Sashe 34
Farhatul Qalbi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
tana kallo cikin nutsuwa. "Muje kiyi alwala..." "Me zanyi?" "Sallar nafila mana .." "Oh..." Ta miqe dakyar. Tana tafiya tana kallon tv sauran kadan suyi gware da Zayn Dukkanin su sukayi alwalar. Zayn ya ja su sallah. Sai daya matsawa Ahlam da murtuke fuska. Sannan ta iya kashe kayan kallon suka kwanta. Ta juya masa baya shima ya juya mata. A haka kowannen su yayi bacci. Kafin ayi kiran sallar asubah. Zayn ya fita masallaci da rakiyar baba mai gadi. Ita kuma Ahlam ta yi tata agida. Haka dai zaman nasu ya kasance. Da dadi ba dadi. Satin su daya da aure kullhm daga the adams family ake kawo musu abinci na safe na rana dana dare. Ba gajiyawa bare kosawa. Kwanan Ahlam 10 bata girki. Kullum Zayn takeaway yake mata saboda excuses din Ahlam..Sam taki yin girki. .. Wata sunna ta auratayya sam bata taba shiga tsakanin su ba. Saboda Ahlam din taki bari Zayn ya kusanceta. Saboda Wani uzuri nata daban. Daya ga hakama. Sai shima ya guje mata. Ya koma dakin sa da kwana. Da safe yayi mata takeway da rana ma haka har zuwa dare Shi kuma kullum yana gidan Maa. Acan yake cin abinci. Har tahowa yake da wani ya saka a fridge kdan ya kwana yayi reheating yaci . Haka zaman na su ya cigaba da kasancewa. Sababbun halayen Ahlam da Zayn bai sani ba sunata fitowa. Don haka yake danne zuciyar sa. Wataran idan ya fita baya komawa sai bayan ishai. Karshen abunda Ahlam ke nema wajen Zayn bai wuce sumba ba da runguma da sauran su. Bayan nan sam babu ruwan ta da daya raya sunnar. Tun lamarin na damun Zayn har ya dena. Sai ya kara daukar ta ma a matsayin waddaa suke ciki daya. Ko sha'awarta sam baya yi ya dai na... GIDAN MALAM NALADO #FARHATAL QALB!! (FARIN CIKIN ZUCIYA) _ASSALAMU ALAIKUM..._ _YAU MUN KAWO KOKEN KU KARSHE . MUN NEMO MUKU INDA ZAKU SAMU LUSH AND COMFY BUBUS CIKIN FARASHI MAI RAHUSA DA INGANCI_ _LUSH/COMFY BUBUS BY: MRS. ZP_ _08147243787_ _WHATSAPP:+234 9332_ _WADANNAN BUBUS SUNA DA MATUKAR LAUSHI KUMA A SAKE SUKE BABU MATSI_ _KALA KALA NE DA SIZES DABAN DABAN...KUMA KOWANNE IRIN LIYAFA ZAKU SAKA KUJE. IRIN RICHLY LOOKS DINNAN DA SAI AN KALLE KU AN SAKE KALLA SABODA KYAWU DA INGANCIN SU. BUBUS DIN A HADE SUKE DA MAYAFAN SU.. ZAKU KUMA IYA PAIRING DA WASU MAYAFAN DABAN_ _WADANNAN BUBUS ANA BADA SU NE AKAN FARASHIN SAYA DAYA DAYA KO SARI..... 12K AKAN GUDA DAYA. IDAN SARI NE KUMA 11K. WADANNAN FARASHIN KASUWA NE. DUK INDA ZAKU ZAGA KUDIN SU YAFU HAKA.. MUNA ARHA NE DON KOWACCE MACE TA IYA MALLAKAR SU._ _MUNA TURA KAYAYYAKIN MU A KOINA A FADIN NAJERIYA DA KETARE .._ _ADIRESHIN SU: NA'IBAWA ZARIA ROAD, KANO.._ _IDAN ANJE SIYA ACE DAGA ZAFAFA NE. DOMIN MUN YABA DA KAYAYYAKIN SU. KUNSAN DAI BAMA TALLATA MUKU ABUBUWAN DA BASUDA KARKO_ _KYAU, INGANCI, RAHUSA SAI COMFY BUBUS DIN MRS. Z.P_ -------- _FARHATAL QALB_ _(FARIN CIKIN ZUCIYA)_ _NA_ _NANA HAFSATU_ _PG:38_ [11/23, 9:01 PM] Mummyn Yara: _ASSALAMU ALAIKUM..._ _YAU MUN KAWO KOKEN KU KARSHE . MUN NEMO MUKU INDA ZAKU SAMU LUSH AND COMFY BUBUS CIKIN FARASHI MAI RAHUSA DA INGANCI_ _LUSH/COMFY BUBUS BY: MRS. ZP_ _08147243787_ _WHATSAPP:+234 9332_ _WADANNAN BUBUS SUNA DA MATUKAR LAUSHI KUMA A SAKE SUKE BABU MATSI_ _KALA KALA NE DA SIZES DABAN DABAN...KUMA KOWANNE IRIN LIYAFA ZAKU SAKA KUJE. IRIN RICHLY LOOKS DINNAN DA SAI AN KALLE KU AN SAKE KALLA SABODA KYAWU DA INGANCIN SU. BUBUS DIN A HADE SUKE DA MAYAFAN SU.. ZAKU KUMA IYA PAIRING DA WASU MAYAFAN DABAN_ _WADANNAN BUBUS ANA BADA SU NE AKAN FARASHIN SAYA DAYA DAYA KO SARI..... 12K AKAN GUDA DAYA. IDAN SARI NE KUMA 11K. WADANNAN FARASHIN KASUWA NE. DUK INDA ZAKU ZAGA KUDIN SU YAFU HAKA.. MUNA ARHA NE DON KOWACCE MACE TA IYA MALLAKAR SU._ _MUNA TURA KAYAYYAKIN MU A KOINA A FADIN NAJERIYA DA KETARE .._ _ADIRESHIN SU: NA'IBAWA ZARIA ROAD, KANO.._ _IDAN ANJE SIYA ACE DAGA ZAFAFA NE. DOMIN MUN YABA DA KAYAYYAKIN SU. KUNSAN DAI BAMA TALLATA MUKU ABUBUWAN DA BASUDA KARKO_ _KYAU, INGANCI, RAHUSA SAI COMFY BUBUS DIN MRS. Z.P_ -------- _FARHATAL QALB_ _(FARIN CIKIN ZUCIYA)_ _NA_ _NANA HAFSATU_ _PG:39_ *Karasa* karin kumallon nata tayi. Ta nannade sauran wainar yar tsalar ta doni dakakken kuli kulin daya sha hadi a baki. Kana ta kafa kai ta shanye ruwan shayi marar madara. (Ruwan bunu). "Yaya Waheedah ..." "Na'am Najib." "Yauwa baki tafi ba ashe..? Ga shi inji Yaya Kamal." Ya daga asaberin da ke dakin ya shiga. Ya mika mata nera hamsin. "Na meye?" "Kudin makaranta mana." "Kai Yaya baya gajiyawa dai? Ai tayi yawa ma.." Ta amsa ta zura cikin yar jakarta. Mikewa tayi ta goga yar jakarta a bayanta. Ta kalli kyakkyawar fuskarta acikin mudubi . Tayi rama sosai saboda rashin Umman su a tare da su. Ba ita kadai ba su Kamal da Najib ma duk sun rame. Safunan ta ta janyo da ke kan katifa. Ko'ina a dakin tas ta share ta gyara. Harda temakon turaren wuta na tsinke data kunna ta soka shi a bango. Ta zura safar tana ta sauri gudun karta makara. Salama a kayo tun daga zaure. Marka da ke zaune kan turmi ta miqe da sauri "Wa'alaykm Salam.Daga gidan gwangwan dinne?" Ta karasa tanbayar su tana mai sakace hakoranta da tsinke. "Eh mune...." "Yauwa ku shigo." Waheedah na kokarin janyo kofar zata rufo. Marka ta bangajeta tana, "Ku shigo nan dakin ne..." Matashin saurayin ya shiga yana duba cikin dakin kusurwa kusurwa. Shi kuma dayan da suke tare yana mai duba wajen dakin. "Me gidah ya ne...?" "Ah maza yayi fa. Mu chakata kawai. " "Toh ya ake ciki?" Marka ta tambaye su hade da zuba musu idanunta ba kakkautawa.. Dayan ya sake juyar da idanun sa ya kallo dakin. Hade da saka hannu ya dan daddaki bangon jikin dakin. "Toh iya....Munga daki, Yaushe za'a kwashe kayan ciki?" "Ke zo nan dan malafar gyatumin Hadiza. " Marka ta fada tana mai hararo fuskar Waheedah. Waheedan ta isa gare ta kanta a k sa. Yayinda kasan zuciyar ta ke bugawa sosai. "Ga ni Marka." "Uhum. Nu na musu baki da ...." Kwas ta sakar mata rankwashi ta cigaba da cewa. "Nuna musu baki da tarbiyyah na ce . " Ta sake sakar mata wani bayan ta gama fada. Kunya da zafin radadin zugin rankwashin da Marka ta sakarwa Waheedah ne yasa wasu hawaye sirara suka zubo mata daga idanu. Ta goge hawayen da kasan hijabin ta Wadannan din da Marka ta jajibo har cikin daki . Ta kuma rankwashe ta agaban su ne. Abokai ne ga Ibrahim. Kuma majalisar su daya. Tare suke zama. "Kiyi hakuri ..." Ta rausayar da kai ta sake bawa Marka hakuri. "Wuce ki tafi. Da kin dawo kuma ki tattare komatsan ki. Kisan yadda zaki dasu. " "Tom." Ta amsa ahankali. Kana ta wuce makaranta kai tsaye. Tana tafiya tana hawaye. Daya bayan diya suka shiga zurara daga idanun ta. Har sai data cire gilashin tukun sannan ta goge idanunta sosai kafin ta mayar dashi ta cigaba da tafiya. A wurin shagon na fulani gab da shiga hanyar new gra shurah . Waheedah ta hango Umman su Hadiza na tafiya. Sanye cikin kayanta riga da zani ta dora da hijabi babba har kasa. Da sauri waheedan ta cimmata. Tanata murmushi "Umma ina kwana...?" "Lapia Lou... Waheedah." Waheedah ta kasa boye farin cikinta na ganin Umma da tayi. Ta rungumeta . Fuskarta lullube da farin ciki marar misaltuwa. Ita kanta Umma Hadizan a nata bangaren dadin farin cikin ganin waheedan itama ya mamayeta. Ta sauke nannauyar ajiyar zuciya tana mai danne hawayen da suke kokarin zubo mata. Nan da nan kuwa Waheedah ta shiga zayyane wa Umma Hadizan dukkanin abubuwan da ke faruwa a gidan na su. Umma Hadizan ta sake kwafar ta kan wasu abubuwan. Ta kuma nusar da ita ga hanyoyin da zatabi ta kaucewa duk wani tarzoma da kutungwila da ka iya tashi nan gaba agidan na su. Suna tafe suna maganar har suka karasa new gra shurah. Dai dai kofar gidan na The Adams Family da suke hangowa hancin motar ya fito. Wata zungureriyar mota jeep data ji kudi ta koshi ce ta fito daga cikin gidan. Dr. Hameedah ce ke a kujerar driver tana tukawa. Rigar data dora akan kayanta kuma wata blazer ce white color . Ta yane kanta da farin mayafi. Tana zuwa dai dai kusa da su ta tsaya da motar. Fuskarta kumshe da farin ciki ta zuge gilashin motar, Dukkanin su suka gaisheta cikin girmamawa . Ta amsa musu fuskarta a sake. Kafin ta dora da cewar, "Ai munyi fushi Waheedah... Shikenan kin dauke kafan ki gaba daya? Moha kullun sai yayi maganar ki . Yayita tambaya kina iya.? Lalle a nemo ki. Idan na tambayi Umman ki sai tace kina gidah.... Uhm? Me ke faruwa ne Waheedah....?" Waheedah cikin subul da baka tace, "Ai Umma tabar gidan...." "Banga ne ba.... Bata gidan kuma?" Sai a sannan Waheedah ta gano 'baram'baramar da tayi. Ta shiga mammatsa hannuwanta tana mai noke kai. Umma Hadiza ta daga idanu ta mata kallon kin kyauta. Daga bisani tace, "Kada mu bata miki lokaci Hajiya .." "Kar dai Waheedah ta makara. . Ba damuwa zamuyi magana insha Allah.Idan kin tashi daga makaranta ki biyo ta nan." "Toh Hajiya sai kin dawo .. Allah ya shi albarka ya bada sa'a Amin...." "Amin Amin " Dr. Hameedah taja motar ta tatafi. Yayin da Umma Hadiza da Waheedah suka cigaba da tafiya. 'umma kiyi hakuri .. wallahi bansan a fili na fada ba." "Sai a kori gaba... Ki tafi makaranta. Allah yabada sa'ar karatu ". "Amin Yaa Rabbi.." "Yauwa ... Ya ya jikin su Najib da Yayan ku?" "Allah ya kara sauki yasa kaffarane." "Amin Amin Umma .." "Najaatu na aiko muku da abinci ko?" "Tana aikowa... Kusan kullum sai mun dumama munci washegari ma" "Yauwa Alhamdulillah... Daman abunda yasa banason daya daga cikin ku yazo nan din ya karba. Ba komai bane fyace sai dai don kada tarzoma tataso. Shi yasaka nake cewa Najan ta turo Wanda zai riqa kawo muku." "Ana kawowa. Allah ya shi albarka...." "Amin Yaa rabbi . Ai ba abunda