Sashe 61
Farhatul Qalbi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*_ZAFAFA BIYAR din samari ne a rayuwar INAYAH,kowanne a cikinsu akwai wani murdadden Al'amari da ya shata layi tsakaninsa da ita,wawakeken sirri wanda a koda yaushe take kiransa da SANADIN LABARINA_* *_Amma babban abun mamakin a koda yaushe shine,ita dai tasan cewa BABU SO tsakaninsu MEYA KAWO SHI?_* *_Duk da haka tana tunanin yun qundun bala ta fitar da FARHATUL K'ALB a cikin ZAFAFA BIYAR din samarinta,duk da batason su zame mata GURBIN IDO wanda har kullum ba ido bane_* *YA KUKAJI SALON MASU KARATU?* *YADDA SALON YA BAMBANTA DAKO YAUSHE HAKA LABARAN SUKA BAMBANTA DA DUKKA LABARANMU NA BAYA* INAYA(riba biyu)___mamughee SANADIN LABARINA___Rano BABU SO___Billynabdul FARHATUL K'ALB___Miss xoxo GURBIN IDO____Huguma *ZAKI YARDA AYI TAFIYAR NAN BABU KE MADAM?* *_GARZAYA KI BIYA NAKI KUDIN KAN FARASHI KAMAR HAKA_* Biyar:::1k Hudu:::700 Uku::::500 Biyu::::400 Daya:::300 *_zaki saka kudin ta wannan account number din_* HAFSAT UMAR KABIR 2270637070 Zenith bank *Saiku tura shaidar biya zuwa ga* 07040727902 *IDAN KUMA KATIN WAYA NE ZAKU TURA TA NAN TARE DA SHAIDAR BIYAR* 09134848107 *_THANKS FOR THE CONTINUED PATRONAGE_* [11/23, 9:02 PM] Mummyn Yara: _*FARHATAL-QALB*_ _(FARIN CIKIN ZUCIYAH)_ _NA_ _NANA HAFSATU_ _(MX)_ _AREWABOOKS:MISSXOXO_ _WATTPAD: MISSXOXO00_ _ZAFAFA BIYAR PAID NOVELS_ _PG:59_ _WANNAN LITTAFI DA MA SAURAN NA *ZAFAFA* NA *KUDI* NE. DAN ALLAH KI/KA BIYA KUDI KI/KA MALLAKI NA KI. DON GUDUN SHIGA HAKKOKIN MASU RUBUTAWAR DA MA WADANDA SUKA CIRE KUDI SUKA SAYA..._ ____ *Cikin* matotowar rawan darin da take yi ne Gwaggo Haule ta shiga dakin ita da Umman su. "Ah'aha... Waheedah? Meya same ki?" Gwaggo haule ta tambaye ta. So take ta amsa. Amman bakin ta ya gaza, Sai sassarke hakoran ta ta ke yi. Sakamakon gabobin ta da suka dauki rawa baki daya. "SubhanAllahi... Hadiza taimaka mun dan Allah." Cewar gwaggo haule. Gwaggo haule ta karasa kusa da Waheedah. Ta tallafota jikin ta ta rungumeta. "Samu abu Hadiza da ruwa a rage mata dumin jikin. Za kiga panadol akan gefen tv a parlor ki dakko .." Umma Hadiza ta mike da sauri. Itama jikin na ta sai rawa ya ke. Kasancewar cutar da zata kwantar da Waheedah ba karama ba ce. Ta ya zasu sanar da ita auren da ke kanta yanzu...? Umma Hadiza ta sauke zuciya kawai Ta dakko maganin ta kai dakin da Waheedah da gwaggo su ke. Ta koma ta debo ruwa da dankwali. Gwaggo haule da kanta ta shiga tsama dankwalin cikin ruwan ta matse sai ta dora akan Waheedah. Ta shiga matsa mata jiki da haka. Har zazzabin ya dan ragu. Sannan ta ballo mata maganin da ruwa ta bata ta sha. Ta ke bacci ya dauke Waheedah. Ganin ta samu bacci. Hakan ya sa suka koma tsakar gidah sukayi zaman curko-curko. Cikin haka sai ga Najan Isubu ta shiga gidan. Bayan ta kuma fannah da Basira ne kawayen Waheedah. "Kin dawo Naja'atu?" "Na dawo gwaggo... Ai badan mun tsaya kan Marka da saadatu ba ma da tuni mun dawo tun dazu." "SubhanAllahi... Fatan dai komai kalau?" Najan Isubu ta girgiza kai kawai. Ta zauna akan wata kujerar tsugunno ta sauke zuciya. "Waheedah bata nan ne?" "Tana ciki. Zazzabi ta ke .Amman ta samu bacci ma yanzu ya tsurga." "Allah sarki Allah yabata lapia." "Aamin.." suka hada baki. "Wai Najaatu wani abunne ya faru a gidan su Markan? Kinsan gaba nayo ai. Tun ranar da naje dinnan tace wallahi babu lefen da za'a karba a gidan... Yau kinga zasu kawo. Daman ranar daurin aure akace. Niyyata yau na samu Waheedah da maganar batun daurin auren nan fa ba kowa bane fyace Zayn . Da shi aka daura " "Wai daman Gwaggo ba ku sanar mata ba? Tabbas nasan kince mata wani yazo kan maganar aure an bashi. Amman batun wanene? Da ranar daurin auren shine ba'a sanar mata ba... To yanzu ya kuke ganin zata fuskanci lamarin? Anya bamu shiga hakkin yarinyar nan ba?" Gwaggo haule ta sauke zuciya kawai. Ta leka ta windown dakin ta hango waheedan nata baccin ta. Ta na mai sauke numfashi ahankali. "Babu wata tarzoma da zata taso insha Allahu a wannan aure. Yadda aka daura lapia. Ubangiji Allah yasa mutuwa ce zata raba su. Duk wata husuma da sharrace sharrace Allah ya kauda shi. Waheedah bata da matsala. Nasan ba zata taba bijirewa zabin da mukai mata ba.... Insha Allahu " "Insha Allahu .. Aamin " "Amin Gwaggo." "Amin..." Dukkanin su suka shiga amsa addu'oin Gwaggo. Kafin Najan Isubu tace, "Ni da Ramman Ukashatu da Hindu ungozoma ne muka karbi haihuwar Deluwa. Don na fito daga gida na kenan zan wuto nan din. Sai ga Ramma da sauri. Shine muka nufi can din baki daya. Allah ya temaka Deluwa ta haifo jarirai mata har biyu, To dai tunda aka shedawa Marka abunda aka samu take kumbure kumbure. Kadaran kadahan. Don na tabbata da ba biki ake ba sai ta saisaye mu da zagi da cin mutunci." "SubhanAllahi.... Albarkar karuwar haihuwar ce bata so ko kuwa?" "Hmm ina kai ki Gwaggo." "Ina sauraron ki " "Yauwa.... Tayi ta cika tana batsewa. Kinsan Allah kin karbar jariran tayi. Tun dai da ta leka ta gano su da idanun ta. Kum baki gansu ba. Yadda kikasan Markan ce tayi kaki ta tofar gwaggo. Kamar su daya. Har bajajjen hancin nan na Marka da bakar fuska.." "Wani abun Markan tayi?" Gwaggo Hadiza ta tambayi Najan Isubu. "Wallahi bata leka dakin Deluwa ta mata barka da arziki ba. Gashi daya jaririyar kwata kwata idanuwan ta a rufe su ke bata bude ba. Numfashin ta wani iri yake fita. Dayar ma bata cika lapiya ba . Amman wallahi ko kadan Marka bata ce kanzil ba. " "SubhanAllahi.. wannan bakar zuciya ta Marka dai Allah ya yaye mata. Tun kuruciya har tsufa ace baka sauya halayen ka ba? To ubangiji Allah ya yaye ma ta yasa ta gane gaskya." "Amin. Amin Gwaggo..." "Amin" "Amin... " Suka shiga amsa addu'oin da Gwaggon ta yi. Najan Isubu ta sake karkacewa kafin ta cigaba da cewa, "Ana cikin haka..... Sai ga shigowar Bashari da wasu abokan sa su biyu. Sallau dan gidan batayya da Harisu dan Malam me gero. Kawai kai tsaye ya dora takarda akan kafar Sa'adatu. Alokacin ta bararraje tana raba abinci. Marka ta shiga tsokanar sa tana ya tsaya su dau hotuna. Zainabu shigowar ta kenan itama gidan ta caba ado cikin wani samfacecen leshi ruwan bula. Iya ganinta sai ya sauya fuska. Ya dage kai zai fita mutane baki daya muka tsaya saroro muna bin su da kallon me ke shirin faruwa. Kai gwaggo kaji tsoron rayuwa. Wato wasu tun a gidan duniya zasu girbi mugayen nufin da suka shuka Gwaggo." "Ina sauraron ki Najaatu.... Zancen ki haka yake. Wasu a duniya Allah ke fara nuna ishara a kansu. Wasu kuma Allah zai musu talala komai nasu yayita tafiya dai dai. Ya yin da rayuwar su babu wani mishkila aciki. Aganin su hakan sunyi nasara basa duba da mugayen abubuwan da suke yi meyakwan su nemi gafara. To wadannan shine zakiji ana wata shari'ar sai a lahira. Suji dadi a duniya su sha wahala a lahira. Allah ya nesanta mu daga aikata mugayen alkaba'i ya kusanta mu da rahamar sa. Allahumma aamin." "Aamin..." Suka amsa ta baki daya. "To na karkare miki zance dai. Takarda da Bashari ya ajiye kowa ya kasa dauka. Basira ce ta dauka ta karanto ko?" Basira da ke gefe ta daga kai. Kafin ta ce, "Eh... Fanna ce ta dakko akan cinyar inna Sa'adatu. Saboda Basharin yace a karanta kafin ya fita. Abunda takardar ta kunsa shine, Assalamu alaikum bayan gaisuwa da kuma fatan alkhairi ga zainabu a gaba. Ni Bashari na saki zainabu saki 3. Allah ya gyara mata halayen da zasu sauya ta ta dawo ta kwarai. Idan ta gyaru Allah ya dube ta ya bata miji nagari amin. Ina karasa karantawa inna saadatu ta yanke jiki ta fadi. Hakama zainabu data zube a k sa tana shure shure kamar sabuwar tabi. Marka kuwa ta sankare a tsaye... Gidah dai ya hautsine... Sai awajen raude nake jin wai zainabun ashe sau 3 . Daniel likita na cire mata ciki. Wai an gaggays masa bai yadda ba. Sai da yaje aka tabbatar masa... " "Innalillahi wa inna ilaihi rajiun..... Ke duniya!!" Gwaggo haule ta fada cikin mamaki da kambama zancen da Basira ta fada "SubhanAllahi.. SubhanAllah." Gwaggo Hadiza ta shiga maimaitawa. Baki daya jikin su yayi sanyi. Cikin haka sai ga shigowar su Haj Aisha abokiyar zaman Haj Hameedah mahaifiyar su Zayn.Da Haj Hameedah Bayan ta kuma su Nadra ne da wasu maza ciki harda Nassem dauke da akwatuna manya manya masu sheki. Irin customized boxes dinnan masu hashtag na #ItWasAlwaysYou:W Da sauran dangin su carpets, Kayan shayi, Gishi da sugar buhu da sauran kayan masarufi ciki harda su indomie da cartons na kayan bacci. Umma Hadiza ta mike da sauri ta shige daki. Ya yinda gwaggo haule ta mayar da hijabi daman tana da alwala ta dubi gabas ta zuba sujjadar godia ga Allah. Hawayen farin ciki daya na bin daya Najan Isubu ta tare da fara'a da wasa da dariya. Ya yin da Basira da fannah suka shimfida tabarmu baki daya suka zazzauna akai. Daga nan aka shiga gayshe gayshen juna. Fannah da Basira sai murna suke suna bin kayan auren Waheedahn da kallo. Kaya ne wanda alkalami yayi kadan wajen zayyano tsaruwar su. Komai na kayan me tsada ne da kuma daraja. "Kaman Hadiza na gani ta tashi ko?" Haj Hameedah ta tambaya tana dariya. "Itace... Kunya take ji." "Kunya kuma? Ai an zama daya. Dabi'ar hausawa ce ai wannan na iyaye su buya ranar karbar kayan auren su. Bayan rana ce ta farin ciki ." "Gaskiya kam." Gwaggo haule ta amsa ta tana dariya. Da kanta ta mike ta kirawo Umma Hadiza da ke cikin daki. Umman ta fito tana sunkuyar da kai. Ta tsugunna suka gaysa baki dayan su. Haj Hameedah sai tsokanar ta take. Fanna da Basira suka shiga dakko kayayyakin da aka tanadar wa zuwan su Haj Hameedah. Dai dai iya karfin su. Da cartons na ruwa da lemuka. Haj Hameedah bata ji dadin kashe kudin da Umma Hadiza tayi ba . Na yin toye toyen kaji da su meat pie. Sun karba da hannu biyu. Sannan aka fara bude akwatuna ana bin kayan da