← Book details Farhatul Qalbi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 82

Sashe 42

Farhatul Qalbi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tana gaba sanye da kayan bacci. Yayinda Waheedah ke biye da ita a baya. Tamkar itace matar gidan.ita kuma Ahlam din a matsayin yar aiki. Ahlam na karasa nuna mata abubuwan. Waheedah nan da nan ta hau yin komai ba sanya. "Bari na dan kwanta.... Kafin ki karasa " "Toh" Har zata fita Waheedah ta dan kirata da sauri. "Sis...." "Naam..." "Ca nayi a ina zanyi gashin kajin? Da ke awajen Maa naga tanayi a irin wancen abun gashin naki..." "Okay kiyi dashi .." "Tam..." Karfin ac din dake busawa kitchen din iska Ahlam ta karawa Waheedah. Yayinda ta kuma ta fi ce ta haye sama dan yin bacci. Kamar yadda ta fada. Waheedah ta shiga aiki ka'in da na'in. Ya yin da Zayn ke zaune a parlorn shi kadai. Ya janyo wayar sa yana duba wasu constructions site blog da yake bi a LinkedIn. ******* Ta dau tsawon lokaci tana aiki. Kafin ta karasa komai. Ta hade dukkanin abubuwan da ta bata ta wanke su tas Zayn da shigowar sa kenan gidan bayan yaje sallah ya dawo. Kofofin hancin sa suka shiga busa masa kamshin girkunan dake fita daga kitchen. Ya lumshe idanu ya bude ahankali. Sakamakon dadin kamshin da ke bibiyar hancin sa. Ruwa ta tara hannunta a wajen sink din kitchen. Ta wanke fuskar ta. Har idanun ta sun sake fitowa. Ba karya tasha aiki. Ta fita parlorn tana kalle kalle . Idanunta suka sauka akan na Zayn dake tokare a bango "Na.... Na gama...." "Okay... Bata tashi ba ne?" "Bansani ba wallahi ..... " Ta bashi amsa cikin karshen gaskiyar ta. "Okay bari na kirata...." Wayar sace ta fara kara. Ya dauka ya kara a kunnen sa. "Eh .. yanzu take cewa ta gama .. Tana sama.. ok bata dauka? Wai tana bacci ne... Alright. Sai kun kara so " Yana gama amsa kiran ya mayar da wayar aljihun sa. Ya haye saman yana mai kiran sunan ta da karfi. "Ahlam... Ahlam...." Tamkar mushe ya hangota ta bararraje akan gado tana bacci. Ya saka hannun sa daya yana tashin ta ahankali "Ahlam... Ahlam...." "Um...." "Tashi mana... Har anyi sallah. Ga su Maa nan fa ..." "Ka kyake ni ..." Ta amsa shi cikin bacci "Tashi mana..." "Oh please...." "Get up please .. Yarinya tun dazu take aiki sai yanzu ta gama. Ko kunya bakyaji kinzo kinata bacci..." "Kai... Mts..." "Tashi ...." Ya shiga janye kanta daga kan pillow yana tashin ta da karfi. Ta shiga bude idanunta ahankali har ta ware su akan sa. Dai dai lokacin da motar su Maa tayi horn.. Baba Mai gadi na tura gate din...Ya bude musu. Suka shiga da motar ciki. "Kingani ko .. ? abunda nake gaya miki. To gasunan ma sun karaso..." Mikewa tayi da sauri ta fada bandaki. Yayinda ya grigiza kai kawai ya koma kasa. Ba Waheedah, Amman yaji motsin ruwa a bandakin kasa. Wucewa yayi kan kujera ya zauna yana mai sakin gwauron numfashi mai tattare da damuwa marar misaltuwa.... _INA MASOYA KUMA MA'ABOTA KAMSHI MA SU KAUNAR KAMSASAWA A KODA YAUSHE? DOMIN KAMSHI RAHAMA NE.._ _TO KU MATSO, DOMIN WANNAN KARON MA ZAFAFA BIYAR SUN ZO MU KU DA TALLAN MASARAUTAR KAMSHI NA KAMFANIN TURAREN *YERWA INCENSE AND MORE*_ _A *YERWA INCENSE AND MORE* ZA KU SAMU TURARUKAN WUTA NA *GIDAH, NA KAYA, NA TSUGUNNO* BA A NAN KADAI SUKA TSAYA BA. AKWAI *KHUMRAHS* MASU KAMSHIN LARABAWA DANA FRUITS KAI DAMA KAMSHIN TURAWA. AKWAI KHUMRAHS TA MATAN AURE DA TA YAMMATA_ _SANNAN SU NA DA *TURAREN WANKA DANA SHAFAWA BAYAN AN KAMMALA WANKA.* BA ANAN TURARUKAN NA SU SUKA TSAYA BA. AKWAI *KULACCAM* MAI MATUKAR KAMSHI DA SANYAYA ZUCIYA, SANNAN SU NA DA *MADARORIN TURARUKA NA JIKI DA NA KAYA*_ _AKWAI TURAREN *AL'AJABU NA TSUGUNNO DA KHUMRAH* DIN SA_ _SANNAN SU NA DA *TURAREN GASHI NA CREAM DA KUMA SPRAY DIN SA NA FESAWA*_ _BA ANAN SUKA TSAYA BA. SU NA DA *TURAREN MOPPING, DA NA BANDAKI AKWAI NA RUWAN WANKI DA NA FESAWA A DRAWER KO AKWATI*_ _AKWAI KAYAN GYARARRAKI NA FATA. KUJERAR TSUGUNNO, KASAKE NA WUTA, COAL IGNITER TA KUNNA GARWASHI, ELECTRIC BURNERS DA ENGLISH COAL_ _AKWAI LAFFAYAS DA SAURAN TURARUKA NA KAMSHI KALA KALA_ _SU NA BADA KAYAYYAKIN SU AKAN FARASHIN SARI KO SAYA AKAN DAYA DAYA. SANNAN SUNA TURA KAYAYYAKIN SU KO'INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE. KAYAN SU YAN CHADI NE DA SUDAN DA KUMA YERWA WATO MAIDUGURI._ _KYAU, INGANCI DA RAHUSA SAI KAYAYYAKIN KAMFAMIN YERWA INCENSE AND MORE. SAI KUN GWADA ZAKU BAMU LABARI_ _NAMBAR TARHON SU DA ZAA KIRA KO MUSU MAGANA TA WHATSAPP ITACE: 08095215215_ _INSTAGRAM HANDLE DIN SU: @yerwaincense_and_more_ _YERWA INCENSE AND MORE: A NUMBER ONE STOP SHOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS AND MORE_ *_ZAFAFA BIYAR din samari ne a rayuwar INAYAH,kowanne a cikinsu akwai wani murdadden Al'amari da ya shata layi tsakaninsa da ita,wawakeken sirri wanda a koda yaushe take kiransa da SANADIN LABARINA_* *_Amma babban abun mamakin a koda yaushe shine,ita dai tasan cewa BABU SO tsakaninsu MEYA KAWO SHI?_* *_Duk da haka tana tunanin yun qundun bala ta fitar da FARHATUL K'ALB a cikin ZAFAFA BIYAR din samarinta,duk da batason su zame mata GURBIN IDO wanda har kullum ba ido bane_* *YA KUKAJI SALON MASU KARATU?* *YADDA SALON YA BAMBANTA DAKO YAUSHE HAKA LABARAN SUKA BAMBANTA DA DUKKA LABARANMU NA BAYA* INAYA(riba biyu)___mamughee SANADIN LABARINA___Rano BABU SO___Billynabdul FARHATUL K'ALB___Miss xoxo GURBIN IDO____Huguma *ZAKI YARDA AYI TAFIYAR NAN BABU KE MADAM?* *_GARZAYA KI BIYA NAKI KUDIN KAN FARASHI KAMAR HAKA_* Biyar:::1k Hudu:::700 Uku::::500 Biyu::::400 Daya:::300 *_zaki saka kudin ta wannan account number din_* HAFSAT UMAR KABIR 2270637070 Zenith bank *Saiku tura shaidar biya zuwa ga* 07040727902 *IDAN KUMA KATIN WAYA NE ZAKU TURA TA NAN TARE DA SHAIDAR BIYAR* 09134848107 *_THANKS FOR THE CONTINUED PATRONAGE_* [11/23, 9:02 PM] Mummyn Yara: _*FARHATAL-QALB*_ _(FARIN CIKIN ZUCIYAH)_ _NA_ _NANA HAFSATU_ _(MX)_ _AREWABOOKS:MISSXOXO_ _WATTPAD: MISSXOXO00_ _ZAFAFA BIYAR PAID NOVELS_ _PG:46_ _WANNAN LITTAFI DA MA SAURAN NA *ZAFAFA* NA *KUDI* NE. DAN ALLAH KI/KA BIYA KUDI KI/KA MALLAKI NA KI. DON GUDUN SHIGA HAKKOKIN MASU RUBUTAWAR DA MA WADANDA SUKA CIRE KUDI SUKA SAYA..._ *Knocking* kofar suka fara yi. Kafin kararrawa (door bell) ta fara kara. Ya tashi ya nufi wajen kofar. Yana mai waiwayon kafar bene ko Ahlam zata sakko. Shiru shiru ba alamun ta. Kawai yasa hannu ya bude kofar. Suka shigo ciki. Haj Hameedah da Haj Aisha sai Ummimi kakar su. Da Umma Hadiza data shiga a karshe. "Ahh mazan fama....." Ummimi kakar su ta fada tana dashare hakoranta. Ya saka hannu ya sosa keyar sa yana murmushi. "Sannun ku da zuwa...." Ya fada cikin girmamawa. Wuce shi sukayi. Suka zazzauna akan kujeru. Ya yinda Umma Hadiza ta nemi waje daga kasa ta zauna. "Ah haba Hadiza. Dan Allah tashi ki zauna akan kujera." "Tashi mana ..." "Tashi 'yar nan ki zauna....." Haj Hameedah...Haj Aisha da Ummimi suka shiga bai wa Umma Hadiza umarni kan ta tashi daga zaunen da take ta koma kan kujera. Umma Hadizan ta zauna daga gefen wata kujera kanta a k Ya yin da Zayn ya tsugunna ya shiga gaishe su daya bayan daya cikin girmamawa da mutuntawa. "Ina Ahlam dinne....?" "Ta... Tana sama yanzu zata sakko." Waheedah ta futo daga cikin dakin da tayi sallah. Ta tsugunna ta gayshe su. Umma Hadiza sai murmushi take "Sannu da kokari Waheedah... Allah ya saka da alkhairi." "Amin Maa.." Sun dan yi mintuna da zama. Shiru ba Ahlam. Sai can daga baya ta sakko daga ita sai dogon hijabi zuwa gwiwa. Kayan baccin ta na dazu ta mayar . Mamakin hakan ya mamaye Zayn. Har ya kasa boye halin da yake ciki a fuskar sa. Zama tayi akan kujera tanata murmushi "Ina wunin ku??. Ummimi na, Maa da Aunty Ai..." Suka amsa. Ya yinda ta juya ta kalli Umma Hadiza. "Ina wuni?" "Lapia kalau amarya." Can dai sunata zaune jugum. Waheedah ta miqe ta shiga kitchen din. Ta shiga dakko trays da plates da cokula da serving spoons. Ta koma ta dakko warmers na abincin ta ajiye musu akan dinning dake gefen parlorn. Ta sake bude freezer ta debo musu ruwa da lemo ta ajiye. "Ahh .. Har na manta ma... Sannu sis." Waheedah ta fada. Haj Hameedah na hankalce da su. Ta dubi Zayn da ke gefe, Kan sa akan tv. Ya yin da Ahlam ke danne danne a wayarta. "Maa ga abincin can kar ya huce." "Toh Waheedah sannu da aiki kinji?" "Yauwa..." Miqewa sukayi suka nufi dinning din. Ita dai Umma Hadiza bata tashi ba. "Zo mana Hadiza.." "Hajia nan din ma yayi .." ta amsa ta cikin ladabi. Kan dinning table suka nufa. Suka ja kujeru suka zazzauna. Ahlam tayi serving dukkanin su abincin. "Waheedah zo ki zuba... Ki zubawa Umman ku ma" "Tohm." Karasawa tayi dinning din. Ta janyo plate babba ta zuba musu abincin ita da Umman ta. "Ki kara muku mana..." "Ya ishe mu haka...." Ta koma can inda Umman tasu ke a zaune ta ajiye plate din abincin a gaban Umman . "Sakko muci Umma..." "Tohm Waheedah..." Kasan carpet suka zauna. Abincin na tsakiyar su. Su kayi basmala suka fara ci. Zayn na kan kujera ya kurawa tv kallo. "Ah ina naka abincin? Zuba ma sa yaci Ahlam." "Na koshi Ummimi." "Dan Allah ka karba ka ci ka ji?" Zai sake cewa wani abun . Haj Hameedah ta masa kallon kar ya yi haka. Ya dan kakaro yake yace, "Toh.." "Yauwa... Sannu Ahlam da aiki. Abinci yayi dadi." Ummimi ta fada tana mai sake yanko loma ta saka a bakinta. Ahlam din ta danyi yake. kafin tace, "Ai bama ni nayi ba Ummimi." "Ai ho to... Na wajen sayarda abinci ne?" "Ah'ah Waheedah ce ta yi komai..." Ta karasa fada hadi da sa ka hannu ta nuna Waheedah da yatsanta. "Ah masha Allahu... Lalle tayi kokari." "Sosai ma. " Cewar Hajia Aisha. Ita dai Haj Hameedah murmushi kawai ta ke. Ahlam ta zuba abincin a plate ta kai gaban Zayn. Yana daga zaune ta tsaya akan sa kerere. Da plate din abincin tamkar zata dora akan sa "Gashi...." Hannunta daya na kan wayarta . Dayan kuma tana miqa masa abincin saura kadan ya bare. Ya sa ka hannu ya karbi abincin ya ajiye a gefe. Kallon abincin ya tsaya yi. Gashi dai komai tsaf
Chapter 42 · 0% Book details