Sashe 49
Farhatul Qalbi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
shigo. Sai yarinyar nan data tafi makaranta ba jimawa ." "Waheedah??" "Eh ita....." Kasa cewa komai ya yi. Ya wuce mota kawai. Har ya shiga ya fito ya zaro kudi ya mikawa baba mai gadi. "Godia nake ... Yau ma? Allah ya amfana. Allah ya shi albarka " "Aamin Aamin Baba... " Ya koma mota ya tayar. Baban ya bude masa gate ya fita. Kai tsaye ya wuce wajen aiki. Zuciyar sa nata tunano masa abincin da yaci. Me kama da na mahaifiyar su Haj Hameedah . Har spices din nan masu kamshi. Duk komai kaman na Maa. Ko da ya tashi daga aiki gidah ya wuce. Ya ci saa kuwa mahaifiyar tasu na nan. Bayan sun gaysa tace da shi, "Ya Ahlam ...?" "Tana gidah Maa." "Masha Allahu! Waheedah na makaranta ko?" "Eh... Haka Me gadi yace." "Bangane ba... Ku din bakwa nan ne baku sani ba.?" "Bantashi da wuri ba ne. Amma dai ko'ina naga a gyare....Maa kin aika da abinci ne?" "Akan wane dalilin zan aika muku da abinci?" Ta tambaye shi fuskar ta dauke da mamaki .. "No na ga ..... I mean naga.." "Kaga me?" "Naji abincin ne kaman na ki .." Murmushin fuskar ta ne ya fad'aad'a. Kafin ta ce, "A'a ..... Waheedah ce tayi ko?" Ya daga kai sannan yace, "Amma ban sani ba gaskia .. " "Batun kasani ko baka sani ba ma bai taso ba. Itace. Ai dama ta iya girki ... Sai kuma lokacin da suka samu hutu kafin ta karasa school tazo nan ta koya wasu abubuwan awaje na. Da su bangaren spices haka... Meya faru?" Murmushi yayi tattausa. Cikin muryar ladabi yace, "Naji kamshin komai kaman na abincin ki.. so na dauka ma an aika mana ne.... Masha Allah" Ya karasa fada fuskar Waheedah na masa gizo a idanun sa . "A'ah....." Kawai taceda shi. Tana duba wasu folders a laptop din da ke gaban ta. "Allah ya kara lapiaa Maa." "Amin. Allah ya kara mana dika." "Aamin." Suna zaune ta re. Sai ga shigowar mahaifin su professor Adams Nasser . Da waya a kunnen sa yana amsa wa. Zayn ya rissina yana gayshe shi. Ya daga masa hannu yana murmushi. Haj Hameedah ta miqe ta nupi dinning area tana kara turaren wuta acikin electric burner. "Abiey.... Barka da rana." "Barkan mu dai Zayn...Ya wajen su Ahlam?" "Alhamdulillah..." "To masha Allah.... Akwai abunda kake bukata?" Ya girgiza kai da sauri kafin yace, "A'a Abiey... Akwai komai. mungode Allah ya saka da alkhairi." "Amin Aamin Yaa rabbi... Allah ya temaka." "Amin Abiey.." Haj Hameedah ta tarbe shi tanata murmushi. Suka sake gaysawa. Kafin su isa wajen dinning din ta janyo masa kujera ya zauna. Ta shiga serving dinsa. Kallon su Zayn ya shiga yi cikin so da kulawa. Bai taba jin kan iyayen na sa ba. Yana alfahari da su. Ahlam ta fado masa arai. Sam baya gabanta. Shi baki daya ya kasa gane wane irin so take masa Anya kuwa? Sam bata kula da shi. Ita kanta bata kula da lokacin kanta .. Gaskia ba son gaskiya ba ne. Ya sauke nannauyar ajiyar zuciya kawai. Ya daga kansa kan saman pop ya zurfafa duniyar tunane tunane. Har mahaifin su yakammala cin abincin ya fita ta kofar gida. Haj Hameedah ta koma parlor kujerar da ke kallon ta Zayn. Kansa a sama bai masan ta dawo ba. Sau uku tana kiran sa baya ji. "Zayn...." Ta fada tana mai girgiza hannun kujerar da yake kai. Ya daga kansa da sauri ya sauke akan ta ... "Maa magana ki ke?" "Me yake damun ka ne? Ka gayamun gaskiya har yanzu Ahlam bata canza halayen ta ba?" "Ba komai Maa..." "Uhm uhm... Zayn!" "Na'am Maa..." "Ga yamun gaskia.... " Ya sauke nannauyar ajiyar zuciya. Yana mai Jan kasan leben sa . Kafin ya furzar da iskar bakin sa. Ya samu kansa da fitowa ya fadaawa mahaifiyar sa gaskia akan dukkanin abubuwan da suke faruwa acikin gidan. Tayi mamaki kwarai matuka . Domin a nata zaton tuni Ahlam ta canza halayen ta ta rungumi auren su da hannu biyu.. Kallon sa tayi. Ya sake ramewa akan da. "Yanzu ya kake son ayi Zayn?" "Maa .... Ku samo mun mafita kawai. Bazan iya boye miki ba Maa. Ahlam ta samun ciwo a cikin zuciyata .. bani da wani sauran FARIN CIKIN ZUCIYAH...." Kayi hakuri Zayn... Zamu yi magana da Abiey din ku. It shall be well insha Allah..." Mikewa yayi bayan ya mata sallama. Ya fice daga gidan. Zuciyar sa na masa zugi da rad'ad'i... _INA MASOYA KUMA MA'ABOTA KAMSHI MA SU KAUNAR KAMSASAWA A KODA YAUSHE? DOMIN KAMSHI RAHAMA NE.._ _TO KU MATSO, DOMIN WANNAN KARON MA ZAFAFA BIYAR SUN ZO MU KU DA TALLAN MASARAUTAR KAMSHI NA KAMFANIN TURAREN *YERWA INCENSE AND MORE*_ _A *YERWA INCENSE AND MORE* ZA KU SAMU TURARUKAN WUTA NA *GIDAH, NA KAYA, NA TSUGUNNO* BA A NAN KADAI SUKA TSAYA BA. AKWAI *KHUMRAHS* MASU KAMSHIN LARABAWA DANA FRUITS KAI DAMA KAMSHIN TURAWA. AKWAI KHUMRAHS TA MATAN AURE DA TA YAMMATA_ _SANNAN SU NA DA *TURAREN WANKA DANA SHAFAWA BAYAN AN KAMMALA WANKA.* BA ANAN TURARUKAN NA SU SUKA TSAYA BA. AKWAI *KULACCAM* MAI MATUKAR KAMSHI DA SANYAYA ZUCIYA, SANNAN SU NA DA *MADARORIN TURARUKA NA JIKI DA NA KAYA*_ _AKWAI TURAREN *AL'AJABU NA TSUGUNNO DA KHUMRAH* DIN SA_ _SANNAN SU NA DA *TURAREN GASHI NA CREAM DA KUMA SPRAY DIN SA NA FESAWA*_ _BA ANAN SUKA TSAYA BA. SU NA DA *TURAREN MOPPING, DA NA BANDAKI AKWAI NA RUWAN WANKI DA NA FESAWA A DRAWER KO AKWATI*_ _AKWAI KAYAN GYARARRAKI NA FATA. KUJERAR TSUGUNNO, KASAKE NA WUTA, COAL IGNITER TA KUNNA GARWASHI, ELECTRIC BURNERS DA ENGLISH COAL_ _AKWAI LAFFAYAS DA SAURAN TURARUKA NA KAMSHI KALA KALA_ _SU NA BADA KAYAYYAKIN SU AKAN FARASHIN SARI KO SAYA AKAN DAYA DAYA. SANNAN SUNA TURA KAYAYYAKIN SU KO'INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE. KAYAN SU YAN CHADI NE DA SUDAN DA KUMA YERWA WATO MAIDUGURI._ _KYAU, INGANCI DA RAHUSA SAI KAYAYYAKIN KAMFAMIN YERWA INCENSE AND MORE. SAI KUN GWADA ZAKU BAMU LABARI_ _NAMBAR TARHON SU DA ZAA KIRA KO MUSU MAGANA TA WHATSAPP ITACE: 08095215215_ _INSTAGRAM HANDLE DIN SU: @yerwaincense_and_more_ _YERWA INCENSE AND MORE: A NUMBER ONE STOP SHOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS AND MORE_ *_ZAFAFA BIYAR din samari ne a rayuwar INAYAH,kowanne a cikinsu akwai wani murdadden Al'amari da ya shata layi tsakaninsa da ita,wawakeken sirri wanda a koda yaushe take kiransa da SANADIN LABARINA_* *_Amma babban abun mamakin a koda yaushe shine,ita dai tasan cewa BABU SO tsakaninsu MEYA KAWO SHI?_* *_Duk da haka tana tunanin yun qundun bala ta fitar da FARHATUL K'ALB a cikin ZAFAFA BIYAR din samarinta,duk da batason su zame mata GURBIN IDO wanda har kullum ba ido bane_* *YA KUKAJI SALON MASU KARATU?* *YADDA SALON YA BAMBANTA DAKO YAUSHE HAKA LABARAN SUKA BAMBANTA DA DUKKA LABARANMU NA BAYA* INAYA(riba biyu)___mamughee SANADIN LABARINA___Rano BABU SO___Billynabdul FARHATUL K'ALB___Miss xoxo GURBIN IDO____Huguma *ZAKI YARDA AYI TAFIYAR NAN BABU KE MADAM?* *_GARZAYA KI BIYA NAKI KUDIN KAN FARASHI KAMAR HAKA_* Biyar:::1k Hudu:::700 Uku::::500 Biyu::::400 Daya:::300 *_zaki saka kudin ta wannan account number din_* HAFSAT UMAR KABIR 2270637070 Zenith bank *Saiku tura shaidar biya zuwa ga* 07040727902 *IDAN KUMA KATIN WAYA NE ZAKU TURA TA NAN TARE DA SHAIDAR BIYAR* 09134848107 *_THANKS FOR THE CONTINUED PATRONAGE_* [11/23, 9:02 PM] Mummyn Yara: _*FARHATAL-QALB*_ _(FARIN CIKIN ZUCIYAH)_ _NA_ _NANA HAFSATU_ _(MX)_ _AREWABOOKS:MISSXOXO_ _WATTPAD: MISSXOXO00_ _ZAFAFA BIYAR PAID NOVELS_ _PG:52_ ___ *Kasancewar* asabar ce. Hakan yasa bai fita aiki ba. Yana zaune a parlorn kasa yana kallon wasan kwallon kafar da ake bugawa na Manchester united da Fc Barcelona. Wayar sace ta fara kara. Kiran waya ne yake shigowa. Daukar wayar yayi kamar ba zai amsa ba. Sai kuma ya dauka ganin me kiran Useey ne abokin sa. Ya dauka yana sallama. Hade da rage muryar talabijin din da ke yi. Gaisawa sukayi can ya zare wayar a kunnen sa yana kallon screen din wayar. Date ya kalla baki daya ya shafa'a ranar itace wadda suka tsayar kan ziyartar da zasu kawo gidan sa. Ya sosa keyar sa kafin ya ce da useey din., "Eh mana maza. Allah ya kawo ku lapia. Bayan sallar la'asar ko? Alright ." Ya katse kiran. "Ahlam.... Ahlam.." "Na'am." Ta amsa shi tana mai sakkowa daga matattakalar benen sama. "Yauwa... " Ya fada yana mikewa tsaye. "Ya akai?" "Baki zamu yi...Mai da me zaa kawo?" "Baki kuma?" Ta tambaye shi idanun ta akan sa. "Eh... Da hausa nayi magana ai." "Tab.. Ni wallahi bansani ba. Tambaya Waheedah mana." Ta fada cikin rashin damuwa da koma su wanene. Ya daga kai ya kalli agogo kafin ya girgiza kai kawai. "Tana ina?" "Tana daki mana." Kai tsaye ya isa kofar dakin ya shiga knocking. Muryar karatun qur'anin da take na tashi ahankali cikin lugga da bil tartil na tajweed. Ya lumshe saboda yadda karatun da qira'ar ke tafiya a sanyaye mai cike da dadi. Ya sake dan bubbugawa ahankali. Waheedah bata tsaya ba sai data kai karshen ayar tukun sannan ta ajiye qur'anin. Ta mike sanye take cikin rigar atamfa doguwa samfarin A shape marar kamawa ta daura dankwali daurin channel o. Ta janyo hijabin ta ta zura kafin ta bude kofar. Kamshin jikin ta da nasa suka hadu waje daya suka ba da wani sihirtaccen kamshi mai sanyaya zuciyar duk wanda ya shaaqa. Kasa cire idanun sa yayi daga kanta. Zuciyar sa na zillo tamkar zata fado daga kirjin sa. Ya lumshe idanun ya sake bude wa. "Ina kwana?" Ta dan rissina ta gayshe da shi. Shiru bai amsa ba. Gabansa ya tsananta bugawa da sauri da sauri. Dakyar ya iya sai saita kan sa. Ya ce da ita, "Ki., Ki zo." Yana karasa fada ya bar wajen da sauri. Ya koma tsakiyar parlorn. Ita kuwa gambal habaru Ahlam wayar ta na hannunta tana danne danne. Ta bude wani video a Instagram tana gani. "Ga ni aunty...." Waheedah ta fada cikin girmamawa. "Okay ba ka gaya mata ba?" Ahlam ta daga kai tana duban Zayn da ya maida kallon sa kan tv. Ita dai Waheedah ta zubawa sarautar Allah idanu tana jiran cewar su. Zayn ya sauke numfashi zazzafa kafin yace, "Zamuyi baqi ne... Abokai na ne zasu zo. Su uku. Kinga ai zaa dan yi