Sashe 27
Farhatul Qalbi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
halak. Allah shine shahidi " "Marka... Kinajin abunda yarinyar nan ke fada? Ah lalle dan zaki ya girma." Marka kuwa tamkar ruwa ya cinyeta ta kasa magana sam. Sai ma sake zubawa Waheedah kallo da tayi." "Marka Allah ya baki hakuri idan na bata miki rai. Magana ta gaskia ni idona ba a bude yake ba. Sannan mahaifiya ta ba haka halinta yake ba. " Tana kasara magana ta koma daki. Yayinda Marka ke tsaye sandandan da yatsanta a baka tana gatsawa. Inna Sa'adatu ta ja dogon tsaki tana hararar Marka. Can ta koma cikin dakin ta. Tana kutuntumo ashariya tana saukewa da sunan Waheedah, Umma Hadiza da danginta baki daya. Zubewa Waheedah tayi akan katifa tana hawaye daya na bin daya. Hakurin ta ya kai makurar da ba zata iya tsayawa bata mayar da martani ba. Duk tarin shekarun nan bata taba cewa uffan ba sai fa yau ta hakurin ta ya kai makura. Marka ta shiga zaramboto a tsakar gidah . Tayi nan tayi can ita kadai. Ga uban tsaki kamar tsaka. Can ba dadewa kuwa sai ga Umma Hadiza ta dawo tanata sauri baiwar Allah. Da kular abinci a hannunta. Bakinta dauke da sallama ta shiga gidan . Tanata zabga sauri ganin ba abincin da su Kamal zasu ci na rana. "Waheedah kina ina ne baki tafi ba? Maza maza ki shirya ga direba nan da ya kawo ni zai dauke ki. Su Nadra suna jiran ki." Ta karasa fada hadi da zare mayafin jikinta ta ajiye a gefe. Tashiga duba kwanukan da zata rabaa musu abincin. "Ni ce na hanata... Shafaffiya da mai. Ko kina da ja?" Marka ta fada. Ta dasa wani bokitin karfe ta zauna akansa Waheedah ta fito daga cikin dakin su Kamal ta tsugunna a kusa da Umma Hadiza. "Gani nan Umma... Sannu da dawowa. Allah ya saka miki da alkhairi." "Eh muma da bakya fada. Alkhairin Allah kullum cikin sa muke. Makirar wofi." Da jin haka, Sai Umma Hadiza ta tsame hannunta daga dakko wainar da take ta fuskanci Marka. Cikin ladabi tace, "Kiyi hakuri ... Bansan tayi lefi ba. Allah ya huci zuciyar ki. Marka." Ta waiga ta dubi Waheedah dake tsugunne tana karta tsinken tsintsiyar kwakwa a k sa . "Me kikai mata waheedah. Je ki nemi gafarar ta " "Umma na bata hakuri... Wallahi ba abunda nayi ." "Laaa masalli ila. Ke ni zaki dubi tsabar idanuna ki ce ba abunda kikai mun? Yarinyar nan ba dan na matsa ba da bugu zata kai mun dazu. Ga Sa'adatu nan idan karya na ke...." "Haka akayi. Don sai da na tura ta daki saboda yadda ta hayayyako wa Marka. Da girman Allah da yarinyar nan yau nima ta dake ni. Don banason jan magana ne shi ya sa na shige daki." Umma Hadiza tayi shiru. Tama rasa abun cewa, Sarai tasan ba halin Waheedah bane. Dukkanin abunda suka fada karairakin su ne kawai suka shirya don kawowa waheedan suka. "Kin bi bayanta kenan... Ko?" Marka ta sake fada tana kwafa. 'hum' Umma Hadiza ta rausayar da kai. Hadi da sake mayar da kanta wajen Waheedah. "Ki basu hakuri Waheedah.... Marka, Sa'adatu.. Dan Allah ku gafarceta. Allah ya tausashi zukatan ku." Tayi gurfane agaban su. Yayin da Sa'adatu ke wani munafukin murmushi. Ita kuma Marka ta shiga jijjiga kai tana kada kafafun ta. "Marka Allah ya baki hakuri..... Inna Sa'adatu Allah ya baki hakuri " Tana gama fada ta shige daki. Ta kwantar da kanta akan katifa yayinda gangar jikinta ke a k sa. Hawaye ne ke zuba a idanunta. Ganin karyar da suka shirya bayan ba ayi hakan ba. Tasa bayan hannunta ta goge hawayen alokacin da Umma Hadizan ta shiga daki hannunta dauke da plate da waina akai da miya dataji nama. "Zauna ki ci.... Kinji." Idanunta sukayi rau rau. Ta dago ta dubi mahaifiyar ta su, Cikin baki innocently tace, "Wallahi Umma ba'ai haka ba....." Ta kwashe dukkanin yadda sukayi ba tarage komai ba ta gayawa Umman ta su. Umman ta sauke nannauyar ajiyar zuciya kafin tace, "Duk nasani Waheedah. Nasan ba halin ki bane. Amma ki dai na mayar da magana idan sunayi ko da kuwa kece da gaskiya ko akasin haka. Sun haife ki koda kuwa babu yan uwan taka a tsakani. Kinji?" "Insha Allah Umma..." "Maza kici abincin." Umman zata tashi kenan sai ga shigowar Nadra gidan. Tanata doka sallama "Abbas ka tabbata nanne?" Ta tanbayi direban dayayo musu kwatancen zuwa gidan na su Waheedah. Nadran ta kira direban ya waya akan rashin dakko Waheedah da baiyi ba. Nan ya ke shaida mata tun dazu daya sauke Umma Hadizan yana jiran Waheedah a kofar layin bata fito ba. Shine Nadran ta saka dayan direban bisaga kwatancen Abbas daya kai Umman . Aka tuka ta aka kawota kofar layin. Da tambaya suka gane gidan na su Waheedah saboda bashida wuyar ganewa. Da kace gidan Nalado ba wanda baisan yan gidan ba baki dayan su... *_ZAFAFA BIYAR din samari ne a rayuwar INAYAH,kowanne a cikinsu akwai wani murdadden Al'amari da ya shata layi tsakaninsa da ita,wawakeken sirri wanda a koda yaushe take kiransa da SANADIN LABARINA_* *_Amma babban abun mamakin a koda yaushe shine,ita dai tasan cewa BABU SO tsakaninsu MEYA KAWO SHI?_* *_Duk da haka tana tunanin yun qundun bala ta fitar da FARHATUL K'ALB a cikin ZAFAFA BIYAR din samarinta,duk da batason su zame mata GURBIN IDO wanda har kullum ba ido bane_* *YA KUKAJI SALON MASU KARATU?* *YADDA SALON YA BAMBANTA DAKO YAUSHE HAKA LABARAN SUKA BAMBANTA DA DUKKA LABARANMU NA BAYA* INAYA(riba biyu)___mamughee SANADIN LABARINA___Rano BABU SO___Billynabdul FARHATUL K'ALB___Miss xoxo GURBIN IDO____Huguma *ZAKI YARDA AYI TAFIYAR NAN BABU KE MADAM?* *_GARZAYA KI BIYA NAKI KUDIN KAN FARASHI KAMAR HAKA_* Biyar:::1k Hudu:::700 Uku::::500 Biyu::::400 Daya:::300 *_zaki saka kudin ta wannan account number din_* HAFSAT UMAR KABIR 2270637070 Zenith bank *Saiku tura shaidar biya zuwa ga* 07040727902 *IDAN KUMA KATIN WAYA NE ZAKU TURA TA NAN TARE DA SHAIDAR BIYAR* 09134848107 *_THANKS FOR THE CONTINUED PATRONAGE_* [11/23, 9:01 PM] Mummyn Yara: _*FARHATAL-QALB*_ _(FARIN CIKIN ZUCIYAH)_ _NA_ _NANA HAFSATU_ _(MX)_ _AREWABOOKS:MISSXOXO_ _WATTPAD: MISSXOXO00_ _ZAFAFA BIYAR PAID NOVELS_ _PG:30_ ==== *Waheedah* da ta zura waina a baka dakyar ta iya hadiyewa tana kallon Umma Hadiza. "Kaman muryan Ya Nadra ko...?" Umma Hadiza ta leka ta taga nan ta hango Nadra a tsaye "Wallahi itace " Tana karasa fada ta fice tsakar gidan. Alokacin Marka tafuto daga daki itama tana karewa Nadra kallo. Hakama inna Sa'adatu dake leqe ta wundo. Marka da saadatu sai bin ta suke da kallo kaman jinjirayen mayu. "Ina wuninku?..." Ta gayshe su a ladabce. "Nadra..." Cewar Umma Hadiza da ta fita tsakar gidan tana murmushi "Naam Waheedah . Ina Waheedah ? Lapia take? Naga shiru shiru Abbas bai dakko ta ba. Sai da na kira shi a waya yace shi dai gashinan a zaune yana jira waheedah bata fito ba. Shine nasa jibril ya kawo ni. Abbas din ya kwatanta mana. Da mukazo layin kuma se na fadi sunan abban su Waheedah sai aka nunamun gidan " "Allah sarki Nadra.. An wahalar da ke. Tana daki Waheedan...." Tayi shiru ta kasa karasawa don rashin sanin abunda zata fada. Tunda dai Marka ta hana zuwan. "Waheedah... Dear sis" Nadra ta fada. Yayinda Umma Hadiza tayi mata nuni da dakin. "Naam Ya Nadra...Ina wuni?" "Lapia Lou. Na jiki shiru. Meya faru?" Waheedah tayi shiru tana lankwasa hannaye. Can ta sauke zuciya kafin tace. "Kai na ne yake dan saramun..." "Ayya bakya jin dadi?sannu Allah ya kara sauki." "Amin Yaa rabbi..." "Karasa cin abincin. ... Sai muje pharmacy." Cikin rawar murya Waheedah tayi hanzarin girgiza kai kafin tace, "Ai .. Kan ya de na." "Toh Allah sa kaffarane." "Aamin..." Ta zaro wayarta da ke ringing. Dauka tayi ta kara a kunnenta. "Naam Maaa. Eh naje, Ashe batajin dadi ne. Tohm Insha Allahu, Aamin. Amin. Alright." Ta katse kiran ta mayar Jakarta. Gumi sai sharara yake a fuskarta. Abun ka da aje butter tazo gidan aje kuka. Bata saba da zafi ba. Waheedah ta janyo muhuci da sauri ta miqa mata. "Kiyi fiffita.." Dan murmushi tayi ta karba tana yi. "Zaki je bikin amma de ko?" Waheedah ta dan yi yake kafin ta miqe ta fita zuwa tsakar gidah. Umma Hadiza na tsaye . Marka na daga gefen kofar dakinta a tsugunne. "Umma...." "Na'am Waheedah..." "Ya Nadra na tambayar zanje amma taron yau ko?" Umma Hadiza tayi shiru bata ce komai ba. Marka ta yamitsa fuska tana kallon gefe, "Ba inda za ki " Can sai ga futowar Nadra da wayarta kare a kunnenta "Nazo daukan Waheedah ne... Gamu nan insha Allah..." Tana rufe baki Marka tace, "Kin tsaya sandandan yarinya tun dazu take jiran ki. Ko sai kin nuna mata daya daga cikin baqar halayyar taki? ". Waheedah ta cika da mamakin da yasa ta kasa ko motsi. "Ina miki magana kin tsaya chak kina bina da kallo? Wannan yarinya, Wannan yarinya na rasa yadda zanyi da halin ki." Nadra ta dan matsa kusa da Marka tana bata hakuri . "Kiyi hakuri ....." "Kiyi hakuri Marka .. Amman da kikace ba zani dinba shysa na hakura. " Nan da nan Marka ta fashe da kuka wiwi tana dukan kirjinta. "Ni wahidin zata wulakanta? Innalillahi wa inna ilaihi rajiun. Wayyo! Wohoho, Duniya ina zaki damu?? Ke ni kikewa karya? A'ina mukayi haka da ke? Da girman Allah yarinyar nan karya take mun. Wato kin zauna da uwar ki a daka tana kitsa miki munafurci ko?" Waheedah ta fashe da kuka. Hannun ta daya akan bakinta. Jikinta sai rawa yake... Hakama Umma Hadiza da baki dayan abun da Marka tayi na kunyata su duk ya dubibiyeta tamkar kasa ta tsage ta fada haka take ji. "Wadannan biyun basuda mutunci...Jikatah." Marka ta fada tana wa Nadra murmushi. Hakoranta sun gauraye sun zama kalar ja saboda goro. Nadra ta rasa abun cewa. Tayi gaba kawai bayan tace, "Toh Umma sai kun fito... Bari na jiraku a mota. Baba sai anjima." Ta dan rausayar da kai datace wa Marka sai anjima. Ta fice . Umma Hadiza baki daya tarasa abun cewa. Yau Marka ta tabbatar bata kaunar ta itada yaranta. Da har zata kirkiro sharri ta fada. Wasu hawaye sirara suka zubo mata. Saboda ba kadan ba ta kunyata su