← Book details Farhatul Qalbi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 82

Sashe 41

Farhatul Qalbi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

da sauri ya zauna akan dinning sai daya cika uwar kashin sa tukun sannan ya koma ya zauna akan kujera. Ta sake tambayar sa kamar koda yaushe gamin yadda ya dan rame. Idanuwan sa tubarkaAllah sun sake manyanta. "Akwai wani abunne?" "A'ah Maa..." Ya bata amsa tamkar ko da yaushe "Ya Ahlam din... Lapiar ta kalau?" "Alhamdulillah...." "Masha Allahu.... Yau mukace zamu kai ziyara kuwa. Amman sai an jima " "Eh... Insha Allah " ya fada yana lankwasa hannuwan sa. Hade da shafa keyar sa. "Akwai wani abunne?" Ta sake tambayar sa. Don tasan halin sa da zurfin ciki. Amman dai a matsayin ta na mahaifiya ta hasaso akwai yar tangarda a zaman sa da Ahlam "Dama...Ahlam dince tace ko zaa kai me aiki ta tayata abinci..." "Ta tayata ko ta mata?" "Ta mata...." "To gaskia dai kaga nan gyara suke tamun. Kuma Hadiza itace karfin aikin wallahi. Sai dai ko na tambaye ta idan Waheedah na nan sai taje.." "Waheedah kuma Maa?" "Eh Waheedah... Ai ta iya girke girke yarinyar nan. Sai ta mata din.." "Tohm." Ya amsa badan ya so ba. "Hadiza... Hadiza!! Hadiza!!" "Naam hajiya..." Ta karasa da sauri tayi gurfane agabanta. "Dan Allah Waheedah na nan kuwa? Wai Ahlam ai kingane ta ko?" "Kwarai na game ta... Wadda akayi bikin su ko?" "Yauwa ita... Idan anjima ne zamu je gidan . Har da ke ma insha Allah. To shine takeson a ara mata wadda zata mata girki. Na yaba da hankalin Waheedah da kuma fasaharta na iya girki. Ba matsala taje?" "Babu......Hajia. Tana makaranta. Amman nasan an kusa tashin su. Tunda yau jumu'ah...." "Yauwa masha Allahu... Ai kace kasan makarantar ko. ? Ko ku tafi da Nassem ya muku rakiya. Da Nadra na nanne sai taje . To sai watan gobe zata dawo " "Nadra an sha hutu kam." "Tabbas ana kan sha ma. " "Shikenan Hadiza je ki .." "Tohm Hajia." Umma Hadiza ta miqe ta koma kitchen Shi kuma suka cigaba da zaman kurmaye. Sai da Maa ta tashi ta kira Nassem . Wajajen 11 da mintuna suka dauki hanyar makarantar su Waheedah. Ba jimawa kuwa aka tasa su Nassem ya shiga da kansa makarantar aka nuna amsa ajin su Waheedah bayan ya tanbaya. Suna gaban me youghurt yana yanka musu na 20 kowannen su "Waheedah...." "Naam..." Ta juya don ganin me kiran na ta. Nassem ta gani a tsaye yana kare fuskar sa. Saboda ranar dake dallare shi Karasawa tayi wajen sa tana murmushi. "Yau kai ne a makarantar mu?" Dan murmushin shima yayi kafin yace, "Rakiya nayo ma.. Ni yanzu zan koma gidah. Zaku sauke ni." "Ni da su wa?" "Ke da akiey... Ya Zayn." Yana karasa fada gabanta ya yanke ya fadi. Mumuguncin mutumin nan me zatayi masa.? "Me zan masa?" Ta tanbaya batare da tasan ta fito ha. "Kede muje... Sa ce ki zamuyi.." suna saka dariya baki dayan su . Har mota suka isa. Nassem ya hide mata ya shiga ya zauna. Gabanta na tsananta bugawa. Juyawa yayi ya kalleta. Fuskar sa a daure. "Ku sauke ni a kwanan layin mu. " Cewar Nassem. "Alright....." Har kofar layin suka sauke shi. Ya sauka har ya tafi. Zayn bai ja motar ba. Waheedah kuma bata tanka ha. Ya juya ransa a bace "Ke waye driver din ki? Common dawo gaba ki zauna...." Ta bude da sauri ta koma gaban ta zauna. Tana gatsina fuska. Murmushi ya so kufce masa dakyar ya danne suka dauki hanyar gidan sa. _INA MASOYA KUMA MA'ABOTA KAMSHI MA SU KAUNAR KAMSASAWA A KODA YAUSHE? DOMIN KAMSHI RAHAMA NE.._ _TO KU MATSO, DOMIN WANNAN KARON MA ZAFAFA BIYAR SUN ZO MU KU DA TALLAN MASARAUTAR KAMSHI NA KAMFANIN TURAREN *YERWA INCENSE AND MORE*_ _A *YERWA INCENSE AND MORE* ZA KU SAMU TURARUKAN WUTA NA *GIDAH, NA KAYA, NA TSUGUNNO* BA A NAN KADAI SUKA TSAYA BA. AKWAI *KHUMRAHS* MASU KAMSHIN LARABAWA DANA FRUITS KAI DAMA KAMSHIN TURAWA. AKWAI KHUMRAHS TA MATAN AURE DA TA YAMMATA_ _SANNAN SU NA DA *TURAREN WANKA DANA SHAFAWA BAYAN AN KAMMALA WANKA.* BA ANAN TURARUKAN NA SU SUKA TSAYA BA. AKWAI *KULACCAM* MAI MATUKAR KAMSHI DA SANYAYA ZUCIYA, SANNAN SU NA DA *MADARORIN TURARUKA NA JIKI DA NA KAYA*_ _AKWAI TURAREN *AL'AJABU NA TSUGUNNO DA KHUMRAH* DIN SA_ _SANNAN SU NA DA *TURAREN GASHI NA CREAM DA KUMA SPRAY DIN SA NA FESAWA*_ _BA ANAN SUKA TSAYA BA. SU NA DA *TURAREN MOPPING, DA NA BANDAKI AKWAI NA RUWAN WANKI DA NA FESAWA A DRAWER KO AKWATI*_ _AKWAI KAYAN GYARARRAKI NA FATA. KUJERAR TSUGUNNO, KASAKE NA WUTA, COAL IGNITER TA KUNNA GARWASHI, ELECTRIC BURNERS DA ENGLISH COAL_ _AKWAI LAFFAYAS DA SAURAN TURARUKA NA KAMSHI KALA KALA_ _SU NA BADA KAYAYYAKIN SU AKAN FARASHIN SARI KO SAYA AKAN DAYA DAYA. SANNAN SUNA TURA KAYAYYAKIN SU KO'INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE. KAYAN SU YAN CHADI NE DA SUDAN DA KUMA YERWA WATO MAIDUGURI._ _KYAU, INGANCI DA RAHUSA SAI KAYAYYAKIN KAMFAMIN YERWA INCENSE AND MORE. SAI KUN GWADA ZAKU BAMU LABARI_ _NAMBAR TARHON SU DA ZAA KIRA KO MUSU MAGANA TA WHATSAPP ITACE: 08095215215_ _INSTAGRAM HANDLE DIN SU: @yerwaincense_and_more_ _YERWA INCENSE AND MORE: A NUMBER ONE STOP SHOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS AND MORE_ *_ZAFAFA BIYAR din samari ne a rayuwar INAYAH,kowanne a cikinsu akwai wani murdadden Al'amari da ya shata layi tsakaninsa da ita,wawakeken sirri wanda a koda yaushe take kiransa da SANADIN LABARINA_* *_Amma babban abun mamakin a koda yaushe shine,ita dai tasan cewa BABU SO tsakaninsu MEYA KAWO SHI?_* *_Duk da haka tana tunanin yun qundun bala ta fitar da FARHATUL K'ALB a cikin ZAFAFA BIYAR din samarinta,duk da batason su zame mata GURBIN IDO wanda har kullum ba ido bane_* *YA KUKAJI SALON MASU KARATU?* *YADDA SALON YA BAMBANTA DAKO YAUSHE HAKA LABARAN SUKA BAMBANTA DA DUKKA LABARANMU NA BAYA* INAYA(riba biyu)___mamughee SANADIN LABARINA___Rano BABU SO___Billynabdul FARHATUL K'ALB___Miss xoxo GURBIN IDO____Huguma *ZAKI YARDA AYI TAFIYAR NAN BABU KE MADAM?* *_GARZAYA KI BIYA NAKI KUDIN KAN FARASHI KAMAR HAKA_* Biyar:::1k Hudu:::700 Uku::::500 Biyu::::400 Daya:::300 *_zaki saka kudin ta wannan account number din_* HAFSAT UMAR KABIR 2270637070 Zenith bank *Saiku tura shaidar biya zuwa ga* 07040727902 *IDAN KUMA KATIN WAYA NE ZAKU TURA TA NAN TARE DA SHAIDAR BIYAR* 09134848107 *_THANKS FOR THE CONTINUED PATRONAGE_* [11/23, 9:02 PM] Mummyn Yara: _*FARHATAL-QALB*_ _(FARIN CIKIN ZUCIYAH)_ _NA_ _NANA HAFSATU_ _(MX)_ _AREWABOOKS:MISSXOXO_ _WATTPAD: MISSXOXO00_ _ZAFAFA BIYAR PAID NOVELS_ _PG:45_ _WANNAN LITTAFI DA MA SAURAN NA *ZAFAFA* NA *KUDI* NE. DAN ALLAH KI/KA BIYA KUDI KI/KA MALLAKI NA KI. DON GUDUN SHIGA HAKKOKIN MASU RUBUTAWAR DA MA WADANDA SUKA CIRE KUDI SUKA SAYA..._ *A* wani junction da ke kusa da layin gidan sa. Suka tarar da hold off agaban su. Yaja siririn tsaki yana mai danne kasan leben sa. Waheedah na zaune akan kujera . Yayin da fuskar ta ke kallon gefen waje. Ya dan juyar da kansa ya sauke idanun sa akan ta. Gefen fuskarta idanun sa suka sauka. Kwantaccen gashin gefen fuskarta wajen kunnenta ya kwanta luf . Girar ta mai cikar yalwar gashi.. Leben ta duk kuwa da gefen sa ne. Kana iya hango kalar sa. Pinkish in color. . Kasa cigaba da kallon nata yayi. Ya juyar da kan sa gefe da sauri. Hade da saka hannu ya karo gudun air-conditioner dake busa musu sanyi. Sannu a hankali hold off din ya ja baya. Zayn ya samu hanya ya shige cikin layin da gidan sa yake. Baba mai gadi da ke zaune a bakin gate din akan benchi. Yana hango motar. Baba mai gadi ya mike da sauri ya bude gate din. Zayn ya shiga da matar ciki bayan ya tsaya sun gaisa. Ya faka motar a rumfa. Ya kashe, Waheedah ta bude kofar ta fita tana dan kalle kallen gidan. Yayi mata kyau kwarai da gaske. "Allahumma arzuqni...." Ta fada kasan maqoshi tana bin garden din gidan da ke cike da shuke shuke da kallo "Muje ko....?" Zayn ya ce da ita.. Yayi gaba tana biye da shi a baya. Door bell ya danna. Sai da yayi ta dannawa wajen sau shida kafin Ahlam ta bude kofar. Ya kare mata kallo. Kayan baccin dazu da ya barta ne. Bata canza ba . Ba sannu bare ban gajiya. Ta janyo hannun Waheedah dake bayan Zayn. Hakan har yayi sanadiyyar gugar jikin Waheedah ana Zayn. Wani baqon yanayi ya ziyarci dukkanin su. "Ina wuni sis...?" "Lapia kalau my dear sweet sis... Ya kike?" "Lapia Lau ..." "Masha Allah.... Zo ki zauna Waheedah.." "Tam..." Tabi bayanta . Jikinta a darare. Gidan ya sha kayan alatu. Ya gaji da haduwa. Kayan gidan baki daya sun tsaru. Na gwanantawa da bajinta. Dangin masu kudi da farcinan susa... Zayn ya zauna akan kujera. Hadi da janyo remote ya shiga chanza channel . From Telemundo to Alzajeera news. Ya kwantar da kansa saboda sarawar da yaji yana yi m sa lokaci daya. "Sis akwai abunda zaa tayaki?" Waheedah ta fada cike da biyayya. "Ah ,.... Ya Zayn. Waheedah ce wadda zatayi girkin?" Ahlam ta tambaya. Hannunta daya akan wayarta "Uhmmm" ya amsata da haka kawai. "Kin iya girkuna ne?" Ta tanbayi Waheedah. Fuskarta kumshe da mamaki . "Eh sis..." "Okay.... To shinkafa zaki dafa da miya. Sai gashin kaza. Akwai kuma frozen snacks a freezer sai ki soya.... Da sponge cake ma sai ki yayyan ka.." "Tam... " Waheedah ta amsa. Kafin ta sake cewa, "Akwai zani da zan daura?" "Ina zuwa.." Sama ta haye bada jimawa ba ta dakko wata doguwar riga baka da dankwalinta. "Gashi ... Ga daki can sai ki canza ko?" "Tohm .." Dakin ta shiga. Tana ta binsa da kallo. Komai na dakin Turkish royals ne. Ta cire kayan makarantar ta zura rigar. Tamkar dama tata ce. Waheedah ta tsaya tana kallon kanta a mudubi. Can ta yane kanta da mayafin abayar ta fita parlorn. Zayn na zaune a kujera daban. Hakama Ahlam tana gefe tana danna waya sai murmushi take. "Sis .... Na gama." Ahlam bata daga ta dubeta ba. Saboda tsananin yadda chatting din da take baki daya ya dauke mata hankali. Ahankali Zayn ya daga wutsiyar idanun sa ya kalleta. Da sauri ya janye kallon sa. Saboda yarda zuciyar sa ke faman zillo. Daya kasa gane manufar hakan. "Sis...." "Na... Naam." "Na gama...." "Okay muje na nuna miki komai..."
Chapter 41 · 0% Book details