← Book details Farhatul Qalbi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 82

Sashe 37

Farhatul Qalbi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sauran yan kayayyakin nasu Waheedah ta mayar dakin su Yaya Kamal. Kudin kuma Najan ta riqe su a hannunta bayan ta basu ajiya sun ki. Kan zata kaiwa Umma Hadizan da kanta. Haka rayuwar ta cigaba da garawa. Kwanakin Waheedah 3 agidan Najan Isubu. Da asubah take komawa wajen su Yaya Kamal . Kudin kayan da aka sayar. Umma Hadizan ta baiwa Najan Isubun dubu daya dakyar ta karba Sauran kudin kuma ta barwa su waheedan a hannun su. Saboda karin kumallo da sauran abubuwan dazasu bukaci kudi na yau da kullum. Sati daya kuwa da tashin Waheedah. Wata mata ta tare adakin. Bazawara ce dake sana'ar abinci da zobo. Najan isubu da kanta bisa jagorancin gwaggo haule suka samu Marka da maganar karbar Waheedah . Marka tace batasan zance ba. Ta gwammace waheedan tayita karakainan neman matsugunin kwana amman bata amince tafiyar ta ba baki daya. Bayan ba wani abun take mata ba. Hassada ce zalla take yi. Don kada waheedan ta je inda zata huta taci cima mai dadi... Hakan ya sanya su Umma Hadiza suka dakata da zancen. Har yazamto ma Umma Hadizan ta dakatar da zuwan Waheedah gidan na su the Adams family saboda gudun kar Moha yayi kuka. Yayinda rana ke zama yammaci. Yammaci ta zama dare. Dare ya waye. Lalle Allah buwayi ne gagara misali. Ranar wata sanyayyar juma'a da asubah. Bayan Najib ya tafi masallaci. Waheedah Kuma na tsakure a daki wajen Zainab suna kwance. Haka kawai waheedan tun kafin safiya ta nemi bacci a idanunta ta rasa. Yayinda gabanta keta faduwa. Tana idar da salla tadauki kwano don siyo musu yar tsala da kunu. Najib ya dawo daga sallah. Ganin Yayan nasu har yanzu a kwance yake. Ga lokaci nata tafiya. Duk kuwa da bashida lapia shi ya sama bai tashe shi sunje masallaci ba saboda jikin nasa ba kwari gwara yayi agidah. Hakan ya sa har ya kwanta akan katifar sa ya mike da sauri. Ya shiga tashin dan uwan nasa. "Yaya.... An yi asubah fa. Ban tashe ka ba saboda naga baka jin dadi ne...." Ya shiga tashin sa shiru. Yasake tattaba kafafun sa yana kiran dan uwan na sa. "Yaya.... Ka tashi kayi sallah...."Nan ma shiru ba amsa. Hakan yayi dai dai da shigar Waheedah dakin. Ta cire hijabin ta ta a jiye a kyauran kofa. "Bacci yake har yanzu?" "Eh...." Najib ya amsata a sanyaye. Hannu tasa ta dago nasa da sauri hannun ya koma baya luuuu ya fadi. "Yaya Kamal.... Yaya... Yayan mu." Ta shiga tashin sa sosai tana kallon Najib. "Daman haka yakan yi ..?" "Be taba wannan nauyin baccin ba..." Ta saka kunnenta a kofar fuskar sa wai ko zata ji numfashin sa. Nan ma shiru. Da sauki jikinta na rawa ta fita . Malam nalado ne a tsaye yana gyara rigar jikin sa. "Baba." "Naam Waheedah..." "Baba zo kaga Yaya be tashi ba." Da sauri ya bi bayanta suka shiga dakin. Ya tattaba Kamal din. Ya mirginar da fuskar sa. Ya taba jijiyar wuyan sa da ta hannayen sa. Doguwar ajiyar zuciya ya sauke kansa a kasa. "Baba menene?" Bai ce komai ba. Ya janyo zanin gadon dake jikin katifar ya rufe Kamal din baki dayan sa. Ya mike ya fuce zuwa kofar dakin Marka. Waheedah ta bishi. Yayinda gabanta ke tsananta bugawa da sauri da sauri. "Ya akai me sunan malam?" "Marka.... Allah ya yiwa..." "Menene . Yayiwa me? Iyye?" Ta fada yayinda zaninta ke neman kuncewa. "Kamalu ne Marka.... Allah ya masa rasuwa...." ._INA MASOYA KUMA MA'ABOTA KAMSHI MA SU KAUNAR KAMSASAWA A KODA YAUSHE? DOMIN KAMSHI RAHAMA NE.._ _TO KU MATSO, DOMIN WANNAN KARON MA ZAFAFA BIYAR SUN ZO MU KU DA TALLAN MASARAUTAR KAMSHI NA KAMFANIN TURAREN *YERWA INCENSE AND MORE*_ _A *YERWA INCENSE AND MORE* ZA KU SAMU TURARUKAN WUTA NA *GIDAH, NA KAYA, NA TSUGUNNO* BA A NAN KADAI SUKA TSAYA BA. AKWAI *KHUMRAHS* MASU KAMSHIN LARABAWA DANA FRUITS KAI DAMA KAMSHIN TURAWA. AKWAI KHUMRAHS TA MATAN AURE DA TA YAMMATA_ _SANNAN SU NA DA *TURAREN WANKA DANA SHAFAWA BAYAN AN KAMMALA WANKA.* BA ANAN TURARUKAN NA SU SUKA TSAYA BA. AKWAI *KULACCAM* MAI MATUKAR KAMSHI DA SANYAYA ZUCIYA, SANNAN SU NA DA *MADARORIN TURARUKA NA JIKI DA NA KAYA*_ _AKWAI TURAREN *AL'AJABU NA TSUGUNNO DA KHUMRAH* DIN SA_ _SANNAN SU NA DA *TURAREN GASHI NA CREAM DA KUMA SPRAY DIN SA NA FESAWA*_ _BA ANAN SUKA TSAYA BA. SU NA DA *TURAREN MOPPING, DA NA BANDAKI AKWAI NA RUWAN WANKI DA NA FESAWA A DRAWER KO AKWATI*_ _AKWAI KAYAN GYARARRAKI NA FATA. KUJERAR TSUGUNNO, KASAKE NA WUTA, COAL IGNITER TA KUNNA GARWASHI, ELECTRIC BURNERS DA ENGLISH COAL_ _AKWAI LAFFAYAS DA SAURAN TURARUKA NA KAMSHI KALA KALA_ _SU NA BADA KAYAYYAKIN SU AKAN FARASHIN SARI KO SAYA AKAN DAYA DAYA. SANNAN SUNA TURA KAYAYYAKIN SU KO'INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE. KAYAN SU YAN CHADI NE DA SUDAN DA KUMA YERWA WATO MAIDUGURI._ _KYAU, INGANCI DA RAHUSA SAI KAYAYYAKIN KAMFAMIN YERWA INCENSE AND MORE. SAI KUN GWADA ZAKU BAMU LABARI_ _NAMBAR TARHON SU DA ZAA KIRA KO MUSU MAGANA TA WHATSAPP ITACE: 08095215215_ _INSTAGRAM HANDLE DIN SU: @yerwaincense_and_more_ _YERWA INCENSE AND MORE: A NUMBER ONE STOP SHOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS AND MORE_ *_ZAFAFA BIYAR din samari ne a rayuwar INAYAH,kowanne a cikinsu akwai wani murdadden Al'amari da ya shata layi tsakaninsa da ita,wawakeken sirri wanda a koda yaushe take kiransa da SANADIN LABARINA_* *_Amma babban abun mamakin a koda yaushe shine,ita dai tasan cewa BABU SO tsakaninsu MEYA KAWO SHI?_* *_Duk da haka tana tunanin yun qundun bala ta fitar da FARHATUL K'ALB a cikin ZAFAFA BIYAR din samarinta,duk da batason su zame mata GURBIN IDO wanda har kullum ba ido bane_* *YA KUKAJI SALON MASU KARATU?* *YADDA SALON YA BAMBANTA DAKO YAUSHE HAKA LABARAN SUKA BAMBANTA DA DUKKA LABARANMU NA BAYA* INAYA(riba biyu)___mamughee SANADIN LABARINA___Rano BABU SO___Billynabdul FARHATUL K'ALB___Miss xoxo GURBIN IDO____Huguma *ZAKI YARDA AYI TAFIYAR NAN BABU KE MADAM?* *_GARZAYA KI BIYA NAKI KUDIN KAN FARASHI KAMAR HAKA_* Biyar:::1k Hudu:::700 Uku::::500 Biyu::::400 Daya:::300 *_zaki saka kudin ta wannan account number din_* HAFSAT UMAR KABIR 2270637070 Zenith bank *Saiku tura shaidar biya zuwa ga* 07040727902 *IDAN KUMA KATIN WAYA NE ZAKU TURA TA NAN TARE DA SHAIDAR BIYAR* 09134848107 *_THANKS FOR THE CONTINUED PATRONAGE_* [11/23, 9:01 PM] Mummyn Yara: _*FARHATAL-QALB*_ _(FARIN CIKIN ZUCIYAH)_ _NA_ _NANA HAFSATU_ _(MX)_ _AREWABOOKS:MISSXOXO_ _WATTPAD: MISSXOXO00_ _ZAFAFA BIYAR PAID NOVELS_ _PG:42_ _WANNAN LITTAFI DA MA SAURAN NA *ZAFAFA* NA *KUDI* NE. DAN ALLAH KI/KA BIYA KUDI KI/KA MALLAKI NA KI. DON GUDUN SHIGA HAKKOKIN MASU RUBUTAWAR DA MA WADANDA SUKA CIRE KUDI SUKA SAYA..._ *Tana* jiyo sanda mahaifin su ke sanar da rasuwar Yayan na su. Jijiyoyin jikinta suka saki. Ta nemi kwari ta rasa. Ta zube zaman dabaro. Hannuwanta dafe da bakinta. Wasu hawaye masu dumi suka shiga kwaranya daga fuskarta. "Innalillahi wa inna ilaihi rajiun..... Innalillahi wa inna ilaihi rajiun... Innalillahi wa inna ilaihi rajiun.... Shikenan? Shikenan Yaya ka tafi ka bar mu? Yaya shikenan babu kai? Wayyo Allah na.... Ummanmu. Yayan mu ya rasu. Ya rasu Umma... Na shiga uku..." Inna Sa'adatu ta leka fuskarta cikin dakin don ganewa idanunta "Toh.... Allah ya jikan rai... Allahu Akbar." Ta furta tana girgiza kai. Marka ta koma ta zauna tana daga kai. "Allah sa karshen wahalar kenan ... Yarannan yadda ake jelar asibiti da su. Gwara ai da Allah ya karbi ran sa. Uwar ta huta itama...." Marka ta fada gatsal ba tare data auna rashin hankalin zancen na ta ba. Sosai Najib ke kuka... Yanata girgiza Yayan nasu. "Yaya... Ka tashi Yaya... Baka rasu ba Yaya... Dan Allah ka tashi." Kuka yake sosai wiwiwi. Jijiyoyin goshin sa sun fito radau. Yanata birgima yana kuka. Yayin da Waheedah ma ke kukan a kofar dakin Marka . "Bar birgima yar nan...." Cewar Deluwa matar da ke haya. Malam Nalado ya fice yanata sauri ya gayawa liman. Liman din ya sanar da rasuwar da lokacin da za'ayi masa sallah a kai shi madakata. Najan Isubu na jiyowa ta isa gidan tanata salati da sallallami. Tayi kuka sosai tana girgiza kanta. "Marka ... Yanzu kin kyauta da abunda kikayi? Gashi nan kin raba da da mahaifiyar sa. Bai rasu agabanta. Sati wajen nawa? Basa ganin juna. Sai dai taga gawar ta sa. ? Innalillahi wa inna ilaihi rajiun... Kamalu Allah ya jikan ka da rahama. Annabi yasan da zuwan ka. Allah ya shayar da kai ruwan alkausara kamalu... Bakada wani hali na daban fyace na kirki da girmama na gaba da kai... Allah ya dubi biyayyar ka ya saukaka maka tambayar kabari kamalu .. Allah ya kyautata makonci ya jikan dukkanin wadanda suka rigamu da gidan gaskiya. Muma idan tamu tazo Allah yasa mu cika da Imani .. wannan jinya da ka sha kamalu Allah yasa kankarar zunubai ce . ...Aamin" Sai data kai karashe. Marka ta ja Wani dogon tsaki. Ta tashi daga zaunen da take a daki ta fito har gaban Najan Isubu. Tamkar zata tsone mata idanu. Haka ta daga yatsa tana mai mata nuni. Cikin dakushewar murya da tsantsar jin haushi ta shiga ce wa, "Kinga Naja... Kisan ire iren maganganun da zasu dinga fitowa daga bakin ki. Da girman Allah ko Ruwaida kinga dai itace kusan tsarata ko? To ko ita ki tambayeta tayi kadan a gayan magana .. Zaki ce na raba su da Hadiza waye waye .. Kina so ki nuna ni na kashe shi ne ko me? Bayan wannan cutar tasu ance tun suna 'kankana take kashe su. Bayan shi din da yayi dogon zango? ..... Yo wannan da rayuwar sa ai gwara da yake a ma .." "Dan Allah marka kar ki karasa......" "Yo ai kece naga kina neman doramun lefi bayan dama can nakasassu ne. Da samun su gwara r..." "Ko wanne rayayye fa matacce ne watan watarana Marka . Lapia ko akasinta bashi ke sa Allah ya karbi rai ba. Rigar gado ce mutuwa. Wanda kowanne dan adam seya sakata ..Kinga Waheedah an sanarwa Umman ku ne?" Waheedah dake tsiyayar da hawaye bata samu damar magana ba. Sai jujjuya kai da take kawai . Yayin da hawaye keta kwaranya a kyakkyawar fuskar ta . Kawai tunano zaman shakuwar su take da Yayan nasu. Yayan su mai fara'a da mutunci. Sam bashida girman kai.
Chapter 37 · 0% Book details