Sashe 19
Farhatul Qalbi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ka rakani mu kira Nase me kyamis." Cewar Kamal. Ya fice dan tsabar kidimewa jikin sa ko riga babu sai dogon wando. Yayinda Najib ke binsa a baya yanata sauri shima. Jikin su baki daya yayi laasar ganin yadda mahaifiyar tasu ke tsiyaya amai. Marka ta ja kwafa tana girgiza kafafu. "Wannan amai dai a bincike sa , Ahto " Malam Nalado yayi mata alamar da tayi shiru. Fuskar sa da alamun rashin jin dadin kalaman mahaifiyar tasa. Umma hadiza na jin su. Ta kasa cewa komai. Baki daya amai ne ke kwarara tamkar zata amayar da kayan cikinta saboda azaba harda kakkari. "Sannu Umma..." Kada kai kawai take. Ta kasaa amsa waheedan Cikin haka sai ga Najan Isubu ta zo ta da sauri. Mayafinta ko gama yafuwa baiyi ba. Ta shiga gidan cikin kidimewa . Da sauri tayo kan Hadizan tana sallallami "Sannu Hadiza. Yanzu su Kamal ke gayamun ...." "Gayyar Munafukai... " cewar Marka. "Debo kasa a waje Waheedah ki sauri " Nan da nan Waheedah ta fita ta ebo kasar ta kawo. Najan ta zuba awajen da Hadiza ke aman. Tanata doka mata sannu. "Ni fa nagaji da nuniyar isar da ake a gidan nan mai sunan Malam." "Marka kiyi hakuri." "Sai yaushe ne Hadiza zata bar gidan nan?" Da sauri Najan ta juya tana kallon Marka. Hakama Umma Hadiza da Malam Na lado. Waheedah baki daya sai kanta ya kulle sahoda meyasa Umman su zata bar gidan akan me? Bayan ga Inna Sa'adatu nan da yaranta "Shekara nawa kenan kuna rokana da rufa rufar zancen nan? Nagaji. Nace nagaji. An kai ni makura. Ai yaranta sun girma ba jinjiraye bane. Ko yanzu aka aurar da Wahidin zata haihu. Don haka maganar a boye zance haka nan ya isa." "Marka d..." "Ya isheki Naja" "Shekara nawa Hadiza zata dauka tana zaman yaranta... Bayan tun tuni auren su da mai sunan Malam ya kare? Iyye? Nace sai yaushe zata tashi ta bar mana gidah?........ *_ZAFAFA BIYAR din samari ne a rayuwar INAYAH,kowanne a cikinsu akwai wani murdadden Al'amari da ya shata layi tsakaninsa da ita,wawakeken sirri wanda a koda yaushe take kiransa da SANADIN LABARINA_* *_Amma babban abun mamakin a koda yaushe shine,ita dai tasan cewa BABU SO tsakaninsu MEYA KAWO SHI?_* *_Duk da haka tana tunanin yun qundun bala ta fitar da FARHATUL K'ALB a cikin ZAFAFA BIYAR din samarinta,duk da batason su zame mata GURBIN IDO wanda har kullum ba ido bane_* *YA KUKAJI SALON MASU KARATU?* *YADDA SALON YA BAMBANTA DAKO YAUSHE HAKA LABARAN SUKA BAMBANTA DA DUKKA LABARANMU NA BAYA* INAYA(riba biyu)___mamughee SANADIN LABARINA___Rano BABU SO___Billynabdul FARHATUL K'ALB___Miss xoxo GURBIN IDO____Huguma *ZAKI YARDA AYI TAFIYAR NAN BABU KE MADAM?* *_GARZAYA KI BIYA NAKI KUDIN KAN FARASHI KAMAR HAKA_* Biyar:::1k Hudu:::700 Uku::::500 Biyu::::400 Daya:::300 *_zaki saka kudin ta wannan account number din_* HAFSAT UMAR KABIR 2270637070 Zenith bank *Saiku tura shaidar biya zuwa ga* 07040727902 *IDAN KUMA KATIN WAYA NE ZAKU TURA TA NAN TARE DA SHAIDAR BIYAR* 09134848107 *_THANKS FOR THE CONTINUED PATRONAGE_* [11/23, 9:01 PM] Mummyn Yara: _*FARHATAL-QALB*_ _(FARIN CIKIN ZUCIYAH)_ _NA_ _NANA HAFSATU_ _(MX)_ _AREWABOOKS:MISSXOXO_ _WATTPAD: MISSXOXO00_ _ZAFAFA BIYAR PAID NOVELS_ _PG:20_ ====== "Haba Marka.... Menene haka fisabilillahi?"Najan Isubu ta fada cikin tsantsar takaicin Markan. "Yo ai gaskia ne. Hakurina ya kare . Sai yaushe ne Hadiza zata bar gidan nan.?" "Marka wai meyasa kike mantawa da igiyar aure baa hannun ki take ba? Menene riba shiga tsakanin su da kike yi? Idan ya shikata na menene tana zaman yayanta za ki takura sai ta tafi?" "Saboda bana raayin zamanta anan din." "To ki rabu da ita mana tunda ba akan ki take ba ." "Kinga Najaatu tun muna sheda juna ki bar shiga hancina ki kudundune. Ina tsoron ranar da zan samu Isubu na sanar masa duk tsegemun da kike yi. ... " "Yo Marka idan kin gaya masa ma ai ba wani muguntar nake ba. Na menene don ina aminta da surukar ki zaki dasamun qusar tsana? ... Me Hadiza ta miki? Tun ranar da aka kawo Hadiza a matsayin matar Malam kika tsaneta. Saboda me? " "Saboda Tsayyabu uban Dan Ali....(mahaifin Najan) idan kin gano su wanene to saboda su na tsaneta. Akeken banza da wofi, Afiruwa. Ke ba tsaran maida magana ta bace. Kinyi kadan " Marka ta karasa fada tana nuni da yatsanta a fuskar Najan Isubu tamkar zata tsone mata idanu. Waheedah ta kasa magana. Ta kasa zama Kuma . Tana tsaye tamkar sanda. Gaba daya duk wata laka ta jikinta ta mutu. Sam ta kasa gane inda maganar su ta dosa . "Umman su da Babansu auren su ya rabu tun shekarun baya? Kai gaskia bata yadda ba. Ta shiga girgiza kai ita daya. Tana yin baya da baya ...saura kadan ta doka kanta a bango Najan Isubu ta riqota da sauri "Menene haka Waheedah.?" "Dan Allah dagaske ne? Dagaske ne auren Umma ya rabu? Dagaske ba aure?" Ta shiga tambayar Najan Isubu. Muryar ta cikin kidima da tsantsar tashin hankali. "Kinyi wanka kinci abinci?" Tambayar da Najan ta mata kenan. "Eh." "Toh zura hijabin ki. Kije gidan aikin mahaifiyar ku. Ki sanar musu batada lapia ne. Duk aikin da takeyi su gaya miki kiyi. Kafin Allah ya tashi kafadunta kinji ko?" "Ai t...." "Bar musu Waheedah. Jeki kawai " "Bansan inane bangaren ba Aunty " "Inde kin shiga gidan ki tanbayi sashen da Umman ke aiki. Kingane? Shine na fari kafin dayan sashen." "Tohm " Bata sake cewa komai ba. Ta shiga dakin ta dakko hijabinta. Dan turaren ruwanta da Yayan su ya bata ta dakko ta dan diga a tafun hannunta ta shafe jikinta da shi. Ta zura hijabin gabanta na tsananta bugawa Sai waiwayon Umman su dake durkushe tana numfarfashi take. Najan Isubu ta daga mata hannu ta nai mata alamar da ta tafi kawai. Waheedah ta fice daga gidan . A kwanar layin gidan ta ci karo da su Kamal . Suna ganinta dukkan su su biyun suka shiga tambayar abun da ke damunta ? Ganin yadda hawaye daya na bin daya ke kwarara a idanunta. Musanman da suka bar mahaifiyar tasu a gidah cikin matsanancin hali na rashin lapia. "Menene wai Waheedah .. Umma ce? Wani abun ya sake faruwa da ita?" Cikin sake fashewa da wani sabon kukan. Hadi da kifa kanta a jikin bango tace, "Marka tace lalle Umma tabar gida." "What nonsense....!!! Akan wane dalili?" Kamal ya tambaya cikin zafin rai. "Wai ba aure a tsakanin su da ...." "Bangane ba aure ba. Wannan wane irin rayuwa ce?. A yanzu ta sa ya saki Umman kenan? Kuma dan tsabar renin hankali a ...." "Wai yaya sun dade da rabuwa ..." "Innalillahi wa inna ilaihi rajiun!!! " Kamal ya shiga maimaitawa. "Yaya kai ma baka sani ba da ma?" "Bansan komai akai ba Waheedah... Yanzu ina Umman?" "Tana can tana amai... Aunty Naja na temaka mata." "Yanzu me kyamis din zai karaso .. Ina zaki?" "Gidan aikin Umma ..." "Yauwa gwara kije kar su jita shiru. Ki kuma share kukan nan haka. Nasan koma menene sharri ne na tuggun Marka. Duk ma menene itace kan gaba akan ganin ya wakana. Amman ba komai, Ai Allah ba azzalumin sarki bane. Zai ma Umma sakayya nan kusa da yardar Allah " "Insha Allah.... Je ki " Tafiya tayi tana waiwayon su. Kamal ya samu gefe ya tsugunna. Yayinda Najib ke a tsaye ya tokare bayansa da kafar sa daya. Kansa a sama yana tunani. Daman tun sanda Yayyun nasa suka fara magana. Zuciyar sa ke kai kawo akan zancen. Cikin haka mai kyamis din ya zo ya same su. Daman ca yayi suyi gaba kafin ya tattara komai ya cinmasu Najib ya yi masa iso cikin gidah. Dakyar Marka tayi shiru tana yada zance. Har mai kyamis din ya shiga yana yan gwaje gwajen sa da tanbayoyin sa akan Umma Hadiza da saboda aman data jera lokaci tanayi baki daya ta rame. Manyan idanunta sun kara firfitowa waje tubarkAllah. NEW GRA SHURAH Waheedah na tafe iska mai sanyayawa na kadata. Sanye take cikin doguwar riga ta atamfa baka mai zanen kujera ja Sai hijabin dake jikinta shi ma ja ne daya amshi kwalliyar jikin atamfar ja Kai dakaga yanayin yadda kayan suka zauna a jikinta zaka rantse gugar iron ce. Nan kuwa kayan ma ninkin guga ta musu. Ko'ina na jikinta tsaf tsaf hatta takalmin da ke dogayen sahunta na samfarin dan madina. Sanyayyen turaren jikinta mai dadi bame hawa kai ba nata gauraye ilahirin jikin ta. Gabanta na tsananta bugawa. Haka ta shiga tafiya a unguwar da Umman tasu ke aiki. Karar karnuka da tsuntsaye sai tashi suke. Haka dai Waheedah ta daure ta karasa har ya zuwa kofar gidan na The Adams family!! Daya daga cikin masu gadin yana ganinta ya tashi yana nufar inda take "Ina kwana?" Ta gayshe shi kanta a k "Lapia lau...wajen wa kika zo? Ko masu kawo goron nanne na sayarwa? Na shekaran jia ko?" "A'ah bani ba ce ..." Ta amsa shi cikin sanyayyar muryar ta Dai dai lokacin da wasu manyan motoci masu nishi da kyawu suka danno kansu zuwa gingimemen gidan na the Adams family. Nan da nan masu gadin suka bude musu gate. Jufa jufan su 3 suka kutsa kai cikin gidan. Waheedah ta zubawa sarautar Allah idanu tana bin yadda motocin suka tulesu da kura da kallo. "Yauwa ke menene ne? Sauri muke munada baki?" Mai gadin dazu da suka rufe gate ya cigaba da tanbayarta. Don tambayar farko daya mata bata kaiga sake bashi amsa ba baqin suka zo. Yabar inda take zuwa wajen baqin "Sunana Waheedah. Nazo nan gidan ne taya su aiki." "Akan me zaki tayasu aiki. Ko irin masu barar nan ce ke! ? Malama yi gaba. Ga ki komi fes fes kankanuwar yarinyar ki da ke saboda mutuwar zuciya shine kikazo nan din maula ko? Zaki matsa ko sai na mauje keyar ki?" Waheedah ta girgiza kai kawai "Mahaifiyata ce ke aiki anan gidan. To yau bata d...." "Kyaleta Labaran..Ke yar Umma Hadiza ce?" "Eh .." waheedan ta amsawa wata kyakkyawar budurwa data fito waje. "Okay shigo ciki. ...." Nadra na gama fada ta karasa shiga ciki. Daman mahaifiyar ta Dr. Hameedah ce tace tazo ta ko Hadiza tazo masu gadi sun hana