe su please " "Zasu ji, In sha Allah... Sai na dawo." "Okay dear sis " Waheedah ta fita daga cikin gidan bayan ta kullo kofar. Su kayi sallama da baba mai gadi ta futa don hawa dan adaidaita sahu da zai kai ta gidah Tana tafe cikin nutsuwa akan hanya. Sai ga dosowar Zayn Adams. Tun daga mudubi yake hango ta. Tana tafiya ahankali tamkar mai tausayin kasa. Ya samu kansa da kallon gefe. Yar majalisar mazan layin sun zuba mata idanu Kishi ya taso ya harde masa a wuya. Tsayawa yayi chak da motar ta sa. Ya kira number dinta da dayan layin sa da yake a matsayin Zayn ba wanda suke chatting da sunan Dawood ba. "Assalamu alaikum" sanyayyar muryar ta. Ta doki kofar kunnen sa. "Wa'alaykm Salam.... Ina zakije haka?" Dan daga kai tayi ta hango shi a mota "Zanje gidan mu ne ..." "To karaso .." Karasawa tayi. Ya zuba mata idanu. Da har sai data janye idanun ta akan sa. "Shigo na ajiye ki." "Ka bar shi Ya Zayn . " "Shigo na ce " Bata sake musu ba. Ta bude murfin mota ta shiga tana adduar hawa abin hawa Ya juya ya kalli jakar da ke hannun ta . Kafin ya tambaya ta yi saurin gaya masa duba da a karkashin su ta ke, "Zanje gidah ne sai Monday zan dawo insha Allah ..." "Meyasa?" Yayi subutar baki wajen tambayar ta. "Zaa kawo kayan yayata ne.... " "Okay.... Allah ya sanya alkhairi " "Amin...." Yaja motar suka dauki hanya. Na'urar sanyi nata busa su. Ya yin da wakar forever ta gyakie ke tashi ahankali. Yana so yagaya mata sakon zuciyar sa amman zuciyar sa ta hana shi. Sai jan kasan leben sa ya ke yana taune shi. A haka suka karasa har layin su wajen gidan su Basira. "Ajiye ni anan ma .. Nagode." "Ba gidah kika ce ba?" "Zan karba notebook dina ne awajen Basira " Ibrahim da ke zaune acikin yan majalisar su hangen Waheedah da yayi ya mike da sauri sai murmushi ya ke. Zayn ya samu kan sa da sauya fuska. "Kawai dai wajen saurayin ki kika zo." "Haba Allah ya kiyaye ... Nagode bari na sauka. " Zayn yaci magani, "Shiga ki karbo na sauke ki agidah " "Ai zan..." "No buts .... Plz" Ta shige gidan su Basira ba dadewa suka fito tare da ita. Ta tsaya suka gaysa da Ibrahim. Zayn na ta aika mata da sakon harara. Suka shiga ya sauke su a kofar gidan su Waheedan. "Mungode sosai..." Har zasu shiga gidah yasamu kansa da cewa, "Waheedah...." Ta juya da sauri . "Naam Ya Zayn..." "Shikenan ma, Take care " Sukayi waving ta shige gidan su dasauri. Shi kuma ya ja mota ya koma gidan sa. Ransa duk ba dadi. Ya kara tabbatarwa kansa lalle Waheedah FARIN CIKIN ZUCIYAr sa ce. Gashi daga rabuwar su. Ya samu zuciyar sa da radadin rashin ta ..... A haka ya karasa parking a harabar gidan sa ya shiga ciki bakin sa dauke da sallama.... _INA MASOYA KUMA MA'ABOTA KAMSHI MA SU KAUNAR KAMSASAWA A KODA YAUSHE? DOMIN KAMSHI RAHAMA NE.._ _TO KU MATSO, DOMIN WANNAN KARON MA ZAFAFA BIYAR SUN ZO MU KU DA TALLAN MASARAUTAR KAMSHI NA KAMFANIN TURAREN *YERWA INCENSE AND MORE*_ _A *YERWA INCENSE AND MORE* ZA KU SAMU TURARUKAN WUTA NA *GIDAH, NA KAYA, NA TSUGUNNO* BA A NAN KADAI SUKA TSAYA BA. AKWAI *KHUMRAHS* MASU KAMSHIN LARABAWA DANA FRUITS KAI DAMA KAMSHIN TURAWA. AKWAI KHUMRAHS TA MATAN AURE DA TA YAMMATA_ _SANNAN SU NA DA *TURAREN WANKA DANA SHAFAWA BAYAN AN KAMMALA WANKA.* BA ANAN TURARUKAN NA SU SUKA TSAYA BA. AKWAI *KULACCAM* MAI MATUKAR KAMSHI DA SANYAYA ZUCIYA, SANNAN SU NA DA *MADARORIN TURARUKA NA JIKI DA NA KAYA*_ _AKWAI TURAREN *AL'AJABU NA TSUGUNNO DA KHUMRAH* DIN SA_ _SANNAN SU NA DA *TURAREN GASHI NA CREAM DA KUMA SPRAY DIN SA NA FESAWA*_ _BA ANAN SUKA TSAYA BA. SU NA DA *TURAREN MOPPING, DA NA BANDAKI AKWAI NA RUWAN WANKI DA NA FESAWA A DRAWER KO AKWATI*_ _AKWAI KAYAN GYARARRAKI NA FATA. KUJERAR TSUGUNNO, KASAKE NA WUTA, COAL IGNITER TA KUNNA GARWASHI, ELECTRIC BURNERS DA ENGLISH COAL_ _AKWAI LAFFAYAS DA SAURAN TURARUKA NA KAMSHI KALA KALA_ _SU NA BADA KAYAYYAKIN SU AKAN FARASHIN SARI KO SAYA AKAN DAYA DAYA. SANNAN SUNA TURA KAYAYYAKIN SU KO'INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE. KAYAN SU YAN CHADI NE DA SUDAN DA KUMA YERWA WATO MAIDUGURI._ _KYAU, INGANCI DA RAHUSA SAI KAYAYYAKIN KAMFAMIN YERWA INCENSE AND MORE. SAI KUN GWADA ZAKU BAMU LABARI_ _NAMBAR TARHON SU DA ZAA KIRA KO MUSU MAGANA TA WHATSAPP ITACE: 08095215215_ _INSTAGRAM HANDLE DIN SU: @yerwaincense_and_more_ _YERWA INCENSE AND MORE: A NUMBER ONE STOP SHOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS AND MORE_ *_ZAFAFA BIYAR din samari ne a rayuwar INAYAH,kowanne a cikinsu akwai wani murdadden Al'amari da ya shata layi tsakaninsa da ita,wawakeken sirri wanda a koda yaushe take kiransa da SANADIN LABARINA_* *_Amma babban abun mamakin a koda yaushe shine,ita dai tasan cewa BABU SO tsakaninsu MEYA KAWO SHI?_* *_Duk da haka tana tunanin yun qundun bala ta fitar da FARHATUL K'ALB a cikin ZAFAFA BIYAR din samarinta,duk da batason su zame mata GURBIN IDO wanda har kullum ba ido bane_* *YA KUKAJI SALON MASU KARATU?* *YADDA SALON YA BAMBANTA DAKO YAUSHE HAKA LABARAN SUKA BAMBANTA DA DUKKA LABARANMU NA BAYA* INAYA(riba biyu)___mamughee SANADIN LABARINA___Rano BABU SO___Billynabdul FARHATUL K'ALB___Miss xoxo GURBIN IDO____Huguma *ZAKI YARDA AYI TAFIYAR NAN BABU KE MADAM?* *_GARZAYA KI BIYA NAKI KUDIN KAN FARASHI KAMAR HAKA_* Biyar:::1k Hudu:::700 Uku::::500 Biyu::::400 Daya:::300 *_zaki saka kudin ta wannan account number din_* HAFSAT UMAR KABIR 2270637070 Zenith bank *Saiku tura shaidar biya zuwa ga* 07040727902 *IDAN KUMA KATIN WAYA NE ZAKU TURA TA NAN TARE DA SHAIDAR BIYAR*