← Book details Farhatul Qalbi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 57 OF 82

Sashe 57

Farhatul Qalbi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

TURARUKAN WUTA NA *GIDAH, NA KAYA, NA TSUGUNNO* BA A NAN KADAI SUKA TSAYA BA. AKWAI *KHUMRAHS* MASU KAMSHIN LARABAWA DANA FRUITS KAI DAMA KAMSHIN TURAWA. AKWAI KHUMRAHS TA MATAN AURE DA TA YAMMATA_ _SANNAN SU NA DA *TURAREN WANKA DANA SHAFAWA BAYAN AN KAMMALA WANKA.* BA ANAN TURARUKAN NA SU SUKA TSAYA BA. AKWAI *KULACCAM* MAI MATUKAR KAMSHI DA SANYAYA ZUCIYA, SANNAN SU NA DA *MADARORIN TURARUKA NA JIKI DA NA KAYA*_ _AKWAI TURAREN *AL'AJABU NA TSUGUNNO DA KHUMRAH* DIN SA_ _SANNAN SU NA DA *TURAREN GASHI NA CREAM DA KUMA SPRAY DIN SA NA FESAWA*_ _BA ANAN SUKA TSAYA BA. SU NA DA *TURAREN MOPPING, DA NA BANDAKI AKWAI NA RUWAN WANKI DA NA FESAWA A DRAWER KO AKWATI*_ _AKWAI KAYAN GYARARRAKI NA FATA. KUJERAR TSUGUNNO, KASAKE NA WUTA, COAL IGNITER TA KUNNA GARWASHI, ELECTRIC BURNERS DA ENGLISH COAL_ _AKWAI LAFFAYAS DA SAURAN TURARUKA NA KAMSHI KALA KALA_ _SU NA BADA KAYAYYAKIN SU AKAN FARASHIN SARI KO SAYA AKAN DAYA DAYA. SANNAN SUNA TURA KAYAYYAKIN SU KO'INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE. KAYAN SU YAN CHADI NE DA SUDAN DA KUMA YERWA WATO MAIDUGURI._ _KYAU, INGANCI DA RAHUSA SAI KAYAYYAKIN KAMFAMIN YERWA INCENSE AND MORE. SAI KUN GWADA ZAKU BAMU LABARI_ _NAMBAR TARHON SU DA ZAA KIRA KO MUSU MAGANA TA WHATSAPP ITACE: 08095215215_ _INSTAGRAM HANDLE DIN SU: @yerwaincense_and_more_ _YERWA INCENSE AND MORE: A NUMBER ONE STOP SHOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS AND MORE_ *_ZAFAFA BIYAR din samari ne a rayuwar INAYAH,kowanne a cikinsu akwai wani murdadden Al'amari da ya shata layi tsakaninsa da ita,wawakeken sirri wanda a koda yaushe take kiransa da SANADIN LABARINA_* *_Amma babban abun mamakin a koda yaushe shine,ita dai tasan cewa BABU SO tsakaninsu MEYA KAWO SHI?_* *_Duk da haka tana tunanin yun qundun bala ta fitar da FARHATUL K'ALB a cikin ZAFAFA BIYAR din samarinta,duk da batason su zame mata GURBIN IDO wanda har kullum ba ido bane_* *YA KUKAJI SALON MASU KARATU?* *YADDA SALON YA BAMBANTA DAKO YAUSHE HAKA LABARAN SUKA BAMBANTA DA DUKKA LABARANMU NA BAYA* INAYA(riba biyu)___mamughee SANADIN LABARINA___Rano BABU SO___Billynabdul FARHATUL K'ALB___Miss xoxo GURBIN IDO____Huguma *ZAKI YARDA AYI TAFIYAR NAN BABU KE MADAM?* *_GARZAYA KI BIYA NAKI KUDIN KAN FARASHI KAMAR HAKA_* Biyar:::1k Hudu:::700 Uku::::500 Biyu::::400 Daya:::300 *_zaki saka kudin ta wannan account number din_* HAFSAT UMAR KABIR 2270637070 Zenith bank *Saiku tura shaidar biya zuwa ga* 07040727902 *IDAN KUMA KATIN WAYA NE ZAKU TURA TA NAN TARE DA SHAIDAR BIYAR* 09134848107 *_THANKS FOR THE CONTINUED PATRONAGE_* [11/23, 9:02 PM] Mummyn Yara: *FARHATAL-QALB*_ _(FARIN CIKIN ZUCIYAH)_ _NA_ _NANA HAFSATU_ _(MX)_ _AREWABOOKS:MISSXOXO_ _WATTPAD: MISSXOXO00_ _ZAFAFA BIYAR PAID NOVELS_ _PG:57_ *GIDAN MALAM NALADO* Zahara'u ce a tsakar gidan su tana wanke kanta da kumfan los. Marka na daga gefe akan yarkacacciyar kujerar ta. Mikewa tayi daga zaunen da take. Ta shiga kai da kawowa tana daga hannuwa sama. Zahara'u ta mike da jikakken diddigaggen gashin kanta. Daya zama kuda kuda duk ya gwaigwaye. Ta ja dankwali ta daure kan nata tana gyara zaman zanin jikin ta. "Ban hamsin Marka. " Marka ta kalleta sama da kasa ta tabe baki. "Ke kuma me zakiyi da hamsin?" "Zuwa zan a kitsen kai na mana. Dan Allah bani kar na tarar da layi." "Ah kiji ki. Ina da kudin ne? Zaki tsaya gansan gansan akai na ki ce na baki hamsin. ?" "Na fa ga kudi a karkashin tabarmar ki." "Wannan yarinya bansan yadda zan da halayen ki ba. Au dan uban ki caje kike mun? Ajiya kika ban?" Zahara'u ta ture baki gaba. Tana yatsina can ta banka kasar tabarmar ta kwashe chanjin ta zura a rigar mama. Marka ta bude baki kafin ta yo kanta tana zuba hannuwa sama. "Bani dan uban ki. Na ki ne? Da zaki saka hannu ki dauke mun? Ajiya kika ban?" Suka shiga kokawa kacar kacar. Zahara'u ta fincike Marka daga jikinta tana sauke numfashi. "Sanda ina gidan Adamushe wata rana ta laraba munzo kikace a sayo miki ruwan leda . Na ciro dari biyu ta kenan na baki da niyyar kiban chanji na. Har muka tafi baki ce mun gashi ba. Alhalin ba baki nayi ba duka. Don haka dole ne na dauki abu na. " Tana karasa fada ta fice waje da sauri. Ya yin da Marka ta shiga tafa hannuwan ta tana salati. Bata rufe baki ba badamasi dan Zahara'u ya bugo yar randar ta ta fashe a k Ya kwasa a guje ta bi bayan sa tana kururuwa "Sai kaci malafar kan uban ka. Dan kwal uba da rafkeken kai. " Tana tsaki tana tattare gutsattsarin fashasshiyar randar. Sai mita take tana zundumawa sunan sa ashariya "Randar nan jaka biyu na saye ta tun duniya na kwance. Amma saboda tsabar kiriniya da rashin ji irin na ka sai da kasa kafa ka shure mun ita.." Ta ja dogon tsaki ta shuri mayafi ta fice waje. Daga can nesa ta hango Deluwa da malam na lado suna tahowa. Ya riko mata wata leda fara ta asibitin malam aminu kano. Turtsetsen cikin ta ya fito tamkar zai yago ya fado. Dakyar take iya tafiya saboda cikin nata yana da girma ta kuma kusa haihuwa. Marka ta kwasa da sauri ta isa gare su tana mai dokawa Deluwa sannu. "Allah dai ya raba ku lapia . Sannu Deluwa." "Amin Marka.. Sannu da kokari . Unguwa zaki je ?" "Barka da rana Marka." "Yauwa mai sunan Malam. Eh Deluwa fitowa nayi ko zan ga zahara'u. Yarinyar nan ta dauka mun kudi ta tafi kitso. Shi ne zanje na rutsa ta " Deluwa tayi murmushi. Ta karbi ledar hannun malam na lado . Markan sai kallon gefen ido take yi wa Deluwa. "Bari na ta fi." Ta fada tana tafiya. "Kai dan Allah Marka ki kyaleta.. Har nawa ne kudin?" "Kai Deluwa. Allah karki biya mata. Rabu da ita. Ni da ita ne." "A'ah dai Marka dan Allah. Kawai dai ca nai ki kyaleta. Ga dan chanjin da yayi ragowa " Ta mikawa Markan nera dari biyar. "Ayi haka? Deluwa." "Dan Allah." Da sauri Marka ta karbi kudin ta soke a kullin zanin ta. Ta sake dashare hakora tana murmushi tamkar zata yage bakin ta. "Ga ruwa can na doran ki. Muje na sauke. Ki samu ki gashe jikin ki . Allah ya sauke ki lapia Deluwa. Ya kawo malam tsalha ko mai sunan Malam lapiya cikin aminci. Dan ni dai ina kan gabana. Na'urar baturen karya. Wagga ciki na ki yan biyu zaki haife. Maza. Ba guda daya ba." Deluwa ta kakaro murmushi kawai. Kafin tace, "Sannu da kokari Marka . Nagode da adduoin ki gare ni." "Ba godia tsakanin mu. Mai sunan Malam yo sauri ku karasa gidah mana." Malam na lado ya riko hannun Deluwa suka dauki hanyar shiga gidah. Ya yin da Marka ta lelleka bata hango zahara'u ba ta koma cikin gidah. A yammacin ranar aka kawo kudi da kayan sa rana ta Zainab 'ya ga malam na lado da Inna Sa'adatu. Bashari magini zata aura . Yan ganin kaya sai zuwa suke suna yaba kaya. Akwatuna 3 da kit. Inna Sa'adatu sai yatsine ta ke tana hura hanci yar ta tayi goshi Haka ma Marka da ke ta sakin guda tana mai kuranta kudin kayan. Kawayen ta tsofi duk sun zo ganin kaya. "Gaskia zainabu tayi goshi. Kaya maya maya gasu nan." Cewar lawuri kawar Marka. "Wallahi ga bashari sharfacece dashi. Du kayan da zai saka sai ya hada da shawul kalar kayan. Zaki ga ya dora a wuyan sa Wannan yarinya zainabu na da kashin arziki. " Indodo ta fada Marka ta mike daga zaunen da ta ke. Ta daga hannu ta saka akan hancin ta. Ta saki katuwar gud'a tana taka rawa . Sai da ta yi mai isar ta tukun sannan ta zauna tana mai rangada wata gudar. "Jika ta kam tayi goshi. Tun zamanin adaman badamasi baa taba kawo kayan aure irin wannan ba na Zainab. Sai ma kunga gidan. Dakuna biyu dandatsa dandatsa ga uwar falo da dakin girki. Bandakin ta fa irin na korawa dinnan ne masan. Kur'an ga rijiya tafkekiya harda murfin ta. Ga ruwan pampo. Ai zainabu ta gama da ce " Inna Sa'adatu da ke gefe aka hura hanci ita ga uwar 'ya. Can wata cikin yan ganin kayan ta ce, "Ina Hadiza ne. Da yarinyar wajen ta?" Marka ta ja tsaki tana yamutsa fuskar ta, "Waya sani ne? Yarinyar dai ta kan zo nan ta kwan. Ta zama yar kwalta. Suna fakewa da boko ta ke. Can ta matse musu." "Na gama ta kara zama sharfaceciya " "Yo a banza ai. Girman shirme ba namijin aure? Gansansan da ita. Sai ma kunga yad da tayi kwailin taci uwar sabada na bilicin." Lawuri ta kece da dariya. Suka hada hannu da Marka. Ji ka ke raf sun tafa. "Bangan su ba." "Kayya rahanatu ni kin ishe ni da maganar gayyar tsiya wallahi. Yo ta yazasu zo? Suna bakin ciki da hassada. Ile kuma wahidin din ta sani. Don an gayan ta sanda tazo nan din kwana ki " Matar ta jinjina kai kafin tace, "To Allah ya kyauta ." "Salama alaikum " Najib yayi sallama ya shigo cikin gidan hannun sa dauke da rake yana sha Matan wajen suka amsa. Ya hanga ya gano Marka. Daman wajen ta aka aiko sa, "Marka " "Ya akai? Ba abinci. Ka shigo kana rurruntuma kai. " Murmushi yayi kawai kafin yace, "Na'Ateeku ne ya ke kiran ki awaje." Mikewa tayi da sauri. Zanin ta saura kadan ya fadi don sauri dakyar ta gyara ta fice wajen tana dashare baki tamkar gonar auduga "Na'Ateeku..." Zubewa yayi a k sa duk kuwa da shekarun sa. "Barka da yammaci Markan mu." "Barkan mu dai Na'Ateeku. Iyalin kalau?" "Alhamdulillah wallahi " ya amsata yana sosa keya. "Masha Allah " "Allah ya sanya alkhairi zainabu na zo miki." "Allah sarki Na'Ateeku. Godia na ke. Allah ya saka da alkhairi." "Amin..." Ya dan sake sosa keyar sa. "Ina sauraron ka Na'Ateeku." "Marka .... Dama nace.... Zan... Zan zo da kai na. Domin zuwa da kai yafu sako. Dan ba na so abun yadauki lokaci ne." Marka ta sake gyara tsayuwar da tayi kafin tace, "Eh .. Ina sauraron ka Na'Ateeku. Allah sa muji alkhairi." "Amin. Alkhairi ne ya kawo ni ....Magana
Chapter 57 · 0% Book details