← Book details Farhatul Qalbi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 68 OF 82

Sashe 68

Farhatul Qalbi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ne a rayuwar INAYAH,kowanne a cikinsu akwai wani murdadden Al'amari da ya shata layi tsakaninsa da ita,wawakeken sirri wanda a koda yaushe take kiransa da SANADIN LABARINA_* *_Amma babban abun mamakin a koda yaushe shine,ita dai tasan cewa BABU SO tsakaninsu MEYA KAWO SHI?_* *_Duk da haka tana tunanin yun qundun bala ta fitar da FARHATUL K'ALB a cikin ZAFAFA BIYAR din samarinta,duk da batason su zame mata GURBIN IDO wanda har kullum ba ido bane_* *YA KUKAJI SALON MASU KARATU?* *YADDA SALON YA BAMBANTA DAKO YAUSHE HAKA LABARAN SUKA BAMBANTA DA DUKKA LABARANMU NA BAYA* INAYA(riba biyu)___mamughee SANADIN LABARINA___Rano BABU SO___Billynabdul FARHATUL K'ALB___Miss xoxo GURBIN IDO____Huguma *ZAKI YARDA AYI TAFIYAR NAN BABU KE MADAM?* *_GARZAYA KI BIYA NAKI KUDIN KAN FARASHI KAMAR HAKA_* Biyar:::1k Hudu:::700 Uku::::500 Biyu::::400 Daya:::300 *_zaki saka kudin ta wannan account number din_* HAFSAT UMAR KABIR 2270637070 Zenith bank *Saiku tura shaidar biya zuwa ga* 07040727902 *IDAN KUMA KATIN WAYA NE ZAKU TURA TA NAN TARE DA SHAIDAR BIYAR* 09134848107 *_THANKS FOR THE CONTINUED PATRONAGE_* [11/23, 9:02 PM] Mummyn Yara: _*FARHATAL-QALB*_ _(FARIN CIKIN ZUCIYAH)_ _NA_ _NANA HAFSATU_ _(MX)_ _AREWABOOKS:MISSXOXO_ _WATTPAD: MISSXOXO00_ _ZAFAFA BIYAR PAID NOVELS_ _PG:63_ _WANNAN LITTAFI DA MA SAURAN NA *ZAFAFA* NA *KUDI* NE. DAN ALLAH KI/KA BIYA KUDI KI/KA MALLAKI NA KI. DON GUDUN SHIGA HAKKOKIN MASU RUBUTAWAR DA MA WADANDA SUKA CIRE KUDI SUKA SAYA..._ _______ Dake asabar ce. Ya dan jima yana bacci tun bayan da yayi sallar asubah. Yana tashi ya faada bandaki yayo wanka. Hade da yin brush. Ya sauya kayan sa zuwa manyan kaya . Samfurin riga da wando na shadda. Amman bai saka hula ba. Ya dai taje sumar kansa data kwanta luf. Ya kuma taje ta sajen sa. Ya bulbula turarukan kamshi ajikin sa ya sauka kasa. Babu Ahlam a duk wani daki da parlorn da ke kasa. Ba kuma ta kitchen ba ta farfajiyar waje. Hakan ya bashi damar ganowar tana sama. Don haka ya koma saman. Tana cikin dakin ta. Ya murda ya jita a datse alamun ta saka makulli. Har zai juya sai kuma ya tsaya jiyo wayar da ta ke a handsfree ne kuma da aminiyar ta Bushra suke wayar. Don ya gano muryar. Ahlam din na kuka tana daga sautin muryar ta. Wayar sa ya janyo. Ya danna wajen recording ya seta ta. "Wallahi ita dai Bushra... Ko a mafarki ban taba kawowa yarinyar nan itace wadda Zayn zai auro ba.. Bushra Zayn ya cuce ni.. Ya gama da rayuwa ta. A iya tsara rayuwa ta da nayi wallahi ban taba kawowa Zayn zai mun kishiya ba...Ya illata ni.. " "Kiyi hakuri bestest ..Shawarar dana baki dai itace final solution.. Itama yarinyar ai na gaya miki ba ta zauna ba. Bare sunga gidan dadi ne. Ita da mahaifiyar ta zasu bazama bokaye su dasa soyayyar ta acikin zuciyar sa. Ina Zayn ina wannan kucakar yarinyar? Ita ba wata kyakkyawa ba . Dan wallahi kin fita kyau, Ita ba class ba. Ita ba wadataccen ilimi ba. Ba kuma daga babban dangi tafuto ba na mulki ko sarauta.. Ai ke kina ganin lamarin kinsan asiri ne ba yin kansa ba ne. Soyayyar jinnu ce. Ai shiya sa gwara da kika kaurace masa. Kika hanashi kusantar ki har sai ya dawo cikin hankulan sa..." "Gaskiya nima nayi wannan tunanin da farko. But babes lamarin fa babba ne. Allah tun lokacin bikin mu bana gaya miki ba? Ya kira ni da Waheedah, Nace Waheedah kuma? Ko bayan auren ma. Tunda ta dawo nan gidan. Yanayin yadda yake bin ta da kallo zaki gane he's into her." Zayn ya girgiza kai kawai. Ya sake gyara tsayuwar sa. Yana mamakin sakarci irin na Ahlam da ke bin zugar kawaye . Meyakwan tayi kokari ta gyara rayuwar auren ta dake neman tabarbarewa. Ji yake tamkar ya dakko spare key ya bude kofar. Ya shiga ya kashe wayar ya kuma buga ta da kasa. Saboda tsananin yadda zuciyar sa ke tunzura shi. Ya dakata kawai. "Kibar aikin bokonci Ahlam. Na ke gaya miki. Kaunar da yake miki hatsabibin bokan su ya dauke ya dasa a zuciyar Waheedah din. Shine ya mato akanta. Tsinannu. Nagaya miki na samo hanya. Sha yanzu magani yanzu. Aikin sa kamar yankan wuka yake. Idan ma so kike ya rabata da iska. Zai kashe ta. Ta hanyar mata turen ciwo. Ko ya haukata ta. Ko ya mata kurciya ta shiga duniya a nemata a rasa. Ko a saka mata mantau ta manta komai nata.... Ko" "Noo bestest.... Duk bana kaunar wadannan abubuwan. Kar a mata ko daya daga ciki. Banda kisa, Banda hauka, Banda mantau din da kikace banda kuma kurciya din. If there's no other way.. Mu hakura kawai." "Ke dai wani lokacin banza ce wallahi. Tazo har gidah ta shiga jikin ki.. Ta aure miki miji kice duk wadannan ba zaki iya ba? Kar ki manta ta kaudar da hankalin mijin akan ki . Ni gidan ki da tazo ta zauna ma tun farko bai kwanta mun ba... Saboda nasan da wata kulalliyar tazo. Maybe ta dauki kayan sawar ki ma ta kai da su akai amfani. Ke wasu mutanen fa mugaye ne. Da kuma na gaya miki nace mahaifiyar sa bata kaunar ki. Har da ita a masu ruwa da tsakin.." "Ai nima da kika fada na gano haka ne. Bata kaunata. Tana wani murmushin mugunta. Daman can ita ta hada auren. Tunda agidan ta suke aiki yarinyar da mahaifiyar ta. So ni dai yanzu so na ke yarinyar nan a lalata rayuwar ta kawai taji batason zaman auren ni yafiye mun. Shi ma yatsaneta.. Kingane?" Zayn ya kara harzuna. Gumi na keto masa na tsananin bacin rai. Ya danne ransa. Yana jiyo sanda Bushra ke ce mata, "Zan gayawa bokan kan ya shafe gaban waheedan. Kar ma Zayn din yaga komai idan yazo auratayya da ita. Ya shafe shafin siminti (cement) Ya kuma cire kaunar sa a zuciyar Zayn din ta zama itace bakin cikin sa a rayuwa. Sannan ya kara mata da warin jaba. Ta dinga hamamin doyi. A kuma cire kaunar da yake mata . Da shi da mahaifiyar ta sa. Ke long story short shi ma a rabashi da mahaifiyar ta shi. Ya juya mata baya. Ta yadda ke kadai zai dinga jin maganar ki. Ya kuma saki Waheedah din. Ya zama ya dawo a tafun hannuwan ki. Sai yadda kikayi da shi . Koya kika ce?" Ahlam ta kyalkyale da dariya har tana kyakyatawa tamkar ba ita ke kuka dazu ba. "Sha kurumin ki. Ki bar zubar da hawayen ki. Hanyar gidan boka ba wanda bamu sani ba. Kede kawai dukkanin umarnin daya ketara miki kiyi . Ko sallah yace ki bari ta yan kwanaki ce kingane? " "Nagane kawata... Na gaya miki banda kisa dai. Banda dik sauran. Kawai a shafe gaban nata a kuma saka mata doyin. A kuma cireta a ransa. Sannan yadda kikace din. Na aminta .A raba shi da mahaifiyar tasa. Daman yadda yake kaunar ta yana ci mun tuwo a kwarya . Komai Maa. Komai Maa. Sai abunda tace. Kullum yana can wajenta na tsani hakan. " "Sha kurumin ki. Tamkar an raba su ne. Ina nan shigowa dana harhada komai zan je wajen sa. Da kai na zan biyo flight na zo. Na gaya miki aikin sa kamar yankan wuka ya ke. Zan hado miki da wanda Zayn din zai bude miki bakin aljihun sa ma. Duk kudaden sa ke zaki rika juyawa. Ki kuma mayar da shi rakumi da akala sai yadda kikayi da shi. Ta yadda idan kika ketara kara ba zai tsallaka ba. Idan kikace da bakin abu fari. To ta zauna.. kawata.. ki kokarin samun tufafin su ki aiko ko da ta tasha ne.. " "Masha Allah tawaje na. Amanar zuciyata. Bugun numfashin senator gallauro.. Allah ya biya ki da alkhairin sa. Ya yi auren ku da sanata." "Amin kawata.... Sai na kira ki " "Yauwa.. Godiya na ke." Suka katse wayar da suke yi. Yana jiyo sakin karar farin cikin da Ahlam tayi tana buga kafafu Kasa tabuka komai yayi. Ya yin da kafafun sa suka gaza daukar sa. Ya jingina da bango yana runtse idanu. Maganganun su Ahlam sai yawo suke masa a kwakwalwa. Innalillahi wa inna ilaihi rajiun... Ya shiga maimaitawa yana mai dafe goshin sa da jijiyoyin sa suka daga saboda tashin hankali. Dakyar ya iya mikewa ya sauka kasan. Kai tsaye ya wuce wajen freezer ya dakko ruwa ya zauna ya sha. Tukun sannan ya fice daga gidan bayan ya shiga mota. Gidan su ya nufa kai tsaye. Haj Hameedah ya samu a karamin parlor tana karatun jaridah. Bayan sun gaysa ne take tambayar sa ya Ahlam da fatan dai zaman su ba matsala? Ta lura ainun da damuwar da ya shiga don haka ta shiga tambayar sa akan me ke faruwa? Ya kasa boyewa saboda gudun faduwar abun Allah ya kyauta. Don haka ya janyo wayar sa ya kunna mata recording din da yayi na hirar Ahlam da kawarta. Haj Hameedah ta saurara gaba daya tana kada kai. Ta tsorata da mamakin yadda suna kananun yara amman suke kokarin kulla wannan mugunta haka? Don haka bata tsayar da zancen ba. Ta tasa Zayn agaba suka tafi sashen Abiey dinsu. Allah ya temaka ma su Ummimi sunzo tare da sauran iyalan nata. Bayan sun gaggaysa. Ummimi na tambayar Zayn Ahlam. Maa ta bashi umarmin daya kunna musu recording dinnan domin abun yafi karfin ta Don haka aka samu babban music player aka hada ta da wayar aka kunna yadda kowa zai saurara dakyau. Hirar su tafara tiryan tiryan. Parlorn ya dauka da salati da sallallamin girman maganganun da suke futowa ta recording din. Ummimi ta shiga girgiza kai kawai tana mai kambama mamakin zantukan. Suna karasa saurara kuwa ta sa lalle a je a dakko Ahlam . Hakan kuwa akayi. Basher aka tura ya dakko Ahlam din. Tanata tambayar sa daukowar menene? Yace su Ummimi ne zasu gaysa. Ko da ta shiga parlorn. Hada gaisuwar tayi ta jimlanta. Suka amsa baki daya. Banda mahaifin ta. Da yake jefa mata kallo mai tattare da bakin cikin abunda tayi. Yana mai tir da munanan halayen ta. Ummimi ta saka Ahlam din ta dawo gabanta. Bayan tayiyyi nasiha mai ratsa ta shiga cewa, "To
Chapter 68 · 0% Book details