Sashe 71
Farhatul Qalbi Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read
takama da kyau, Shiyasa idona baya gajiya da kallonki ayayinda murmushina yake bayyanuwa alokacinda nake kallonki Waheedah... A koda yaushe tun farkon haduwar mu da ke. Kika zama mamallakiyar ZUCIYA ta. Tun ban tabbatar ba Waheedah.. Ko kinsan yawan zuwan da nake sashen nan duk akan ki ne? Wani lokacin zakiga idan kin gayshe ni ina basarwa ko naki amsawa wallahi Waheedah kaunar ki ce ta mun illa acikin zuciyata. Ta mun wani irin kamun da idan banyi tozali da ke ba ranar ZUCIYA tah ba ta samun FARIN CIKI....My permanent relationship status taken forever by the most gorgeous woman in this universe. Love ya soo much wifey.. Waheedah.." "Uhmm" "Wait.. Ni fa nagaji da sauraron uhm da um dinki tun dazu. Ki bude baki ki mun magana. Dan Allah ki dena azabtar da ni da rashin jin muryar ki... Waheedah " "Na'am..." Ta amsa shi a hankali... "Ki ce wa Maa zaki bini mu kuma gidan mu .. Kinji?" Tayi shiru bata amsa shi ba. Don ba zata taba aikata wannan magana ta rashin kunya ba. "Kinji?" Ya sake fada mata yana zagaye labbanta da hannun sa. "I can't... I won't" "Haka kikace?" "Eh..." "Okay fine...." Tayi shiru bata sake cewa komai ba. Ya sake gyara mata kwanciya yana shafa gadon bayan ta . Gaba daya ya hanata komawa bacci. Ta rasa yadda zatayi. "Kinyi shiru ..." "Bacci nake ji dan Allah..." "Ni mamaki kike ban. Har kina iya bacci a gidan sirikan ki. Ga gidan mu can ki zo mu koma kin ki. Itama Maa ta bani matata taki. Gaskia an kusa kai ni karshe. Hakuri na ya kusa karewa. Allah zan zo na sace ki mu gudu. Ba zasu kara ganin ki ba sai kinzo haihuwa gidah . Ko kuma mu zo mu su da jaririn ko jaririyar..." Ita dariya ma zancen na sa yaso bata. Ta dan murmusa kawai. Wannan murmushin da tayi ya sake tabo kaunar ta dake zuciyar Zayn. Hakika Waheedah na da wani murmushi da ke kara mata kyau. Haka kawai idan tayi sai kaji ka samu nutsuwa. Zayn ya samu kansa da dago da habarta. Ya sumbaci saman bakin ta da karan hancin ta. Ita dai ta kulle idanunta gam. Tana kambama kokarin sa da baya gajiyawa da showering dinta da kisses.. "Waheedah... So tamkar hasken rana yake da yake haske fuskar da take d'auke a jikin gangar jiki, ma'abociyar ZUCIYAr da take 'kunshe da so. Kasantuwar so a cikin zuciya kan motsa ruhi ya kuma busar da idanuwa daga barin yin bacci a mafi yawancin dare, So kan samar da wasu rassa a cikin ZUCIYA bayan bayyanar sa, wato bakin-ciki da kuma FARIN CIKI. Zan ci gaba da son ki a cikin kowane irin yanayi. Ina kaunar ki sosai...You fill all the emptiness in my heart. I m so thankful to have you in my life. I love you very much...." Daman bacci ne yake fizgar su duka. Murmushi kawai tayi jin karshen kalaman sa. Ya kundune ta tamkar itace bargon su. Dakyar ya kyaleta taja bargo ta lullaba. Yanata neman maganar sa bata kula shi ba. Saboda baccin da ke cin ta. Nan da nan kuwa ya dauketa ba jimawa kuwa shima baccin ya sace shi. Dukan su numfashin su na fita ahankali. Suna baccin su gwanin ban sha'awa. Zaka rantse irin masoyan nanne da sukai shekaru suna dakon kauna...