Sashe 72
Farhatul Qalbi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*WAYEWAR GARI* Waheedah ta riga Zayn tashi bayan da gari ya waye. Ta dubi yadda ya cukwikwiyeta tamkar kayan wanki. Ta shiga kokarin zame hannun ta da jikinta daga nasa. Amman ta kasa, Saboda tsananin yadda yayi mata rikon da ba na wasa ba A dole haka ta hakura ta koma ta kwanta. Sai bayan wajen minti talatin tukun sannan Zayn ya farka. Ya kishingida yana kallon Waheedah da wani baccin ya sake dauke ta. Kallon ta yake tamkar zai hadiyeta dajya. Kallon ta yake cikin so da kauna. Kallon ta yake cikin silar FARIN CIKIN sa. Kallon ta yake kallo na mamallakiyar ZUCIYAr sa da gangar jikin sa baki daya. Shi kansa bai san adadin kaunar da yake yi wa Waheedah ba. A hankali ta shiga bude idanun ta har ta sauke kallon ta baki daya akan sa. Ya kai saitin bakin sa labbanta kenan aka shiga bugo kofar dakin. Da sauri waheedan ta mike tana inda inda. Yatsanta a baki. Zayn sai murmushi yake. "Waheedah... Kin tashi?" Muryar Maa ta doki kofofin kunnuwan su. Zayn ya saka murmushi. Waheedah ta juya ta dankara masa harara. Ta matsa kusa da shi kasa k sa tace, "Kace na tafi makaranta.." "Weekend din?" Ya bata amsa yana daga girar sa. Sankarewa tayi a tsaye. Kafin da sauri ta shige bandaki. Shi kuma Zayn ya mike dama. Daama yake nema kuma ya samu a kusa. Ya bade idanun sa da kasa. Ya bude kofar da mukulli. Yana murmushi. "Ah.... Maaa.! Barka da safiya" ya durkusa har kasa yana gayshe ta. Ita kanta Maa din sai kunya ta kama ta. Gefe daya kuma tasan da biyu yayi hakan. Don ya nace a bashi Waheedah taki. Shine ya biyo mata tanan. Don da daddare ita ta rufe kofar sashen don haka da asubah ya shigo . "Alhamdulillah..... Kana lapia? Kace kanka yana ciwo jiya da safe." "I've never been this better .... Jazaki Allah bil jannah Maa.. oh Waheedah tana wanka" Ya karasa fada yana sosa keya. Bata sake cewa da shi komai ba. Ta sauka kasa. Shi kuma ya danne leben sa yana murmushi. Ya koma cikin dakin ya zauna a bakin gado. Sai murmushi yake shi kadai. ZUCIYAr sa dankare ta ke da FARIN CIKI.... _____________________ Sosai Umma Hadiza kasuwancin da take ya karbe ta. Allah ya sanya mata albarka aciki. Tana ciniki sosai. Don ta dawo da Najib ma gaban ta. Shagon da ke wajen gidan gwaggo haule anan Najib din ke kwana. Haj Hameedah ce ta bawa Umma Hadizan jari me tsoka ta kuma kara mata da wanda farfesa Adams yake bawa maaikatan sa na zakkah. Ranar Umma Hadiza har kukan FARIN CIKI tayi. cikin ZUCIYAr ta babu wata sauran damuwa sosai Ta samu albarka na suturu da kayan abinci sosai alkhairi kala kala. Hajia Hameedah da danginta sukai mata. Bataso rabuwa da ita ba. Sai dai babu yadda za'ayi tacigaba da aiki a karkashin su duba da uwnzun ta zama sirika awajen su. 'yar ta na auren 'dan su. Yanzun Najan Isubu ke mata aikin. Duk sauran bakin cikin da ke ZUCIYAr Umma Hadiza da ahalinta ya kare. Sai FARIN CIKI da ya maye gurbin sa. Hakika hakurin su yayi riba. Allah kuma ya karbi adduoin su. Ya dubi wankakkun zuciyoyin su ya musu zabi da mafificin alkhairin sa. Tarin manema nata zuwa mata. Neman auren ta, Amman Umma Hadizan ta dakatar da dukkanin su. Musanman yanzun da bata fita ko'ina. Tana dai zaune tana mai kula da lapiar Najib.... *GIDAN MALAM NA LADO* _INA MASOYA KUMA MA'ABOTA KAMSHI MA SU KAUNAR KAMSASAWA A KODA YAUSHE? DOMIN KAMSHI RAHAMA NE.._ _TO KU MATSO, DOMIN WANNAN KARON MA ZAFAFA BIYAR SUN ZO MU KU DA TALLAN MASARAUTAR KAMSHI NA KAMFANIN TURAREN *YERWA INCENSE AND MORE*_ _A *YERWA INCENSE AND MORE* ZA KU SAMU TURARUKAN WUTA NA *GIDAH, NA KAYA, NA TSUGUNNO* BA A NAN KADAI SUKA TSAYA BA. AKWAI *KHUMRAHS* MASU KAMSHIN LARABAWA DANA FRUITS KAI DAMA KAMSHIN TURAWA. AKWAI KHUMRAHS TA MATAN AURE DA TA YAMMATA_ _SANNAN SU NA DA *TURAREN WANKA DANA SHAFAWA BAYAN AN KAMMALA WANKA.* BA ANAN TURARUKAN NA SU SUKA TSAYA BA. AKWAI *KULACCAM* MAI MATUKAR KAMSHI DA SANYAYA ZUCIYA, SANNAN SU NA DA *MADARORIN TURARUKA NA JIKI DA NA KAYA*_ _AKWAI TURAREN *AL'AJABU NA TSUGUNNO DA KHUMRAH* DIN SA_ _SANNAN SU NA DA *TURAREN GASHI NA CREAM DA KUMA SPRAY DIN SA NA FESAWA*_ _BA ANAN SUKA TSAYA BA. SU NA DA *TURAREN MOPPING, DA NA BANDAKI AKWAI NA RUWAN WANKI DA NA FESAWA A DRAWER KO AKWATI*_ _AKWAI KAYAN GYARARRAKI NA FATA. KUJERAR TSUGUNNO, KASAKE NA WUTA, COAL IGNITER TA KUNNA GARWASHI, ELECTRIC BURNERS DA ENGLISH COAL_ _AKWAI LAFFAYAS DA SAURAN TURARUKA NA KAMSHI KALA KALA_ _SU NA BADA KAYAYYAKIN SU AKAN FARASHIN SARI KO SAYA AKAN DAYA DAYA. SANNAN SUNA TURA KAYAYYAKIN SU KO'INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE. KAYAN SU YAN CHADI NE DA SUDAN DA KUMA YERWA WATO MAIDUGURI._ _KYAU, INGANCI DA RAHUSA SAI KAYAYYAKIN KAMFAMIN YERWA INCENSE AND MORE. SAI KUN GWADA ZAKU BAMU LABARI_ _NAMBAR TARHON SU DA ZAA KIRA KO MUSU MAGANA TA WHATSAPP ITACE: 08095215215_ _INSTAGRAM HANDLE DIN SU: @yerwaincense_and_more_ _YERWA INCENSE AND MORE: A NUMBER ONE STOP SHOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS AND MORE_ *_ZAFAFA BIYAR din samari ne a rayuwar INAYAH,kowanne a cikinsu akwai wani murdadden Al'amari da ya shata layi tsakaninsa da ita,wawakeken sirri wanda a koda yaushe take kiransa da SANADIN LABARINA_* *_Amma babban abun mamakin a koda yaushe shine,ita dai tasan cewa BABU SO tsakaninsu MEYA KAWO SHI?_* *_Duk da haka tana tunanin yun qundun bala ta fitar da FARHATUL K'ALB a cikin ZAFAFA BIYAR din samarinta,duk da batason su zame mata GURBIN IDO wanda har kullum ba ido bane_* *YA KUKAJI SALON MASU KARATU?* *YADDA SALON YA BAMBANTA DAKO YAUSHE HAKA LABARAN SUKA BAMBANTA DA DUKKA LABARANMU NA BAYA* INAYA(riba biyu)___mamughee SANADIN LABARINA___Rano BABU SO___Billynabdul FARHATUL K'ALB___Miss xoxo GURBIN IDO____Huguma *ZAKI YARDA AYI TAFIYAR NAN BABU KE MADAM?* *_GARZAYA KI BIYA NAKI KUDIN KAN FARASHI KAMAR HAKA_* Biyar:::1k Hudu:::700 Uku::::500 Biyu::::400 Daya:::300 *_zaki saka kudin ta wannan account number din_* HAFSAT UMAR KABIR 2270637070 Zenith bank *Saiku tura shaidar biya zuwa ga* 07040727902 *IDAN KUMA KATIN WAYA NE ZAKU TURA TA NAN TARE DA SHAIDAR BIYAR* 09134848107 *_THANKS FOR THE CONTINUED PATRONAGE_* [11/23, 9:02 PM] Mummyn Yara: _*FARHATAL-QALB*_ _(FARIN CIKIN ZUCIYAH)_ _NA_ _NANA HAFSATU_ _(MX)_ _AREWABOOKS:MISSXOXO_ _WATTPAD: MISSXOXO00_ _ZAFAFA BIYAR PAID NOVELS_ _PG:65_ _WANNAN LITTAFI DA MA SAURAN NA *ZAFAFA* NA *KUDI* NE. DAN ALLAH KI/KA BIYA KUDI KI/KA MALLAKI NA KI. DON GUDUN SHIGA HAKKOKIN MASU RUBUTAWAR DA MA WADANDA SUKA CIRE KUDI SUKA SAYA..._ ____ *A kwance* Marka ta ke, Ya yin da ambaliyar hawaye ke tsiyaya daga idanun ta. Jikokin ta , Yaran wajen Zahara'u na kewaye a dakin suna wasan oji-oji. Tsakar gidan kuma yan biyun Deluwa ne akan katifa an kwantar da su. Dayar jaririyar idanunta a juye. Makauniya ce bata gani. Anyi maganin anyi sai addu'oi da ake bin ta da shi. Shigowar Najib kenan gidan ya hangi Marka tana kokarin motsa bakin ta ta kaa sa. Ya yinda ambaliyar hawaye ke tsiyaya daga idanunta. Da sauri ya karasa wajenta. Ya tattake ya daga ta dakyar yana sauke numfashi. Ya tokare ta da bango. Ruwan shan ta da ke kofi ya dauko yana mai mata nuni da shi. "Ruwa?" Ya tambayeta yana mai binta da kallon tausayi. Domin kwarai matuka Marka ma cikin halin haulai na kakanikani. Marka rigimammiyar tsohuwa da bata ganin kan kowa da gashi. Wai itace cikin wannan halin. Da bakinta ma ta bude tayi magana ta kasa. Sai dai a kwantar a kuma tayar. Bakin kofin ya kafa mata a baki . Ta shiga sha tamkar zata hadiye har kofin. Cikin haka sai ga Zahara'u ta rafka sallama. Ta shiga gidan tana tafe tana taunar cingum .. "Sai kira na ake ta wani faman yi. Kai innalillahi wa inna ilaihi rajiun. Ni dai da wannan jinyar dama warewa kikayi yasin." Ta fada cikin ko in kula da gabatarin maganar da tayi. Ba tare da ta auna zancen ba. Cikin yatsina ta shiga dakin ta zauna tana jan kwan cingum. "Ina wuni anti zahara'u?" "Lapia... Kai kuma yaushe ka zo?" Ta tambayi Najib. Duk kuwa da ya koma gidan gwaggo haule wajen Umman su da zama. Kullum safe da rana yana gidan na su na malam na lado. Duk kuwa da kyama tar su da muzantawa da marka tayi wa rayuwar su a baya . Hakan bai hana shi kula da ita ba. Dai dai karfin ikon sa. "Ban dade da shigowa ba. Anti." "Okay.," Zahara'u ta zauna a k sa. Ta yage dankwalin kanta tana sosa gashin ta. Marka na biye mata da kallo. Wani kwaro dai dai saitin marka . Zai shige jikin ta. Cikin wauta ji ka ke tas. Zahara'u ta wanke fuskar Marka da mari. Kwaron ya fadi kasa matacce. Marka ta fashe da kukan zafin mari. Najib dariya ta so kufce masa ya danne kawai. "La. Sattin ta ubangiji don na cire miki kwaron ne. Ashe ke zan samu . Kai Allah ya shirya ni. Yi hakuri marka ta".. Sai da Marka ta sha kukan ta. Tukun sannan tayi shiru tana jan majina. Marka ta kaikaice tana dan yamutsa fuska. Ji kake sirr ta iska ta fito. Zahara'u ta mike da sauri tana mai toshe hancin ta da bayan kasan hijabin ta. "Kai Kai Kai. Haba Marka. Na gaya miki ki dai na baje duwaiwai kina bada iska. Ko kashi zaki?" Nan ma Marka ta bude idanaun ta ta lumshe. Hakan ya bawa zahara'u damar ciccibar markan ta ajiye ta gefe. Sannan ta dakko fo na manya ta dora marka. Najib ya fice daga gidan da sauri yabar Marka a kan fo. Ta karasa yi. Dakin ya budade da hamamin bahayar Marka. Dakyar zahara'u ta mata tsarki ta fita da fon zuwa bandaki. Dakin ya dau tsami. Ta dawo ta tsaya kerere a kanta. "Zulfa'u ta zo kuwa?" Nan ma Marka ta lumshe idanu ta bude alamun a'ah. "Zabba'u fa?" Nanma Marka ta mata alama da bata zo ba. Ta dora hannunta akan cikin ta. Tana shafawa. Can ta mike bayan ta gantsare. "Bari na tafi . Idan Malam na lado ya zo ya karasa miki