Sashe 31
Farhatul Qalbi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ubanme zanyi? Kama ki zan na saka a garke na daure ko kuwa? Ai babu abunda ke tsakani na da ke Hadiza. Ba auren 'da na kike ba .... Shekaru masu dadewa." Umma Hadiza ta tamke idanunta tana dartse bakinta. Baki daya kanta ya mata nauyi. Duk tarin shekarun nan da aka dauka. Bata taba buda baki tacewa yaranta basa tare da mahaifin su ba. So take akwai lokaci da ta ware zata sanar musu idan Allah ya so. Amman baki daya Marka ta tarwatsa mata lissafi. Kusan kullum seta goranta mata. Tayi ta shelan ba aure tsakanin ta da dan ta. Tamkar wani lefi tayi babba da yasa ya saketa. Bayan Markan ce ta saka dole ya saketa babu wata kwakkwarar hujja. Hawaye sirara suka shiga zuba a idanun Umma Hadiza. Marka ta kalleta tana yamutsa baki. "Ni fa kukan munafurci ne banaso. Uban me na miki iyye?" Umma hadiza ta girgiza kai kawai. Hade da saka hannu ta share hawayen ta. "Babu komai .." "Toh mai sunan Malam... Yau magana ta kare. Idan Allah ya kai mu wayewar gari. Inason Hadiza ta tattare nata ya nata ta bar mun cikin gida. Kar kuma ta sake tako kafarta kofar gidan nan idan ba da wani dalili ba kwakkwara. Wannan shine zancen da na yanke. " "Tohm Marka.. Allah ya tashe mu lapia " Umma Hadiza ta fada hade da miqewa tsaye. Ta kamo Kamal ta temaka masa ya shiga daki. Dan sauran kayan kwalam da suka samu awajen bikin ta juye musu akan faranti ta raba musu shi da Najib. Sannan ta kunna musu maganin sauro tasa daga bakin kofar daki. Tayi sai da safe ta koma daki. Waheedah ta cire kayanta ta mayar da na gidah. Wata riga da ta mayar da ita ta bacci. Sai hula da ke kanta "Baki kwanta ba....? Tara da kwata fa " "Zan kwanta Ummaa. Yanzun dai bana jin bacci " Umma Hadiza ta sauke nannauyar ajiyar zuciya. Hawayen da ta ke kokarin zubowa ya shiga tsiyaya . Tayi sauri ta goge . Nan ta fara jiyo sautin na waheedah har da shessheka. Tayi saurin janyo ta jikinta tana lallashinta. "Bar kuka Waheedah ... Kowane dan adam da tasa kaddarar., Mu ta mu ..... *_ZAFAFA BIYAR din samari ne a rayuwar INAYAH,kowanne a cikinsu akwai wani murdadden Al'amari da ya shata layi tsakaninsa da ita,wawakeken sirri wanda a koda yaushe take kiransa da SANADIN LABARINA_* *_Amma babban abun mamakin a koda yaushe shine,ita dai tasan cewa BABU SO tsakaninsu MEYA KAWO SHI?_* *_Duk da haka tana tunanin yun qundun bala ta fitar da FARHATUL K'ALB a cikin ZAFAFA BIYAR din samarinta,duk da batason su zame mata GURBIN IDO wanda har kullum ba ido bane_* *YA KUKAJI SALON MASU KARATU?* *YADDA SALON YA BAMBANTA DAKO YAUSHE HAKA LABARAN SUKA BAMBANTA DA DUKKA LABARANMU NA BAYA* INAYA(riba biyu)___mamughee SANADIN LABARINA___Rano BABU SO___Billynabdul FARHATUL K'ALB___Miss xoxo GURBIN IDO____Huguma *ZAKI YARDA AYI TAFIYAR NAN BABU KE MADAM?* *_GARZAYA KI BIYA NAKI KUDIN KAN FARASHI KAMAR HAKA_* Biyar:::1k Hudu:::700 Uku::::500 Biyu::::400 Daya:::300 *_zaki saka kudin ta wannan account number din_* HAFSAT UMAR KABIR 2270637070 Zenith bank *Saiku tura shaidar biya zuwa ga* 07040727902 *IDAN KUMA KATIN WAYA NE ZAKU TURA TA NAN TARE DA SHAIDAR BIYAR* 09134848107 *_THANKS FOR THE CONTINUED PATRONAGE_* *_RANO SCRUMPTIOUS MEAL_* _(Where every flavour tells a story .....)_ *_By HAFSAT RANO_* _(Mother/wife/writer)_ _08030811300_ _IG:Rano_scrumptious_meal_ _INA MA'ABOTA ABINCI? WATO *TRADITIONAL FOOD IN KANO*? GANGARIYAR ABINCI NA AL'ADUN HAUSA DA NAHIYAR KETARE? BA ANAN KADAI MUKA TSAYA BA. MUNA DA LEMUKA WATO *LOCAL DRINKS*. ZAKU IYA KAWO NA HIDIMOMIN LIYAAFA MUYI MUKU_ _MU NA YIN:_ *_FUNKASO_* *_ALKUBUS_* *_SINASIR_* *_WAINA_* *_ASSORTED MEAT (KAYAN CIKI)_* *_COW TAIL/COW LEG (DAB'URI)_* *_CHICKEN AND FISH PEPPER SOUP_* *_LOCAL DRINKS:_* _HIBISCUS (ZOBO)_ _GINGER_ _AMAANI FRUITY SHAKE_ _MUN TANADAR MUKU MOUTHWATERING ABINCI KALA KALA WADANDA KE GINA JIKI DA KARA LAPIA. ABINCIN MU A TSAFTACE YAKE. KUMA MUNA YIN SU NE AKAN YADDA KOWANNE MUTUM ZAI IYA CI . AKWAI SPECIAL SOUPS NA MASU ULCER WADANDA BABU YAJI. AKWAI KUMA NA PEPPER DEM GANG GA MASU SON HOT AND SPICY...._ _KADA KU MANTA MUNA YIN NA TAKEAWAY/ORDER . MUNA KUMA YIN NA BIKI (WE CARTER TO SMALL/LARGE EVENT...._ _FUNKASO TO PAIR WITH COW TAIL:2K_ _WITHOUT COW TAIL:1K_ _ALKUBUS TO PAIR WITH ASSORTED MEAT (KAYAN CIKI) 2K. WITHOUT ASSORTED MEAT :1K_ _PLS NB: PAYMENT VALIDATES INTEREST..... DELIVERY WITHIN KANO:500 NAIRA_ ________ *_FARHATAL-QALB_* _(FARIN CIKIN ZUCIYA)_ _NA_ _NANA HAFSATU_ __PG: 36_ *Dakyar* Waheedah ke iya bude idanunta. Saboda tsananin yadda kanta ke sarawa. Kanta na mata madaukakin ciwo. Ya yinda gangar jikinta ta dauki zafi rau tamkar garwashin wuta. A haka Kamal ya shiga dakin a daddafe don shima ba dadin yake ji ba. Ya nemi waje ya zauna akan wata kujera ta tsugunno. "Sannu Waheedah..." Bude idanun tayi da suke rufewa da kansu. Sunyi jawur da su. Sun kara furfutowa waje tubarkaAllah. "Yaya Kamal.... Kai zan wa sannu. Ya jikin?" "Da sauki ... Alhamdulillah. Ya jikin?" "Da sauki..." Ta fada tana mai cije labbanta. Ta miqe ta zauna dakyar daga kwanciyar da ta ke. "Yanzu Najib ze kawo miki ruwan gishiri ki sha. Saboda karfin jikin naki .. Kin sha panadol din ko?" "Ban sha ba... Zan sha yanzu." "Yana ina?" "Gashi nan..." Ta nuna masa kan murfin samira. Ya dakko ya tashi ya tafi dakin su ya dawo da pure water guda 3. "Ungo sha maganin... Wannan sai a hada miki ruwan gishirin ko . (ORS). ?" "To Yaya ... Ka koma ka huta." Ta fada a wahalce Ya danyi murmushi kawai. Yana dada kallonta sosai. Lalle Waheedah batata lapia sosai. Don bata kwanciya akwai kazar kazar. Bata taba cewa ta gaji akan aikace aikace. "Mu idan muna kwance ba lapia Waheedah ba ki taba kosawa. Komai da komai yi mana kike yi ba gajiwa. Ubangiji Allah ya baki lapia ya sa kaffarane. " "Aamin Yaya..." "Kibar kukannan haka kinji? "Tohm ...Yaya" Ta fada muryar ta na rawa. Ba jimawa kuwa Najib ya shigo hannun sa dauke da leda baka. Ruwan gishirin ne sachet 3 aciki da kuma pure water rabin leda a dayan hannun sa. "Dakko jug dincan ka hada mata. Ka ga ka fara dauraye shi tukun ka ji?" "Tom Yaya." Najib ya debi ruwa a kwalla ya wanke jug din ya hada mata ruwan gishirin ya miqa mata. "Ka da ki sha ruwa sai kin gama shan sa.." "Tohm Yaya...." Ta amsa shi. Kasan zuciyar ta ta tuno yayan nasu da tuni yanzu yana aiki a asibiti ko wata ma'aikata data shafi harkar lapia ko kamfani. Domin chew (community health extension worker) ne shi kafin ciwo ya kankame shi baki daya.. Har ya mike yar wayar sa mai torch light ta shiga kara a aljihun sa, Ganin number Najan Isubu ce. Hakan ya sa ya dauka da sauri. Ya kuma koma ya zauna "Wa'alaykm Salam... Ina wuni? Ah Alhamdulillah wallahi. Waheedah? Da sauki gata ta dan zauna... Eh shima yana nan. To bara na turo shi. Mungode, Allah ya saka da alkhairi. Amin. Okay tohm " "Ka karasa hada mata...?" "Eh. Gashi nan tana sha ma " "Yauwa. Kaje gidan Najan Isubu ka karbo abinci. Umma ce ta bata ta kawo mana.." "Allah sarki Umma. Muna ran ta. Uwa mai dadi. Allah ubangiji ya saka mata da mafificin alkhairi. " "Aamin Yaa Rabbi ." "Aamin." "Bara na dan watsa ruwa " "Tohm Yaya..." Kamal ya fice zuwa bandaki. Yayin da Najib ya fice zuwa gidan Najan Isubu. Daki ya zama sai Waheedah ita kadai tana zaune. Kanta a sama. Marka ta leka ta windown tana tabe baki. Kafin ta shiga ciki ba ko sallama ba re sannu " A koke." "Naam Marka ." "Ungo debo mun ruwa acikin nan..." Ta miqa mata wani bokitin karfe kato. Waheedah ta cika da madaukakin karshen mamakin halin ko in kula irin na Marka. Yanzu yanayin da take ciki na rashin lapia haka zata fita ta ebo ruwa bayan ga su Zainab can tana jiyo karakainan surutan su. "Ko ba zaki ebo bane? Yo naga ma fuskar ki a murtuke kaman zararriyar zakan ya. Zaki hau kai na da bugu ne?..." Waheedah ta girgiza kanta da a'a. Ta miqe dakyar. Jiri na neman kayar da ita. Amman a haka dai ta daure ta karbi bokitin tana dafa bango. Har ta fice daga dakin. "Mene nan? Gayyar munafurci." Marka ta shiga bude kwanuka. Harda daga jug din ruwan gishirin da kalar sa tayi kaman lemo. Ta kwankwada zata sha banza ta dauka lemo ne. Da sauri ta fuce ta isa ga rariya ta amayar da shi tana tabe baki Wani jiri ya kwashi Waheedah. Tayi sama dabas tayi zaman yan bori a k sa. Nan da nan ta sa kuka. Ba wai kukan faduwar da tayi bane. A'ah kuka ne akan zallar kiyayyar da Marka ke nuna musu a cikin dukkanin jikokin ta... Sun zama saniyar ware acikin jikoki. Tsana ce ta ke musu mai yiwuwar fassarawa. Kamal ya fito daga bandaki da sauri. Ya ajiye kwandon sosan wankan su a gefen daki. Ya nufi wajen Waheedah da ke sheme ta na kuka babu mai tanka mata. Ya dagata da sauri yana dudduba kafafunta da hannuwan ta. "Ba inda kika ji rauni ko? Eh Waheedah." "Babu Yaya..." "Me zakiyi da bokitin nan.?" "Ruwa.. Zan debowa Marka." Ya dauki bokitin ya fice waje ya ebo ruwan ya kai dede kofar dakin Marka ya ajiye . "Ba kai daya nake so ba .... Kai biyar nake bukata." Ta karasa fada tana yatsina. "Yaya zan ebo." "Keda baki da lapia. Barshi " "Uhm se an ebo dai. " Marka ta sake fada hade da sakin guda. "Wai ni Marka karfe nawa zamu tafi ne. Naga garin ya fara hadewa " cewar Inna Sa'adatu. Marka ta sheke da dariya tana murna . Farin ciki ya wanzu a fuskar ta sosai tace, "Mai jegon ma ta kira wayar mai sunan Malam. Tace ko mai dare da yardar Allah zasu zo nan. Anan zatayi wankan ina tunani " 'ahto Alhamdulillah.. Allah ya kawota." "Aamin." Kamal ya cigaba da zubawa Marka ruwa. Har sai da yayi kai biyar tukun sannan ya ajiye bokitin. Ya koma ya temakawa Waheedah ta koma daki. Sannan ya shige dakin su. Saboda jikin sa har ya