← Book details Farhatul Qalbi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 82

Sashe 18

Farhatul Qalbi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

na kwanta." "Ko dan gaba ki dena kina cin abinci ki kwanta. Ki dinga bari se abincin yayi digesting first. " "Dajastan.?" "Afuwan. Ina son nace ki bari abincin ya ., Wannan . Sorry. ..Ah" "Tanason tace ki dinga bari abincin da kikaci ya tsurga. Kafin ki kwanta " cewar Nassem daya shiga alokacin. "Oh yes. Tsurga." Umma Hadiza tayi murmushi "Kingane ko Hadiza? " "Nagane Hajia. Allah ya saka da alkhairi." "Aamin ya rabbi " "Da akwai abunda zan kama kafin na tafi?" "A'a babu. Ki tsaya kici abincin rana ko zaki tafi da shi kici a gidah ?" "To Hajiya." "Okay great. " Dr. Hameedah da kanta ta nufi kitchen din. Masu dafa abincin gidan har sun dafa sun kawo. Wata food flask ta dakko me girma ta zuba mata abincin aciki . "Daga yau ga food flask din abincin ki Hadiza. " "Hajia du wannan?" "Eh..." "Nagode. Allah ya saka da alkhairi. Abincin yayi yawa Hajia. Kinga na dazu ma na rage zan tafi dashi. Da kin rage." "Ki dena cewa haka Hadiza. Naga yaran naki ba maza bane. Sai mace daya dake zuwa makaranta ? Ko ta iya girki?" "Eh su uku ne Hajia. Eh ta iya babu lefi." "To banason musu Hadiza. Kije kuci da yaran dan Allah kinji?" "Toh Hajia. Allah ya saka muku da alkhairi. Yasa a mizani" "Amin Hadiza " Dr. Hameedah ta fice daga kitchen din. Yayinda Umma Hadiza ta sharce hawayen farin ciki. Ta zura hijabinta. Hadi da harhada komai ta zura a hijabi. "To Hajia zan tafi. Sai zuwa da safen ko?" "Allah ya kai mu Hadiza. Ki gayda yaran." "Zasuji insha Allah. " Ta fuce daga cikin gidan tana mai kambama dattako irin na uwar dakin nata Haj Hameedah. Har ta karasa gidah. Zuciyar ta bata dena yaba kyawawan halaye na Hajia hameedah ba. Tabbas an nuna mata karamci da tsantsar mutunci . Ta shige gidan bakinta dauke da sallama. Zainab ta amsa tana kan kujera turmi agabanta tana dakan kuli. "Umma sannu da zuwa " cewar Waheedah data fito daga cikin daki "Yauwa Waheedah. " "Waye ne ... Iyye?" Kande ta shiga kwarara murya fitowarta kenan daga bandaki. Zanin ya dage ana hango jemammun duwaiwukanta a waje. Bayan sarai tasan ummah Hadiza ce. "Ni ce Marka." "Ah ni fa in ce naga anyi wuff an shige. Ashe sarki da nadi ce. An dandalo arziki an boye a kurya." "Kayya Marka kiyi hakuri. Ba haka bane." Ta yamitsa fuska bayan ta daga hannu ta nana shi a shamilallun cinyoyinta da ba tsoka sai kashi "Kaji tsoron mutum. Wato Hadiza tunda aka samo miki aikatannan kike wani daga kai kina hura hanci. To bari kiji hurerar bappajo (mahaifiyar Umma Hadiza ) itace tsarar cacar baki na ba ke ba. Dande ta mutu ne da girman Allah da yau har gidan bappajon senaje mun kwashi yan kallo da ita. Mtssss! Aikin kawai." Ta karasa fada hade da kwafa ta koma cikin bandakin Jikin ummah Hadiza a sanyaye ta shige cikin dakin su. Waheedah nata rarrashinta. Duk yadda taso ta cije sai data kasa. Wasu zafafan hawaye suka shiga reto a fuskar ta. Domin dan aikin nan data samu ya tsolewa Marka idanu har bata iya boye hassadarta . Dakyar da temakon Waheedah Umma Hadiza ta dena kukan . Ta kasafta abincin. Kuskus ne da jar miya dataji kaji da daffaffen kwai guda 3 . Ta ware musu nasu. Sannan ta dibawa Marka da na MalamNalado da na Inna Sa'adatu. Ko da aka kaiwa Marka sam tace ba zata karba ba sai an canza mata da kashin hakarkari an saka mata cinya mai tsoka. A Kuma kara mata miyar. Babu ma. Sai takan abicinta Umma Hadiza ta kalato ta karawa Markan Waheedah ta mayar mata ta karba. Tana danna loma tana aibata su Inna Sa'adatu ma da Waheedah ta kai catai ba zata karba ba. Karamun dan tah hamisu yasa kukan seyaci. Sai data talle masa keya sau 3. Da karin rankwashi biyu a tsakar kansa. Sannan ta dungurar masa abincin a gaban sa hade da doriyar lailayo ashar ta dura masa Su kuwa su Waheedah sunaci kunnuwan su na motsawa. Ga karin na safe na Zayn da aka barwa Umman na su dana kitchen da akace ta hade. Su Najib sai yagar nama suke suna hadawa da abincin. Farin ciki marar misaltuwa ya bayyana a fuskokin su. Ciki harda Kamal da ke kwance a gefe shima yaci ba laifi. Umma Hadizan nata basu labarin yadda ake mutinta ta agidan na THE ADAMS FAMILY!!! *_ZAFAFA BIYAR din samari ne a rayuwar INAYAH,kowanne a cikinsu akwai wani murdadden Al'amari da ya shata layi tsakaninsa da ita,wawakeken sirri wanda a koda yaushe take kiransa da SANADIN LABARINA_* *_Amma babban abun mamakin a koda yaushe shine,ita dai tasan cewa BABU SO tsakaninsu MEYA KAWO SHI?_* *_Duk da haka tana tunanin yun qundun bala ta fitar da FARHATUL K'ALB a cikin ZAFAFA BIYAR din samarinta,duk da batason su zame mata GURBIN IDO wanda har kullum ba ido bane_* *YA KUKAJI SALON MASU KARATU?* *YADDA SALON YA BAMBANTA DAKO YAUSHE HAKA LABARAN SUKA BAMBANTA DA DUKKA LABARANMU NA BAYA* INAYA(riba biyu)___mamughee SANADIN LABARINA___Rano BABU SO___Billynabdul FARHATUL K'ALB___Miss xoxo GURBIN IDO____Huguma *ZAKI YARDA AYI TAFIYAR NAN BABU KE MADAM?* *_GARZAYA KI BIYA NAKI KUDIN KAN FARASHI KAMAR HAKA_* Biyar:::1k Hudu:::700 Uku::::500 Biyu::::400 Daya:::300 *_zaki saka kudin ta wannan account number din_* HAFSAT UMAR KABIR 2270637070 Zenith bank *Saiku tura shaidar biya zuwa ga* 07040727902 *IDAN KUMA KATIN WAYA NE ZAKU TURA TA NAN TARE DA SHAIDAR BIYAR* 09134848107 *_THANKS FOR THE CONTINUED PATRONAGE_* [11/23, 9:01 PM] Mummyn Yara: _*FARHATAL-QALB*_ _(FARIN CIKIN ZUCIYAH)_ _NA_ _NANA HAFSATU_ _(MX)_ _AREWABOOKS:MISSXOXO_ _WATTPAD: MISSXOXO00_ _ZAFAFA BIYAR PAID NOVELS_ _PG:19_ Sannu ahankali, Kwanakin mu nata ja, Ya yinda awanni da mintuna suke shudewa. Kwanakin Umma Hadiza da fara aiki bakwai cif. Sati daya kenan Hakan kuma yayi dai dai da kammalawar karashen aji na daya na babban sakandiren su Waheedah. Lamarin sai godiyar ubangiji. Don zance na gaskiya Allah ya kara saukakawa Umma Hadiza da ahalinta. Ci da shan su acan acan. Don na safe kawai suke saya su ci. Na rana da wanda zasu ci da daddare Umma Hadizan na tahowa dashi daga gidan aikin na ta. =========. ===========. Tunda ta tashi da safe bayan ta gama zuba ruwan, Dauraye kwanuka tayi ta kife hade da kunna turaren wuta na tsinke. Daki ta koma. Umman su na kwance . Idanunta sun kada sunyi jazir. Ya yinda jikinta ya dau zafi sosai. Waheedan ta taba jikinta tana rausayar da kai. Cikin rawar murya tace, "Umma .. Jikin ki zafi." "Waheedah ya akai?. Bari na tashi ." "Umma baki da lapia. Muje kyamis" "Lapia ta lau Waheedah." Ta fada cikin dauriya. Nan da nan hawaye suka shiga reto a kyakkyawar fuskar waheedan. "Umma Allah ya baki lapia. Wayyo Allah na Umma." Umma Hadiza taja siririn tsaki. Cikin kufulewa ta dubi Waheedah "Allah zan make ki idan kika sake mun kuka. Shikenan ni ba dan adam bace kamar kowa da ba zanyi rashin lapia ba? Haba Waheedah." "Ummah kiyi hakuri " "Yauwa, Kin leqa dakin su Yayan na ku?" "Eh ya koma bacci shi " "Toh. Ki duba kasan samirar can akwai dari biyu ki sayo kosai ga ragowar biredin jiya nan sai ku hada ku ci. " "Umma ke fa?" "Je ki ki sayo ke dai" "Tah " Bata sake cewa komai ba, Ta miqe ta dauki kudin bayan ta zura hijabin ta. Tana tafe tana tunanin halin da ta baro mahaifiyar tasu aciki. Ta sayo kosan ta dawo gidah. "Umma gashi " "Toh. Dibi naki ki kai musu" "Umma ke fa?" "Wai Waheedah menene haka iyye? Ina magana kina yi. Zaki tashi ko sai na bar miki wajen?" "Kiyi hakuri Umma." Da sauri ta dibi nata jikinta na bari. Ta gutsiri biredin ta mayar musu nasu Ta tashi ta kai dakin su Najib. Bayan ta kwankwasa yar kofar kafin ta shiga. "Umma na kai musu " "Madalla " cewar Umma Hadiza. Ta miqe dakyar tana gyara zaman hijabin jikinta. Tun dazu take son tatafi gidan aikinta . Amman data yunkura zata tashi sai jiri ya debeta. Tanata daurewa dai. Har ta tsaya a tsaye. Waheedan nata kallonta cike da tausayawa. Har ta kai kofa jikake luuuuuu! Wani jirin ya sake dibanta. Sai dabas tayi zaman dabaro a kofar dakin. Ya yinda kanta ya bugu da kofar dakin. "Wayyo sannu Umma." Waheedah tayi kanta da sauri cike da tausayawa "Umma sannu " "Uhum." "Ina ne yake maki ciwo Umma?" "Ba ko'ina Waheedah." "Umma gashi kin fadi " Umma Hadiza bata sake ce mata komai ba. Ta miqe zata tashi nanma ta sake zubewa a k Da sauri waheedan ta nufi wajen Yayan su Kamal. "Yaya" tace da shi Ya tsaya yana sauraron me zata ce? Hannun sa dauke da biredi da kosai yana ci , "Umma ce Yaya." "Meya faru da ita?" "Batada lapia. Tanata faduwa da ta miqe " Bai sake cewa komai ba. Bai kuma tsaya ta karasa fada ba. Ya miqe dukkuwa da shi dinma jikin sa babu kwari. A bakin kofar dakin ya hangi Umman tasu tanata kokarin tashi. Har tayi amai awajen dan kadan sai nishi take "Ummah.. SubhanAllah! Ashe baki da lapia?" Ta dan juyar da kanta gefe kawai. So take ta miqe ta kasa "Waheedah gyara wajen bara na sako riga mu tafi asibiti " "Babu inda zanje Yayan su. Lapia ta lau " "Ummah bakida lapia. Maybe zazzabin malaria dinnan ne da aketa yi wallahi. Kiyi hakuri " Umma Hadiza ta sake miqewa cikin dauriya wai ita gidan aikinta zata je. Tana tafiya tana kama bango. Marka dake kofar dakinta tana kallon su ta tabe baki kawai. Cikin haka sai ga malam Nalado ya shiga gidan yana wakar garaya. Yaja yai turus ganin su baki daya a tsakar gidan "Menene haka. ? " "Umma ce batada lapia Baba." "Zo nan mai sunan malam. Ni na aika na iro ya kira mun kai." Cewar Marka cikin muryar isa da gadara. "Umma batada lapia Baba." "Meye garungamun sa da ita? Iyye? Ni fa Malam nagaji da saye sayen da kukeyi." Cewar Inna Sa'adatu data fito daga cikin dakinta. Daman tun dazun tana leken su ta wundo. "Najib zo
Chapter 18 · 0% Book details