← Book details Farhatul Qalbi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 82

Sashe 38

Farhatul Qalbi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gashi da biyayya da kyautatawa. Kenan duk shawarar da yake gaya mata da adduuoin da yake yi. Na tafiya ne kenan? Sallama ce yake yi ta haka? Ashe duniyar zai bari baki daya? Ta sake fashewa da kuka sosai . Har tana shessheka... Najib ma na ta rera kukan sa mai ban tausayi ga duk wanda ya saurara. Najan isubu ta fice daga gidan tanata sauri. "Ina wuni aunty ..?" Cewar wani dan adaidata sahu da suke makota. "Kwana dai ko... Ina kayi dan Allah..?" "Gangaren durumi.." "Yauwa muje ka saukeni dan Allah a gidan gwaggo haule ." "Me kankara?" "Eh.." "Toh shigo.... Ance wai yaran nan kamalu ya rasu ko?" "Ya wuce wai... Ya rasu da gaske. " "Innalillahi wa inna ilaihi rajiun... Allah yasa karshen wahalar kenan... Gaskia gayen nan ya jima yana jinya." Ya karasa fada yana girgiza kai "Aamin..." Har kofar gidan ya sauketa. Ta janyo nera hamsin ta miqa masa. "Ah ki basshi... Allah ya kara hakuri..." "Aamin...." Jikinta asanyaye ta shiga cikin gidan bakinta dauke da sallama.. "Wa'alaykm Salam...." Suka amsa. Alokacin Umma Hadiza har ta zura hijabinta .zata tafi gidan aikin ta "Ahh Najan Isubu... Maraba lale..." Cewar gwaggo haule dake zaune akan wata tabarma tana tsintar shinkafa. "Naam gwaggo..." "Ahh Najaatu...." "Naam Hadiza.... Har zaki tafi?" "Eh wai so na ke na kammala aikina da wuri. Inason zuwa wambai na tsinto rigunan sanyin su kamalu.." Najaatu ta dan kwakwalo murmushi kawai ta nemi waje ta zauna . "Wani wajen kika je ne?" Umma Hadiza ta sake tambayar ta. "A'ah daga gidah na ke...." Tanata jujjuya yadda zata sanar da zancen mutuwar. "Wani abun ya faru ne Naja?" Gwaggo haule ta tambayeta. Suka zuba mata idanu su duka suna jiran amsar da zata bayar "Ai daga gidan su Waheedan nake..." "Toh.... Rashin lapiar ce dai?" "Kinji ko gwaggo? Daman wallahi baki daya kwanakin nan haka naketa wasu irin mafarkai.." "Kwarai har kikace zaki sa a kirawo su kamalu ku gaysa ki ga jikin na su . To ya ake ciki najaatu..?" Najan Isubu ta sauke nannauyar ajiyar zuciya ta kasa cewa komai. Kanta a k sa. Yayin da idanunta suka kawo ruwa. Umma Hadiza ta zauna a gefen gwaggo haule. Ta hada hannuwanta biyu . "Waye ya rasu acikin yaran najaatu?" Najan Isubu ta daga kai ta dubi Umma Hadiza da sauri. Gwaggo haule ma ta kalleta tana mamakin maganar da tayi. "Rasuwa kuma?" Gwaggo haule ta tambaya. "Eh gwaggo.... Tabbas cikin yaran ne wani ya rasu... Ko dukan su ne? Kadan daga iko da kudira ta ubangiji..." "Hakane .... Innalillahi wa inna ilaihi rajiun.. Naja waye ya rasu?" Najan Isubu ta daga kai ta kallesu. Hawaye daya na bin daya "Kamalu ne gwaggo... Allah ya karbi ran kamalu.." Umma Hadiza ta sauke zuciya. Ta ja salati "Innalillahi wa inna ilaihi rajiun... Allah ka jikan kamalu .. Allah kayi masa rahama. Allah ka gafarta masa. Allah ka kyautata makwancin sa. Ka sadashi da annabin rahama... Allah ka bashi nasarar amsa tambayoyin kabari. Allah ka yalwata kabarin sa. Allah kasa aljannar firdwas ce makoma agare shi . Da dukkanin musulmai baki daya... Aamin" Umma Hadiza ta fada. Batayi hawaye ba. Amman idanunta sun kada sunyi cazir. Da alama kukan zuci take yi. "Aamin Aamin Hadiza..." "Kiyi hakuri Hadiza ..." "Hakuri mun godewa Allah Naja'atu. kowa ai dan haka ne... Ko ba jima ko ba dade . Lokacin sa ne yayi..." "Hakane.. Allah ya gafarta masa. " "Aamin...." "Na yafe maka kamalu .. Duk kuwa da babu abunda ka yi mun. A iya sani na da wanda ban sani ba .. Na yafe maka duniya da lahira Kamalu... Allah ya gafarta maka...." Najan Isubu kawai zuba idanu tayi tana bin Umma hadiza da kallon namijin kokarin da tayi. Gwaggo haule ta mike ta shiga daki ta dakko hijabi ta zura . Can sai ga mijinta ya shigo yanata sauri shima . Suka gaysa da Najan Isubu . Ya shiga daki ya dakko hula ya fito.. "Malam kai ma ka ji ne?" "Eh wallahi .. Jana'iza karfe 10. Allah ya jikan kamalu ya rahama masa. Ya dace da yardar Allah. Don yaran nan sam ba yada matsala. Baya fada da kowa. Ba shi da hayaniya ba rashin kunya. Ba bin yaran banza . Insha Allahu aljanna ce makoma agare shi.. Anata yabon sa" "Aamin Yaa rabbi .... " "Allah ya baki hakurin rashi Hadiza..." "Aamin ..." Ya fuce da sauri ya bar su. Kafin su ma su tattara komai su barshi. Su fita "Ni Marka tace kar na soma takawa kofar gidan nan...." "Mutuwa ce yanzu ai Hadiza. ." "Ta zama dole ai ... Dole ki je Hadiza.." Suka gangara suka samu adaidaita suka shiga. Ya kai su har kofar gidan. Mutane sun fara taruwa sosai. Maza nata alwalar sallar Janaza. Suka shige cikin gidan. Waheedah na ganin Umman su tatafi ta rungumeta tanata kuka. Umma Hadizan ta sake dakewa bata zubar da hawaye ba. Yayin da labbanta keta kwarara adduar samun ceton rahamar Allah ga kamalu. "Shigo kuyi sallama Hadiza ... Waheedah kema.. Kai Najib zo." Umma Hadiza ta shiga ciki. Fuskar Kamal ce kawai a bude. Yayin da dukkanin jikin sa ke a rufe da likkafa ni. "Allah ya gafarta maka kamalu.. Allah ya yafe maka dukkanin zunuban ka.. Allah yasa aljanna ce makoma agare ka. Allah ya maka rahama. Allah ya maka rahama. Kyawawan halayen ka nagari Allah yasa su bika Kamalu.. " Tana karasa fada ta mike ta koma tsakar gidah kan tabarma ta zauna Waheedah da Najib kuwa sai da akayi da gaske aka bambare su daga cikin gawar aka fita da ita. Aka sallaceta aka tafi da ita makabarta. Yan taaziya sai tudadowa sukeyi anata yiwa Umma Hadiza taaziyyah. Masha Allahu ba wanda ke binsa bashi ba kuma wanda yake bi. Ya samu shedu da dama daga bakuna nagari Yar tsalar da kunun dakyar gwaggo haule ta tasa Najib da Waheedah a gaba suka ci. Sauran akayi sadaka da su . Nan da nan kuwa mutane keta kawo kayan abincin don samun lada. Najan Isubu ta kira Indo ta sheda mata halin da ake ciki. Ya yin da indon ta sanarwa the Adams family. Washegarin rasuwar kuwa Haj Hameedah da Nadra da indon suka zo gidan sukayi musu taaziyyah . Da sadakar buhun shinkafa da carton na taliya da jarkar mai da kuma dubu biyar. Haka akai ta zaman makoki har na tsawon kwanaki. Kafin aka share makokin kowa ya koma inda ya fito. Gwaggo haule ta tasa Waheedah agaba tatafi da ita. Najib kadai aka bari anan din. Amman kullum abincin safe , Rana dana dare duk suna kawo masa. Hakama magungunan sa basa yankewa. Sosai ya kara samun kulawa. Musanman da yanzun shi kadai ne ya rage babu kamalu.... _INA MASOYA KUMA MA'ABOTA KAMSHI MA SU KAUNAR KAMSASAWA A KODA YAUSHE? DOMIN KAMSHI RAHAMA NE.._ _TO KU MATSO, DOMIN WANNAN KARON MA ZAFAFA BIYAR SUN ZO MU KU DA TALLAN MASARAUTAR KAMSHI NA KAMFANIN TURAREN *YERWA INCENSE AND MORE*_ _A *YERWA INCENSE AND MORE* ZA KU SAMU TURARUKAN WUTA NA *GIDAH, NA KAYA, NA TSUGUNNO* BA A NAN KADAI SUKA TSAYA BA. AKWAI *KHUMRAHS* MASU KAMSHIN LARABAWA DANA FRUITS KAI DAMA KAMSHIN TURAWA. AKWAI KHUMRAHS TA MATAN AURE DA TA YAMMATA_ _SANNAN SU NA DA *TURAREN WANKA DANA SHAFAWA BAYAN AN KAMMALA WANKA.* BA ANAN TURARUKAN NA SU SUKA TSAYA BA. AKWAI *KULACCAM* MAI MATUKAR KAMSHI DA SANYAYA ZUCIYA, SANNAN SU NA DA *MADARORIN TURARUKA NA JIKI DA NA KAYA*_ _AKWAI TURAREN *AL'AJABU NA TSUGUNNO DA KHUMRAH* DIN SA_ _SANNAN SU NA DA *TURAREN GASHI NA CREAM DA KUMA SPRAY DIN SA NA FESAWA*_ _BA ANAN SUKA TSAYA BA. SU NA DA *TURAREN MOPPING, DA NA BANDAKI AKWAI NA RUWAN WANKI DA NA FESAWA A DRAWER KO AKWATI*_ _AKWAI KAYAN GYARARRAKI NA FATA. KUJERAR TSUGUNNO, KASAKE NA WUTA, COAL IGNITER TA KUNNA GARWASHI, ELECTRIC BURNERS DA ENGLISH COAL_ _AKWAI LAFFAYAS DA SAURAN TURARUKA NA KAMSHI KALA KALA_ _SU NA BADA KAYAYYAKIN SU AKAN FARASHIN SARI KO SAYA AKAN DAYA DAYA. SANNAN SUNA TURA KAYAYYAKIN SU KO'INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE. KAYAN SU YAN CHADI NE DA SUDAN DA KUMA YERWA WATO MAIDUGURI._ _KYAU, INGANCI DA RAHUSA SAI KAYAYYAKIN KAMFAMIN YERWA INCENSE AND MORE. SAI KUN GWADA ZAKU BAMU LABARI_ _NAMBAR TARHON SU DA ZAA KIRA KO MUSU MAGANA TA WHATSAPP ITACE: 08095215215_ _INSTAGRAM HANDLE DIN SU: @yerwaincense_and_more_ _YERWA INCENSE AND MORE: A NUMBER ONE STOP SHOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS AND MORE_ *_ZAFAFA BIYAR din samari ne a rayuwar INAYAH,kowanne a cikinsu akwai wani murdadden Al'amari da ya shata layi tsakaninsa da ita,wawakeken sirri wanda a koda yaushe take kiransa da SANADIN LABARINA_* *_Amma babban abun mamakin a koda yaushe shine,ita dai tasan cewa BABU SO tsakaninsu MEYA KAWO SHI?_* *_Duk da haka tana tunanin yun qundun bala ta fitar da FARHATUL K'ALB a cikin ZAFAFA BIYAR din samarinta,duk da batason su zame mata GURBIN IDO wanda har kullum ba ido bane_* *YA KUKAJI SALON MASU KARATU?* *YADDA SALON YA BAMBANTA DAKO YAUSHE HAKA LABARAN SUKA BAMBANTA DA DUKKA LABARANMU NA BAYA* INAYA(riba biyu)___mamughee SANADIN LABARINA___Rano BABU SO___Billynabdul FARHATUL K'ALB___Miss xoxo GURBIN IDO____Huguma *ZAKI YARDA AYI TAFIYAR NAN BABU KE MADAM?* *_GARZAYA KI BIYA NAKI KUDIN KAN FARASHI KAMAR HAKA_* Biyar:::1k Hudu:::700 Uku::::500 Biyu::::400 Daya:::300 *_zaki saka kudin ta wannan account number din_* HAFSAT UMAR KABIR 2270637070 Zenith bank *Saiku tura shaidar biya zuwa ga* 07040727902 *IDAN KUMA KATIN WAYA NE ZAKU TURA TA NAN TARE DA SHAIDAR BIYAR* 09134848107 *_THANKS FOR THE CONTINUED PATRONAGE_* [11/23, 9:02 PM] Mummyn Yara: _*FARHATAL-QALB*_ _(FARIN CIKIN ZUCIYAH)_ _NA_ _NANA HAFSATU_ _(MX)_ _AREWABOOKS:MISSXOXO_ _WATTPAD: MISSXOXO00_ _ZAFAFA BIYAR PAID NOVELS_ _PG:43__ _WANNAN LITTAFI DA MA SAURAN NA *ZAFAFA* NA *KUDI* NE. DAN ALLAH KI/KA BIYA KUDI KI/KA MALLAKI NA KI. DON GUDUN SHIGA HAKKOKIN MASU RUBUTAWAR DA MA WADANDA SUKA CIRE KUDI SUKA SAYA..._ A hankali ta shiga bude manyan idanunta. Ta sauke su akan Umma Hadiza dake zaune tana zuba sukari acikin kunu . "Kin tashi.....?" "Eh.... Umma." Ta miqe tana salati. "Na so makara ..." "Ai da naga kince kina hutu (al'ada) shi ya sa ban tashe ki ba." "Ai ko na samu bacci . Godia nake Umman mu. Barka da safiya." "Barka ka dai Waheedah .." Kwandon sosan wankan
Chapter 38 · 0% Book details