Sashe 26
Farhatul Qalbi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
taba wanda ba muharrami ba. Ka wayar mata kai. Sannu ahankali zata dena...." Ya sake sauke zuciya a karo na takwas kafin yace, "Dole ne auren dangin nan ne Maa? " "Dole ne. Kana gani ai ba akan ka farau ba. Junan ku kuke aure, Mutum yanaso ko bayaso haka ze hakura dole yayi. Haka kuma ba kai kadai za'a aurar a wannan karon ba kai da wasu daga cikin yan uwa zaa aurar. Na menene zaka janyowa kan ka ka janyo mun? Salon ace ni na hana ka saboda ban taba aurarwa ba sai akan ka. ..." "Maa ni fa bansan yadda ake kaunar mace ko so ba. Bantaba ba wallahi " "To ka fara akan Ahlam... Sai Allah yasa albarka a abun " "Maa please...." "Tashi ka fita Zayn. Zan saba maka idan har ka sake tarata da makamancin zance irin wannan wallahi, Kaji na gaya maka " Dai dai sanda Waheedah suka shiga itada Moha. Nadra na biye da su. "Tashi ka fita Zayn " ta fada a tsawance Da sauri ya mike ya fice. Waheedah tabi bayan sa da kallo. Mamakin ganin dazu sunata hira yanzu kuma ga akasin haka . Ta cigaba da rubuce rubucen da take a notepad. Su kuma suka haye sama. Dakin Nadra suka shiga. Dakinta mai dauke da kayan gado da furnitures komai purple and white. Suka zauna akan wasu sofas. Moha yanata tsalle tsalle. Nadra can ta nisa tace, "Auren su zaai kinsan.!" "Oh haba?" "Allah... Shi da Ahlam." "Allah sarki Allah yabasu zaman lapia." "Amin... Kinsan mu bama auren bare sai iya cikin dangin mu kawai. Ko kanaso ko baka so ." "Masha Allah... Allah ya kara muku zumunci " "Amin. Nima an mun miji . First cousin dina ne .. Dan yayar Abiey dinmu yana Istanbul " "Masha Allah. ALLAH sa albarka. Amin" "Amin .. Ahlam ita yar yayan Abiey dinmu ce." "Kuna kama ma ...." "Tohm shi yayan namu bayaso. Kuma shine auren farko da zaa fara na dan dakin mu. Kuma ba yadda zeyi sede ya hakura. " "Tab... Allah sarki ." "Hmm! Kede bari wallahi. Allah yabamu saa duka kawai " "Amin.." "Yauwa na manta..." Ta bude drawer dinta ta dakko wani material ja daya sha dinkin gown da dankwali harda mayafin sa baki sabo ta ajiye wa Waheedah akan cinyar ta. Ta sake ciro laffaya sabuwa pink me torches black ta ajiye mata " "Na menene wannan?" "Kayan fitar biki ne .. Na Zayn and Ahlam." Waheedah ta girgiza kai kawai. Ta kasa ma magana. "Meye size din takalman ki?" Waheedah ta sauka daga kan kujerar ta zube akan gwiwoyin ta. Hawaye daya na bin daya na farin ciki. "Na rasa bakin godia..." "Kar ma ki soma sis." "Nagode Ya Nadra.. Allah ya saka miki da mafificin alkhairn sa. Ya biya miki dukkanin bukatin ki na duniya da lahira " "Bar kuka please. " "Ahhh Waheedah ." Moha ya rungume ta shima zeyi kukan "Ga yaron ki nan zeyi kukan shima.dan Allah ki dena wannan kokekoken meye haka? Ai an zama daya " Waheedah kuwa sai da ta tabbatar ta karasa godia. Ta sauka kasa wajen Maa nanma ta shiga nuna mata tana godia. Ita dai Maa murmushi kawai take. Ta dakko wani material da ba a dinke yake ba wanda tayiwa dukkanin ma'aikatan da ke karkashinta su. Ta hada da debo kudi yan dari biyar biyar guda 5 ta mika mata wai na dinki. Nanma Waheedah ta cigaba da godia. Again Nadra ta sake bata takalmi sabo dal. Ranar haka Waheedah ta wuni agidan nan tana farin ciki . Mai kunshi datazo yi har ita akayiwa. Nadra kuma ta wanke mata kanta ta mata stretching ya sake tsayi. Sai yamma lis ta koma gidah da tarin kayan. Umma Hadiza ta Yaba sosai ita dasu Kamal. Har kwanciyar bacci Waheedah bata dena godia ba. Tayi sallar nafila rakaa biyu tanata shararawa su Nadra godia. Da fatan dacewa a rayuwa. Kamar ko da yaushe a al'adun bukukuwan bikin su. Daurin aure ne yake zuwa farko. Bayan sunje sunyi gwaje gwaje komai nasu kalau zasu iya auren junan su Ranar alhamis akayi bridal tea party a wani eatery dake kan nassarawa GRA. Iya kawaye mata kawai Ranar jumu'ah bayan an sakko daga masallaci. Dubban mutane. All the who is who. Suka hallara wajen daurin auren amare da angwaye Ango Zayn Adams Nasseer da amaryar sa Ahlam Nouh Nasser. Sai amarya da ango na biyu wato: Jannat Adams Nasser da angonta Zaid Nouruh Nasser. 'Yayan Yaya da kanne. Biyu daga yaran professor Adams. Saia daya a yayan su wato Nouh Nasser. Sai daya ta kani gare su wato Nouruh. Aka daura auren a babban masallaci. Akan sadaki mafi daraja. Daga nan akayi reception a farfajiyar dakin taro da ke gidan na farfesa Adams. Anci an sha anyi hani'an. An kuma yi addoin zaman lapia ga amare da kuma angwayen su.... *_ZAFAFA BIYAR din samari ne a rayuwar INAYAH,kowanne a cikinsu akwai wani murdadden Al'amari da ya shata layi tsakaninsa da ita,wawakeken sirri wanda a koda yaushe take kiransa da SANADIN LABARINA_* *_Amma babban abun mamakin a koda yaushe shine,ita dai tasan cewa BABU SO tsakaninsu MEYA KAWO SHI?_* *_Duk da haka tana tunanin yun qundun bala ta fitar da FARHATUL K'ALB a cikin ZAFAFA BIYAR din samarinta,duk da batason su zame mata GURBIN IDO wanda har kullum ba ido bane_* *YA KUKAJI SALON MASU KARATU?* *YADDA SALON YA BAMBANTA DAKO YAUSHE HAKA LABARAN SUKA BAMBANTA DA DUKKA LABARANMU NA BAYA* INAYA(riba biyu)___mamughee SANADIN LABARINA___Rano BABU SO___Billynabdul FARHATUL K'ALB___Miss xoxo GURBIN IDO____Huguma *ZAKI YARDA AYI TAFIYAR NAN BABU KE MADAM?* *_GARZAYA KI BIYA NAKI KUDIN KAN FARASHI KAMAR HAKA_* Biyar:::1k Hudu:::700 Uku::::500 Biyu::::400 Daya:::300 *_zaki saka kudin ta wannan account number din_* HAFSAT UMAR KABIR 2270637070 Zenith bank *Saiku tura shaidar biya zuwa ga* 07040727902 *IDAN KUMA KATIN WAYA NE ZAKU TURA TA NAN TARE DA SHAIDAR BIYAR* 09134848107 *_THANKS FOR THE CONTINUED PATRONAGE_* _*FARHATAL-QALB*_ _(FARIN CIKIN ZUCIYAH)_ _NA_ _NANA HAFSATU_ _(MX)_ _AREWABOOKS:MISSXOXO_ _WATTPAD: MISSXOXO00_ _ZAFAFA BIYAR PAID NOVELS_ _PG:29_ _____ Tuni mayukan shafawa. Da shower gel na wanka harda night cream da face mask da Nadra ta bawa Waheedah. Sunyi matukar karban jikinta. Kalar fatar ta ta kara haskakawa . Ko'ina luwai luwai na jikinta tamkar kifi tarwada. Very smooth and clear. Gashi cimar da suke ci ta the Adams family ta matukar kara gina jikin su . Dukkanin su sun maro akan da da suke a kandare saboda yunwa. Ranar jumu'ah din da aka daura aure za'ayi mother's eve. Shine wanda zasu saka red material dinnan. Don haka tun da safe Waheedah tayo wanka. Ta shiga tsaftace komai da killace su zuwa inda ya kamata. Tana zaune akan kujerar zama. Tana wanke wanke. Marka ta fito daga dakinta. Ta saki wata bahaguwar miqa tana gantsarewa sosai. Tayi kan Waheedah tana tafa hannuwan ta. "Wannan kwailin din da kike narasa na menene.... Karfi da yaji sai kin koma baturiya. Kinata bilicin. Da girman Allah Sa'adatu kalli yarinyar nan yadda ta mayar da kanta " Cewar Marka, Ta juya tana gayawa inna Sa'adatu. Dake zaune a tsakar gidan tana yankan farce. "Ai lamarin se kallo kawai Marka... A deyi a hankali . Kuma abu duniya a sannu. Kuna bin kwadayi sannu ahankali zaku faada halaka." Inna Sa'adatu ta fada tana yatsina fuska. Suka cigaba da bin su da zagi da mugayen alkaba'i. Ita dai Waheedah ta toshe kunnuwanta ta hanyar qin cewa komai. Ta karasa wanke wanken ta kai kwanukan daaka. Ta sharce inda tayi wanke wanken tanata sauri. Don tuni Umma Hadiza ta tafi gidan aikin nata da sassafe dan kama musu wasu aiyukan. Kayan da Nadra ta bata da material din wajen Maa da aka dinka ta saka a leda don kai wa wajen guga. Tanata sauri ta fito daga cikin dakin sanye cikin riga da skirt yan kanti sai hijabi babba wanda take zuwa islamiyya da shi. "A yawo. A yawata...Sai ina kuma zaa sake harbawa. ?" "Yawan ta zubar m..." Inna Sa'adatu bata karasa fada ba. Waheedah ta daga mata hannu Idanuwanta sun kawo ruwa sosai. Don abu kalilan ne ke sakata kuka saboda raunin zuciyar ta. Ta saka hannunta daya ta goge hawayen dake tsiyaya a idanunta. "Ke ni kike dagawa hannu.?" Ta fada cikin fushi da kufulewa . "Ki dena aibata ni Inna... Ki dena fadan maganganun da ba haka suke ba .. Ya zaki dinga cewa yawon ta zubar za ni?" Inna Sa'adatu na daga zaune sai ta miqe tana sallallami hadi da tafa hannuwan ta. Bakinta a bude cikin tsantsar mamakin kalaman Waheedah "Ke da ni kike? Ni ki ke mayarwa martani dan uban ki?" Waheedah ta sauke zuciya tana kallon gefe. "Ni ka..." Kwas!!! Marka ta zuba mata rankwashi a kwanyar kanta da yasha mai da kananun kitson da Najan Isubu ta yarfa mata. "Karya ta miki? Ba halin uwar ki bane kika gada? Shegiya da idanuwa tsuru tsuru. Gaskia Sa'adatu ta fada. Kin koma mai kwailin. Jikin ki ko'ina ya cicciko bayan da ba ahakan kike ba. Idanuwan ki sun bude. Kina wani gani gani. Duk iskancin da kike a boye zai fito fili duniya tasan ke kike aikata komai." Waheedah ta sake fashewa da kuka ganin yadda haka kawai sun tsara zancen su suna magana tamkar suna da tabbacin hakan. "Zaki bar wannan kukan munafurcin ko sai na tashi na hanbare ki? Kayan meye kike sussunnewa a leda?" Cikin kuka da rawar murya tace, "Kayan fitar bikin ce zan kai guga." "To koma 'daka. Babu inda zaki. " "Dan Allah kiyi hakuri Marka " "Karki bari na sake magana...." "Uwar tata ma tun duku duku ta fice daga gidan nan. Ai awajenta ta koya. Gado girman 'da. Hadiza kam watsattsi..." Inna Sa'adatu bata karasa ba Waheedah ta miqe da ga tsugunnen da tayi . Da karfi tace, "Ya isa !! Ya isheku haka. " Gaba daya sai suka cika fam da mamakin kalaman ta. Wai yau Waheedah ce ke mayar da martani? "Wa kike cewa ya ishe su haka?" Ta saka hannunta daya ta goge hawayen dake zuba . "Ummanmu ba watsattsiya bace. Sannan uwa ce mai nagarta da jajircewa akan komai. Bisaga addini da al'adun hausa. Umman mu kamilace acikin kamilallu. Tana neman hakkinta ta hanyar