Sashe 63
Farhatul Qalbi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
da Zayn zukata da yawa sunyi farin ciki. Auren ki da Zayn abubuwa da yawa zasu gyaru. Domin ke din wani haske ce a tattare da rayuwar mu baki daya Waheedah. Kaunar da na ke miki ta sa na amince da auren ku. Na kuma yi farin ciki marar misaltuwa da kasancewar hakan Waheedah.. Ki dau wannan auren a matsayin taki kaddarar. Ki kuma yafe mana da zartar da hukuncin auren ku batare da an shawarce ki ba. Kauna ce ta kawo hakan.., Idan kuma kina kan bakan ki na rabuwar ku... Ba zan shiga hakkin ki ba. Zan samu Zayn ya sawwake miki a yau ba sai an ja da nisa ba. Kinji Waheedah? Kiyi hakuri bazan takura ki ba wallahi. Wannan auren ba zai ruguza zumuncin mu da ke ba. Zaa warware shi da yardar Allah.... Bar kuka." Haj Hameedah ta karasa fada muryarta na rawa. Yayin da itama hawayen ke tsiyaya a fuskar ta. Gwaggo haule da Umma Hadiza suka shiga basu hakuri duka. Haj Hameedah ta zame jikin ta daga na waheedah ahankali ta mike. Soro ta nufa ta kira Zayn a waya. Ta sheda masa dukkanin yadda sukayi da Waheedah. Don shi ma sai a satin daurin auren ake sanar masa da na su zaa hada. Ya yita FARIN CIKI yana azumin godia ga Allah na gwarzon sa'ar samun mallakar Waheedan . Maa ta tilasta masa da lallai yazo wajen waheedan ya sawwake mata tunda dai ta tsaya akan bakan ta. Idan kuma ta amince to yasanar da ita yadda suka tsayar da matsaya. Ko da Haj Hameedah ta fita daga dakin. Gwaggo haule ta shiga tausasar Waheedah. Amman sam waheedan ta ki bada kai sai ma ambaliyar hawaye da ta ke ta zubarwa. Fuskar Ahlam kawai take hangowa .. Gefe daya kuma ta Zayn da ko a baya ranar bikin sa yake sanarwa Dawood kan meze yi da Waheedah yar ficika da ba budurwa ba ce bata isa aure ba. Kuma a yanzu shi aka bata a matsayin miji? Ta girgiza kai kawai tana cije lebe tare da sake kyakkyabewa da wani sabon kukan. Nadra ta shiga dakin. Su gwaggo haule suka basu waje. Nadran ta shiga bawa waheedan shawarwari duk kuwa da ba sauraron ta take ba kuka take mai fitar da sauti ahankali. Duk da haka Nadra bata fasa ba sai da ta karasa maganganun ta tukun sannan ta shiga tsokanar waheedan har tana mintsinin ta. "Bakiga customized boxes dinki ba. Harda hashtag na #ItWasAlwaysYou:W ? Ni dai daman na san dan kumbure kumburen da Akiey yakeyi idan ya ganki duk kauna ce. Ya yita saki aiki duk wayon ya kare miki kallo ne. Shi kadai yasan labarin da ke cikin zuciyar sa . Ashe dai Waheedah itace FATHATAL-QALBin Ya Zayn.. Sai yanzu na kara amincewa da hashtag dinnan na It was always you Waheedah... Kaunar ki a zuciyar sa ta dade tana tsumuwa ke din ce always and forever dinsa. Bai taba soyayya ba sai akan ki. Ashe yar mutan shurah ce ta sace zuciyar Yayan mu har ya kasa hakuri sai da ya mallaketa? Ina muku fatan alkhairi. our newest sister in-law... Aunty Waheedah.... Mrs Zayn Adams Nasser. U r highly welcome to the Adams family... Allahumma bareek " Tana karasa fada ta sumbaci kan waheedan ta mike bayan ta mata sallama ta fice daga dakin Tunda ta fara magana har ta karasa Waheedah bata kulata ba. Tana dai sauraron duk wata kalma data ambata. Tana jiyo sanda suka karasa wasa da dariyar su. Kafin daga bisani su tashi su tafi . Fannah da Basira suka bi su da kayan makulashen da suka tanadar musu. Da dan tukwicin da suka bayar a matsayin su na marasa shi. Ko bayan sun musu rakiya sun dawo. Akan Waheedah suka taru suna bata baki. Banda Umma Hadiza da ta zauna agefe kawai tana canza channel din yar rediyon da ke hannun ta. Da suka takura mata da magana kuka ta fashe da shi. Daga karshe ma ta bi su fannah da Basira gidan su wajen Deluwa dubo yaran kamar yadda Gwaggo haule tace. Suna zuwa kuwa Waheedah adan guntun ilimin ta take sanar da su Basira ko ciwon idanun jaririyar dayar anophthalmia/microphthalmia ne? Daga baya kuma su Gwaggon suka kai kayan lefen gidan wajen Marka. Inna Sa'adatu na asibiti bata farfado ba Ya yin da zainabu ke gadon asibiti itama batasan wanda ke kanta ba. Marka kuwa tamkar sabuwar tabi. Don kayan lefen da aka kawo mata tagani ma zugii su ka karawa zuciyar ta. Ta shiga kokawa tana bubbuga kirji. Sai hararar kayan take. Ya yin da makota na kusa da na nesa suka debo kafafuwa don ganewa idanun su akwatunan shake da lefen Waheedah. Kaf ko a tarihi babu wanda aka taba kawowa kaya himili guda irin Waheedah. Lalle duk mai hakuri zai ci riba watan watarana. Saboda tsabar bakin mutane. Kit da gwalagwalen ke ciki Najan Isubu kasa fitowa tayi da su. Kar abi dare a sace su tas. Ko bakuna su tsige auren . Masoya sun sanya albarka da fatan zaman lapia tsakanin Waheedah da mijin nata. Sam marka batasan dan masu kudi Waheedah zata aura ba. Da bata amince da auren su ba. Ta hararo lefen da wutsiyar idanun ta . Hade da saka yatsanta a baka ta gartsana shi cikin tsantsar hassada da bakin ciki. Kasa jurewa tayi ta koma cikin dakin ta. Ko da yan kallon kayan suka kammala gani. Aka mayar da su gidan gwaggo haule. Kafin washegari a mayar da su gidan na The Adams Family don gudun barayin dare masu bin lefunan mutane su sace su. ******* Kallon kansa ya tsaya yi a gaban mirror. Yana sanye cikin dakakkiyar wagambari da ta sha aikin hannu. Da hular data dace da aikin kayan . Sai hula data sha kari ta zanna bukar. Agogon sa ya hau da kayan jikin sa. Hakama takalman da ke sanye cikin kafafun sa. Ya yi matukar kyau. Ya dakko turaruka ya shiga feshe dukkanin lungu da sako na jikin sa. Ya goga chappete a bakin sa. Ya gyara zaman zobunan azurfar da ke yatsan sa. Sannan ya dau wayar sa ya zura a aljihun gaban rigar sa ya fuce daga dakin nasa cikin takun kasaita irin ta angwaye. Dake tattare da farin ciki da annushuwa. Kamshi ne kawai ke tashi daga jikin sa. Ga wani kyawu daya kara haskaka shi. Yana sauka daga mattakalar bene ya na mai bare ledar chewing gum din hannun sa. Me mint flavour ya jefe a baka yana taunawa ahankali. Ahlam na zaune a doguwar kujera da wayarta a hannu. Ta dube shi ta watsar. Tun da Ummimi ta zo da kanta gidan ta sanar mata rana i ta yau daurin auren Zayn.. Amman bata gaya mata wadda zai aura ba. Ta ja mata kunne sosai tare da mata nasiha akan zamantakewar aure da hakkokin sa..... Da harara tabi shi. Yayi murmushin gefen fuska kawai. Ya zauna akan hannun kujera yana kare mata kallo. Ya kasa gane muhimmancin da ta bawa zama da kayan bacci. Ta kwanta ta tashi da su. Da rana ma tayi wanka ta mayar da su. Ya dan lekar da fuskar sa ga wayar da ke hannun ta hausa novel take karantawa na: zafafa biyar "Meye zafafa biyar kuma?" "Ina ruwan ka? Littattafan hausa ne mana.." "Amma...I'm very sure. Inde littattafan hausa ne suna muku koyi ta yadda zaku dinga kula da tarairayar mazajen ku. Kula da tsaftar jikin ku.. da sauran su. Su kan su ba zasu baku gurbatacciyar shawara ta fatali da ayyukan gidajen auren ku ba ." Bata bashi amsa ba ta juyar da kanta gefe tana turo baki gaba. Gyara zaman sa yayi ya shiga yi mata nasiha mai ratsa jiki tare da bata hakuri akan dukkanin wasu lefukan da yayi mata a bisa rashin sani. Da kuma wanda yayi da sanin, Ya kuma karkare da batun, "Game da wacce na auro kuma.... Bata da masaniyar neman auren ta ma ballanta na batun daurin auren mu da ita. Kuma ko da aka sanar mata tanacan tace dole awarware auren nan... Badan komai ba saboda tamkar cin amana ne awajen ki. Duk kuwa da bata kauna ta. Tana mai jin kunyar kasancewar abokiyar zaman ki .. Ahlam!! Wannan ba kowa bace fyace..." Ahlam ta daga kai da sauri ta dube shi. Gabanta na tsananta bugawa. Zayn ya kada kai alamun tabbatarwa da zancen sa kafin ya ce, "Waheedah itace wadda na aura ba tare da masaniyar neman auren ta da nayi ba. Ballanta na kuma daurin auren mu da aka daura yau .." Kasa magana Ahlam tayi. Idanuwan ta suka shiga kiftawa. Hawaye sirara suka shiga reto a kyakkyawar fuskar ta. Ta mike da sauri tayi sama tana mai fashewa da wani sabon kuka.. Ya dan jima yana sake sake a zuciyar sa. Ya bita saman yana ta roko ta bude dakin taki. Ya sauka fice daga gidan. Kai tsaye ya nufi gidan Gwaggo haule. *WAHEEDAH....* Suna tsakar gidah baki dayan su. Ciki harda Waheedah data rufe kafarta saboda soro. Tana mai karanta sakon da ya shigo wayar ta ta lambar Dawood, "Nikah Mubarak my wife, You are a missing ingredient of my life that has everything..D has now been completed. For me it's not just about showering you respect, you are and always will be my respect, My queen and I honour and respect your family at all times .May Allah give me ability, power and strength to make you happy, for the rest of your life... I love soo much... With every fiber of my being darling... " Tana karasa karanta sakon, Zayn yayi sallama. Sai da aka bashi iso ya shiga. Ya gayshe da su cikin girmamawa. Waheedah ta gayshe shi fuskar ta a kumbure. Ya karaci zaman sa. Suna hira da gwaggo da yake jefa kalamai daya biyu. Ya musu sallama yana sosa keya ya fuce. Gwaggo tasa Waheedah ta raka shi. Har waje ta raka shi. Yana gaba tana biye masa a baya. Sun danyi tazarar har zuwa wajen motar sa. Dake ba mutane awajen layin shiru. Hakan ya sanya Zayn rarumo Waheedah tanata ture shi amman yaki sakinta. Ya rungume ta tsam a faffadan kirjin sa. Yana sinsinar wuyan ta dake