Sashe 67
Farhatul Qalbi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ta yi reshe a cikin ZUCIYA tah .. Kwarjini da fargabar ki suka hana ni fitowa na nuna miki ni ke kaunar ki... Hakan yasa na fito da dabarar shiga zuciyar ki da sunan Dawood. Tabbas nayi babban lefi agareki..... Kauna ce ta haddasa hakan ba komai ba. My prayers were answered the day that I met you. Tun kallon farkon da nayi miki..." Ya karasa fada yana murza hannunta. Hade da sunkuyawa ya sumbaci tafukan hannayen nata. Dai dai lokacin da ta daga idanu ta sauke akan fuskar sa. Ta ke ta tuno ranar da suka taba haduwa sukayi gware.. Girar sa da suke cike da gashin da suka kusa hadewa saboda yalwar su... Ya sake daga kansa ya sauke akan idanun ta. Ta janye nata da sauri. Ya cigaba da cewa, "Waheedah .. You are a blessing in my life, and I'm so lucky to call you my partner for the rest of our lives. Your smile is my everything. Cikin soyayyar ki babu sirki, na gani kuma na gamsu kuma na tabbatar da ke me kauna tace ta... Ko bakya mun kallon miji kina mun kallon dan uwa. Waheedah, hakika, ki sani, ni bazan taba son wata ya mace wacce bake ba, domin zuciyata bazata taba jindadin zama da wata ya sama dake ba, duk wani jin dadin duniya bai damen ba indai babu ke...." Kalaman sa suka sata dariya. Wasu mazan iyayen karya, Sam ba ta ido.. Ta yamutsa fuska tana mai sake dunkufar da kanta gefe... Kafin tace da shi, "Ni kuma? Ai na dauka ba zaka iya soyayyah da karamar yarinya ba .. Renon ta zakai ko? Domin karamar yarinya ai ba matar da zaa aura bace. Ballantana har ayi rayuwar aure ta re..." Nan da nan Zayn ya harbo jirgin maganar ta. Ranar da kishi yasa yayi barambarama. Da event din bikin sa ne. Alokacin da Dawood abokin sa yace yana kaunar Waheedah da aure. Shine Zayn din yake bashi amsa da wannan karamar yarinyar ze aura? Kasan leben sa ya kamo ya cije. Ya sosa keyar sa yana marairaicewa, "Allah... Ba wai har zuci maganata take ba. Na gaya miki tun kallon farko da nayi miki zuciyata ta kamu da kaunar ki... Kishin kaunar da nake miki ne. Ina burin na mallake ki ki zama a matsayin matata... Sai kuma dawood din ke nuni da yimin shigar sauri. Wallahi kishi ne da kaunar ki suka saka na fadi haka a lokacin. Ba wai har zuci da gaske nake nufi ba. Ki mun afuwa my love.... Ai laifukan da nayi da yawa .." ya karasa fada yana mai saka hannuwan sa akan kunnuwan sa alamun ban hakuri . Kafin ya cigaba da cewa, "Rayuwata fansarki ce, Zuciyata tuni ta rikirkice, Kunnuwana sun ki karban zance, idanuwa na sun so su makance. Duk sanadin ki amshi soyayyar tawa da zaki kokarta ki amince mini, Mulkin ZUCIYAr ki shine aiki na, samun FARIN CIKIN ki jindadi nane, Murmushinki anashuwa ce ga zuciyata, Waheedah... Ni bawa ne ga zuciyar ki....." Agogon da ke daure a wutsiyar hannun ta ta kalla. Ta mike da sauri . Ya tashi shima a tsayen yana jiran ta. "Muje na sauke ki...." Ba ta ce masa komai ba. Ta bude kofar da mukulli ta fice . Tana sauka kasan ta ja ta tsaya. Ganin Maa da tayi itada Nadra . Ta kakaro murmushi ga kunya data ishe ta. Bayan ta kuma Zayn ne. Me su Maa zasu zata. Wayyo! Inama kasa ta tsage ta fada, Haka takeji saboda yadda kunya ta dubibiyeta. Ga haushin Zayn da duk shi ya ballo wannan babban aiki. "Maaa.." Ta fada a kunyace. Hade da tsugunnawa har kasa. "Naam yar gidan Maaa. Har zaki tafi?" "Eh.. Barka da safiya! An tashi lapia?" "Alhamdulillah Waheedah .. Allah yabada sa'ar karatu." "Aamin... Ai yanzu ya zo...." "Wa?" Maa ta tambaya . Hannu Waheedah tasa ta nuna bayanta. Gaba daya a kunyace ta ke. Haj Hameedah tayi murmushi kawai. Kafin tace, "Allah sarki... Allah ya miki albarka." "Amin Maa." "Aunty Waheedah nah. Barka da safiya." "Barkan mu sis Nadra." "Maa Ina kwana?" Ya tsugunna har kasa shi ma. "Alhamdulillah.. Fita zakai?" "Eh... Zaz..zan...zanje office. Na shigo zan gayshe ki ai naga ba kowa a parlorn " "Masha Allah... Ya Ahlam din?" "Alhamdulillah...... " "Okay kaje ka dawo zamuyi magana." "Okay Maa." "Zaka ajiye Waheedah ne. Ko driver ya kai ta?" "No! Zan kai ta" "Alright..." Fita suka yi.. Yana gaba tana biye da shi a baya. Suka karasa wajen motar. Nadra ta nata kallon su ta window tana murmushi. Ya bude mata kofar ta shiga...Sannan ya koma matakin driver ya zauna . Ya tashi motar da addua suka fice daga gidan... Akan hanyar tafiyar su. Go slow suka hadu da shi. Zayn ya saki tsaki kawai. Yana kallon waje. Dandazon yan makarantar su Waheedah ta sakandire a baya sunata wucewa. Ya saki murmushi kafin ya juya ya kalleta. Ya kamo hannunta daya yana mai jan yatsun. "Haduwar da nayi miki ta biyu anan ce... Kun taho ke da kawayen ki ku uku an taso ku daga makaranta.... Ina gano ki bugun ZUCIYA ta ya tsananta Waheedah... "Ya kamo hannun ta ya saka a saitin zuciyar sa ... "My love for you knows no borders, knows no limits, never fades, and will last forever. Insha Allah ... Waheedah, Your happiness means everything to me.I would cross a hundred oceans just to be with you and hold you in my arms. I would climb the tallest mountains just to fall asleep next to you. I would do anything for you. I love you long time ... Waheedah ta sauke zuciya.... Kalaman sa na dada ratsa duk wasu sassa na zuciyar tah. Ba karya ya iya kalamai masu ratsa ZUCIYA da yalwatar FARIN CIKIn tah.. Mamaki ya dada mamaye ta. Ita kanta ta kasa gane wacce irin madaukakiyar kaunar da Zayn ya ke ma ta.. Kauna ce ya ke mata tacacciya marar gauraye. Ita ba yar kowan kowa ba. Gaba da baya yar talakawa ce. Batada wani usuli na manyan gidah. Ba ficacciya ba ce a gurbin karatu yanzu ta sanya kafafu. Ita ba shahararren kyau ba da zaa ce ya mato akan hakan. Duba da shi din da tsatson sa gaba da baya larabawa ne. Amman sai ita? Ita tasan ba dan sharrin soyayyah ba. Ita din ba ajin Zayn ba ce. Da har ko da yaushe sai ya roketa da ta tallafa ta amince da kokon barar soyayyar sa... Wani sashen na zuciyar ta ya hasaso mata Ahlam... Ta runtse idanun ta da sauri tana mai cije lebe. kunyar Ahlam kadai ta isa ta hanata nunawa Zayn kaunar da take masa. Duk kuwa da bata kai tasa ba. Har an basu hannu. Don haka ya gangara gefen titi yayi parking motar. Ya mayar da nutsuwar sa da kallon sa kacokam akan ta. Hawayen dake tsiyaya ahankali. Ya janyo tissue ya goge mata. Ta kalle shi da sauri tana gogewa kafin ta mayar da zaman gilashin idanun nata... Shiru ya biyo baya. Kafin Zayn ya tada motar. Suka koma kan titi suka cigaba da tafiya. Ya kai ta har cikin makarantar. Har kofar twin theatre inda zasuyi lectures... Zata fita taji kofar a rufe. Ta juya ta kalle shi ya daga mata gira yana murmushi. Murya kasa kasa yace, "Kin hakura....? Maganan Dawood? Ki yafemun please.... Da maganar da nayi kan cewa ba ki isa yin aure ba. Kai na bisa wuya ki mun afuwa." "Allah ya yafe mana baki daya..." Ya zare seatbelt dinsa ya matsa . Ya sakar mata peck a gefen kumatun ta. "Wannan turaren na ki kullum cikin tunanin sa na ke.... Waheedah, I am forever thankful to have met you. You are my breath and my light. You are the reason my days are filled with happiness. I love you more than I knew possible. You are my soulmate.You bring me to life! I ve fallen in love many times and always with you! Allah ya miki albarka... Wannan soyayyar ta mu daga Allah ce... DESTINED LOVE.... Tayi murmushin jin dadin kalaman sa da adduar da yayi mata. "Amin.... Nagode" Ya zaro 1500 cikin aljihun sa ya zura mata a jaka. Zatayi magana ya dora yatsan sa akan labban ta "Ayi karatu lapia..." Ta sauka daga cikin motar. Kai tsaye ta shige cikin theatre. Ya dan jima a zaune cikin motar yanata murmushi kamar sauna. Tukun sannan ya tada motar ya wuce ofishin su kai tsaye.. #FARHATAL QALB _INA MASOYA KUMA MA'ABOTA KAMSHI MA SU KAUNAR KAMSASAWA A KODA YAUSHE? DOMIN KAMSHI RAHAMA NE.._ _TO KU MATSO, DOMIN WANNAN KARON MA ZAFAFA BIYAR SUN ZO MU KU DA TALLAN MASARAUTAR KAMSHI NA KAMFANIN TURAREN *YERWA INCENSE AND MORE*_ _A *YERWA INCENSE AND MORE* ZA KU SAMU TURARUKAN WUTA NA *GIDAH, NA KAYA, NA TSUGUNNO* BA A NAN KADAI SUKA TSAYA BA. AKWAI *KHUMRAHS* MASU KAMSHIN LARABAWA DANA FRUITS KAI DAMA KAMSHIN TURAWA. AKWAI KHUMRAHS TA MATAN AURE DA TA YAMMATA_ _SANNAN SU NA DA *TURAREN WANKA DANA SHAFAWA BAYAN AN KAMMALA WANKA.* BA ANAN TURARUKAN NA SU SUKA TSAYA BA. AKWAI *KULACCAM* MAI MATUKAR KAMSHI DA SANYAYA ZUCIYA, SANNAN SU NA DA *MADARORIN TURARUKA NA JIKI DA NA KAYA*_ _AKWAI TURAREN *AL'AJABU NA TSUGUNNO DA KHUMRAH* DIN SA_ _SANNAN SU NA DA *TURAREN GASHI NA CREAM DA KUMA SPRAY DIN SA NA FESAWA*_ _BA ANAN SUKA TSAYA BA. SU NA DA *TURAREN MOPPING, DA NA BANDAKI AKWAI NA RUWAN WANKI DA NA FESAWA A DRAWER KO AKWATI*_ _AKWAI KAYAN GYARARRAKI NA FATA. KUJERAR TSUGUNNO, KASAKE NA WUTA, COAL IGNITER TA KUNNA GARWASHI, ELECTRIC BURNERS DA ENGLISH COAL_ _AKWAI LAFFAYAS DA SAURAN TURARUKA NA KAMSHI KALA KALA_ _SU NA BADA KAYAYYAKIN SU AKAN FARASHIN SARI KO SAYA AKAN DAYA DAYA. SANNAN SUNA TURA KAYAYYAKIN SU KO'INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE. KAYAN SU YAN CHADI NE DA SUDAN DA KUMA YERWA WATO MAIDUGURI._ _KYAU, INGANCI DA RAHUSA SAI KAYAYYAKIN KAMFAMIN YERWA INCENSE AND MORE. SAI KUN GWADA ZAKU BAMU LABARI_ _NAMBAR TARHON SU DA ZAA KIRA KO MUSU MAGANA TA WHATSAPP ITACE: 08095215215_ _INSTAGRAM HANDLE DIN SU: @yerwaincense_and_more_ _YERWA INCENSE AND MORE: A NUMBER ONE STOP SHOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS AND MORE_ *_ZAFAFA BIYAR din samari