← Book details Farhatul Qalbi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 82

Sashe 44

Farhatul Qalbi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

munufiki ne." 'haba Sa'adatu. Wanmnan wace itiyar rayuwa ce haka. Zaki wulakanta ni acikin abokai na. Dubi yadda sukayi cirko cirko suna binmu da kallo. Suna kuma sauraron abunda muke fada." "Kunyar duniya kenan ma. Kafin kaje ka hadu data azabar lahira saboda baqin halin ka da muguntarka. " 'cikani wai menene haka wai?" "Allah ya kwashe maka albarka malam." "Sa'adatu wai meye haka eh...?" Ya fada da karfi Abokan sukayi kansu. Ta daga musu hannu tana nuna shi. "Munafiki ne. Annamimi ne, Kuma bakin mugu.." "Assha. Assha. Dan Allah ki dena fadar haka. " Cewar malam Isubu mijin naja. "Idan ba tsabagen tsagwaren rashin mutunci da tsantsar butulci ba. Me na rage shi da zeyi aure? Kuma ze karo din be fadamun ba. Ina cikin bacci ma jiyo hayaniyar yan kawo amaryar.. Wannan ya dace.?" "Kiyi hakuri....." Suka shiga bata baki suna bata hakuri. Tayi kwafa kawai ta juya ta koma gidah. Tana shjga zaure ta hadu da Deluwa. Ta gogeta zata wuce . Deluwar ta hana ta hanyar riko gyalenta. "Cika ni...." "Dan tsaya mana... Yayata." "Algunguma .." "Kash Ina ki tsaya kin ki. Bakyacin ribar zance..... Ina kwanaki da mukayi cacar baki da ke akan butar ki da Marka ta kawo?." "Matsalar ki ce ni sau ni dalla ..." "Ki saurara .. Idan baki mance ba . Kin kirani da shashasha matsoraciya.. Na ce miki ki jira ramuwa ta... Dan ramuwar gayya tafi ta gayya zafi... Wannan itace ramuwar da na ce ki tsumayi zuwan ta . Na aure miki mjii har gidah.. sirikar ki da mijin duk sun juya miki baya.... Gidah yazama namu gaba daya.... Daga haya na haye igiyar auren me gidan.. . Me yafi wannan ramuwar dadi? Uhm.... Yayasko... Yayata mai buta." Inna Sa'adatu maganganun Deluwa sun tsaya mata a rai. Sun taba mata zuciya. Sun raunata damuwarta. Hawaye ya taho ta danne hade da cijewa tace, "Miji ne dai ko? Gaki nan ga shi... " "Miji, uwar miji da gidan baki daya...Ga kuma karin ki amatsayin abokiyar zama na.. Riba uku" Inna Sa'adatu ta tattare ta fisge mayafin ta da Deluwa ta riqe tayi gaba tashige dakinta tanata mita kasan makoshi. Baki daya tun daga ranar ta nemi farin cikin zuciyar ta ta rasa. Zuciyar ta ta rubanya da baqi mai ciwo da tsantsar na dama... To haka rayuwar take.., sai dai fatan Allah ya yayi mana me kyau Amin... *BAYAN SHUDEWAR WASU LOKUTA* *Dare* ya zama safiya. Safiya ta zama rana, Ya yinda rana kan zamo yammaci. Kwanakin mu nata shudewa. Lalle Allah buwayi ne gagara misali. Kuma mai kowa da komai . Cikin ikon sa da qudurar sa hadi da buwayar sa. Waheedah Nalado ta kammala zana jarabawar makarantar kare sakandire. Wato ssce. Wanda ake kira da senior secondary school examinations na waec da neco. Da rarrafe yaro kan girma. To hakan yake a bangaren na waheedah. Ta zama cikakkiyar budurwa mai jini a jika. Kyawunta ya kara yalwatuwa. Hakama cikar gashin kan ta. Hasken fatar ta. Dara daran idanun ta. Dan karamun bakin ta. Bugu da kari ta sake tsawo tubarkaAllah. Duk wanda ya daga kai ya kalli Waheedah a karo na farko. To babu shakka sai ya sake daga idanu ya kara kallon ta a karo na biyu. Sam ba gajiyawa. Tanada shiga rai ga duk wanda ke tare da ita ko ya santa. Mutane na yabawa da dimbin hankalin ta da nutsuwar ta da kaifin girmamawa da tarbiyyar ta. Ga fara'a da ta wuce duk inda mutum kan tsammata. Waheedah na da ilimi na boko dana islama. Domin har sun sauke Qurani a tahfiz din su. Hakama ranar asabar da lahadi tana zuwa wata islamiyyar ta matan aure. Ranar litinin zuwa jumu'ah tana zama da kwana ne awajen gwaggo haule. Yayin da ranakun asabar da lahadi tana kwana ne agidan su na malam na lado.... _INA MASOYA KUMA MA'ABOTA KAMSHI MA SU KAUNAR KAMSASAWA A KODA YAUSHE? DOMIN KAMSHI RAHAMA NE.._ _TO KU MATSO, DOMIN WANNAN KARON MA ZAFAFA BIYAR SUN ZO MU KU DA TALLAN MASARAUTAR KAMSHI NA KAMFANIN TURAREN *YERWA INCENSE AND MORE*_ _A *YERWA INCENSE AND MORE* ZA KU SAMU TURARUKAN WUTA NA *GIDAH, NA KAYA, NA TSUGUNNO* BA A NAN KADAI SUKA TSAYA BA. AKWAI *KHUMRAHS* MASU KAMSHIN LARABAWA DANA FRUITS KAI DAMA KAMSHIN TURAWA. AKWAI KHUMRAHS TA MATAN AURE DA TA YAMMATA_ _SANNAN SU NA DA *TURAREN WANKA DANA SHAFAWA BAYAN AN KAMMALA WANKA.* BA ANAN TURARUKAN NA SU SUKA TSAYA BA. AKWAI *KULACCAM* MAI MATUKAR KAMSHI DA SANYAYA ZUCIYA, SANNAN SU NA DA *MADARORIN TURARUKA NA JIKI DA NA KAYA*_ _AKWAI TURAREN *AL'AJABU NA TSUGUNNO DA KHUMRAH* DIN SA_ _SANNAN SU NA DA *TURAREN GASHI NA CREAM DA KUMA SPRAY DIN SA NA FESAWA*_ _BA ANAN SUKA TSAYA BA. SU NA DA *TURAREN MOPPING, DA NA BANDAKI AKWAI NA RUWAN WANKI DA NA FESAWA A DRAWER KO AKWATI*_ _AKWAI KAYAN GYARARRAKI NA FATA. KUJERAR TSUGUNNO, KASAKE NA WUTA, COAL IGNITER TA KUNNA GARWASHI, ELECTRIC BURNERS DA ENGLISH COAL_ _AKWAI LAFFAYAS DA SAURAN TURARUKA NA KAMSHI KALA KALA_ _SU NA BADA KAYAYYAKIN SU AKAN FARASHIN SARI KO SAYA AKAN DAYA DAYA. SANNAN SUNA TURA KAYAYYAKIN SU KO'INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE. KAYAN SU YAN CHADI NE DA SUDAN DA KUMA YERWA WATO MAIDUGURI._ _KYAU, INGANCI DA RAHUSA SAI KAYAYYAKIN KAMFAMIN YERWA INCENSE AND MORE. SAI KUN GWADA ZAKU BAMU LABARI_ _NAMBAR TARHON SU DA ZAA KIRA KO MUSU MAGANA TA WHATSAPP ITACE: 08095215215_ _INSTAGRAM HANDLE DIN SU: @yerwaincense_and_more_ _YERWA INCENSE AND MORE: A NUMBER ONE STOP SHOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS AND MORE_ *_ZAFAFA BIYAR din samari ne a rayuwar INAYAH,kowanne a cikinsu akwai wani murdadden Al'amari da ya shata layi tsakaninsa da ita,wawakeken sirri wanda a koda yaushe take kiransa da SANADIN LABARINA_* *_Amma babban abun mamakin a koda yaushe shine,ita dai tasan cewa BABU SO tsakaninsu MEYA KAWO SHI?_* *_Duk da haka tana tunanin yun qundun bala ta fitar da FARHATUL K'ALB a cikin ZAFAFA BIYAR din samarinta,duk da batason su zame mata GURBIN IDO wanda har kullum ba ido bane_* *YA KUKAJI SALON MASU KARATU?* *YADDA SALON YA BAMBANTA DAKO YAUSHE HAKA LABARAN SUKA BAMBANTA DA DUKKA LABARANMU NA BAYA* INAYA(riba biyu)___mamughee SANADIN LABARINA___Rano BABU SO___Billynabdul FARHATUL K'ALB___Miss xoxo GURBIN IDO____Huguma *ZAKI YARDA AYI TAFIYAR NAN BABU KE MADAM?* *_GARZAYA KI BIYA NAKI KUDIN KAN FARASHI KAMAR HAKA_* Biyar:::1k Hudu:::700 Uku::::500 Biyu::::400 Daya:::300 *_zaki saka kudin ta wannan account number din_* HAFSAT UMAR KABIR 2270637070 Zenith bank *Saiku tura shaidar biya zuwa ga* 07040727902 *IDAN KUMA KATIN WAYA NE ZAKU TURA TA NAN TARE DA SHAIDAR BIYAR* 09134848107 *_THANKS FOR THE CONTINUED PATRONAGE_* [11/23, 9:02 PM] Mummyn Yara: _*FARHATAL-QALB*_ _(FARIN CIKIN ZUCIYAH)_ _NA_ _NANA HAFSATU_ _(MX)_ _AREWABOOKS:MISSXOXO_ _WATTPAD: MISSXOXO00_ _ZAFAFA BIYAR PAID NOVELS_ _PG:48_ _WANNAN LITTAFI DA MA SAURAN NA *ZAFAFA* NA *KUDI* NE. DAN ALLAH KI/KA BIYA KUDI KI/KA MALLAKI NA KI. DON GUDUN SHIGA HAKKOKIN MASU RUBUTAWAR DA MA WADANDA SUKA CIRE KUDI SUKA SAYA..._ *GIDAN MALAM NALADO* *Waheedah* na tsakar gidan su tanata share share. Kawayen ta suka shigo bakunan su dauke da sallama. Tsantsar farin ciki ya bayyana a fuskokin su. Tana ganin su ta tsaya da sharar. Ya yinda tsintsiyar ke hannun ta na dama. Kallon su take tana son magana ta kasa . Basira da fanna suka sheke da dariya. Cikin tsantsar farin ciki marar misaltuwa suka rungumeta a tare. Ta cillar da tsintsiyar hannunta ta kankame su. Cikin muryar zakuwa ta dube su, "Ya ake ciki...? " "Kin samu admission Waheedah .. kin samu." Fannah ta fada tana mai sake kankame Waheedah cikin farin ciki. "Waheedah sunan ki ya fito.kin tsallake...."Basira ta fada tana dariya itama. Waheedah ta dubi gabas tayi sujjada. Hawaye daya na bin daya na farin ciki "Allah ka karawa annabi daraja, Aamin. Alhamdulillah! Alhamdulillah! Alhamdulillahi da'iman wa Abadan. Allah mungode maka da wannan babbar kyauta.... Ni Waheedah na samu nursing...? Rabbi ka dafa mana ka iya mana..... " "Aamin . Amin" suka hada baki wajen amsa adduoin ta... Inna Sa'adatu dake leken su ta window ta tabe baki ta koma ta kwanta akan katifa tana jera tsaki. Mikewa tayi ta sake rungemu su kafin ta saka kasan rigar ta tana goge hawayen dake zuba. Cikin farin ciki ta sake cewa da su, "Nawa kawai ku ka fada .... Ku fa? Sai kace ni kadai ce ke neman admission din? " Ta jefe su da hararar wasa. Fanna ta tuntsire da dariya sannan tace, "Muma duk mun samu..." Sake rungume juna sukayi sunata murna. Cikin haka Marka da Deluwa suka shigo. "Ife ifen menene haka har waje ana jiyo shewar ku?" "Mun ci jarabawar shiga makarantar school of nursing ..." "Ah masha Allah.... Allah yasa ku fara a saa " Deluwa ta amsa su tanata murmushi. Domin babu lefi suna mutunci da Waheedah. Ita kan tayata aikin komai idan tazo kwana. Da sauran hidindimu da ke deluwan ta samu karuwa juye ne batayi ba. Cikin har ya dan tasa. Kuma kullun tana basu abinci har da Najib. Marka ta ja tsaki tana yamutsa fuska. "Sai kuyi tayi ai... Boko ko jaraba. Bokon ce agaban ku ba aure ba. Gandama- gandama da ku. Meya kwan ku rufawa junan ku asiri ku tsaida mazaje kuyi aure? Kun gwammace ku yita yawo a titi da sunan karatu. Allah shi kyauta." Ta shige cikin dakin ta tanata doka mita. "Aunty akwai abunda zan tayaki da shi ?" Waheedah ta tambayi Deluwa. "A'ah Waheedah... Babu komai" "Tohm.." Daki tayi saurin shigewa. Najib yana kwance akan katifar sa. Ya yin da hannun sa daya ke kan kafarsa yana matsawa. "Sannu Najib..." "Yauwa Yaya.." "Kana sauraron mu ko?....." Ta karasa tanbayar sa tana murmushi.. "Yanzu na tashi ..." "Sannu.... Ya jikin naka?" "Da sauki.." "Allah ya kara sauki . Amin" "Amin..," "Na samu admission fa .." Mikewa yayi daga kwancen da ya ke. Fuskar sa lullube da farin ciki. "Har na hango ki cikin farin uniform dinnan..." "Kai de bari Najib... Alhamdulillah." "Na tayaki murna Yaya... Allah ya cigaba da kara miki nasara. Ya bada sa'ar karatu." "Amin Aamin .." "Umma ta sa ni?" "A'ah yanzu na ke son zuwa na gaya mata... Bansamu naje na dubo ba... Su Basira ne ke sanar mun" "Masha Allah ... Alhamdulillah." Kayan ta ta ciro da ke cikin
Chapter 44 · 0% Book details